Showing 30001 words to 33000 words out of 117953 words

Chapter 11 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4731

saman kafaɗarsa amma tana ƙare ko ina da kallo amma bata bari ta haɗa ido da soja ko ɗaya ba, gani tayi an buɗe musu wani makeken gate wanda ya tsaru mai tsayin gaske, ginin gidan gaba ɗaya a zagaye yake da tiles, suna shiga ciki wasu sojoji ta ƙara gani su biyar sun ƙame guri ɗaya ko motsi babu, ga jerukan motoci kala-kala ko wanne da design ɗinsa da kuma kamfaninsa sun kai guda ashirin domin duk ƴan gidan babu wanda bashida mota duk ba'a barinsu suyi driving saidai security yakaisu duk inda zasu je, ga wasu irin flowowi na alhurma masu kyan gaske, a cikin motocin ne ya zaɓi guda ɗaya ya saka Baiwar ALLAH a seat ɗin baya sannan shima ya shiga, domin babu yanda zaka iya shiga gidan ba tare da mota ba, saida suka ƙarayin tafiya mai nisa kuma du wasu security suka ƙara buɗe musu wani gate na biyu, suna shiga taga wani makeken swimming pool a tsakiyar filin gidan wanda a tsakiyar ruwan wani abu kamar flower ne yake bada feshin ruwa sai ruwan yayi sama kafin ya zubo a cikin S-pool amma sai dai wannan swimming pool ɗin bana wanka bane just anyi shi ne don ado domin flowers ne a ciki, saida suka zagaya wannan S-pool tukun zaka iya bi ta ɓangaren dama sannan zaka iya zagayawa ta ɓangaren hagun domin a tsakiya yake, ta order side wani makeken filin ball ne wanda yake can nesa dasu, nan ma suka sake miƙar hanya,
ata gaba aka sake buɗe musu wani gate na uku kuma du, Baiwar ALLAH zaro ido waje tayi ganin tafiya taƙi ƙarewa, saita fara tunanin kodai gidan masu satan mutane ne, nan danan gumi ya fara keto mata, wannan part kam basu yi wata tafiya mai nisa ba taga anyi parking a waran ajiye motar, cikin zafin nama yasa ƙafa ya ture murfin motar sannan ya zagayo ya ɗauketa saman kafaɗarsa, kai tsaye cikin compound suka nufa anan ne part uku ya kasu, part ɗin da yake ɓangaren dama suka nufa nan ne babban falon General wajen da yake ajiye manyan baƙinsa, part ɗin da yake tsakiya kuma babban part ne wanda ɗakunan kowa yake ciki idan ka shiga ciki yayi jirgi ya sauƙa a iya falon kawai tsabar girmansa,
Baiwar ALLAH kallon gidan take a baibai domin tsarin gidan ya fara wuce misali, ganin kanta take kamar ba'a Nigeria take ba, ga wani irin sanyi mai daɗin gaske yanda yake ratsa sansanin jikinta, gidan ne ta ko wane ɓangare ansa A.C mai bada sanyin gaske, da cemerori ga flowowi masu bada nasu sanyi suma, tana cikin wannan yanayin bata san lokacin da aka direta ƙasi ba, saita para tangal-tangal zata faɗi ƙasi domin ji take kamar zata nitse ƙasi ne tsabar tudun carpet da laushisa, ko ciwon ƙafar ma ta daina jinsa tsabar yanayin jin daɗin data tsinci kanta a ciki, weather falon Chief of Army's mAh ya isheta jin daɗin rayuwa, ga wani irin ƙamshin da yake badawa, falon ta tsaya kallo gaba ɗaya ta rikice tsabar tsaruwar falon,
kafin General ya fito daga cikin order room ɗin na falon domin nan ne bedroom ɗinsa idan yanason hutawa, Sojan yana mata magana akan ta zauna amma sam bata jin mai yake faɗi tsabar hankalinta yana kan tsaruwar falon, cike da takaici yasa ƙafa ya girbe mata ƙafafu sai yaraf ta faɗi a ƙasan carpet, a nan ne ta dawo cikin hayyacinta, faɗuwar da tayi a ƙasan carpet mai makon taji ciwo saima ƙara miƙewa da tayi ta baje tayi shame-shame tana lumshe ido a hankali, tama manta ina suka zo, sanyin falon ne da ƙamshinsa duk ya ruɗe ta,
wani irin harara sojan ya wurga mata amma ko kallon yanda yake batayi ba, yana shirin yi mata mugunta yaso ya taka ruwan cikinta saiga General ya fito yana sanye da jallabiya fara har ƙasi, yana ganin Baiwar ALLAH a kwance bai wani damu ba saima murmushin da ya sake tare da zama yana gyaran murya, jin anyi gyaran murya yasa ta firgita ta tashi a zabure tana kallace-kallace, daƙer ta iya tsayar da idonta akan General ta ƙura masa ido kamar wanda ta sanshi, a cikin zuciyarta tana raya abubuwa da dama a cikin ranta take faɗin "wannan kamar na sanshi, wasu lokuta yana zuwa gidan marayu, tabbas shine domin daman soja ne...."

General maida idonsa yayi kan sojan yace "Tall man ya akayi ne?..."

Anan Tall man ya kwashe Abinda ya faru ya sanar masa amma bai sanar masa zaluncin da sukayi mata ba, ya ƙarasa maganar da cewa "daman mun riƙeta ne akan saika dawo tukun, duk hukuncin da ka yanke shi zamu aiwatar...."


General ya jinjina kai ya maida idonsa kan Baiwar ALLAH.......



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (11 to 12)



꧁꧂



Ƙura mata ido yayi kamar me tunanin wani abu, ita ko bata san yanayi ba sai kallace-kallacen da take, daga bisani ya ce "meye sunan ki?..."
kamar daga sama taji Muryar ya ɗuro mata kan dodon kunne a firgice tace "amm Baiwar ALLAH..."
cike da mamaki yace "ke ki gaya mun sunan ki saiki tsaya kina mun shirme, what do you means?..."
kamar zatayi kuka ta kuma cewa "wallahi tallahi bansan sunana ba, haka na tashi naji ana ƙirana da Baiwar ALLAH..."

Tallman dake tsaye ganin yarinyar tana shirin rainawa Ogansu hankali yasa yayi saurin kai mata ƙafa a saitin baki, ya yinƙuro Kenam General yayi saurin ɗaga masa hannu alamar ya dakata, cike da mamaki General yace "daga ina kike? sannan me kika zo yi nan area?..."

Baiwar ALLAH kuka ta soma yi ta kwashe komai ta sanar masa, bata ɓoye masa komai ba,
Jinjina kai General yayi sannan yace "Kenam kece yarinyar da Hajia Aliya ta bari a hospital?..."
dasauri Baiwar ALLAH ta ɗaga masa kai cike da fargaba,

Jinjina kai General yayi sannan yace "ina sane dake daman, kafin rasuwar Hajia Aliya ta bani duk wani information ki, ta ce kina cikin damuwa zaman gidan marayu bazaiyu ba domin akwana a tashi wata rana zaki wayi gari bakya doron duniya, hakan yasa na yanke shawarar idan an sallame ku a hospital saita kawo ki nan gidana ki cigaba da zama kafin Allah yasa a samu iyayenki, daga baya nake jin labarin mutuwar Aliya, naje har hospital domin duboki amma bakya nan kin tafi,
Yanzu dai tinda Allah yasa kin kawo kanki yanda zaki zauna ki cigaba da rayuwarki cikin ƴanci Alhamdulillah...."

Baiwar ALLAH farin ciki kamar bazata mutum ba, sai murmushi take ta zabgawa ganin a gidan da zata zauna, amma lokaci guda data tuno da Ƴar Amana sai taji kamar ta rausa ihu, babu yanda ta iya haka take danne zuciyarta domin bata son General ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita...

General ne yace mata "tashi maza na kaiki ciki yanda mutanen gidan suke koh?..."
Dasauri ta miƙe tana ɗingishi daƙer take jan ƙafar, General ganin haka yasa shi cewa "what! meya faru dake haka?..."
Girgiza masa kai tayi tare da faɗin "babu komai" idonta akan sojan dake tsaye yana jinsu,
General idonsa yakai kan sojan cikin ɓacin rai yace "ku baku san mace bace? daga ganin mutum baku san dame yazo ba shin da Alkhairi ne ko da sharri baku sani ba, just kun fara ɗaukar hukunci akai, wani irin abu ne haka? ku kiyaye saurin ɗaukar hukunci banaso...."

Sojan dake tsaye yana kallon gabansa ya ce "Yes Sir, Insha Allah zamu kiyaye..." daga baya General ya ɗaga masa hannu akan ya wuce, Bayan fitar sa itama Baiwar ALLAH fitowa tayi tare da shi General, kai tsaye compound dazai sadasu da cikin babban falon na gidan suka shige,

General ganin yanda Baiwar ALLAH take ta kallace-kallace yasa ya riƙo hannunta suka ƙarisa shigewa, a cikin babban fallon suka tarar da kowa na gidan duk sun hallaru dake a yau Aunty Yolash dake Bauchi itama tazo ta abunda ya kawota shine ta'aziyyar Hajia Aliya,

Hajiya Kilishi ce zaune itama da zankaɗa-zankaɗan ƴan matan gidan wato yaran Hajia Kilishi dake duk yaranta mata ne su biyar, Babbar cikinsu wato Minal tana kwance akan sofa 3 seater ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana sanye da gajeren jeans wanda ya tsaya mata a iya gwiwa sai faman daddanna wayar hannunta take mai ƙirar iphone 15 sai tauna ciwgum take tana ƙararass, asalin ƴar girman kai kenam ga iya ɗaukar fashion, bata hulɗa da ƙananun mutane sai manya-manyan ƴaƴan masu kuɗi kamar yanda take ƴar Babban mutum, ta tsani ganin talaka marar class a rayuwarta, yanzu tanada shekara 25 ta kammala Degree ɗinta a ƙasar England.....

Sai waɗanda suka biyo bayanta wato
Pinky and Ruky ƴan biyu ne duk mata Hajia Kilishi ta haifa, waɗannan yaran sune masifaffun gidan, banda wulaƙanta mutum ba abinda suka iya, ga gadara da isa da burga, Pinky and Ruky their are too stubbornness, yaran masu kuɗi kenam jiki duk madara, su biyu suna kwance suma akan 5 seater wannan ta ɗorawa wannan ƙafa wannan ma haka, sai faman danna wayoyin hannayensu suke maka-maka, yanzu suke da shekara 20 cif cif suna karatun Degree ne a ƙasar London.....

Sai gambonsu wato Ummy dake zaune a 1 seater ta nannaɗe ƙafafuwa ta sanya farin glass akan dararan idanuwanta kana ganin glass ɗin kasan na medical ne mai tsadar gaske, dake tanada matsalar ido, tana riƙe da ƙaramin littafin Alkur'ani mai girma baki da motsi a hankali take karantawa acikin zuciyarta domin yayunta sun tsawatar mata akan cewa kada ta toshe musu kunne da karatunta, Ummy uwar masu gida Kenam, full name Maryam mai sunan mahaifiyarsu General da mai martaba sarkin ƙasar Jidda da kuma Aunty Yolash, Ummy batada matsala ko kaɗan Sarkin haƙuri, bata fiye yin magana ba, ta kammala Secondary school anan school of Nursing, ana son turata ƙasar waje akan taje ta cigaba, tace ita bata son zuwa ƙasar waje tafison tayi school anan Nigeria dalilin da yasa bata cigaba ba Kenam saboda mahaifiyarta Hajia Kilishi tace nan duniya duk ƴaƴanta babu wacce zata cigaba da school a nan Nigeria tace saidai yarinyar tabar karatun kwata-kwata indai a Nigeria zata yi,
shiyasa Hajia Kilishi bata sa Ummy a ranta ba saboda ita kaɗai ce bata ɗauko halinta na rashin mutunci ba,
yanzu Ummy uwar masu gida tanada shekara 17 a duniya amma sai halin dattawa......

Daga kan Ummy Hajia Kilishi ta dakatar da haihuwa domin a cewar ta yawan haihuwa yana lalata mace, bata son tara yara kamar ɓeraye a gida, waɗannan huɗun sun isheta Minal, da twins Pinky and Ruky sai Ummy, bayan nan ta ɗau shekaru bata sake haihuwa ba sai daga baya ta samu cikin Ƴar Tiny ba'a son ranta ba, bata san ya akayi ta samu cikin ba domin ba ƙaramin planning tayi ba, anan sun samu matsala sosai da General mijinta akan saita zubar da cikin, shi kuwa yace saidai ya sake ta, haka ta haƙura babu yanda ta iya harta haifi Ƴar Tiny, tasha wahala sosai Saida aka mata Operation, ganin mace ta ƙara haifa yasa tace a cire mata mahaifa saboda ta fidda rai akan samun yaro namiji gashi yara sun taru mata, tayi kuka sosai duk yaranta babu namiji...
Ƴar Tiny yanzu shekarar ta 5, fitinanniyar yarinya ga rashin jin magana da yawan ɓarna,
Ita kaɗai ce a tsakiyar falo tana zaune akan carpet sai wasa da ƴar tsanarta take tana mata kitso,

Aunty Yolash itama tana zaune akan kujera 2 seater idonta akan wayar hannunta tana jiran shigowar General tanaso tayi masa sallama zata koma Bauchi,
A yayinda ita kuma Hajia Kilishi take kan 3 seater itama tana press ɗin wayar ta tana tauna ciwgum, inta ɗago saita harari Aunty Yolash domin basa jituwa sosai akwai ƴar tsama a tsakaninsu,
Ita Aunty Yolash a rayuwarta ta tsani mutum ya cika wulaƙanta ɗan Adam don yanada ƙarfin iko, shiyasa Aunty Yolash bata shiri da Hajia Kilishi domin halinta Kenam wulaƙanci da girman kai gashi harta koyawa yaranta banda Ummy wacce ta fita daban a cikinsu sai Tiny wacce ita yarinya ce ba'a san wata kala bace ita....


Suna cikin wannan halin saiga General ya shugo yana riƙe da hannun Baiwar ALLAH da sallama a bakinsa,
Baiwar ALLAH gaba ɗaya tayi bususu da ita ga ƙafa ba takalmi ga tayi wani irin datti har farinta yaɗan disashe,
Aunty Yolash ce da Ummy kawai suka ɗago tare da amsa masa sallama a yayinda ita kuma Hajia Kilishi da sauran yaran ko ɗagowa basuyi ba domin sun san da cewar Abbansu ne ba wai wani ba,
Ƴar Tiny ce ta tashi tana faɗin "Abbah Oyoyo! Abba ina abinda nace a siyo mun, ina alƙawarinaaa...."
Abbah yace "kiyi haƙuri Auta ki bari sai kowa yayi bacci da daddare zan baki kinji koh...."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login