Showing 87001 words to 90000 words out of 117953 words
Mai martaba gaba ɗaya ya rasa yanda zai yi akan wannan batun shi kuma fargaban ƙiran Yayansa yake akan maganar bayan haka yasan halin Razhdeen ba Amincewa zaiyi ba,
Hura iskar bakinsa yayi sannan ya ce "Amma Mamy kin dai san halin Razhdeen, ba irin mutanen nan ne masu sauƙin kai ba! ba lallai ya yadda ba
ina laifin kice Roshan amma Razhdeeeeen kaiiiiii ......"
tinin harya haɗa gumi domin lamarin Razhdeen sai Allah amma Mamy ta kasa ganewa ita burinta ta haɗa Ramlat da Razhdeen,
yana cikin nazari yaji ta fashe masa da kuka tana faɗin "saboda ban taɓa haihuwa ba shine komai na roƙa ba'a yarje mun, yanzu fisabilillah so nake na haɗa jinsi da ahalinku sakamakon bana haihuwa amma furr kaƙi yadda ......"
Mai martaba ya ce "kina ji ba, bawai nine ban yadda ba sannan ba Yayana bane bai yadda ba shi kanshi Razhdeen ɗin ne bazai yadda ba....."
A tsawace ta ce "toh baza ku saka shi dole ba? ku ba iyayensa bane? dole idan kuka tsayar masa zai amince....."
Ya ce "Uhmmm! Mammy kenam Razhdeen ba yanda kike tunani bane shi, meyasa bazaki zaɓi Roshan ba sai Razhdeen wanda yafi ƙarfin ai masa dole,
Ai yanzu Mace ma ba'a mata dole balle namiji....."
Gaba ɗaya Mamy ta kasa fahimtar shi sai faman zuba masifa take, ganin bazai iya jurewa ba yasa ya tashi zai fice a room ɗin......
Duk tattaunawar da sukayi Ramlat tana tsaye a bakin ƙofa tana jinsu, jin mai martaba yana shirin fitowa yasa tayi saurin tura ƙofa zata shiga da sallama a bakinta dai-dai lokacin da zai fito shi kuma,
Cikin ɓacin rai ya wuce yayi tafiyarsa,
Ramlat ce ta ƙarisa gurin Mamy tana faɗin "wai ke Mammy meye damuwarki da dole saina Auri Uncle Deen? Na gaya miki Ni Yaya Roshan nake so, inasonsa sosai har cikin zuciyata....."
Mammy ta ce "ke Dallah rufe mun baki, ai ke mahaukaciya ce shiyasa baki san rayuwa ba,
Meye Roshan yake dashi?....."
Ramlat ta ce "a'ahhhh ai kuwa Mamy bazaki ce Roshan ba kyakkyawa bane....."
Mammy ta ce "Shashasha rufe mun baki, wani kyau kuma? Ai kuɗaɗe sune kyau, duk wanda yafi kuɗi toh shine kyakkyawa,
Toh bari kiji na gaya miki Roshan ko kamo ƙafar Razhdeen baiyi ba a yawan kuɗaɗe,
Ke kinsan adadin yawan motocin Razhdeen kuwa? kinsan adadin yawan gidajensa a nan Nigeria kuwa? kinsan adadin yawan gidajensa a ƙasar Australia kuwa? kinsan adadin yawan jirgayensa kuwa? kinsan adadin yawan gwalagwalen da yake dasu kuwa? kinsan adadin yawan dalolin da yake dasu kuwa? kinsan adadin yawan Nairorin da yake dasu kuwa?
Bugu da ƙari ga kyau ga ƙiran sura mai kyau, wallahi kin more yarinya idan kika Auri Razhdeen,
Shi Roshan bai kai Razhdeen dukiya ba,
toh bari in taƙaice miki ko Ni Razhdeen yazo yace zai Aure Ni a halin yanzu toh wallahi da gudu zan kashe Aurena na Aure shi......"
Zaro ido waje Ramlat tayi sannan ta ce "Mamy kina Auran Baffansa kuma kice zaki Aure shi? ai babu Aure a tsakanin ku tinda mai martaba kamar mahaifi yake a gurinsa ...."
Mamy tana turɓune fuska ta ce "yooo ina ruwana da wani tsarin addini, Ni kuɗi kawai na sani, ke wawuya Arziƙi na bin mu da gudu ke kuma kina ƙoƙarin kaucewa, inaso ki Auri Razhdeen mu ci Arziƙi mubar Arziƙi,
Mu tashi a cikin dukiya, mu ci dukiya, mu sha dukiya, mu kwanta a cikin dukiya, mu mutu acikin dukiya....."
Jinjina kai Ramlat tayi ta ce "ai kuwa Mamy yanzu ma baza kice a cikin talauci kike ba, tinda a koda yaushe bakya rasa kuɗaɗe manya-manya....."
Mamy ta ce "shuru dallah, bakya son mu cigaba ne?...."
Ramlat ta ce "shikenam Mammy ya wuce...."
Mamy ta ce "atoh ko naji dai....."
Mai martaba bayan ya fita a ɗakin Mamy kai tsaye part ɗin A'ishansa ya wuce,
yana shiga ya tarar da ita sai faman goge jeren kumbon ta take irin na sarakuna masu kyan gaske da sheƙi,
Sallama yayi mata tareda faɗin "kaga manyan mata Ƴar gidan sarki, jikar sarki, matar sarki! Amarya kenam Maman Reematu....."
Ɗagowa tayi da murmushi kan fuskarta ta ce "sannu da shugowa mai martaba, duk wannan yabon a Ni kaɗai?...."
Ya ce "kin cancanci hakan ne shiyasa...."
Ta ce "godiya nake mai martaba....."
Jinjina kai yayi yana kallonta cike da ƙauna ya ce "kiyi haƙuri yau ranar ki ce amma na shiga ɓangaren Mamy akan wani batu...."
Ta ce "Tabb lallai mai martaba yanzu akan hakan ne sai an bani haƙuri?
babu komai wallahi ...."
Yaja dogon numfashi tareda faɗin
"Allah ya miki Albarka....."
ta amsa cikin girmamawa ......
lokaci guda fuskarta ta sauya kamar zatayi kuka ta cigaba da goge kumbonta,
riƙe hannunta mai martaba yayi tareda juyo da ita suna fuskantar juna ya ce "meya faru dake Sarauniya?...."
ta ɗan sau murmushi ta ce "banaso na rinƙa ɓoye maka abu maganar gaskiya idan ana ambato mun sunan Reemah gaba ɗaya kaina juyawa yake,
sai na rinƙa jin bugun zuciyata yana ƙaruwa, inaji a jikina cewa Ɗiyata Reemah tana nan a raye domin inajin motsinta acikin zuciyata,
Bugu da ƙari ma tin daga kanta ban ƙara samun haihuwa ba, abun yana damu na a raina......"
Shima mai martaba ya damu sosai ganinta acikin wannan halin ya ce "ki kwantar da hankalinki insha Allahu komai zai dai-daita, kamar yanda kike tunanin cewar Reemah tana raye insha Allahu zata bayyano, ki cigaba da addu'a kinji...."
kai kawai ta ɗaga masa ......
✍️✍️✍️
Roshan yayi iya ƙoƙarinsa ganin ƙofar bedroom ɗin Uncle Deen ya ɓallu amma babu alamu, yayi bugawar har ya gaji, yana hawaye haka yabar ɗakin kai tsaye falo ya sauƙa ya nemi kujera ɗaya ya zauna tareda dafe goshinsa da hannaye biyu yana zubar da hawaye,
zuciyarsa ce take wani irin tafasa wanda tinda yake bai taɓa shiga yanayi irin na yau ba,
Shi kuwa Uncle Deen kwantar da Baiwar Allah yayi kan gadonsa shima ya nemi kujera ya zauna ta gefen gadon, yana jin yanda Roshan yake buga ƙofar amma ko motsi baiyi ba,
yana mamakin yanda Roshan zai iya ɗaukan hannu ya buge shi, yana ji a ransa cewa inda wani ne daban yayi mishi haka da za'a zo a ɗauki gawarsa ne.....
suna wannan halin har suka wuni a haka zuwa yamma dai-dai lokacin dawowar sauran mutanen gidan daga gurin aiki,
Roshan yana zaune a falo sallah ma a falo yayi shi, yana zaune kan sallayar Ummy data kawo masa, ita kuwa tana gefensa sai faman rarrashinsa take, ganin yanda idanuwansa sukayi jawur tsabar kuka yasa Ummy itama ta fashe da kuka,
A ranar yau babu wanda ya shiga kitchen domin girka abinci, Pinky da Rukky daman suma tin kafin a fara wannan al'amarin suka fita zasu je ziyara old school ɗinsu,
Hajiya Kilishi ce ta fara shugowa daman yanzu da wuri take dawowa gida,
Ganin Roshan a tsakiyar falo akan sallaya yasa gabanta yankewa a tsorace ta ce "waye ya mutu a cikin yarana?....."
Roshan kasa yin magana yayi sai Ummy ce ta ɗago tana kuka ta ce "ba mutuwa akayi ba, matsala suka samu shi da Uncle Deen....."
Hajia Kilishi zaro Ido tayi cikin yanayin farin ciki yau kamar anyi mata bishara da gidan Aljanna, acikin ranta ta ce "wonderful, wannan kyakkyawan albishir haka....."
harararsa tayi sannan ta ce "Allah ya sawwaƙe toh...."
ba tareda ta tambayi dalili ba tayi wucewar ta dasauri ta haura upstairs......
Bayan wasu mintuna saiga Pinky da Rukky suma sun dawo suna ƴar hirarsu ganin abun mamaki yasa suka tsaya baki a wangane
Pinky ta ce "Yaya Roshan lafiya kuwa, kuka fa kake yi? wannan wani irin mummunar rana ce haka?....."
Rukky cike da mamaki ta ce "tinda uwata ta haifeni ban taɓa ganin fushi matuƙa a fuskar Yaya Roshan ba balle Kuka innalillahi wa inna'ilaihi raju'un......"
Ummy tana jinsu bata kulasu ba kanta a ɗore kan kafaɗar Roshan,
suma ƙarasowa sukayi gurinsa suka zazzauna suna fuskantar sa kafin kace mai suma sun fara hawaye,
Suna cikin wannan halin saiga Ƴar Tiny ta dawo daga school tana goye da jakarta hannunta kuma yana riƙe da lunch bag ta shugo tana tsallenta,
Ganinsu yasa ta nufi yanda suke da gudu ta faɗa saman cinyar Roshan tana faɗin "Yaya Yocan Oyoyo...."
ɗagowar da zatayi taga fuskar Roshan yayi jawur tsabar kuka da ɓacin rai buɗe baki tayi tana kallonsa lokaci guda kuma ta fashe da kuka tana faɗin
"Wayyo Ayyah nahhh Yaya Yocan yana kukaaaaa, Yaya Yocan meya came kaaaa ....."
Ummy ce ta darara mata tsawa da cewa "ke Dallah rufe wa mutane baki, murya sai kace gyare ....."
tashi tayi da gudu tana faɗin "bajanyi cuyu baaa kuma wayyayi tayyayi cena gaya wa mommy nahhh....."
ta ƙarasa maganar tareda haurawa upstairs yanda part ɗin Hajia Kilishi yake,
Itama Minal shugowa tayi ta same su a haka, abun yayi matuƙar bata mamaki ganin Yaya Roshan acikin wannan halin,
Ta tambaya akan meke faruwa Pinky ta ce "mu ma haka mukazo muka same su...."
Ummy ta sani amma sai dai taƙi cewa komai bare shi kuwa bashi ma da bakin magana, zuciyarsa ce take ta faman harbawa da ƙarfin gaske,
Turo ƙofa akayi da sallama a bakinsa ya shugo ganinsu a haka yasa Abbah firgicewa ya ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Allah yasa dai komai lafiya, amma da dukkan alamu ba lafiya ba....."
Zama Abbah yayi akan kujera yana facing ɗin Roshan sai tambayarsa yake meke faruwa amma sam yaƙi cewa komai,
Sai Ummy ce ta zayyanar masa da duk abubuwan da suka wakana dake a lokacin da abun ya faru tana bakin ƙofar Uncle Deen tana jin duk faɗan da sukayi.......
Abbah ya ce "yanzun shi ɗin Razhdeen yana ciki shi da Dota?....."
Ya tashi tareda haurawa saman upstairs ɗinsu kai tsaye part ɗin Uncle Deen ya nufa,
Dasauri Roshan ya miƙe tareda bin bayan Abbah ko za'a dace,
Minal jin akan Baiwar Allah ne duk wannan matsalar yasa taja dogon tsuka ta wuce part ɗinsu,
Suma su Pinky cewa suke "yanzun akan Baiwar Allah muma mukayi kukan? tirrrrrr....."
suma haura part ɗinsu sukayi domin abun bai dame su ba,
Amma ta wani ɓangaren mamaki suke meya haɗa Roshan da Baiwar Allah kuma? meye alaƙar dake tsakaninsu har ta kai ga haka?
waɗannan tambayoyin ne suke ta yawo akawunansu....
Abbah yana zuwa yasa hannu zai buɗe ƙofar falonsa yaji a ƙarƙame,
Roshan cike da mamaki ya ce "wahatttt? nan ma ya kulle? me yake nufi da hakan? Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un....."
Ummy ta ce "Yaya Roshan ka kwantar da hankali Please banason ganin hawayen jarumin namiji ......"
Abbah buga ƙofar ya shiga yi yana ƙiran sunansa:
"Razhdeen! Razhdeen!! Razhdeen!!! kazo ka buɗe ƙofar nan tin kafin ranka ya ɓaci....."
Haka shima Abbah yayi yayi har ya gaji amma Razhdeen bai zo ya buɗe ba, kuma yana kwance a doguwar kujerar falonsa ya miƙar da ƙafafu yana facing ceiling idanu a lumshe kamar mai yin Bacci amma sai dai ba Bacci yake ba,
duk yana jin bugawar da ake ya sharar, ba ƙaramin ɓata masa rai Roshan yayi ba shiyasa gaba ɗaya zuciyarsa yake a hargutse......
Ita kuwa Baiwar Allah tana kwance a bedroom har zuwa wannan lokacin bata farfaɗo ba...
Haka su Abbah suka haƙura suka koma falo har zuwa misalin ƙarfe 12 na dare,
Abbah ba yanda baiyi da Roshan akan yaje ya kwanta a ɗakinsa amma yaƙi sai cewa yayi "Please Abbah zan zauna anan falo har zuwa Asuba nasan zai iya fitowa zuwa masallaci....
Abbah ya ce "shikenam Roshan mu zauna toh, domin bazan iya barinka anan ba cikin wannan halin,
Ka