Showing 93001 words to 96000 words out of 117953 words

Chapter 32 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4753

dasu a baya, haka suka nufi hospital....

A ranar a hospital suka kwana Abba ne yake zaune agurin Roshan sai Sojojin da akazo dasu,
A washe gari duk mutan gidan suma suka yo hospital har da uwar gayyar wato Hajia Kilishi....

Razhdeen kuwa duk halinda ake ciki bai sani ba, ga yayi switch up ɗin wayarsa balle a ƙira shi a sanar masa, yana zaune a falo kamar yanda ya saba yana dafe da goshinsa haka kawai yake jin gabansa yana yankewa wanda bai san dalilin hakan ba,
Ƙirjinsa ne yake bugawa da ƙarfin gaske ga kansa yanda yake sarawa da duk kan alamun akwai mummunan abinda yake shirin faruwa dashi,
yana cikin wannan halin yaji ƙarar ihun Baiwar Allah daga ciki, a ɗan ruɗe ya ɗago da kansa yana juyar da eyes ɗinsa waɗanda suka faffaɗa suka rame, hatta fuskarsa ma ta ɗan rame, sake jin ihun yayi a karo na biyu a hanzarce ya miƙe tsaye tareda nufan bedroom ganin bata ciki yasa yakai eyes ɗinsa bakin ƙofar bathroom,
a karo na uku ya sake jin ihun ya daki dodon kunnensa, zuwa bakin ƙofar yayi yasa hannu zai buɗe, yaɗan dakata yana fargaban shiga gudun kar ya tarar da ita acikin wani hali amma jin nishinta da ƙarfi yasa ya tura ƙofar bathroom ɗin ya shige, ganinta yayi a ƙasi tana kwance shame-shame tana riƙe da cikinta sai murtsukuku take tana juyi tareda fitar da nishi da ƙarfi-ƙarfi,
Daga ita sai towel kawai a jikinta, haka yake binta da kallo cike da mamakin abinda ya sameta, idanuwansa ne suka sauƙa akan jinin da ya ɓata tiles ɗin toilet, jini ne yake bin ƙafarta yana gangarowa daga ƙasinta, zaro ido yayi yana Binta da kallo a ruɗe ya nufi kanta,
hannu ɗaya yasa ya ɗagota ganin bazata iya tsayuwa ba yasa ya mannata ajikinsa,
Zagayo da hannayenta tayi ta bayansa ta ƙanƙame shi sosai jikinta na kakkarwa tana kuka tareda faɗin
"Cikina ciwo, marata ciwo dan Allah ka temaka mun zan mutu, bazan iya cigaba da rayuwa ba ciki nahhhh, Marataaaa....."
nan itama ta fashe da kuka,
gaba ɗaya ya rasa yanda zaiyi da ita, ga duk ta ɓata towel ɗin da jini dake farin towel ne,
wani dabara ne ya faɗo masa nan ya yi mata ɗaukar luɗa ya zaunar da ita acikin farin baho na wanka yasa hannu ya zamar mata da towel jikinta idonsa a lumshe domin baya ƙaunar ganin tsaraicin mutum, da sauri ya waiwaya bayansa bayan ya kunna mata ruwan fanfo mai ɗumi-ɗumi,
juyawa yayi ya fice daga cikin toilet ɗin ya nufi wardrobe ya ciro new towel baƙi sannan ya koma cikin bathroom idonsa a lumshe, da haka ya gyarata ya temaka mata tayi wanka sannan ya ɗagota tareda ɗaura mata towel ya ɗagota ya saɓata kan kafaɗarsa yayi bedroom da ita, duk wannan ɗawainiyar a makance yayi mata ko sau ɗaya bai yadda ya buɗe eyes ɗinsa ya kalleta ba,
Itama kallonsa take duk da wahalar da take sha amma bai hanata yin mamakin ƙarfin hali irin na Razhdeen ba,

Bayan ya fita da ita zaunar da ita yayi akan kujerar bedroom wanda yake beside bed,
A hankali ya buɗe idonsa sai kyawawan eyes ɗinsa suka sauƙa akan kyakkyawar fuskar Baiwar Allah wanda itama kallonsa take, nan suka fara kallon juna, sun ɗau tsawon minti biyar a haka daga bisani ya fara motsa lips ɗinsa a hankali ya ce "Are you okay?...."

ɗaga masa kai tayi ba tareda tace komai ba,
Ya ce "ok! kina period ne?...."

ɗaga masa kai ta kuma yi...
Ya kuma cewa "daman haka kike idan zakiyi period?....."

Dasauri ta ɗaga masa kai alamun ey...."

Jinjina kai yayi sannan ya ce "akwai maganin ciwon cikin da zan baki kisha yanzu insha Allahu bazaki ƙara shan wahala ba dazaran zakiyi period....."

Kallonsa kawai take ba tareda ta ce komai ba,

Ya tashi a hankali ya nufi drawer mirror ya buɗe gida na tsakiya ya ɗauko wani magani ƙananu acikin ƙwalinsa, buɗe guda biyu yayi sannan ya ɗauki gorar faro yazo gabanta ya durƙusa sannan ya miƙa mata maganin,
Hannu tasa ta karɓa sannan ta jefa a baki ta kafa gorar ruwan tasha....

tashi yayi yana faɗin "wait for me...."

ya nufi falo kai tsaye bakin ƙofa ya nufa yasa key ya buɗe ya fice, domin yasan babu kowa a gidan, yana jin fitar su da motar amma baiyi tunanin wata matsala bane........


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 43 to 44



꧁꧂


A hankali yake sauƙa down stairs ganin babban falo wayam ba kowa yasa kai tsaye ya miƙi room ɗin Baiwar Allah,

(Ohh Ni kuwa na ce daman Razhdeen yasan ɗakin Baiwar Allah 🤔🤔🤔)

Shiga yayi ya nufi wardrobe ɗinta ya fara dube-duben abinda yazo nema, cikin sa'a kuwa yana buɗe wardrobe ɗin ƙasa ya tarar da jerin pants da ledojin pad, ya ɗauki pant guda uku da ledar pad guda ɗaya domin bazai iya tsaya farkewa ba, yana ɗauka ya yi saurin ficewa ya nufi upstairs zai koma part ɗinsa gudun kar a kama shi domin yana mungun fargaban haɗuwa da Abbah,
Bayan ya koma room ɗinsa key yasa a ƙofar ya koma bedroom ya tarar da Baiwar Allah a yanda ya barta tana zaune ta kwantar da kanta a jikin sopa,
Ganinsa yasa ta ɗan ɗago da kanta tana kallonsa fuska a jagalgale tsabar wahalar ciwon cikin da take fama da shi, lokaci guda ta zamo kamar abun tausayi,
zama yayi a gefenta tareda miƙa mata pant sannan ya buɗe ledar pad ya ciro mata guda ɗaya ya miƙa mata tareda faɗin "ki shiga bathroom kisa...."

yamutsa fuska tayi kamar zatayi kuka a shagwaɓe ta ce "a halin yanzu bazan iya amfana da komai ba, bazan iya yin wani aiki ba marata ta riƙe sosai bazan iya miƙewa tsaye ba balle na iya tafiya...."

Dogon numfashi yaja eyes ɗinsa akanta ɗan cije lips ɗinsa na ƙasi yayi tareda faɗin "toh yanzu ya kike so ayi? idan kika zauna a haka zaki ɓata jikinki ne, ki daure ki tashi kisa...."

Girgiza Kai tayi tana zubar da ƙwallah,
ya ce "Kinga maganin ne yake aiki da zaran kinci abinci kin kwanta kinyi bacci shikenam zaki daina jin ciwon...."

wani irin murɗa taji ita kanta bata san lokacin data zabura ta kamo hannunsa ta riƙe sosai ba, jikinta har wani kakkarwa yake tana riƙe da hannayensa duk biyun idonta a ƙanƙame, haƙwaranta har dukan juna suke tsabar kakkarwar da suke kamar mai jin zunzurutun sanyi, ita kaɗai tasan tsananin azabar da take ji, addu'o'i kawai take jerawa,
Shima kansa ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, a hankali ya zamar da hannayensa sannan ya kwantar da ita a jikin kujerar, ya ɗauki pant ɗin ya saka pad a ciki,
yana gama haɗawa yakai pant ɗin saitin sawayenta ya ɗago dasu tareda zura sawayen acikin pant ɗin, ƙirjinsa ne yake bugun uku-uku da ƙarfin gaske hannunsa na kakkarwa haka yake jan pant ɗin sama har yazo saitin kyawawan manyan cinyoyinta masu laushin masifa gasu farare tass har wani ɗaukan ido suke,
saitin zuciyarsa ne yake wani irin bugu Rass! Rass!! Rass!!! a yayin da yayi ido huɗu da cinyoyinta masu ɗaukar hankali, wani irin haɗiyar yawu yayi gaba ɗaya jikinsa ya tsimu sai kakkarwa yake, a hankali yake ɗago da kansa har yakai eyes ɗinsa saitin fuskarta ga yanda take fitar da numfashi a hankali ɗumin numfashin yana dukan fuskarsa, eyes ɗinta a lumshe kamar wanda bacci ya ɗauke ta, hannunta a saitin mararta duk biyun,
maida kallonsa yayi saitin cinyoyinta yana fargaban ƙarasar da hannunsa can ciki, babu yanda ya iya da haka ya ƙarasa sanya mata pant ɗin mai ɗauke da pad, kansa na kallon gefe gaba ɗaya ya rikice har idanunsa sun kaɗa sunyi ja,
jawo ta yayi saman faffaɗan ƙirjinsa sannan yayi mata ɗaukar luɗa ya miƙe tsaye tareda nufar waran katafaren ƙaton gadonsa da ita, yana zuwa ya kwantar da ita daga ita sai towel a jikinta,
tashi yayi ya nufi mirror ya ɗauko turare mai bala'in ƙamshi yazo ya feffeshe duk ilahirin jikinta dashi domin baya ƙaunar zama haka ba turare, uwa uba yaga a halin da take ciki dole ta kasance cikin ƙamshi indai tana tare da shi domin Razhdeen ma'abocin son turare ne shi da Roshan jirginsu ɗaya ne....
Bayan gama feffesheta da turare ya janyo blanket ya rufe ta dashi, shima bathroom ya faɗa domin yin wanka.....


🄷🄾🅂🄿🅸🅃🄰🄻

Roshan ne kwance an sanya masa oxygen yana lumshe da ido alamun ya samu yin Bacci, fuskar tayi fiyau ba ƙaramin ramewa yayi ba ga yayi wani irin fari fatt da shi,
Abbah yana zaune a bakin gadon da yake sai kuma sauran kuma suna zazzaune a kujerun ɗakin, babu wanda aka bari a gida,
Doctor ne yake tsaye yana kora jawabi a Abbah cewar "dole idan ana son kwanciyar hankalinsa ayi masa abinda yake so, akwai abinda ya dame shi a ransa wanda ya gagara cire shi har takai ga taɓa lafiyar zuciyarsa, amma shin ciwonsa ya taɓa tashi kuwa? kodai yanzu ne farkon tashinsa?...."

Dogon numfashi Abbah ya sauƙe tareda jinjina kai muryarsa har ta ɗan disashe shima ya ce "haƙiƙannin gaskiya wannan ciwon nashin yanzu tashinsa na biyar kenam, lokacin da yake yaro ƙarami sau uku yana tashi toh amma da aka fitar shi can ƙasar waje akayi masa aiki bai ƙara tashi ba sai kwanakin baya kusan shekara uku lokacin da budurwarsa ƴar classmate ɗinsa ta samu hatsari ta rasu, a lokacin ya jijjiga matuƙa tsabar tsananin son da yake mata, naje na nema masa Auran yarinyar har an bashi ita Allah ya shiga tsakaninsu, ciwonsa ya tashi sosai nan ma saida muka fita dashi ƙasar Ethiopia tukun rayuwarsa ta dai-daita,
an kafa mana sharuɗa da dama akan Roshan muddin muna son rayuwarsa, shiyasa bana son abinda zai taɓa shi, bana ƙaunar ɓacin ransa domin muddin idan Ran Roshan ya ɓaci toh abu ne mai tsananin gaske saboda shi mutum ne mai kawaici da rashin sa abu a ransa, bashi da abokin faɗa sannan baya fushi akan abu saidai idan abun yakai maƙura, toh idan har ɓacin ran nasan yakai maƙura toh akwai matsala......."

Abbah yana kai ƙarshen maganarsa ya sunkuyar da kansa ƙasi yana zubda ƙwallah domin ko kaɗan baya son ciwon Roshan...

Doctor ne yake rarrashinsa game da faɗin "kayi haƙuri Chief kaima yanada kyau ka rage shiga damuwa saboda hawan jininka....."
Abbah a zabure ya ɗago yana kallon Doctor ya ce "na ƙwammace gwara ciwo na yaita tashi akan na yaron nan wallahi...."

Doctor ya ce "it's okay! But meye musabbabin faruwar hakan? Sannan tin jiya da aka kawo Roshan banga ɗayan ɗan nakan ba wato Razhdeen shin kodai ya koma U.S ne?....."

Abbah kamar zai haɗiyi ransa tsabar takaici ya ce "bani da Ɗa mai sunan Razhdeen, Roshan kawai nake Da...."

Doctor cike da mamaki yake bin Abbah da kallo,
Hajia Kilishi itama dasauri ta ɗago tana kallonsa,
Itama Minal dake zaune buɗe baki tayi tana kallon Abbah a yayinda take riƙe da phone ɗinta,
Pinky da Rukky kuwa kallon juna suka shiga yi ko wacce fuskarta a hargutse,
Ummy cike da mamaki ta ce "Abbahhh......"

Ɗaga mata hannu Abbah yayi tareda faɗin "kada ko waccen ku ta kuskura tayi mun magana indai akan Razhdeen ne, baya daga cikin jerukan ƴaƴana, na fidda shi ba Ni ba shi daga yau....."

Doctor cike da mamaki ya ce "Subhanallahi amma me yayi zafi haka Chief?...."

Abbah ya ce "haka kawai na yanke hukuncin nan domin bazan taɓa haifan yaron da zai saka mun ciwon kai ba ko ya bijirewa maganata ba impossible,
haka kuma duk wacce zata bijirewa maganata toh wallahi zan cire hannuna ne akanta sai dai ku nemi wani uban, koda zan zauna babu yaro ko ɗaya ......"
ya ƙarashi maganar yana nuna su da yatsa,
Hajia Kilishi ganin ya sako ƴaƴanta aciki yasa ranta ya ɓaci sosai ta ce "amma ko wani irin laifi suka yi maka bai kamata kayi musu wannan hukuncin ba, faɗan da kake yi ma babu daɗin ji....."

Abbah ya ce "dole abi dokata indai anason zaman lafiya kuma kema harda ke ban ware kowa ba, zan iya baki takardar sallamarki indai baki canza ɗabi'unki ba....."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login