Showing 69001 words to 72000 words out of 117953 words
rashin fahimtar abinda yake nufi yasa shi kallon plasman yaga ana showing namomin halittu kamar su kaji da talotalo har da su Ɗawisai, a tunaninsa kallo yake ya jinjina kai tare da faɗin "okay amma eyes ɗinka ba'a kan plasman suke ba...."
jin Roshan yayi masa shuru kuma sai sakin murmushi yake ya tsayar da idonsa guri ɗaya,
Razhdeen ne ya kalli waran da yake kalla, ganin Baiwar ALLAH tanata goge goge yasa shi ƙara kallon Roshan, ya lura kamar yarinyar yake kallo, girgiza kai Uncle Deen ya yi yana motsa lips ɗinsa a hankali ya ce "you are crazy...."
ya yi juyawarsa zai fita domin akwai waranda yake son zuwa,
buɗe get ɗin compound yayi ya tarar an kawo masa motar da zai shiga, ta ciki akwai wani soja wanda ya kasance shine mai driving ɗinsa, Uncle Deen fuska a ɗaure ya ce "yau Ni kaɗai nake son fita...."
Sojan ne ya fito yana faɗin "okay Sir..."
Bayan ya fito ya shiga yana murɗa key ɗin motar, a hankali ya fara jan motar har saida yaje bakin gate na biyun ƙarshe da haka ko wani gate akwai sojoji haka akaita buɗe masa ana sara masa tare da bashi gaisuwa har ya fice daga gidan gaba ɗaya,
yana fita ya ɗau hanya a ɗari nan danan ya ɓace a layin unguwar ko bayan motar ba'a gani,
akwai waran da Uncle Deen zai tafi hakan yasa ya buƙaci tafiyar shi kaɗai kuma babu wanda yasan inda zai je,
tafiya yake mai nisan gaske har saida ya fara barin gari,
a bakin titi ya tsayar da motarsa yana kallon cikin dajin da farkon zuwansa anan yake jin sautin da ya saba ji acikin mafarkinsa,
꧁𓇽꧂
Baiwar ALLAH tana kitchen tana yankan naman kaji manya-manyan irin kajin turawan nan,
ji tayi anyi sallama cikin sassanyar murya batare da ta waiwayo ba ta amsa sallamar domin tasan Roshan ne,
a wannan lokacin yazo ne da niyar yi mata magana saida yaje dab da ita ya tsaya idonsa akan kayan chickens,
ya ce "bakya gajiya da aiki ne?..."
girgiza kai tayi idonta akan abun yankanta ta ce "daman ana gajiya da aiki ne?..."
kallonta ya yi fuska ɗauke da murmushi ya ce "of course indai mutum ba robot bane ba ..."
ɗan murmushi ta saki sannan ta ce "toh waya sani ko robot ɗin ce...."
ya ce "ahh indai robot ce ke zaki yi aikin da yafi haka ...."
murmushi tayi ba tare da ta ce komai ba,
ya kuma cewa "kina buƙatar tayi ne?..."
girgiza kai tayi ta ce "a'ah Nagode..."
ya ce "gaskiya Ni kuma Inaso na tayaki ya za'ayi Kenam?..."
ta juyo tana kallonsa da dara-daran idanuwanta ta ce "Babban mutum baya aiki...."
ya ce "Uhmmm! haka kika ce amma Ni duk a ayyukan gida babu Abunda ban iyaba hatta girke - girke kala kala saidai na koya miki...."
Jinjina kai Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "Okay yau kai zakayi mana ferfesun kajin nan, Ni kuma bari na ɗora rice...."
bata ankara ba taji yana tapa hannayensa cikin nuna farin ciki yake faɗin "wow am so glad, dakyau haka nake so, daga yau Ni zan rinƙa taya ki aikin girke-girke....."
Kallonsa tayi da murmushi kan fuskarta ta ce "Dakyau...."
ta miƙo masa abun hura Gas ta ce "amshi ka hura wuta ga pot ɗin da zakayi using dashi sannan ga can kayan spices komai da komai....."
karɓan abun ya yi yana jujjuya shi yasan abun amma kuma bai san ta yanda ake using dashi ba,
gudun kar ya dizgar da kansa yasa yakai abun dab da Gas ɗin yana manna abun ajiki ko wuta zai kawo,
jin ta tintsire da dariya yasa shi juyowa yana kallonta, shima murmushi yake saki ganin yanda Dariyar yake yi mata kyau, tinda ya dawo bai taɓa ganinta tayi dariya ba sai yau, a hankali ya furta " *WOW* beautiful girl..." ba tareda ta ji ba ......
Saida tayi dariyarta mai isarwa sannan ta karɓi abun hannunsa tana faɗin "kawo nan ka gani, a wannan ɓangaren ka samu 0 mark sauran na gaba...."
ta murza yanda abun yake kamar torch light sai ga wuta yana burtsowa tasa hannu ta kunna Gas ɗin sannan ta kunna,
ta kalle shi taga idonsa a kanta ko ƙibtawa bayayi ta katse shi da cewa "ehen ɗora pot ɗin...."
yayi firgit kamar mai yin tunani yayi saurin ɗora pot a ruɗe yake faɗin "ina oil..."
Murmushi tayi sannan ta ce "saika fara tafasa tumatur saboda tsamin jikinta...."
ya ɗauki tumatur kamar yanda ta ce hakan yayi ya juye a cikin pot ɗin,
yana kallon cikin tukunyar ya ce "ai ya tafasa a sauƙe?..."
dariya tayi tana dafe da goshinta ta ɗago tana cewa "sai ruwan jikin tumatur ya tsotse tukun ka sauƙe saika soya oil ɗinka....
Ɗan turo lips ɗinsa yayi sannan ya ce "ai baki gaya mun haka ba .."
zaro ido tayi tareda faɗin. "kai daka ce ka iyaaa?...."
ɗan buɗe eyes ɗinsa ya yi yace "hakane fa na iya ashe ...."
A wannan lokacin haka suka wuni a kitchen suna hira tare da yin Ayyukan su cikin farin cikin kasancewa da juna,
Baiwar ALLAH ba ƙaramin nishaɗartuwa tayi ba kasancewarta da Roshan domin mutumin ya iya mu'amala da mutane kuma yanada saurin shiga rai da shaƙuwa,
a wannan ɗan haɗuwarsu har sun shaƙu sosai kamar wanda sukayi shekara suna tare,
suna cikin hirar su Roshan ya ce "Ni in tambayeki mana idan ba damuwa...."
Baiwar ALLAH tana satar kallonsa ta ce "ina jinka...."
ya ce "Meye asalin sunanki?...."
Saida taji gabanta ya yanke lokaci guda ta sauya daga yanayin farin cikin da take, kai a sunkuye cikin sassanyar murya ta ce "Nima bansan sunana ba ...."
Roshan yana cikin juya miyan kajin da yake yi yaji ta bashi wannan amsar kamar bata cikin farin ciki, jiki ba ƙwari ya cire ludarin miyan ya ajiye a gefe sannan ya ƙarasa yanda take tsaye tana zuba shinkafar data dafa a cikin kuloli,
yana fuskantar ta yasa hannu ya tallafo haɓarta sannan ya juyo da ita saitinsa suna fuskantar juna kamar zaiyi kuka
ya ce "sorry na ɓata miki rai koh?
banso hakan ta faru ba, inda nasan tambayar sunanki zai jawo ɓacin rai da banyi gangancin yin haka ba, kiyi haƙuri *AMMATA NAH* ....."
tasau murmushi haɗi da bugar ƙirjinsa ta ce "it's okay, ko a labarinka ban taɓa jin ka ɓatawa wani rai ba, saboda haka nima abu ne mai wuya naji ɓacin rai akan ka *YAYANAH*....."
Da haka suka cigaba da hirarsu har suka kammala girkinsu tsab, ferfesun miyan kaji dai Roshan ne ya yi girkinsa ita kuma tayi sauran girke-girke domin ba girki ɗaya ake yi ba....
A wannan ranar tare suka jera kayan abinci akan dinning suka shirya komai tsab tsab...
Ummy ce ta sauƙo daga upstairs tana murtsuka ido alamun daga bacci ta tashi bugu da ƙari kuma taga Yaya Roshan shi da Baiwar ALLAH suna shirya kayan abinci tare suna ƴar hirarsu mai armashi,
Cike da mamaki ta ƙaraso wajen tare da faɗin "my love wai kaine yau da Aunty Baiwar ALLAH?...."
yana ɗauke da murmushi ya ce "very surprised koh?....."
Dasauri ta jinjina kai ta ce "yeah...."
Itama Baiwar ALLAH murmushi tayi tare da faɗin "Meye abun mamaki toh?...."
Ummy ta ce "Uhmmm! bazaki gane bane but there's something going on, yau Ranar farin cikinsa ne kasancewarsa dake, damar da yake nema tintini Kenam sai yau ya samu....."
ta ƙarasa maganar tana kanne masa ido ɗaya ayayin da shi kuma ya sake baki yana binta da kallo, yanda ta dizgashi a gabanta,
girgiza kai yayi sannan yace "toh Sarkin surutu anji...."
Dariya tayi tare da kai idonta kan Baiwar ALLAH wacce tayi shuru tana sauraronsu Ummy ta ce "wayyo yau bacci nayi shiyasa banzo na tayaki aiki ba, sai yanzu na tashi ayi mun afuwa..."
Roshan ya ce "da bakizo kin tayata ba ai Ni na tayata ga ferfesun chicken dana haɗa sai ƙamshi yake...."
Ummy ɗan turo lips ɗinta tayi ta ce "yoo Yaya Roshan ai wani ne zai yabi girkinka ba kai da kanka ba,
waima da gaske kai kayi mana ferfesu? cabbb zamu ci ciki...."
Ɗan harararta yayi ya ce "bangane zaku ci ciki ba ..."
Ummy ta kalli Baiwar ALLAH sannan ta kuma cewa "haba Aunty Baiwar ALLAH ya za'ayi ki bashi yin girki alhalin ba iyawa yayi ba, matan gidan ma yaushe suka iya girki balle shi yana namiji, ai gwara ki bashi markaɗen tumatur dasu tattasai da kuma wanke-wanke....."
ta ƙarasa tana kanne masa ido cike da zolaya,
shi kuwa yana tsaye ya goya hannayensa akan ƙirji ya zuba mata ido, gaba ɗaya ya rasa abun cewa!
Ummy ganin haka yasa ta cewa "Wayyo na fara ganin fusata acikin ƙwayar eyes ɗinsa bari na fece..." ta ƙarasa maganar dai-dai lokacinda ta juya zata bar wajen,
Baiwar ALLAH tayi saurin cemata "Kinga kafin ki fece ɗan shiga ki ƙirawo su kice an kammala girkin...."
Ummy ta ce "okay don't worry 👌...."
Roshan neman guri yayi ya zauna sannan ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "Ammata yau a kusa dani zaki zauna saboda haka ga kujera zauna...."
ya nuna mata kujerar gefensa, ba musu ta zauna tana jiran fitowar ƴan gidan kafin ta fara zuzzubawa,
ai kuwa ba jumawa sai gasu sun fara fitowa ɗaya bayan ɗaya domin ba ƙaramin yunwa suke ji ba, Pinky da Rukky ne suka fara zuwa duk suka zazzauna tare da cewa "gud Afternoon Yaya Roshan...."
ya amsa musu cikin kulawa, saiga Minal itama ta fito tana ɗaure da fuska daman ita koda yaushe a haka take kamar wanda ake aiko mata saƙon mutuwa, idan kanason ganin fararen haƙwaran Minal toh ka zauna kusa da ita a yayinda take waya da Marshall Mohandas,
zama tayi tana motsi da lips ɗinta ciki ciki ta ce "well done Yaya Roshan...."
Itama amsa mata yayi yana tsokananta da cewar "Amaryar Marshall ba son raini...."
saiga Ummy itama ta sauƙo daga part ɗin su Abbah ta sanar musu cewar an kammala girki....
zuwa tayi ta zauna a gefen Roshan suka saka shi a tsakiya ita da Baiwar ALLAH,
Pinky abun ya ɗaure mata kai cike da mamaki ta ce "Yaya Roshan naga kai kam kai maka abincinka ake can room ɗinka, meyasa yau ɗin kuma?...."
murmushi yayi tare da gyara farin glass ɗin idonsa ya ce "yau ɗin tare zanyi lunch da Ammata nah...."
zaro ido Pinky tayi ta ce "wacece kuma Ammatan ka?..."
Rukky ce ta tsoma baki da cewar "mu mana, su waye Ammatan inba mu ba, tare zamu ci...."
Girgiza kai yayi yana murmushi domin shi yasan abinda yake nufi.....
Su Abbah ne suma suka sauƙo, duk zama sukayi dai-dai lokacin da Baiwar ALLAH ta miƙe tana ƙoƙarin zuzzubawa kowa,
a wannan zaman Ƴar Tiny bata nan tana school, tinda safe idan ta tafi sai yamma take dawowa misalin ƙarfe 6 saboda harda islamiyya take haɗawa.....
꧁꧂
Uncle Deen wuni yayi a wannan dajin yana neman abun harinsa wato wacce take damunsa da sautin sarewa, acikin bacci har a ko ina, abun ya bashi mamaki jin har zuwa yanzu bai ji sautin na tashi ba kuma a waran kwanaki yaji...