Showing 15001 words to 18000 words out of 117953 words

Chapter 6 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4732

Yallaɓai ganin Baiwar ALLAH yasa ya saki kan Ƴar Amana yazo har gabanta suna facing juna, wani irin kallo yake mata daga bisani ya ce "ke ce kika saka mun ƙarara acikin kayana?..."

Baiwar ALLAH tace "lokacin da akayi haka ina can ɗakin duhu .."

Yallaɓai ya kuma cewa "kenam wancan yarinyar ce?..."
ya ƙarasa maganar yana nuna yanda Ƴar Amana take..

Nan ma Baiwar ALLAH ta ce "ba ita bace.." tayi maganar ba tareda ta ɗago ba

Yace "taya kika san ba ita bace?.."

Tace "saboda nasan bazata aikata ba ."

tintsirewa da dariya yayi sannan ya ce "na tabbata duk marayun matan dake cikin gidan nan babu wacce zata iya mun wannan abun sai ku biyu ke da Ƴar Amana..."

ɗagowa Baiwar ALLAH tayi tana kallonsa tace "saboda sun baka haɗin kai shiyasa? mu kuma saboda munyi Allah wadai da halinka shine ka ɗora mana tsanarka akan mu ?..."

tana ƙarasa maganar ya zabgeta da mari yana huci yace "ke Ni zaki tsaya a gaba kina gaya mun maganganu? saboda kin raina Ni?..."

wata ce daga cikin yaran gidan ta ce "Yallaɓai ai tinda muka ganka tsirara zancen raini ya ƙare..."
duk suka kwashe da dariya, haushi kamar zai kashe Yallaɓai cikin tashin hankali ya darara musu tsawa tareda faɗin "duk ku sunkuya kuyita tsallen kwaɗo har yamma..."
haka kuwa suka hau yin tsallen kwaɗo banda Baiwar ALLAH da Ƴar Amana da suke tsaye sai sauran ma'aikatan,
Yallaɓai yana zazzaro ido waje yana fuskantar Baiwar ALLAH yace "ke kika saka mun ƙarara ko ƴar Amana?..."

Shuru Baiwar ALLAH tayi bata bashi amsa ba, yana jinjina kai ya ce "okay don't worry Ƴar Amana yau saita gane kuranta..."

ya juya zai nufi yanda Ƴar Amana take a tsaye ta ƙura masa ido Baiwar ALLAH tayi saurin cewa "Ni ce na saka maka ƙarara acikin kayanka, babu laifin Ƴar Amana..."
Juyowa yayi yana mata kallon up and down ya juyo zuwa gare ta kafin ta ankara yasa mata ƙafa ya girbeta bata san lokacin data doku a ƙasi ba, kafin ta ɗago ya zabga mata mari har saida taga duhu tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fii musibati wa akhlif li khairan Minha, Allahumma inni kuntu mina zalimin..."

haka yasa hannu ya ɗagota ya riƙo fuskarta da hannu bibbiyu ya gwara mata kansa a goshinta sannan ya hankaɗata gefe ta faɗi ƙasi tana mai jin hajijiya,

Ƴar Amana ta kumbura sosai kamar zata fashe ganin yanda yaketa zaluntar Baiwar ALLAH haka ta tafo da gudu yana juyowa kafin ya ankara ta rungumo shi takai bakinta saitin AK-47 ɗinsa ta garzaya masa cizo na gaske,

wani irin gigitaccen ihu yayi har saida mutanen wajen suka toshe kunnuwansu tsabar ƙarfin ƙarar, still Ƴar Amana bata ɗago da kanta ba ta sake kafa haƙwaranta ta garzaya masa kuma du, ihun da yake yi ne yasa security bakin gate suka jiyo sai gasu da gudun gaske, kafin su ƙaraso Ƴar Amana ta ɗago saida ta saita gurin ta kai masa canki da ƙafarta da iya ƙarfinta!

zaro ido yayi waje a yayin da numfashinsa ya tsaya cakk sai luuuuu ya faɗi sumamme,

Duk waɗanda suke wajen sun tsorita sosai ganin yallaɓai a kwance ba motsi, kuma har tayi wannan aikin babu wacce ta dakatar da ita,
Baiwar ALLAH a ruɗe ta tashi tayo gurin Ƴar Amana ta rungumeta tana kuka tareda faɗin "mun shiga uku Ƴar Amana kin kashe shi har lahira, bamu da mafita daga gidan marayu sai gidan prison wayyo ALLAH nah, da rabon baza muga iyayen mu ba har abada...."
ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, itama Ƴar Amana kuka take kanta akan kafaɗar Baiwar ALLAH....

Security suna zuwa basu tambayi meya faru dashi ba suka ɗauke shi domin yin temakon gaggawa saboda halinda yake ciki, ga jini har ya wanke masa wandonsa haka jinin yake bin ƙafafunsa....


Wayyo da wuya Yallaɓai fah ya rayu yanda naga abun nashin yana ƙwararar da jini🥺🤔🤔🤔


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (5)



꧁꧂



Innalillahi wa inna ilaihi raju'un Yallaɓai AK-47 ɗinsa ya daina aiki, amma anyi nasarar ceton rayuwarsa, sai dai yana jin jiki sosai jinya yake bana wasa ba,

saida aka fitar dashi ƙasar waje kafin abun nashin ya daidaita amma babu ƙwari domin bazai iya yin amfanin komai akan matarsa ba,
Matar kuma ta gaza yin haƙuri ta tattari ƴaƴanta Uku tayi tafiyarta domin a cewarta bazata iya rayuwar zaman Aure dashi ba, saboda zata cutu matuƙa haka ta dage har ya sake ta...

Yallaɓai ya ɗauki tsanan duniya ya ɗorawa Ƴar Amana domin ita tayi sanadiyar lalacewar rayuwarsa, babu yanda zaiyi haka ya shigar da ƙara akan Ƴar Amana...

3 months ago Ƴan mata ne suke zazzaune akan kujerun roba wanda yake gidan marayu, ko wanne sun haɗa group ɗinsu sai shan shapta suke ta sha, kura ya mutu ai wasa, Yallaɓai baya nan sun samu ƴancin kansu babu hantara da takura,
A yanzu misalin ƙarfe 4 na yamma
Baiwar ALLAH da Ƴar Amana suna can ɓangaren Lambu, sun sa kayan fruits a gaba Baiwar ALLAH sai sha take a yayin da ita kuma Ƴar Amana take kaɗa sautin jitan ta mai daɗin saurare da hannu bibbiyu, suna zaune babu mai sauraron kowa acikinsu...


Motoci ne waran su biyar na Police suka diddirƙo a filin gidan, ƴan matan gidan ne duk suka mimmiƙe suna ja da baya cike da tsoro da fargaba, kafin kace mai matan gidan duk sun taru ganin motocin Ƴan sanda ga kuma Yallaɓai, D.P.O ne yazo ya tsaya a gaban Ƴan matan tareda faɗin "ina sauran Ma'aikatan gidan?..."

kafin ya rufe baki sai gasu sun tafo da gudu daman su biyar ne
Aunty Habiba da Aunty khadija da Aunty Salma da sauran biyun, suna zuwa suka fara gaishe da D.P.O, daga bisani suka maida kallonsu kan Yallaɓai tareda faɗin "Yallaɓai ya jikin?.."
kawar da kai yayi gefe ko sauraronsu baiyi ba,

D.P.O yace "shin kunsan wannan?..." ya ƙarasa maganar yana nuna Yallaɓai,
Duk suka amsa da "Ehh.."
ya kuma cewa "shin ko zaku iya sanar mana abunda ya faru dashi?..."

matan gidan ne suka fara kallo-kallo suna kallon junansu daga baya suka ce "Gaskiya bamu san abunda ya faru dashi ba, mudai munji labarin bashida lafiya..."
D.P.O yace "bana son ƙarya fah? shin ina Baiwar ALLAH da Ƴar Amana?..."

suka ce "suna Lambu..." ya sanar wa ɗaya daga ciki cewar taje ta ƙira su, nan danan aka tafi ƙiransu..

Yallaɓai kallon yaran yake cike da mamaki lokaci guda sun juya masa baya har suna goyon bayan ƙarya akan su tozarta shi, hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba dajin haka....

nan da wasu ɗan lokaci saiga Baiwar ALLAH da Ƴar Amana sun taho,
Ƴar Amana tana riƙe da ƴar jitar ta hankali kwance,
Baiwar ALLAH ganin Yallaɓai yasa ƙirjinta bugawa da ƙarfin gaske lokaci guda ta dafa ƙirjinta tareda faɗin "Na shiga uku abunda nake gudu zai tabbata..."
D.P.O yace "yadai kika daskare a wajen kodai bakida gaskiya ne?..."
girgiza kai Baiwar ALLAH tayi sannan ta ƙaraso yanda sauran matan suke tsaye,
D.P.O ya ce "Yallaɓai Ibrahim shin wacece acikinsu tayi maka wannan aika aika domin wannan al'amarin ba ƙaramin abu bane, dole zamu ɗau hukunci akanta, sai tayi zaman cell bayan tasha duka ..."

Baiwar ALLAH jin haka yasa idanuwanta suka cicciko da hawaye,
Yallaɓai da yatsa ya nuna Ƴar Amana tareda faɗin "wannan yarinyar zamanta a gidan nan babban illah ce domin ba ƙaramar Mayya bace..."
Baiwar ALLAH ta riƙe hannun Ƴar Amana tace "Dan ALLAH D.P.O kuyi haƙuri wannan yarinyar Kurmiya ce bata ji sannan bata magana kuma ku dubi shekarunta yarinya ce ƙarama ƴar shekara 15 zaman cell bai dace da ita ba..."

Yallaɓai wani irin harara yake wurgawa Baiwar ALLAH domin ta fiye shishshigi a al'amarinsa, kuma sai tana abu kamar sahabiya ....

D.P.O ya ƙurawa Baiwar ALLAH ido sannan yace "shin kinsan abunda ta aikata masa ne?..."
Baiwar ALLAH tayi shuru tareda sunkuyar da kanta ƙasi,

Aunty Habiba ta buɗu baki waran cewa "D.P.O bamu san abunda Ƴar Amana ta aikatawa Yallaɓai ba amma zamu so sanin abinda ta aikata..."
ta juya bayanta tareda cewa "ko ba haka ba Ƴan uwa?..." ta ƙibƙibta musu ido..
Duk suka amsa da "Ehh bamu san komai ba, a sanar mana..."

Yallaɓai a fusace ya maimaita gayan abinda Ƴar Amana ta aikata masa kuma ya sanar cewa a gabansu duk hakan ta faru...
kafin ya rufe baki duk ƴan matan suka fara tintsirewa da dariya,
wata daga cikin ƴan matan tace "daman yallaɓai akan wannan ake maganar? naga hari ka kaiwa Aljanar kuliya ita kuwa ya cabke maka tsuriya agaban mu akayi hakan, shine kake son yiwa ƴar Amana sharri? toh kaji tsoron Allah domin zaifi maka ka sanarwa kowa labarin kuliyan nan..."

wata ma ta fito tazo gaban D.P.O tace "D.P.O shin taya za'ayi yarinyar da bata jin komai sannan bata iya yin magana ta iya yanke ƴaƴan gwailon Yallaɓai alhalin babu abinda yayi mata! indai ba fyaɗe yayi niyyar yi mata ba, toh mudai kuliya muka sani ba Ƴar Amana ba..."

wata yarinya itama tace "shin Yallaɓai ayaban nakan ya daina aiki ne? toh idan kuna son kama kuliyar nan kuje cikin Lambu cikin dare, tafi fitowa acan, mudai ba ruwan mu..."

Ɗaya daga ciki ta kuma cewa "rashin kula da tsuriya ne yasa haka, da kana tattalinsa da hakan bata faru ba, kuliyar tayi maganinka taga duk gidan nan babu namiji, kamata yayi a kawo mana shugaba mace wacce zata ji tausayin mu ehen ..."

wata ce kuma du ta kuma cewa "wata ƙila fyaɗe zai yiwa kuliyar shiyasa ta cabke ƴaƴan masarrafa 🤣🤣🤣..."

D.P.O ganin bazai iya sauraron maganganun ƴan matan nan ba yasa ya juya yana faɗin "shirmen banza kuzo mu tafi, Yallaɓai Ibrahim wannan maganar kawai a rufe shi anan domin waɗannan maganganun da suke faɗi zaisa a ɗaureka saboda zargi zai iya biyowa baya, waɗannan yaran shegen wayo gare su zasu iya sawa a kulle ka a prison domin naji suna maganar fyaɗe, mun Barka lafiya...."

D.P.O da mutanensa gaba ɗaya kunya yabi ya ishesu haka suka ja motarsu suka tafi, shima Yallaɓai jikinsa ne yayi sanyi jin abunda D.P.O ya faɗa, haka yayi zuruuu yana wani irin tunani....

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login