Showing 33001 words to 36000 words out of 117953 words
turo baki Tiny tayi ta ce "toh Abbah wacece wannan yarinyar..." ta ƙarasa maganar tana farfara ido, kama kuncinta yayi yana wasa da ita yace "Auntyn ki ce?..."
Ƴar Tiny ƙara turo baki tayi tare da faɗin "cabb ɗin wannan mai dattin ce Aunty na?..."
Hajia Kilishi dasauri ta ɗago domin tabbatar da abinda ƴar Tiny take faɗi, ai kuwa idonta ya sauƙa akan Baiwar ALLAH nan take ta miƙe tsaye tana harararta cike da takaici ta ce "wannan kuma aina ka samota General?..."
ya ɗago yana kallonta yace "Baƙuwa kukayi kuma zata cigaba da zama ne acikin gidan nan...".
A zabure Hajia tace "whattt!!!! Impossible I swear, ko wani jaki da dabba da alade sai a kawo mana gida? TOH yarana ma sun isheni bana buƙatar ko wani ƙazami ...."
cike da takaici General Yake binta da kallo, ya girgiza kai sannan yakai idonsa kan Aunty Yolash wacce ta taso tazo gaban Baiwar ALLAH ta kamo hannunta tana faɗin "your welcome Baƙuwar mu ki shugo kinji koh...."
Fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi, ta zaunar da ita akan kujera, Baiwar ALLAH ganin kallon da Hajia Kilishi ke mata yasa tayi saurin zamewa ƙasin carpet tace "a'a Aunty a ƙasi ma ya isa...."
Minal juyowa tayi tana wurga mata harara lokaci guda taja tsuka ta cigaba da press ɗin wayar hannu ta,
Pinky da Ruky ƙusu ƙusu suke suna magana ciki ciki Pinky tace "zata ci durun uwarta ne tinda ta kawo kanta kurkukun azaba..."
Ruky tace "barta Ni kaɗai ma na isheta saita ƙwammace gwara tayi zaman daji wallahi, ai ina Abbah ba mazaunin ƙasar nan bane to ai tazo da sauƙi...."
haka suketa wannan mita a junansu....
General ne ya kalli Ummy uwar masu gida da murmushi akan fuskarsa domin aduk lokacin da ya kalli Ummy ko yana cikin ƙunci sai yaji sanyi a ransa, yana matuƙar ji da ita sosai ga mai sunan mahaifiyarsa ce Abar ƙaunarsa,
Yace "Uwar masu gida ga Abokiya na kawo miki...."
itama murmushi tayi ta taso daga zaunenda take tare da ajiye littafin Kur'ani tazo yanda Baiwar ALLAH take itama ta zauna a ƙasin carpet ta rungumeta tana faɗin "Abbah ai wannan tafi ƙarfin Abokiya sai dai Aunty...".
ta kalli Baiwar ALLAH tace "Barkan ki Aunty nah...."
Itama Baiwar ALLAH murmushi ta saki tana kallon Ummy ga glass ɗin yayi mata kyau sosai gata fara ce itama tass,
Hajia Kilishi ta dararawa Ummy tsawa tace "taya ta zamo Auntynki dan ubanki munafukar banza...."
tanayi tana kallon General domin in kanaso ka ƙuntata masa TOH ka zagi Ummy, anan zaku samu matsala,
kafin ta ankara ya wurga mata wayar hannunsa zai kai mata mari Aunty Yolash tayi saurin riƙo shi tana faɗin "kayi haƙuri Yaya, ka ƙyaleta abinda take nema kenam, tinda bata kama girmanta ba kai kuma saika nuna mata ka fita sense ko dan saboda yaran gurin nan...."
General yana Huci ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba,
Hajia Kilishi tana hararar Aunty Yolash tace "Ni ce banida hankali Kenam, ki tsaya a iya matsayinki na ƙanwar mijina karki nemi ki shiga mun gonata wallahi...."
Aunty Yolash ta dubeta dakyau sannan tace "daman ke har gona ce dake? Mttssw....."
General cikin ɓacin rai yake kallon Hajia Kilishi yatsarsa akan Baiwar ALLAH yace "akan wannan yarinyar zakiyi sanadiyar rasa igiyar Aurenki wallahi tallahi...."
Dasauri Hajia Kilishi ta juyo tana kallonsa cike da mamaki.
Minal dake kwance Saida ta miƙe zaune tana faɗin "whatttt!...."
Pinky da Ruky kam sake baki sukayi jin abinda Abbansu ya gayawa Ammynsu...
Minal tashi tayi taja dogon tsuka zata haura upstairs yanda ɗakinta yake, Abbah ya darara mata tsawa yana faɗin "your very stupid, Amina are you mad? ina magana shine zaki ja mun tsuka kibar mun gurin? Ko mahaifiyarki gata nan batada wannan ikon da ina cikin mata magana taja tsuka tace zata bar gurin, Amina ki kiyaye Ni i swear to God zan rufeki a gadurun kiyi kwana biyu muga girman kan nakin..."
ya cigaba da cewa "wallahi tallahi duk yarinyar da naji labarin tana musgunawa yarinyar nan saina sa an rufe ta a barrack aita azabtar da ita kunji da rantse koh, ku bar ganin bana zama a Nigeria duk inajin labarin rashin mutuncin da kukeyi, kuna jamun magana a gari a matsayina na General Sojoji amma ƴaƴana babu tarbiyya tirr wallahi...."
Pinky ce ta kalli Ruky a hankali tace "kuttt buro ubaaa akan wannan matsiyaciyar za'a rufe mu a gadurun?...."
Abbah ne ya kalleta yaji duk abinda tace duk da a hankali tayi maganar, cikin ɓacin rai ya ƙira sunan Ƴar Tiny yace "Auta kije gaban Balkisu da Ruƙayyat duk ki mammare su..."
Ai kuwa da gudun gaske ƴar Tiny taje gabansu da ƴar ƙaramar hannunta ta seta fuskar Pinky ta zabga mata mari sannan ta zabgawa Ruky mAh, ta dawo ta zauna tana dariya,..
Pinky da Ruky abun yayi musu ciwo sosai harda hawayensu,
Abbah yace "wannan shi ake ƙirada ramuwar gayya, tsabar raini ina magana kuma kuna yi TOH mu cigaba...."
Minal zama tayi kai a sunkuye sai zubda ƙwallah take a rayuwarta ta tsani ayi mata faɗa hakan yana ƙuntata mata rai sosai...
Aunty Yolash tana rarrashin Abbah tace "kayi haƙuri Yaya, idan ka biyewa yarannan hawan jininka zai iya tashi, nayi waya da twins Razhdeen da Roshan next week suna kan hanya, ka kusan hutawa da hayaniya...."
Hajia Kilishi ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa jin an ambaci sunan Twins zasu dawo, tana matuƙar jin shakkar su da tsoronsu uwa uba Major general Razhdeen wanda suke ƙiransa da sunan Uncle Deen...
Sauran yaran ma sun girgiza sosai dajin dawowarsu
Ko wacce jikinta ne ya soma kakkarwa, especially Minal Babbar cikinsu duk tasha jinin jikinta....
Banda Ummy wacce take farin cikin dawowarsu,
Ƴar Tiny kuka ta soma yi tana faɗin "banaso su dawo, Uncle Deen dukana yake yiiii..."
𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.
𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦♀️🤦♀️
𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢
𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.
𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈
ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..
𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:
1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.
2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.
3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.
4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.
𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 13 to 14
Aunty Yolash gaban General ta tsaya cikin nuna damuwa tace "Yaya idan ba damuwa ka bani yarinyar na tafi da ita mana tinda mutanen gidan ba son zamanta a gidan suke ba, zata sha wahala ne a gurinsu.."
General a fusace yace "dole zata zauna a cikin gidan nan, kuma naga wacce ta isa ta takura mata, gobe da sassafe zan hau jirgi zan tafi Maleshiya akwai meeting ɗin da zamu gudanar acan, zanyi two weeks wata ƙil su Roshan su rigani dawowa..."
Aunty Yolash girgiza kai kawai tayi tare da faɗin "shikenam TOH, daman Nima yanzu nake son komawa Bauchi..."
General yace "ok akwai saƙon da zan tura miki zaki gani kafin ki isa..."
ya kuma cewa "Ita kuma yarinyar nan ku kaita ɗakin da zata zauna...."
ya kalli Ummy yace "uwar masu gida ganan Auntynki nan zan baki kuɗi kuje ɗaya daga cikin security yakai ku super market kiyo mata siyayyan kayayyakin da zatayi amfani dasu..."
Ummy tace "toh Abbah...."
shi kuwa wuce wa yayi ya haura upstairs yanda ɗakin kwanansu yake,
ita kuwa Ummy hannun Baiwar ALLAH ta riƙo suka miƙe tana cemata "tashi na kaiki ɗakinda zaki zauna koh..."
ɗakinda yake ƙasin stairs ta shigar da ita, itama Aunty Yolash bin bayansu tayi, a yayinda Hajia Kilishi take binsu da harara ta kasa cewa ƙala, cikin takaici taja dogon tsuka itama ta haura upstairs can bedroom ɗinta,
Itama Minal jiki a sanyaye ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta wanda yake saman Upstairs,
Kana shigowa cikin babban falon zaka tarar da gidan beni Three part,
ta bangaren dama akwai beni mai hawa uku , kana kai ƙarshe zata tarar da layi gida biyu right and left, idan kabi layin right shine zai kaika har part ɗin Major general Razhdeen, da ɗan rasa kaɗan kafin ka isa part ɗinsa....
Layin left kuma shine zai kai ka har part ɗin Doctor Roshan shima kafin ka isa akwai ɗan tazara...
Idan ka sauƙo falon kuma still akwai gidan beni ta bangaren hagun mai hawa biyu shi kuma, kana kai ƙarshen Benin zaka tarar da ɗakuna guda biyar a jere, ɗakunan ƴan matan gidan Kenam kowa da ɗakinsa, ɗaki na farko shine ɗakin Minal sai na biyu kuma ɗakin twins pinky and Ruky ɗakinsu ɗaya sai ɗakin Ummy ta gefensu sai kuma ɗakin Ƴar Tiny amma a waran mommynta take kwana ita sai ɗayan ɗakin da babu kowa a ciki,
Kowa ɗakinsa da ɗan tazara dana ɗaya,
Kana komowa falon kuma zaka ƙara tarar da gidan Beni ta tsakiyar right and left, nan ma hawan beni uku ne kana hawa zaka tarar da ɗakuna biyu, ɗakin Hajia Kilishi da kuma General,
A ƙasin falon kuma a ƙasin benin su General wani wantamemen dining table ne sai ƙaton kitchen ata gefe guda da kuma store na kayan Abinci,
A ƙasin benin ƴan matan gidan kuma ɗakuna uku ne a jere wato ɗakin baƙi idan sun zo,
A ƙasin benin su Doctor Roshan nan ma ɗakuna uku ne a jere a ɗaya daga cikine aka ajiye Baiwar ALLAH, sai kuma ta kusa da ɗakinta ɗakin Aunty Yolash ce idan tazo hutu,
Baiwar ALLAH tana zaune a bakin gadonta Ummy itama tana zaune ta gefenta tana riƙe da hannunta tace "Please Aunty Meye sunanki?..."
Baiwar ALLAH kallonta tayi tare da sau murmushi tace Baiwar ALLAH...."
Cike da mamaki Ummy take kallonta tace "ikon Allah sunanki kenam? Allah sarki, toh ki kwantar da hankalinki bazaki sha wahala acikin gidan nan ba Insha Allah, kar kiji fargaban Hajiyar mu just saidai tayi barazanar ta....."
Haɗiyar yawu Baiwar ALLAH tayi tare da jinjina kai tana murmushi ba tareda ta ce komai ba,
Aunty Yolash tana tsaye tana jinsu idonta akan Baiwar ALLAH ta ce "duk abinda akayi miki acikin gidan nan na wulaƙanci kiyi gaggawar sanar mun, za'a ɗau hukunci akai..." ta kalli Ummy sannan ta kuma cewa "Uwar masu gida idan kika ga anyiwa baiwar Allah abinda bai dace ba to ki sanar mun, Ni kuwa na sanarwa Abbanku kinji koh?....."
Ummy jinjina kai tayi tare da faɗin "Insha ALLAH Aunty..."
daga nan Aunty Yolash tayi musu sallama tace "Ni zan koma Bauchi saina sake zuwa..."
Ummy tace "TOH Aunty ko nazo na rakaki ne?..."
Aunty Yolash tace tana murmushi ta ce "Ni da zan tafi a motar! ki kwantar da hankalinki ganan amanar Baiwar ALLAH an baki ita ki kula mana da ita, yanzu tashi ki nuna mata gurare acikin ɗakin da toilet kafin ku fita yin siyayyan kayayyaki...."
Ummy tana murmushi itama tace "TOH Aunty..."
daga nan Aunty Yolash ta tafi...
Bayan Ummy ta nunnuna mata gurare har cikin toilet tacewa Baiwar ALLAH "ganan ɗakinki, yanzu dai tinda yamma ta gabato mu bari sai gobe da safe muje super market koh! saboda idan mun fita yanzu dare zai iya mana, kuma inada burin mu zazzagaya har gidan zoo da waran wasanni, mu ɗan je yawon shakatawa, yanzu dai bari naje na dubo miki kayan da zaki chanza acikin kayana sai kiyi wanka kafin na dawo kiji...."