Showing 63001 words to 66000 words out of 117953 words

Chapter 22 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4740

cewa "Ni wacece mai zuba abincin ne kam gashi Man ɗina ya gaggauta...." ya ƙarasa maganar yana binsu da kallo.

Ummy ce ta ce "Aunty Baiwar ALLAH ce kuma tana fitowa yanzu...."

Banda Abbah da Ummy duk cikinsu babu wanda baiji haushin Baiwar ALLAH ba jinkirin fitowar da tayi ga kowa najin yunwa....

Itama kuma Baiwar ALLAH tana ciki tsananin tsoro ne da fargaba ya hanata fitowa, sai tazo zata fito saita koma da gudu, yanzu ne na ƙarshe Saida tayi addu'a kafin ta jefo ƙafarta na dama waje tukun ta fara taku a hankali jiki duk ba ƙwari, kamar marar lafiya haka take ƙanƙame jikinta kanta a sunkuye sam bata ƙaunar ganin Uncle Deen....

da haka ta ƙaraso wajen da sallama a bakinta,
Uncle Deen ko ɗagowa baiyi ba kai a sunkuye yana pressing phone ɗinsa,
Roshan ne ya ɗago tare da amsa sallamar data yi, yayi ido huɗu da ita, gabansa ne yayi wani irin yanke wa kamar wanda yaga abun tsoro, a hankali ya furta "ƙalu innalillahi wa inna ilaihi raju'un......" ba tare da kowa yaji shi ba,
ya cigaba da cewa "godiya ta tabbata ga sarkin hallitun duniya, ALLAH na gode maka daka halitto wannan kyakykyawar halitta...."

Duk waɗannan maganganun acikin ransa yake yinsa,
yana cikin wannan sambatun yaji Hajia Kilishi ta darara mata tsawa tare da faɗin "Meye amfanin ki acikin gidan nan? Kenam mu zamu zo muna jiranki saboda isarki da gadara? wannan shine na ƙarshe na gaya miki...."

Baiwar Allah kai a sunkuye ta ce "kiyi haƙuri Hajia bazan ƙara ba INSHA ALLAHU...."

Abbah ya ce "kinga Dota zo ki zuzzuba abinci kema ki zauna ki ci koh...."

A hankali ta furta "tam Abbah nagode...."

kafin ta fara zuba abincin Saida taje gefen Razhdeen ta durƙusa ƙasi ta gaishe shi,
hannu kawai ya ɗaga mata ba tare da ya furta komai ba,
Sannan taje gefen Roshan wanda idonsa akanta ya gagara ɗagewa sai ji yayi ta gaishe shi,
Amsawa yayi cikin kulawa ya ce "Barkanki da fitowa Gimbiya...."

Duk ƴanmatan gidan zaro ido waje sukayi jin sunan da ya ƙirata dashi, kallo kallo suka shiga yi cike da mamaki....
Shi kuwa ko a jikinsa,
Tashi tayi jiki a sanyaye ta buɗe kulolin ta fara zuzzuba wa kowa abinci a plate,
ta kaiwa kowa nashi sannan itama ta zauna a gefen Ummy da ƴar Tiny....

A nutse kowa yake cin abincinsa gurin yayi tsittt,
Roshan yana ci idonsa akan Baiwar ALLAH,
Ummy ce kawai ta lura da haka tanayi tana kallon Yaya Roshan da kuma Baiwar ALLAH wacce itama take satar kallonsa idan ta haɗa ido dashi sai tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasi, kuma du saita ƙara ɗagowa ta kalli Uncle Deen tana jinjina girman kai irin nasa, daƙer yake motsa bakinsa idan yakai abinci ciki.....
ta kuma kai idonta kan Uncle Deen sai karaf suka haɗa eyes ɗagowarda zai yi, domin shi a tsarge yake idan ana yawan kallonsa jikinsa ne yake bashi,

Dasauri ta sunkuyar da kanta ƙasi tana jan numfashi daƙer ga wanin irin gumin dake gangaro mata,
Uncle Deen cigaba da uzurinsa yayi bai saurareta ba,

Shi kuma Roshan yana cikin kallon Baiwar ALLAH idonsa ya sauƙa akan na Ummy wacce taketa ƙaresu da kallo,
Murmushi ta sau masa tare da ƙibta masa ido ɗaya,
Harararta yayi da gefen ido yana motsi da lips ɗinsa ya ce "sa'idawa manya...."

Roshan ganin bazai iya yin shuru ba yasa shi cewa "Ni Abbah wacece wannan ban santa ba?...."

kafin Abbah ya buɗe baki yayi magana har ƴar Tiny ta rigashi cewa "wannan ai el aicin gidan mu ce...."

Cike da mamaki Roshan ya ce "ƴar aiki kuma? wannan ɗin? amma naga batayi kama da ƴar aiki ba....."

Hajia Kilishi ce ta watso masa harara tare da faɗin
"au daman ƴan aiki ɗin kamanninsu daban ne? TOH ƴar aikin ce ko zaka canza mata matsayi ne?...."

Roshan shuru yayi baice komai ba,

Uncle Deen yana yamutsa fuska gira a haɗe cool voice ya ce "ƴar aiki meya haɗata da zama acikin mu? hakane tsarin yake daman a rinƙa zaman cin abinci da ƴar aiki?
ya kalli Baiwar ALLAH a tsawace ya ce "Keee! tashi kibar nan Right now I don't want to see your face....."

Baiwar ALLAH jiki na ɓari a tsorace ta tashi zata bar wajen,

Ran Abbah ne yayi mungun ɓaci ya ce "Dota nemi ware ki zauna...."

Baiwar ALLAH idonta akan Uncle Deen ta ɗan ɗosana mazaunenta akan kujera ba tareda ta sake jikinta ba,
Roshan cizan lips ɗinsa yayi ta ƙasi sam baiji daɗin abinda Uncle Deen yayi mata ba..

Abbah ne ya soma magana cikin ɓacin rai idonsa akan Ummy
Ya ce "uwar masu gida meyasa duk abubuwanda suke faruwa acikin gidan nan bakya gaya mun?..."
ya cigaba da cewa "lokacinda na tashi barin ƙasar nan menace miki akan yarinyar nan?
Kenam bazaki iya cika mun alƙawarin da kika ɗaukar mun ba?
Ko dana tashi tafiya nace miki ta zauna a matsayin ƴar aiki ne?
dana kawota nace miki gata nan ƴar aiki na kawo muku?
Gaya mun mana....?
ya ƙarasa maganar a tsawace idonsa akan Ummy,

Dasauri Ummy ta girgiza kai kanta a ƙasi sai faman zubar da hawaye take, ganin duk an ɗora mata laifi...

ya cigaba da cewa "Nasan daga mahaifiyarki har Yayunki babu mai ƙaunarta shiyasa na damƙata a hannunki ashe baki ita bashida wani amfani, meyasa duk abinda sukayi mata bazaki ƙirani ki sanar mun ba kuma muna waya koda yaushe,
TOH daga yau" yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya yana nunnuna musu yatsa ido a waje yanda yake zazzaro su ya ce "idan na sake ganin wani abu ya sake fitowa marar amfani wallahi duk ɗinku sainayi mungun saɓa muku, ba'a matsayin ƴar aiki na kawota ba, yanda kuke a matsayin ƴaƴana TOH haka itama take a wannan matsayin, kada na sake ji na gaya muku...."

ya nuna Hajia Kilishi ya ce "musamman ke kece ummu ƙaba'isu mai haifar da duk wasu matsaltsalu toh ki dakata haka tin kafin mu shiga rana domin abun bazai miki daɗi ba......"

Mommy idonta akan Abbah tana masa kallon takaici ido duk ya cicciko da ƙwallah ta tashi a fusace tabar dinning, kai tsaye upstairs ɗinta ta haura.....

Ƴar Tiny gaba ɗaya ta kumbura jin abinda Abbah yace wai itama ƴarsa ce
ta ce "co co co Abbah wacece uwacca acicin gidan nan?...."

Abbah ya kalli ƴar Tiny ya ce "zan doke ki a waran nan idan baki rufe mun baki ba, kema harda ke koh? kina biye Uwarki da Yayunki kuna shirme zanyi maganinku ai...."

Ƴar Tiny hannu ta ɗora akan fuska tana ƙinƙishin kuka....

Uncle Deen dalilinda yasa baya son cin abinci acikin mutane Kenam hayaniya, ya tsani yawan magana da hayaniya nan danan kansa zai fara ciwo.....
Sai tsuka yake shi kaɗai, shima tashi yayi zai bar wajen Abbah yayi saurin dakatar dashi yana faɗin "zo nan ina zakaje kuma...."

Uncle Deen kamar bazaiyi magana ya ce "am okay..."

Abbah ya ce "ban yadda ba zoka zauna kaji ...."

Ba yanda ya iya haka ya koma ya zauna.....



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 29 to 30



꧁꧂


Abbah ne ya kalli Uncle Deen sannan ya ce "ka ƙarasa cin abincinka bana son zama da yunwa..."

Uncle Deen baice komai ba sai caccakar plate ɗin da yake da spoon,
Waran yayi tsittt kamar ba mutane, sai bayan wasu mintuna da murmushi kwance saman fuskar Roshan idonsa akan Baiwar ALLAH ya ce "Abbah...."

Abbah ya amsa masa cikin kulawa daiden lokacin da yakai one spoon inside his mouth...
sauƙe numfashi Roshan ya yi tare da faɗin "nayi tsintuwar wata kyakykyawar Ɗawisuwa acikin gidan nan...."

Ummy zaro ido tayi waje tana harararsa irin na gatsalin nan domin tasan me yake nufi..

Abbah ya ce "ha'a Ni daman baka san akwai Ɗawisai a gidan bane? ai sunada yawa akwai part ɗinsu na musamman....."

Roshan ya ce "Uhmm! Abbah Kenam wannan Ɗawisuwar dana gani ta daban ce...."

Abbah ya ce "ai duk ba abun tada hankali bane idan kanaso sai muje ka zaɓi wanda kakeso sai a yanka maka koh....."

Murmushi Roshan ya yi sannan ya kuma cewa "wannan bata yankawa bace saidai na sata a gaba naita kallonta...."

Abbah yace "au TOH ai duk yanda kake so hakan zakayi ai..."
ya kalli Ummy sannan ya ce "Ni uwar masu gida Ɗawisai nan sauran guda nawa ne?...."

Ummy tana kumshe dariyarta daƙer ta ce "Abbah sauran basu fi goma ba...."

ya ce "duk ina sauran?...."

Ta ce "Abbah duk an cinye mana..."

"Toh sarakunan cin nama...." A cewar Abbah.

Baiwar ALLAH ta lura da kallon da Roshan yake yi mata itama ɗagowa tayi ta sauƙe eyes ɗinta akan ƙayataccen murmushinsa mai ƙayatarwa.....
itama bata san lokacin data sau tata murmushin ba, cikin jin kunya ta tashi a hankali zata bar wajen,
Abbah ya ce "yadai Dota....?"
ta ce "amm Abbah na ƙoshi ne.."
ya ce "ok tam shikenam..."
tana barin wajen itama Ummy ta tashi, da haka har sauran ƴan matan suma suka tattashi aka bar iya Abbah da Uncle Deen da kuma Roshan...

Baiwar ALLAH tana shiga room ɗinta taje gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta fuska ɗauke da murmushi, tana cikin wannan halin sai ji tayi ance "Uhmmm daman Nasan za'ayi hakan..."

Dasauri Baiwar ALLAH ta waiwayo bayanta tana bin Ummy da kallo daga bisani tasau ajiyar zuciya tareda faɗin "wallahi har kin tsoratar dani...."

Da murmushi a fuskar Ummy ta ce "daman nasan buddin kuka ga juna sai kun kwarewa junanku...."

Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta ta ce "kamar ya ban ganeba..."

Ta ce "Yaya Roshan mana yanzu baki fahimci komai game dashi bane?..."

Baiwar ALLAH fari tayi da eyes ɗinta sannan ta ce "kamar ya kenam..."

Ummy matsowa itama tayi jikin mirror ta ce "tinda bakya zuwa Ghana bari nayi miki filla filla kamar ƴar nursery,
Yaya Roshan alamunsa ya kware miki ne...."

Zaro ido Baiwar ALLAH tayi cikin rashin fahimta ta ce "kwarewa kuma? Bangane ya kware mun ba, aina kuma yaushe? Kinga rufa mun asiri yaushe ma na ganshi balle ya kware mun?...."

Ummy ta sauƙe numfashi tana bin Baiwar ALLAH da kallo daga bisani ta girgiza kai ta ce "okay tinda baki gane mai nake nufi ba bari na barki haka, zaki gane abinda nake nufi zuwa gaba,
amma dan ALLAH kar in yazo gareki ki wulakanta mana shi domin shi ɗin yanada rarraunar zuciya....."

tana kaiwa nan tayi ficewarta,
Baiwar ALLAH bin bayanta tayi da kallo cikin rashin fahimtar abinda take nufi.....

Abbah da twins Rosh da Razh har zuwa yanzu suna dinning alamun wani ɗan tattaunawa suke yi.....

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login