Showing 66001 words to 69000 words out of 117953 words

Chapter 23 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4747

*BAYAN SATI ƊAYA DA DAWOWAR RAZH DA ROSH....*


Roshan a ɗan waɗannan kwanakin yana bibiyan Baiwar ALLAH amma sai dai ya kasa tin karar ta, amma duk waranda take shima yana nan,
hatta kitchen idan ta shiga ya rinƙa zirga-zirga zuwa kitchen yaje ya ɗauko cup ya fito kuma du ya sake komawa ya ɗauko spoon, still ya sake shiga zuwa ɗaukan wuƙa wai zai yanka Apple, haka zai rinƙa wannan zaryar har Baiwar ALLAH ta kammala da kitchen ɗin ta fito, abun har ya fara bata mamaki, itama Ummy tasa ido akansa sosai ganin Ɗan uwanta yana cutuwa sosai yasata zuwa har part ɗinsa, tana shiga ta same shi yana zaune a bakin gado kai a sunkuye ya rufe fuskar da hannayensa alamun yana cikin damuwa,
Itama Ummy zama tayi dab dashi tana fuskantarsa cikin sassanyar murya ta ce "my love..."

Ɗagowa yayi yana kallonta da shanyayyun eyes ɗinsa da bacci ya ƙaurace musu,

Ta kuma cewa "kana cikin damuwa nasani amma meyasa bazaka nemi na temaka maka ba?...."
Murmushi yayi idonsa akanta ya ce "bazaki iya temaka mun ba my love, Damuwata tafi ƙarfin tunaninki...."

Murmushi tayi sannan ta ce "Damuwarka bazata wuce akan Baiwar ALLAH ba, meyasa kake tunanin bazan iya ba?
tinda kai ka gaza Ni zan sameta na sanar mata halinda kake ciki akanta...."

Roshan yayi saurin katseta da cewa "No no no please karki fara, ki barni zanyi mata magana da kaina...."

Ummy ta ce "Uhmmm! yarinyar da kullum saita shugo ɗakinka ta gyara maka room ta wanke toilet ɗinka ta chanza maka bedsheet sannan ta feffeshe maka ɗaki da turare, idan tayi girki ita zata kawo maka har ɗaki ta ajiye maka akan dinning idan kana kusa ita zata zuba maka a plate duk idanuwanka akanta amma ka kasa sanar mata kana sonta, TOH idan baka sanar mata yanzu ba sai yaushe?
Please My love ka cire tsoro da fargaba ka tinkareta kar kabar damarka ta kuɓuce, toh bari kaji akwai ranar da muka fita da ita wallahi saida tayi samari kusan goma kuma duk manya-manyan mutane babu talaka, shiyasa take fargaban fita outside,
Idan ka tsaya kallon ruwa kwaɗo zai yi maka ƙafa ne, domin yanzu haka burin Abbah ya sama mata nagartacce miji ya Aura mata ne,
yakamata ka fito kayi yaƙin ƙwatar soyayyarka kar ka tashi a tutar babu....."

Roshan gaba ɗaya ya susuce idonsa akan Ummy ko ƙibtawa baya yi tsabar razana da yayi jin tanada manema, jinjina kai yayi sannan ya ce "hakan bazai taɓa yuwa ba, dole a yau zanyi mata magana...."

suna cikin wannan halin sai suka ji sallama daga falo,
Roshan murya na kakkarwa ya ce "come in...."

Ummy tana ƙumshe dariya ta ce "Haba My love wallahi zaka bayar da maza kamar irinsu Uncle Deen...."

kallonta yayi yana tura ƴar lips ɗinsa ya ce "Deen mutum ne daman...."

Buɗe baki tayi tareda rufe bakin da hannu bibbiyu ta ce "wallahi babu ruwana..."

ya juyo yana kallonta ya ce "duka na zai yi ne? ke ƙyale Ni fah yanzu tsoron soyayya nake yi tin lokacin da mutuwa ta riski Abar ƙaunaata...."

kafin ya ƙarasa maganar saiga Baiwar ALLAH ta shugo da sallama a bakinta, duk suka amsa mata cikin fara'a
Baiwar ALLAH ta ce "amm na kammala shirya kayan abincin a dinning...."

idonsa cikin nata ya ce "okay sannunki da ƙoƙari gani nan fitowa amma kar ki tafi ki jirani...."

sunkuyar da kanta tayi tana kallon ƙasi, tana murza yatsunta kamar zatayi kuka ba tare da ta furta komai ba...

ya fahimci kamar tana cikin matsala ya ce "Are you okay?..."

Girgiza kai tayi da sauri bata san lokacin da tayi ba tsabar tsoro..

Ya ce "toh meya faru ne?..."

tayi shuru ta gagara cewa komai
Sai Ummy ce ta tsoma musu baki tare da faɗin "Yaya Roshan kasan fa tana zuwa part ɗin Uncle Deen batason tayi dismiss ne akwai matsala kasan halin mutuminka...."

Jinjina kai yayi sannan yace "okay idan kin gama dashi inason ganinki...."

Dasauri ta furta "TOH...." ta juya....

tana fita ta sauƙa falo ta nufi kitchen nan ma taje ta jido kuloli a dinerset ta sake haurawa saman stairs kai tsaye part ɗin Uncle Deen ta nufa, ta ɗora tray akanta ta fara knocking a hankali kar taje bacci yake yi ta tashe shi ta tsokalo tsuriyar Dodo,
ganin shuru ba'ayi magana ba yasa ta tura ƙofar ta shiga da sallama a bakinta, ganin falon wayam yasa ta nufi dinning ɗinsa taje ta jejjera masa kayan abincinsa, sannan ta nufi frig ta ɗauko kayan fruits da lemuka tazo ta yanyanka masa kayan fruits acikin glass plate mai ɗan faɗi, ta kammala shirya masa komai da komai abubuwan da zai buƙata kamar yanda tayiwa Roshan amma saidai kayan haɗin Uncle Deen yafi na Roshan domin Uncle Deen yanada tsauri sosai,
Sai yace baya cin wannan, ya ce yana buƙatar wancan ya ce baya son wannan haka yake kullum shiyasa saita fara gamawa da Roshan kafin tazo kan na Razhdeen saboda a ɗakinsa tafi ɓata lokaci....

tana kammalawa ta nufi hanyar bedroom ɗinsa tana zuwa nan ma ta sake yin knocking, har saida tayi kusan sau biyar kafin ya amsa mata ya bata umarnin shugowa,
Doka ne indai ta kawo abinci toh saita musu magana kafin ta fita saboda wani sa'in sukan wuni acikin bedroom basu leƙo falo ba balle su san an kawo abinci,
ta turo ƙofar a hankali da sallama a bakinta, ganinsa yasa ƙirjinta bugawa da ƙarfin gaske, dasauri ta sunkuyar da kanta ƙasi tana maida numfashi,
shi kuwa yana tsaye a gaban mirror daga shi sai pant na maza ajikinsa babu riga sai tarin gargasa, alamun wanka zai shiga, ta cikin madubi ya kalleta sannan ya ce "tsayuwar me kike, ki shiga ki haɗa mun ruwan wanka...."

ɗaga masa kai kawai tayi domin kusan kullum ita take haɗa masa, kamar yanda yace haka ta nufi toilet taje ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi-ɗumi saida tasa turaruka kusan kala goma acikin ruwan, tana shirin fitowa sai gashi ya kutso kai ciki, dasauri taja da baya tana jero addu'o'i acikin ranta, tsananin tsoro ne ya bayyana akan fuskarta ganin zugegen mutum a gabanta, du Da du tsayinta a iya saitin ƙirjinsa ta tsaya nan ma bata ƙarasa zuwa ƙirjin ba, wani irin haɗiyar yawu tayi har saida maƙogaronta ya riƙe, dasauri takai hannunta saitin wuyanta tana shafawa jin yanda yake mata ciwo,
ratsa ta gefenta yayi ya nemi guri ya zauna, murya ciki-ciki ya ce "ki zauna ki gyara mun faratu na...."
jiki na ɓari ta ce "toh...."
haka ta jawo farin baho zuwa gabansa mai ɗauke da ruwa aciki, sannan ta ɗauki abun yankan farce ta durƙusa a gabansa,
a hankali ya ɗago da ƙafarsa ya zura cikin ɗan ƙaramin bahon mai ruwan ɗumi, na wankan kuma na gefe guda,
jikinta ne yake ɓari sosai haka hannunta ma da haka takai hannunta cikin ruwan bahon ta kamo ƙafar tana wankewa a ciki kafin a fara gyaran farcen,
Akwai sabulun wanke ƙafa ata gefenta mai ruwa kamar shawer gel inta tatsi sabulun a hannunta saita zoza a ƙafar, ji take kamar bayan kifi take wanke wa tsabar laushin ƙafar, haka ƙafar yake zamewa ya fancala cikin ruwan, haka take kokuwar riƙe ƙafar da zarar ta ɗago da ƙafar saiya zame daga hannunta dake hannunta ma akwai laushi sosai shiyasa ta gagara riƙe ƙafarsa saida akayi haka kusan sau uku,
Idonsa akan screen ɗin wayarsa da yaketa faman pressing ya ce "idan kika sake jefar mun da ƙafa saina canke ki...."

Kamar zata yi kuka ta ce "ƙafar taƙi kamuwa, sulalewa take .."
baice mata komai ba haka ya cigaba da uzurinsa...

Daƙer ta samu ta cabke ƙafar ta ɗora akan cinyarta yanda bazai zame ba,
ta ɗauki abun yankan farce ta fara gyara faratun a hankali gudun karta yanke shi domin abu mai sauƙi ne saboda tsananin laushin ƙafar saika bi a hankali...

cikin nasara ta kammala gyara ƙafar dama, ta kamo na hagun nan ma daƙer ta samu ta wanke kafin ta ɗora ƙafar akan cinya ta fara yanke masa,
tana cikin yanke na babbar yatsa bata ankara ba taga abun yankan ya yanke masa babbar yatsa, nan danan sai jini jajawur, a razane ta zaro manya-manyan idanuwanta waje kamar zasu faɗo, dasauri ta ɗaga kai tana kallonsa cike da mamaki taga ko motsi baiyi ba yanata pressing phone ɗinsa shi baima san an yanke shi bama,
Baiwar ALLAH da sauri tasa rigarta tana goge jinin dake tsirtowa, nan danan gaban kayanta ya ɓaɓɓaci da jini ganin jinin yaƙi tsayuwa yasa ta fara daddanne masa yatsu tana matse jinin da rigar jikinta hawaye kuma haka yake gangaro mata,
Shi kuwa jin yanda take ta danne masa ƙafa yasa shi kallon yanda take a hankali yake motsa lips ɗinsa ya ce "what is going wrong?..."

Ga yanda taketa ɗigo masa ruwan hawaye akan ƙafar, motsa ƙafar yake a hankali yaga rigarta duk ya ɓaci da jini sai a lokacin ya ankara da gurin data yanke shi shati guda still jinin bai daina zuba ba,
a hankali ya zura ƙafar cikin ruwan ɗumin tare da jan dogon tsuka eyes ɗinsa akanta ya ce "tashi ki ban guri ...."

A gaggauce ta tashi gudu-gudu ta buɗe ƙofar toilet ta fice, kamar zata dungura ta nufi falo nan ma ta buɗe tayi ficewarta,
cikin sa'a bata samu kowa a falo ba bayan da sauƙa down stairs haka tayi saurin wucewa room ɗinta,
tana shiga ta fara sauƙe nannauyar numfashi, kafin itama ta nufi toilet, gaba ɗaya kayan jikinta ne ya ɓaci tana mamakin yanda Uncle Deen yake da jini haka a jikinsa.....




🇾 🇦 🇷  ➪ 🇦 🇲 🇦 🇳 🇦 🧘🏻‍♀️🎻🎻🎺

a yawace yawacenta har ta fito cikin gari tana gararamba da ƴar jitar ta a lanƙaye a wuya,
gurin mafaka ta samu wanda koda yaushe tana wajen kuma bata rasa na abincin da zataci ta hanyar kaɗa jitarta,
Wani layin titi ne wanda mabarata suke zama a wajen, da zaran wani mai mota ko mai arziƙi yazo wuce wa su tattashi suna roƙonsu na Annabi,
duk waɗanda suke wajen nakasassu ne daga makafi sai kurmaye sai kuma bebaye sai kutare babu mai cikakken lafiya a gurin,
Sunan titin shine layin nakasassu road,
a waran Ƴar Amana take tazo gurin ta sanadiyar wani mutumi temaka mata yayi ya kawota gurin domin ta samu abinda zata ci yau da kullum, idan sadaka za'a bayar nan za'aje idan ma wani tallafine nan layin za'aje,

Yar Amana tana zaune da zaran taga wani mota yazo zata tashi da gudu taje kusada motar tana kaɗa jitar ta, tsaɓar tsananin daɗin sautin babu mai motar da zai zo ya wuce bai bata kuɗi ba,
wani sa'in kuma ta sanadiyar ta ake bawa duk nakasassun gurin sadaka saboda daɗin sautin jitarta,
da haka take rayuwarta inta tara kuɗi ta siyo abincinta taci da ƙoshi, idan taga wata bata samu kuɗinda zata sai abinci taci ta ƙoshi ba saita raba kuɗinta biyu ta bayar da sauran,
Ƴar Amana bata taɓa samun kuɗi bata raba da wata ba acikin nakasassun, dake duk yawanci tsofaffi ne marasa ƙarfi.......



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 31 to 32



꧁꧂



Around 5 0'clock na yamma acikin ranar Juma'a!
Uncle Deen ne ya sauƙo falo a yayinda ya tarar da Roshan zaune akan kujerar falo yana fuskantar dinning table, a yayinda ita kuma Baiwar ALLAH tanata faman goge dining da farin ƙyalle,
Ji yayi an dafa kafaɗarsa ta baya dasauri ya waiwayo a zabure ganin Razhdeen yasa ya sauƙe nannauyar ajiyar zuciya tareda dafa ƙirjinsa ya ce "kaiii my Man har ka tsoratar dani...."

Uncle Deen yana riƙe da wayar sa ya ce "what are you looking for?...."

murmushi Roshan ya yi sannan ya ce "Ɗawisuwa...." ya ƙarasa maganar dai-dai lokacinda yakai eyes ɗinsa waran da Baiwar ALLAH take...

Uncle Deen cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login