Showing 51001 words to 54000 words out of 117953 words

Chapter 18 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4748

Ummy gyaran murya tayi sannan tace "mommy wata ƙil ke harija ce koh?...."

Hajiya Kilishi tana kuka lokaci guda ta tintsire da dariya tana dukan Ummy a gaba cikin zolaya take faɗin "ke dan ubanki aina kika san akwai Harijai ?..."

Ummy murmushi tayi sannan tace "mommy nifa inada burin zama Doctor kawai dai ƙasar waje ne bazan fita ba, dole Abbah ya rinƙa guduwa kullum baya zama saboda kina shirin ƙarar masa da ruwan jikinsa, mommy inaga Aunty Minal ma ke ta ɗauko domin itama tana cikin wannan halin amma saidai ita bata bin maza, akwai maganinda take sha ta samu sauƙi kafin wani lokaci kuma du, zanje na ɗauko miki kema kina sha zaki samu sauƙin abun sosai...."

Hajiya Kilishi zaro ido tayi cike da mamaki ta ce "Kenam Minal tana fama da irin matsala ta? tabbas tana yawan ciwon ciki amma banyi tunanin akan haka bane, Minal tana buƙatar Aure amma saidai taƙi kawo tsayayye wanda za'a aura mata, ta nace a wancan Christal na ƙasar Australia shi kuma Abbanku bazai taɓa Aura mata shi ba...."

Ummy ta ce "tana masifar son Mohandas ɗan gidan Chief of Defence staff na ƙasar Australia amma sai dai shi ba musulmi bane kuma iyayensa bazasu barshi ya musulunta ba haka itama baza'a barta ta Auri christal ba, but suna son junansu basa son rabuwa....."

Hajiya Kilishi kamar zata ƙara fashewa da kuka jin Minal irin matsalar gare ta tayi matuƙar tausaya mata sosai cikin yanayin damuwa ta ce "TOH tace idan ba Mohandas ba bazata Auri kowa ba TOH ya zamuyi mata?
Kedai Ummy kisan yanda zakiyi ki temaka mun dan ALLAH, bayan isha'i ina jiranki a room ɗina...."

tana ƙarasawa ta miƙe tsaye ita har ta manta da Baiwar ALLAH tana cikin ɗakin sai yanzu tayi ido huɗu da ita, bata ce komai ba tayi ficewarta........



*GA WANNAN KUYI MANAGE ZUWA DARE ZAKU GA ANOTHER PAGE KUYI HAƘURI BANDA CHAJI NE A WAYA SHIYASA.....*


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 23 to 24



꧁꧂


Hajiya Kilishi har ta fita ta ƙara dawowa ta ce "yawwa Ummy kuɗinki dana ɗau zan baki, har ma zan ƙara miki 2millions su zama 5 sai kuje kuyo siyayyar ko? Amma yanzu dare zai yi muku ku bari saida safe idan ta kammala ayyukan gidan...."
ta ƙarasa maganar tana kallon Baiwar ALLAH sannan taja ƙofa ta rufe tayi tafiyarta,

Baiwar ALLAH da sauri ta nufi yanda Ummy take cike da farin ciki tace "gashi na gaya miki komai a hankali ake bin abu, Kinga kuwa kinyi nasara akanta ta sanadiyar fahimtar juna yanzu kuma naga tayi sanyi sosai...."

Ummy ta ce "uhmmm! Sai naga tayi wata guda bata wuce yawonta ba tukun na yadda da nadamar Mommy, a yanzu dai jikinta yayi sanyi akan batun nan amma indai akanki ne mommy bazata ja ki ajiki ba, ai mai hali da wuya ya canza amma ina roƙon ALLAH duk rashin mutuncinda zatayi da wulaƙanci ya tsaya a iya haka banda yawon zina, domin shine babban illar dake damu na a raina, zan temaka mata INSHA ALLAHU....."

Baiwar ALLAH ta ce "Allah sarki!
Allah yasa ta chanza har abada sannan Allah ya kawo mata ɗauki ya bata sauƙi....."
Ummy ce ta amsa mata da Ameen!
A yayinda ƙwayar idon Baiwar ALLAH suka sauƙa akan wani photo dake cikin akwatin Ummy dake buɗe bata zuge ba,
Ummy jin Baiwar ALLAH tayi shuru ne yasa ta waiwayo tana kallonta, itama idonta takai kan photon da take kalla, murmushi Ummy tayi sannan ta kai hannu kan photon ta ɗauka tana kallo,
Idonta akan photon ta ce "wannan shine......"
Bata ƙarasa maganar ba taji Baiwar ALLAH tayi hanzarin cewa "RAZHDEEN...."
ta ƙira sunan a yayin da zuciyarta ke bugun uku² gumi ne yake keto mata a duk ilahirin jikinta, wani irin yawu ta haɗiya still idonta akan photon da Ummy take riƙe da shi,

Murmushi Ummy ta kuma yi sannan ta ce "yanayinsa yayi zubi da sunansa, jarumin maza Kenam kallo ɗaya mace take masa ta razana, daga kallon photonsa gaba ɗaya kin fita hayyacinki shin ina da kin ganshi a zahiri?..."
ta juyo tana kallon Baiwar ALLAH ta kuma cewa "yadai? shin kina jin wani abu akansa?..."

Dasauri Baiwar ALLAH ta girgiza kai tareda faɗin "ko kaɗan wallahi, wannan ba mutum bane, kyansa yayi yawa sannan ga ƙirar jiki kamar basamude sannan ga sumar gashi har gadon baya kamar mace, ina! Ina!! Ina!!! Sam bana yinsa...."

Zaro ido Ummy tayi ta ce "Uncle Deen ne ba mutum baaa?, gashi yana sanye da kayan Sojansa gwanin burgewa....."
ta jinjina kai sannan ta ɗauko wani photo ta ce "wannan pah?...."
sakin fuska Baiwar ALLAH tayi tare da sauƙe nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce "wannan shine Roshan koh?...."

Ummy murmushi tayi tace "zubinsa yayi kama da sunansa Sarkin murmushi kenam...."

Baiwar ALLAH ta ce "yanzu ma gashi da kyakykyawar murmushinsa, dimple a lotse ga farin glass akan darara eyes ɗinsa gwanin burgewa wannan shine jarumi nah....."

Murmushi Ummy ta kuma yi tare da ajiye photunan acikin akwatinta ta ce "saima kin ganshi anan zaki zauce ganin kyakykyawar murmushinsa dake ƙayatar da kyakykyawan fuskarsa....."

BAIWAR ALLAH ta ƙagu da taga wannan kyakykyawan mutumi mai kyakykyawan zuciya wato Roshan,
a hankali ta furta "wow that's awesome, ma sha ALLAH 🥰....."






🇾 🇦 🇷  ➪ 🇦 🇲 🇦 🇳 🇦 

Sai da tayi wata guda a wannan yankin bata motsa ko ina ba, ga jita a waran saidai ta kaɗa jitarta ta kwanta a ƙasin wajen mai laushin gaske har bacci ya ɗauke ta, da zaran ta farka kuma zata tarar da ƙayatattun girke-girke masu ɗaukar ido, kullum da kalar abincin da ake kawo mata ga nama baje-baje haka zata zauna ta take cikinta tam tasha lemuka kala-kala, har zuwa yanzu babu mutum ko ɗaya wanda ta gani, kayan sakawa kuwa sai dai taga an chanza mata kaya Kuma kullum acikin ƙamshi take,
yanzu ma kamar yadda ta saba tana zaune da wata ƙaramar jita a hannunta tanata kaɗawa sauti mai daɗin gaske yana tashi, tana cikin wannan halin taga wani ƙaramin kifi ya fito bakin ruwa ya kasa komawa sai mutsil-mutsil yake, a hankali ta miƙe tsaye tana riƙe da jitarta a hannu ta nufi bakin ruwan wanda tinda aka kawota nan bata taɓa zuwa wajen ruwan ba balle tayi ƙoƙarin shiga sakamakon ganin kalar ruwan mai launin green ne sai ruwan yake bata tsoro,
a wannan lokacin tazo dab da ruwan da niyar temakawa kifi tasa hannu ta ɗauki kifin a hankali ta zura hannunta acikin ruwan ta maida kifin ciki, wanin irin sanyi taji ruwan yayi mai ratsa jiki, jin daɗin ruwan yasa ta zura ƙafafunta ciki ta zauna a bakin ruwan tana murmushi, ta ɗauki jitar ta fara kaɗawa a hankali, gani tayi ƙafafunta sun fara komawa kalar ruwan wato green, yana bin duk ilahirin jikinta nan danan fatar jikinta ya koma launin green har fuskarta,
Daga wannan lokacin bata tsinci kanta ba sai a bakin titin ƙwalta tana kwance ga jitarta a gefe tana riƙe dashi amma saidai ba'a cikin hayyacinta take ba,
Bata tashi farfaɗowa ba sai tsakiyar dare sakamakon ruwan sama da aketa zabgawa domin ruwan ne ya farfaɗo da ita, tashinta ta fara waige-waige ko zataga wani a gefenta amma babu kowa ga yanda ruwan sama yake dukanta, ta koma asalin launin jikinta daman wannan ruwan shine zai kai mutum ainahin yanda yake da zarar ka shiga wannan ruwan, a yanzu dai Ƴar Amana ta tsira daga zaman can ta dawo Nigeria yanda take, yanzu kuma zata fara neman mafita akanta tinda a halin yanzu ba'a hannun kowa take ba, tana free.....



Bayan Watanni Uku

(Three months later)



Wasu Manyan Jirage ne suka sauƙa a airport guda biyu,
Ɗaya jirgin Australia (U.S)
Ɗaya kuma jirgin ƙasar Egypt ne,
Sai jerukan motoci guda ɗari manyan baƙaƙen motoci masu taya ta baya guda hamsin sai motoci masu kakin Soja suma sunada taya ta baya guda hamsin,
Ga manya-manyan security masu manyan bindigu, security masu baƙaƙen kaya sune motocinsu baƙaƙe sai kuma motoci masu kakin Soja su kuma sojoji ne aciki,

Wanda yake jirgin ƙasar Egypt ne ya fara fitowa,
Innalillahi wa inna ilaihi raju'un 😳😳
wani kyakykyawan gabjejen saurayi ne fari tass yana sanye da fararen kaya suit ajikinsa, fuskar nan yana ɗauke da kyakykyawar murmushi, hannunsa ya miƙawa na gefensa wanda yake escort nashi ya miƙa masa wani ɗan siririn farin glass saida yasa farin handkerchief sannan ya goge ya ɗora glass ɗin akan dara-daran idanuwansa farare masu ɗaukar ido, haka yake bin security wajen da kallo da ko ina still da wannan murmushi akan fuskarsa, ga wasu ma'aikanta waɗanda suke jan akwatinansa zuwa motocin da aka tanadar musu,
Wani ne daga cikin security sa masu baƙaƙen kaya yazo gabansa yana faɗin "your welcome Doctor, we should go......"

Hannu ya ɗaga masa ba tare da yace komai ba, idonsa akan jirgin Australia yana jiran fitowar twins ɗinsa,

kafin ya ɗage eyes ɗinsa sai ga wani sangamin mutumi ya sauƙo daga nashi jirgin,
Innahu min Sulaimana wa Innahu Bismillahi Rahmani Rahiim,
Alla ta'àlu alayya wa'àtuni muslimiinn........

RAZHDEEN yanda kasan ba jinsin mutane ba tsabar kyau da ƙirar sura mai kyau ga sumar gashi mai ɗaukar ido sai sheƙi yake tsabar baƙi shi kuwa kamar jini zai fito a jikinsa, Sojan hutu kenam,
Duk farin Roshan da kyansa bai kamo ƙafar Razhdeen ba duk da shima Roshan ɗin Duniya ne,
Fitowar Razhdeen tsayawa yayi yana lumshe Golding eyes ɗinsa, yana sanye da farar t-shirt a jikinsa ga rigar ta kama jikinsa sosai sai ƙirar ƙarfin jikinsa kake gani yana bayyanowa, wandon jikinsa kuma kakin Sojan U.S ne, takalminsa mai sawu ciki ne na sojoji shima mai kakin Soja, sumar gashinsa yasha gyara sosai zuwa sajen fuskarsa ba ƙaramin kyakykyawan mutum bane Razhdeen sai dai fuskar nan ba Annuri ko kaɗan,
A hankali yake taka ƙasi kamar mai tambayar ƙasa nufan gurin Roshan yayi,
Shima Roshan da murmushi a fuskarsa ya nufi yanda Razhdeen yake, suna haɗuwa suka rungumi junansu sosai kowa yana kewan ɗan uwansa, daga bisani suka rabe jikinsu Roshan kamar zai tashi sama tsabar farin cikin ganin ɗan uwansa twins ɗinsa tsawon shekara guda ba'a haɗu da juna ba,
Cikin nuna farin ciki Roshan ya ce
"I missed you my Man...."

Shima Razhdeen duk da ba dariya yake yi ba sannan ba murmushi yake ba amma fuskarsa a sake yake alamun nuna farin ciki shima ya ce
"I missed you too my twins...."

suka sake rungumar juna a karo na biyu daga bisani suka rabe jikinsu suka jeru suna taku cikin ƙasaita da nuna mulki, duk da tsayin Razhdeen amma da kaɗan yafi Roshan tsayi domin shima Roshan gabjejen mutum ne ba laifi amma saidai Razhdeen yafi Roshan faɗin jiki da faɗaɗɗan ƙirji sosai....

Duk wanda ya gansu sun jerun nan suna taku sai ya yabesu domin ba ƙaramin burge mutanen wajen sukayi ba,
Suna isa dab da wata kyakykyawar mota wanda sabo ne yau aka ɓarota saboda twins, a gaggauce Security yayi saurin buɗe musu murfin motar duk suka zauna a back seat iya su biyu sai wanda zai yi driving nasu,
Sauran yawan motocin kuma duk ƴan rakiya ne,
Motarsu ce ta fara yin gaba sai sauran motocin suka biyo bayansu a jere cikin slow ake bin motocin ba hayaniya ko jiniya,
wannan taryar da akayi musu ko president iyakaci, duk yanda suka wuce sai an tsaya ganin motocin da yawansu kuma gasu a jere suke tafiya, sauran motocin kan hanya ne suka fara kakkauce musu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login