Showing 102001 words to 105000 words out of 117953 words

Chapter 35 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4764

kallo,
ta gagara tantancewa shin namiji ne ko mace, amma ta lura da damtsen hannunsa da kuma ƙirar jikinsa haɗe da faffaɗar ƙirjinsa irin na ƙarfafan mazan nan waɗanda ake nunowa a film ɗin India,

har zuwa yanzu jira yake tayi masa magana koda godiya ne kamar yanda sauran mabaratan suke ta zabga masa godiya da fatan alkhairi,
Ƴar Amana sai dai ido kawai, wani irin kallo take masa kamar mai harara, ba komai bane illah hararar domin a rayuwarta ta tsani yawan kallo, shi kuwa ya kasa ɗauke eyes ɗinsa akanta,
Ganin irin hararar da take wurga masa ne yasa ya dawo hayyacinsa, a ɗan zabure ya miƙe domin bayaso ya yi abinda zaisa a gano shi,
kai tsaye motarsa ya nufa ya buɗe drive seat ya shige yana kallonta ta cikin Black glass ɗinsa wanda na waje bazai iya ganin na cikin motar ba,
a haka yaja motar ya yi tafiyarsa zuciyarsa cike da tambayoyi game da nazarurruka, lokaci guda yaji ransa yayi sanyi duk wata damuwa ta yaye masa,
yana driving shi kansa bai san lokacin da yake sakin wata rikitacciyar murmushi ba,
maganar zuci ya fara yi
"ina ji a jikina wannan ce yarinyar da nake nema, domin babu abinda ya chanza daga launin ta, duk da ban taɓa ganin fuskarta ba but I known she is my dreamer,
but she's too young, yarinya ce ƙarama how comes zata iya kaɗa jita haka? can't believe....."
ya ƙarasa maganar zuci haɗi da girgiza Kai, yana mamakin al'amarin,
Da wannan tunanin ya isa yanda zaije.....

Ƴar Amana jujjuya kuɗin hannunta take tana tunanin ina zata kai waɗannan maƙudan kuɗaɗen...

Tsohuwar ce ta kalleta sannan ta ce "me kike tunani ne ƴata?...."

Ƴar Amana nuna mata kuɗin hannunta tayi tana girgiza Kai alamar bata san yanda zatayi dasu ba,
Dariya tsohuwar tayi har saida jajayen haƙwaranta suka fito ta ce "ƴata kenam waɗannan kuɗaɗen ai kashe su abu ne mai sauƙin gaske a wurin ki,
yanzu mu kuɗin da aka bamu sai suyi shekara basu ƙare ba amma ke a yau zaki ƙarar dasu......"

Ƴar Amana ɗagowa tayi tana kallon tsohuwar sam bata fahimci mai take nufi ba amma taji duk abinda ta ce....

Tsohuwa ta cigaba da cewa "a siyan sutura kaɗai zaki kashe fin rabin kuɗin nan, uwa uba Azo kan takalma da turarukan gashi
Shiyasa kullum sumar kan ki baya rabuwa da ƙamshi, amma baki damu da siyan kayan abinci ba kuma baki damu da yin kwalliya ba ke kullum kin ƙare a siyan kayayyaki....."

Kau da kai Ƴar Amana tayi jin abinda tsohuwar take faɗi,
Ƴar Amana sam bata son zama da ƙazanta kullum acikin gyaran jiki take gata yarinya ƙarama amma ta tsani ƙazanta,
ma'abociyar son tsabta ce da kuma son ƙamshi, da zaran ta samu kuɗi masu dama zata wuce super market ne, idan taje bata magana a kowa zata ɗauki basket ta kutsa ciki, ita da kanta zata zazzaɓo abubuwan da take buƙata sannan tazo su lissafa yawan kuɗaɗen kayayyakin su, haka zata ciro kuɗi ta miƙa musu idan akwai canji su bata,
amma yawan kuɗin da take kashewa sun kai kimanin dubu ɗari biyar ko fin haka....
shiyasa tsohuwa take faɗin "kashe kuɗi a gurin ƴar Amana babu wuya....."

Daren yau ko sau ɗaya Uncle Deen bai rimtsa ba, fuskar Ƴar Amana ce take masa gizo shi har yanzu bai yadda cewar mutum bace, ganin yawan tunanin bazai kai shi ba yasa ya tashi ya nufi bathroom ya ɗauro alwala sannan ya fito tare da zura jallabiyarsa ya ɗoru akan sallaya a nutsi ya tsaida sallar darensa,

𝕭⃤𝖆⃤𝖎⃤𝖜⃤𝖆⃤𝖗⃤ 𝖆⃤ 𝕬⃤𝖑⃤𝖑⃤𝖆⃤𝖍⃤


Baiwar Allah tana cikin mawuyancin hali domin itama a cikin daren nan bata rimtsa ba, wani irin zazzaɓi take fama dashi mai rikitarwa ga tunanin Uncle Deen,
wani irin zafi take ji acikin zuciyarta game da raɗaɗin tafiyarsa, duk wulaƙancin da ake mata acikin gidan saboda tafiyarsa sam bata damu ba, damuwarta ɗaya shine Uncle Deen ya tsaya mata a rai,
a halin yanzu ji take tamkar a cikin kabari take,
shaƙuwar da tayi da Razhdeen ya wuce misali, gani take inta buɗe idonta zata ganshi a gefenta, ko kaɗan bata taɓa jin tsanarsa acikin zuciyarta ba,
tana matuƙar jin wani abu akansa,
tana kwance ta fashe da matsanancin kuka haɗe da maganar zuci
"Uncle Deen ka dawo gare Ni dan Allah, meyasa zaka tafi ka barni cikin wannan mawuyancin hali, bazan iya samun nutsuwa ba tare da kai a kusa dani ba, meyasa? meyasa saida na gama sakaka acikin zuciyata lokaci guda zaka tafi ka barniiii......"
kuka take bana wasa ba, jikinta har wani ɓari yake,
haka ta kwana da wannan ciwon raɗaɗin son kasancewa da Uncle Deen,
Daƙer ta iya tashi ta nufi bathroom domin ɗaurowa Alwala anata ƙiraye-ƙirayen sallar asuba,
yanda taga rana haka taga dare....


Misalin ƙarfe 10 na dare Abbah yana zaune a falo ya tara duk mutanen gidan,
Hajia Kilishi itama tana zaune akan sopa ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana son jin dalilin da Abbah ya tara su gaba ɗaya,
Shima Roshan yana zaune a one seater yana sanye da blue jeans da blue t-shirt wanda ya kama jikinsa sosai kai kace saboda shi aka ƙero rigar sannan ya ƙara ɗora sweater a saman rigar mai launin Black and blue,
Sauran yaran gidan kuwa suna ƙasin carpet iya Baiwar ALLAH ce bata gurin,
Abbah ne ya kalli ƴar Tiny ya ce "Auta je ki ƙira Auntynki....."

Ƴar Tiny ƙura masa ido tayi haɗi da cewa "naga gashu nan jajjaune..."

"Aunty Daughter zaki ƙira a room ɗinta...."
a cewar Abbah.

tsayawa tayi tana turo baki ta ce "ita ɗim Aunty na ne?...."

wani irin tsawa Abbah ya daka mata saida ta gigita bata san lokacin da ta nufi ɗakin Baiwar ALLAH ba tana kuka,
suma duk waran ba wanda bai tsorita ba,
Roshan ne ya kalli Abbah sannan ya ce "Please Abbah cold down...."

kafin wasu ɗan mintuna saiga Baiwar ALLAH ta fito sanye da zureren hijab alamun tin sallar asuba bata cire ba, zuwa tayi ta durƙusa ta gaishe da Abbah, ya amsa mata cikin kulawa sannan takai idonta kan Hajia Kilishi itama ta gaishe ta,
kawar da kanta tayi gefe ba tare da ta amsa mata ba domin zuwa yanzu ba ƙaramin tsanar Baiwar Allah tayi ba, saboda ita duk yaran gidan basa jin daɗin zaman gidan, koda yaushe suna cikin antara....
Baiwar Allah ganin Hajia bata kulata ba yasa ta kalli Roshan taga ita yake kallo shima ta gaishe shi, cikin murmushi ya amsa mata,
Abbah ya kalli yaran gidan fuska a haɗe ya ce "ku ɗin bazaku gaisheta ba ne?....."

duk suka ɗago suna kallon Abbah cike da mamaki,
Banda Ummy cikin sakin fuska ta ce "gud morning Aunty Daughter...."
ta ƙarasa tana dariya itama Baiwar ALLAH murmusawa tayi,
Roshan ne ya ce "wato kema kin bi bakin Abbah Koh?...."
yayi maganar idonsa akan Ummy..

Pinky ce take kallon Abbah cikin takaici ta ce "Abbah mu fa mun girmeta, ita ya dace ta gaishe mu...."

Itama Rukky ta ce "gaskiya yanzu fa we are almost 23 years ita kuma nasan bazata wuce 20 or 21 ba....."

Minal dai ko ɗagowa batayi ba tanata pressing phone ɗinta,

Abbah ya kalli Minal ya ce "kepah Amina kema bijire mun zaki yi ne?...."

Cike da mamaki Minal ta ɗago tana kallon Abbah ta ce "au wai har da Ni?...."

Abbah ya ce "kina shakku ne?...."
ta juya tana kallon Baiwar ALLAH tareda faɗin "gaskiya ba'a mun adalci ba indai akasa na gaishe da wannan yarinyar....."

Abbah ya ce "adalcin kenam tinda yanzu itace sama daku...."

Hajia Kilishi a fusace ta ce "how comes zata zamo sama dasu? kawai dai kanason zamar mun da yara Agolai waɗanda basu da ƴanci...."

Abbah ya ce "Zata zamo matar Yayansu Kinga kuwa dole su darajata su mutuntata...."

Kallon juna Ƴanmatan gidan suka shiga yi abu yazo muku kamar almara,
Hajia Kilishi cikin rashin fahimta tana jifar Baiwar ALLAH da wani irin mummunan kallo ta ce "ban fahimta ba...."

Baiwar Allah kanta a sunkuye ita kanta bata san ina Abbah ya dosa ba,
Abbah ya ce "ƙwarai da gaske na yanke shawarar Aurawa Roshan Daughter,
Roshan ya sanar mun cewar yana sonta zai Aure ta bayan na bashi labarin ta, haƙiƙannin gaskiya naji daɗin haka sosai domin inaso na sauƙe nauyin dake kaina tabar hannuna ta koma hannun mijinta Roshan,
Amma hakan bashi zaisa na daina lura da al'amuranta ba dole zansa ido akan yanayin zamantakewar ta da mijinta da kuma ku masu nuna ƙiyayyarku akanta tinda ba wani guri za'a Kaita ba, a cikin gidan zasu zauna amma part ɗinta daban,
Ni nayi Na'am da Auren nan....."

a firgice Rukky ta kalli Pinky haɗi da cewa "daman na gaya miki......"
Pinky kamar zata haɗiyi ranta ta ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, amma za'a yi babban buro uba a gidan nan....."
sunyi maganarsu acikin raɗa ba tare da anji su ba

Minal cike da mamaki take bin Baiwar ALLAH da kallo fuska a murtuƙe ta ce "taya zamu zauna da wacce bamu san asalinta ba?...."

Abbah ya ce "ta yanda kuke zaune da ita yanzu...."

Roshan ganin yanda suke ta hararar Baiwar ALLAH yasa yaɗan motsa yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya ya ce "kunga ku dakata haka! na farko baku zaku Aura mun ita ba sannan baku zaku zauna mun da ita ba yakamata ku fuskanci yanda rayuwa take, kuma ku samo mazajen Aure kuyi Auren ku....."

kafin ya ƙarasa Hajia Kilishi ta ɗaga masa hannu tare da miƙewa tsaye tana fuskantar sa ta ce "ka dakata haka Roshan, wannan cin mutunci da cin fuska ya isheni haka! kenam kana musu gorin Aure ne ko meye?
Wawan yaro wanda baka san inda yake maka ciwo ba,
In banda ƙaddara meya haɗaka da wannan yarinyar da ba'a san asalin ta ba, wata ƙil ƴar cikin shege ce aka jefar da ita ta tashi a gidan marayu,
kaine wanda za'a ce ka fuskanci rayuwa yanda take kaje ka nemo ƴar asali bawai ƴar tsintuwa ba......"

Abbah ne shima ya miƙe tare da zabga mata mari a gefen fuskarta,
saida ta faɗa kan kujera tana riƙe da fuskarta,
Duk acikin yaran babu wanda bai zabura ba, ko wacce zuciyarta na bugun 3³,
Baiwar Allah ta kasa ɗago da kanta domin yanayin da take ciki yana shirin fin ƙarfin tunaninta, kuka take ba ƙaƙƙautawa, bata san meyasa wannan al'amarin yake shirin afkuwa ba,

Abbah cikin zafin rai ya ce "idan kika sake faɗin mummunan kalma akan yarinyar nan wallahi zanyi miki abunda bakiyi zato ba...."

Hajia Kilishi ganin bazata iya juran kalar wannan wulaƙanci ba a gaban iyalanta yasa ta tashi a fusace cikin zafin rai take nunawa Abbah yatsa tare da faɗin
"Na faɗa ita ɗin ƴar cikin shege ce marar asali kayi duk abinda zakayi, tinda har wulaƙancinka yakai ka rinƙa dukana a gaban ƴaƴana to meya rage yanzu,
kuma wallahi tallahi bazan taɓa bari ayi Auren nan ba saidai In wata amma banda wannan ƴar jagaliya,
Kuma koda mahaifiyarsa tana raye bazata taɓa barin ya Auri wannan marar asali ba,
saboda bani na haifeshi ba shine zaka nuna mun ban isa dashi ba,
toh sai ayi Auren mu gani ai....."

Murmushin takaici Abbah yayi ya ce "ki cigaba da nuna mun yatsa wata rana zan ɓalla ƴar yatsar ne,
Kuma da kike cewa baza'ayi Auren ba basai kina gidan daki dakatar ba......"

Hajia Kilishi cike da mamaki ta ce "oh kana nufin korata zakayi?...."

Abbah ya ce "ehh! kije ki na sakeki saki biyu...."

A zabure Roshan ya miƙe tsaye yana faɗin "Abbah meye kake shirin aikatawa?...."

Abbah juyowa yayi yana kallon Roshan ya ce "bawai nake shirin aikatawa ba, na ma aikata an gama ka nemi guri ka zauna...."

Roshan ba yanda ya iya haka ya nemi guri ya zauna domin baya ƙaunar kaucewa maganar Abbah,

Minal da Pinky da Rukky da kuma Ummy duk miƙewa sukayi tsaye domin hukuncin da Abbah ya yanke akan Mommy yayi tsauri,
Minal tana kuka ta ce "Abbah yanzu ɓacin ranka har zaisa ka sallami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login