Showing 117001 words to 117953 words out of 117953 words
tafi ƙasar Jidder tare amma ka ƙara bijirewa, idan yaji bazaiji daɗi ba, please kayi haƙuri ka tashi ka shirya kabi bayan Roshan, idan har kanason farantawa mahaifinka...."
Marshall ba ƙaramin nasiha da shawarwari ya bawa Uncle Deen ba, jikin Uncle Deen ne yayi sanyi ya tashi sannan ya shige bathroom ya yi wanka, ya fito ya shirya tsab sannan ya fice,
A falo ya wuce Marshall da Minal yayi ficewarsa, yana fita kuwa yasa sojansa akan ya kaishi airport....
ya sanarwa Sojan akan su bi ta layin mabarata domin yana buƙatar sanya Ƴar Amana a idonsa, hakan kuwa akayi cikin sa'a kuwa idonsa ya sauƙa akanta tana zaune a bakin titi kusa da tsohuwa da jitarta a hannu tanata kaɗawa cikin zazzaƙar sauti mai ratsa zuciya.....
Saida motar ta ɗan zarce kafin ta tsaya sannan saiga Uncle Deen ya zaro ƙafarsa waje ya fito cikin ƙasaita ya nufi yanda take,
bata lura da shi ba sai sauƙar mutum ta gani a gabanta, dasauri ta ɗago da kanta sama tana kallonsa,
Shima durƙusawa ya yi idonsa akanta, saida ya gama ƙareta da kallo sannan ya fitar da wasu kuɗaɗe a aljuhunsa ya ɗora Mata akan cinya dai-dai lokacin wata ƴar ƙaramar jakarsa ta faɗo wanda bai lura da ita ba,
tashi ya yi yabar wajen ya nufi motarsa, yana shiga kuwa suka tafi,
cike da mamaki Ƴar Amana take binsa motarsu da kallo ta rasa gane shin waye wannan wanda yake shirin kutsa mata rayuwa,
sai a lokacin ta lura da jakar daya jefar a wajen,
wannan jakar yanada muhimmanci matuƙa domin aciki har da I.D card ɗinsa na soja da national I.D card dana ƙarin matsayinsa na Major General...
A zabure ta ɗauki jakar tare da miƙewa da gudun gaske take bin motar wanda basu gama yin nisa ba,
babu murya balle ta kwalla musu ƙira, bata gajiya ba haka take bin motar da gudu tana ɗaga musu hannu,
Domin in har yaje airport ba tare da ticket ɗinsa ba akwai matsala dole sai sun juyo kuma duk suna cikin jakar,
Motar ba wani gudu yake ba amma har zuwa yanzu basu lura da cewa ana bin bayansu ba,
Ƴar Amana ganin bazasu tsaya ba yasa ta ɗauki wata ƙatuwar dutsi ta ƙarawa gudunta mai har saida ta kusan iddasu tukun ta wurga wannan dutsen cikin sa'a kuwa ta sauƙa akan glass ɗin motar ta baya,
Burki suka danna jin bugun abu ta bayan motarsu, Security wanda yake driving ne ya buɗe ya fice domin ganowa abinda ke faruwa,
ganin Yarinya ce ta kwaɗo musu dutsi yasa shi fusata ya ɗauki hannu zai zabgeta da mari Uncle Deen ya yi saurin riƙo hannunsa, sojan juyawa yayi yana kallon ogan nasan gani yayi Uncle Deen ya girgiza masa kai tare da sauƙar da hannunsa ƙasi,
Idonsa yakai kan Ƴar Amana yaga ta rufe fuskarta da hannayensa biyu tana kaɗa musu hannu alamar suyi haƙuri,
Uncle Deen gani yayi jakarsa a hannunta da sauri yakai hannu yana rarumar aljihunsa yaga jakarsa ce ya jefar,
Karɓar jakar ya yi tare da rungumota jikinsa domin ta temakashi a karo na farko, sai kuma yaji yarinyar ta ƙara shiga ransa,
Ƴar Amana zamewa tayi daga jikinsa ta rufa da gudun gaske ta juya baya,
tsaya kallon bayanta yayi daga bisani shima ya koma cikin motar suka tafi...
suna isa airport jirgin yana shirin tashi, ganin Major yasa akayi saurin dakatar da jirgin kafin ya tashi,
Uncle Deen ne ya nufi yanda jirgin yake bayan ya kammala register yayi komai, yana shiga ya tarar da Roshan seat ɗin da yake zaune shi kaɗai anan ya samo shi suka zauna tare,
Roshan kawar da kai gefe yayi yana sakin murmushi........!!!!
*TOH MASOYA NAH ANAN NA KAWO ƘARSHEN KASHI NA ƊAYA SAI MUN SAKE HAƊUWA A ZANGO NA BIYU.....*
*DAN ALLAH KUYI HAƘURI AKAN JINKIRIN DA NAYI MUKU WALLAHI BANI DA LAFIYA NE KU MUN UZURI....*
*INSHA ALLAHU NAN BADA JUMAWA BA ZAKU SAKE GANIN UPDATE NA STEP TWO,*
*YANZU DAI ALLAH YA BANI IKON KAMMALA STEP ONE....*