Showing 75001 words to 78000 words out of 117953 words
ya samu lollipop,
ita kuwa 'yar uwa bata san lokacin da ta zagayo hannayenta ta bayansa ba, ta rungumeshi sosai kamar zata mayarshi cikinta,
cikin salo da kwarewa yake fitar da ita daga hayyacinta ta hanyar lips socking, itama lokaci guda ta fara mayar masa da martani a hankali kamar babu rai a jikinta,
suna cikin wannan halin suka ji an turo 'kofar kitchen, a rud'e Baiwar Allah ta kawar da kanta gefe tana 'kokarin kwacewa,
shi kuwa ya ri'ke ta sosai ganin yanda take a rud'e bata cikin hayyacinta, fashewa tayi da matsanancin kuka tana girgiza kai had'in da cewa 'ni ka sake ni dan Allah, na shiga uku ka rufa mun asiri ka sake ni, banasoooo....."
Jawo ta yayi ya rungumeta sosai a jikinsa yana bubbugar bayanta a hankali alamar rarrashi,
Roshan ko waiwaya wa baiyi ba balle yaga wanda ya shugo sai ji yayi ance
"Ya iyaha iyayya! Yaya Yochann me kuceyi haka? wa ce ce ka yunguma ?....."
Ba tareda ya juyo ba ya ce "kinga Mamana jeki waje maza, barkwano ne ya shige mata ido shine nake hure mata, banaso tayi kuka a gabanki ne...."
kafin ya 'karasa maganar ta katse shi da cewa "wayyayi tayyayi bay yadda ba, ai naga cocan bacinta kaceyi, kuma! kuma!! kuma!!! cena gaya wa Ankui Deen da Abba da Mommy....."
tana kaiwa nan ta juya da gudu ko tsaya sauraronsa batayi ba,
yanata 'kiran sunanta "kinga Mamana tsaya mana kiji...."
harta fice abinta...
Baiwar Allah ce ta fizgi kanta daga jikinsa tareda zabga masa mari akan kunci,
tana kuka har idonta yayi jawur tana fad'in "wallahi ka cuce ni, ka zubar mun da mutuncina da kimata acikin gidan nan, yanzu idan Abbah yaji wannan batun ya zanyi da rayuwata, idan Hajiya ta ji shikenam kashina ya bushe......". bata 'karasa ba kuka yaci ranta, da'ker ta iya dakatarwa ta cigaba da cewa " kasa nayi abunda tinda nake a rayuwata ban ta6a aikatawa ba, ata sanadiyarka kasa mutuncina ya zube a idon yarinya 'karama...."
Roshan idonsa a kanta yana ri'ke da kuncinsa ta 6angaren dama yanda ta mare shi, wani irin rad'ad'i yake ji a ransa na ganin hawayen Ammatansa,
lips d'insa na kakkarwa da'ker ya iya furta "kinga Ammata bawai niyata na cutar dake bane, wallahi ina masifar son........."
bai 'karasa iddasa maganarsa ba yaji ta hankad'a shi baya tareda furta "yi mun shuru...." tayi maganar cikin d'aga murya, bata tsaya sauraronsa ba tayi saurin ratsa ta gefensa ta fice daga kitchen, da gudun gaske ta wuce room d'inta tana kuka...
Yar Tiny tana zaune a falo da uniform a jikinta sai faman tura Biscuit take a baki ganin Baiwar Allah ta wuce tana kuka yasa ta fara jinjina kai ta ce "Uhmmm! jaku cani ai, yau kam aciyinku ya conu don wayyayi tayyayi cena gaya wa cu Abba, in in ince Yaya Yocan yana cocan bakin ey aici jidan nan......"
Roshan ne shima ya fito daga kitchen yana goge d'an guntun hawayenda suka gangaro masa, ganin sun had'a ido shi da Yar Tiny yasa ya sau mata murmushi yazo ya zauna kusa da ita yana fad'in "Mamana Biscuits ake ci ne?....."
ta juyo tana kallonsa ta ce "ey Bicci nace ci ...."
Ya ce "kuma baki cire uniform ba?..."
kai kawai ta d'aga masa ba tareda ta ce komai ba,
ya kuma cewa "Mamana kina sona?...."
da sauri ta had'a masa kai alamar ey!
ya jinjina kai sannan ya ce "toh idan kuwa kina sona da gaske banason kowa yaji wannan maganar, idan kuwa kika gaya wa mutum d'aya to kuwa zan sha poison na mutu, bazaki 'kara ganina ba har abada, kin dai san duk wanda ya mutu baya dawowa koh?...."
Fashewa tayi da kuka ta rungumi Roshan tana fad'in "bana co ka mucu Yaya Yocan, wayyayi Tayyayi bajan jayawa kowa ba...."
Ya d'ago da kanta yana fad'in "kin dai san kyan Alkawari cikawa koh?...."
tana kuka ta ce "nayi maca aikawayi Yaya Yocan, bajan jayawa kowa ba......"
Ya ce "shikenam Mamana daina kukan maza, inasonki Mamana...."
itama ta ce "ina conka Yaya Yocan nima...."
Ya ce "ok bari naje na kwanta nayi bacci koh...."
kad'a masa kai kawai tayi ta cigaba da cin Biscuit d'inta.....
Haurawa upstairs yayi yana tunanin Baiwar Allah, sam baiji dad'in abinda ya yi mata, zuciyarsa hargutsuwa take kamar zai fad'i tsabar hajijiyan da yake shirin d'ibarsa, daker ya samu damar 'karasa isa part d'insa, yana shiga falonsa kai tsaye bedroom ya wuce yana tangal-tangal ya fad'a saman katafaren gadonsa.....
Itama Baiwar Allah tana kwance akan gadonta ba abunda take sai kuka, sai a yanzu take nadamar marin Roshan, cikin takaici take dukan kan gadon tana kuka mai cin rai,
wani irin matsanancin ciwon kai ne yake damunta har idonta yana kokarin rufewa, ganin tana kokarin sumewa yasa ta tashi a hargitse ta nufi toilet, tana shiga ta kunna shower a kanta, ruwa mai sanyi ne yake ratsa duk ilahirin jikinta tin daga kan sumar kanta, ta kunna ruwan sanyi ne sakamakon zafin da jikinta ya d'au....
tin daga cikin toilet ta d'auro alwala ta fito, nufan wardrobe tayi ta zaro doguwar riga marar kauri mai hannun singlet ta zura sannan ta sanya hijab har 'kasi ta shimfid'a sallaya tareda tsaida sallah....
Around 8:00 O'clock mutanen gidan suka dawo, saida suka zagaya wuraren shakatawa kafin suka dawo gida, a falo suka tarar da Yar Tiny tana kwance saman doguwar kujera sai sharar bacci take ga Biscuit yanda ta dun'kule kamar wanda za'a kwace,
Abbah ne ya ce "ha'a Auta mutanen rigima har akayi bacci....."
Ummy kuma nufar d'akin Baiwar Allah tayi ba jumawa ta fito tana murmushi ta ce "itama Aunty Baiwar Allah bacci take akan sallayarta...."
Mommy fuska a murtu'ke ta ce "shine ita tana can room d'inta tana shan bacci ta bar mun yarinya a falo ga sanyi A.C kalan mura ya kama ta...."
Abbah ya ce "haba Khadija meye abun fad'a anan? itama bacci ne ya d'auketa kina ji....."
Hajia Kilishi kamar zatayi kuka ta ce "ai daman baka ta6a goya mun baya ba, saboda ka gaji da zama dani...."
tana kaiwa nan ta haura saman upstairs tana gunaguni...
Abbah bai ce komai ba ya kalli Ummy ya ce "uwar masu gida d'auketa kije ki cire mata uniform saiki kwantar da ita...."
Ummy ta ce "toh Abbah...."
tasa hannu ta d'auki Yar Tiny suka haura upstairs dake tare suke kwana, ta juyo ta ce "Abbah saida safe don nima ba fitowa zan 'karayi ba...."
Abbah da murmushi a fuskarsa ya ce "toh Uwar masu gida Allah ya tashe mu lafiya...."
Minal kuwa tin shugowarsu ta haura abinda bata tsaya jin ta bakin kowa ba...
Suma Pinky da Rukky sallama sukayi wa Abbah suka haura saman room dinsu....
Abbah zama yayi a falo shi kad'ai yana fuskantar plasma, so yake yaga dawowar Razhdeen domin an sanar masa cewa ya fita tin da rana kuma gashi yanzu har dare yayi bai dawo ba, sannan ya'ki yin picking calling .....
Misalin karfe 10:30 sai ga Razhdeen ya shigo falo, tarar da Abbah yayi yana zaune sai bacci yake sha,
Da kamar zai wuce part d'insa har ya soma haura upstairs sai ya juyo yana kallon Abbansa, bazai iya barinsa a haka ba yaje ya zaune a gefen Abbah yana 'kiran sunansa cikin sassanyar murya
"Dad! Daddy!! Daddd!!!....."
A rud'e Abbah ya bud'e idonsa yana fad'in "ina kaje Razhdeen? banason yawon daren nan......"
Uncle Deen kallon Abbah yake cike da mamaki,
Na farko daga tashinsa a bacci yake wannan sumbatun, na biyu kuma shi ba wani karamin yaro bane da har za'a damu in bai dawo gida ba....
Abbah yasa hannu yana shafar fuskarsa yana hamma tareda yin hamdala, daga bisani ya juyo yana kallon Uncle Deen cikin nuna damuwa ya ce "Razhdeen ina kaje?...."
Uncle Deen ya ce "Dad nifah am not a small child...."
Abbah ya ce "yes i known that but you support to tell me anyway u want go...."
Uncle Deen ganin yanda Abbah yake nuna damuwarsa akansa ya ce "okay i will take care don't worry...."
ya karasa maganar tareda mi'kewa tsaye yana kokarin tafiya....
Shima Abbah tashi yayi ya haura part d'insa yana jan 'kafa da'ker tsabar tsananin baccin da yake ji......
Misalin karfe 1 saura Uncle Deen yana ta kai kawo a falonsa, yana tunanin yarinyar nan mai busa sarewa tambayoyine cike acikin zuciyarsa
yana maganar zuci cewar "idan har yarinyar nan mutum ce nayi alkawari saina nemota, kuma saina kasheta domin ba karamin wahalar da kwakwkwalwata take ba, kullum ina shiga matsala saboda ita because of why? i will teach her a lesson,
Idan kuma ba mutum bace!......."
ya dakatar da maganar zucin da yake yi tareda hura iskar bakinsa.......
Dai-dai lokacin da Baiwar Allah ta turo 'kofar d'akin da sallama a bakinta tana d'auke da tray na kuloli a hannunta....
Kallo d'aya yayi mata ya kawar da kansa gefe yana cin boom,
ita kuwa wuce tayi ta nufi dinning taje tana jejjera masa kayan abinci,
zuwa tayi tasa hannu zata buɗe ƙofa ta fita sakamakon daren da yayi har ƙarfe 1:00 yanzu, taji yayi mata magana
tsayawa tayi tareda juyowa tana fuskantar sa amma saidai tana kallon ƙasin carpet ne domin bayaso a cika kallonsa,
kamar bazaiyi magana ba daƙer ya ce "tinda meya hanaki kawo mun abinci?...."
cikin sassanyar murya ta ce "kayi haƙuri bansan dawowarka bane ...."
juyowa yayi yana kallonsa ya ce "tin ƙarfe 10 na dawo amma dubi clock 1 O'clock are you stupid?
idan kika sake mun jinkirin kawo food ranki zai ɓaci...."
Dasauri ta ɗaga masa kai tare da faɗin "insha ALLAHU baza'a ƙara ba...."
"Better for you, saiki jira idan na kammala saiki tattara shirginki ki bar mun room...."
a cewar Boss....
zuwa yayi ya zauna a dinning itama zuwa tayi ta fara zuzzuba masa,
tana kammalawa taja ta tsaya tana jiran gamawarsa,
Cikin lokaci ƙanƙani kuwa ta zabura tare da zaro manya-manyan idanuwanta, da sauri takai ƙwayar idonta kan Uncle Deen taga yana shirin kai one spoon cikin bakinsa, a gaggauce tayi saurin riƙe masa hannu wanda itama kanta bata san tayi hakan ba,
hannunta na riƙe sa hannunsa wanda yake riƙe da cokalin abinci,
Dalilin yin hakan a lokacin da bacci ya ɗauketa akan sallaya bata tashi farfaɗowa ba sai yanzu, a gigice ta tashi saboda ta tuna bata kawo wa Uncle Deen abinci ba, tana fita falo kai tsaye kitchen ta nufa, tana shiga ta ɗauki kulolin abincinsa wanda ta ware masa gefe guda ta kai masa,
Gaba ɗaya ta manta ashe abincin yayi gishirin da bazai ciyu ba,
a niyarta daman ta sake masa girki ne sai kuma mantuwa ya biyo baya...
jikinta ne ya hau ɓari ganin hannunta yana riƙe dana Uncle Deen,
Wani irin kallo ya watsa matsa mata bata san lokacin da ta sake masa hannu taja da baya ba, nan danan hawaye har ya wanke mata fuska.....
cikin ɓacin rai ya ce "wani irin shashanci ne haka? Are you a madness?...."
Dasauri take girgiza masa kai!
ya ce "okay ina kin mayar Ni abokin wasan ki koh? Kneel down for here...."
zuwa tayi ta durƙusa a yanda ya nuna mata tana kuka, ta haɗa hannayenta sama tana kallonsa ta wutsiryar ido taga ta yanda zai fara cin abincin nan...
hannu yakai kan spoon yana haɗa miya