Showing 99001 words to 102000 words out of 117953 words
"tinda har bazaka ji maganata ba to zama dakai bashi da wani amfani,
Saboda daga yanzu ka kama hanya ka fita mun a gidana, kaje duk yanda zaka je amma babu ruwa na, duk abinda ya sameka babu hannuna,
Bazan tsine maka ba amma kaje na dena ganinka a gaba na balle na ƙunshi baƙin cikin ka......"
Dasauri Razhdeen ya ɗago yana kallon Abbah ga hawaye yanda yake gangaro masa, lips ɗinsa na kakkarwa daƙer ya iya cewa "Please Dad......"
Abbah ne ya ƙara katse shi da cewa "am not your Dad, please stay away from me,
zansa a duba mun yarinyar idan har wani abu ya sameta toh wallahi zanyi maganinka domin saina shigarka kotu an yanke maka hukunci....."
Abbah ya juyo yana kallon Baiwar ALLAH ya ce "Daughter gaya mun shin ya miki wani abu? kamar dai fyaɗe...."
Dasauri Baiwar ALLAH take girgiza Kai alamar a'a, tana zubda ƙwallah sam bata ji daɗin hukuncin abinda Abbah ya yanke wa Uncle Deen ba,
Abbah ya ce "Kinga kar kiji tsoronsa ina tare dake ki gaya mun gaskiya, kar kimun ƙarya....."
Baiwar Allah fashewa tayi da kuka tana faɗin "wallahi Abbah babu abinda ya mun....."
Abbah ya ce "okay shikenam..."
ya juyo yana kallon Razhdeen ya ce "Allah ya temake ka, now leave my house....."
ya ƙarasa maganar yana nuna masa bakin ƙofa,
Roshan ne ya matso dab da Abbah kamar zaiyi kuka ya ce "please Daddy kar ka kore shi, wannan hukuncin yayi tsauri, dan Allah ka ƙyale shi we need him...."
Abbah fuska a murtuƙe ya ce Da Roshan "babu ruwanka...."
Abbah ya kuma cewa "Razhdeen in har baka bar mun gida kafin na ƙirga ɗaya zuwa biyar ba wallahi zan tsine maka Albarka yanzun nan....."
Zaro ido Roshan yayi yana kallon Abbah cike da mamaki, shi tinda yake bai taɓa ganin ɓacin rai a fuskar Abbah irin ta yau ba,
murya na kakkarwa Roshan ya ce "Daddy......"
Abbah yayi saurin katse shi da cewa "I said shut up......"
Shi kuwa Razhdeen tin tinin har ya haura upstairs ya nufi part ɗinsa kafin ɗan wasu mintuna har ya dawo hannunsa riƙe da troley, eyes ɗinsa har sunyi jawur, haka ya sauƙo yayi hanyar waje,
Roshan ne ya tsayar dashi da cewa "My Man please...."
Razhdeen juyowa yayi yana kallon Roshan yaɗan sau murmushi a hankali ya furta
"Am so sorry my twins, please forgive me....."
Jinjina kai Roshan yayi tareda faɗin "na yafe maka My Man, please stay safe...."
Ɗaga masa kai Razhdeen yayi tareda juyawa yayi tafiyarsa....
Roshan kuka ne yake shirin kuɓuto masa tinin yayi saurin haurawa upstairs ya nufi part ɗinsa,
Shima Abbah yana huci ya nufi upstairs ɗinsa, anan ya tarar da Hajia Kilishi tana tsaye tana kallonsu, ba tareda yace mata komai ba yayi wucewarsa cikin bedroom....
Murmushi tasau tareda bin bayansa itama ta shige ciki..
Baiwar Allah tana sai zubda ƙwallah take gaba ɗaya ta rasa mai yake mata daɗi a duniyar nan,
bata ankara ba taji Pinky ta zunguri goshinta tareda faɗin "ai duk ke kika jawo hakan, munafukar banza kinsa an kori Yaro a gidan ubansa ke kuma da babu dangin iya kina Nam abinki ....."
Rukky ta ce "muma mu shafa wa kanmu ruwan sanyi domin nasan wata rana muma zata sa a kore mu daga gidan uban mu, daman haka take da buri a ranta, ta zama ƴar gaban goshin Abbah......"
Pinky ta ce "waima na kasa fahimtar komai shin daman akwai soyayya a tsakanin Yaya Roshan da wannan ƙazamar yarinya?...."
ta ƙarasa maganar tana kallon Rukky
Rukky ta ce "tambaya kike ko neman sani? ke tinda baki fahimci haka ba, ai saboda ita Yaya Roshan ya ƙwanta jinya,
Kuma idan hasashe na yazo dai-dai shima Uncle Deen kamar sonta yake....."
Pinky ta zaro ido tareda faɗin "Whattttttt? Kema dai kinsan Uncle Deen yafi ƙarfin wannan kucakar yarinyar....."
Rukky ta ce "idan ba haka ba mezaisa ya rufe kansu a ɗaki daga shi sai ita, nifah ina tunanin wani abu ya shiga tsakaninsu, domin ba yanda za'ayi ace Mace da namiji sun keɓe sheɗan bai shiga tsakani ba kuma tsawon sati guda,......"
Pinky ta ce "bana tunanin haka domin Uncle Deen bazai taɓa aikata hakan ba...."
Rukky ta ce "kenam shi ɗin dutsi ne?...."
Pinky ta kuma cewa "bana tunanin abinda kike konkonto akai zai iya zamo gaskiya domin kinfi kowa sanin waye Uncle,
Sannan in har Yaya Roshan shima sonta yake to kuwa za'a kwashi ƴan kallo domin bazamu taɓa yadda a shugo da wannan ƙazamar cikin jinsin mu ba, bamu san asalinta ba wata ƙil mayya ce tazo ta ciccinye mu ɗaya bayan ɗaya,
Kai bazama mu yadda a Aureta ba wallahi....."
Rukky ta ce "taya zaki iya dakatar da wannan al'amarin bayan ke ƙanwa ce ba uwa ba sannan ba Yayar miji ba...."
Pinky tana zunɓuro baki ta ce "ai wallahi ko ta hanyar malamai zan dakatar,
Saboda na tsani yarinyar nan...."
ta ƙarasa maganar tareda jan dogon tsuka tayi wucewarta,
Itama Rukky kallon Baiwar ALLAH tayi wacce tin da take tsaye tana sauraron su itama ta ce "banza kwartuwar banza, karuwar wofi, kariya mai bin mazaje....."
ta ƙarasa tana harararta itama tayi wucewarta duk suka haura upstairs....
Da gudu Baiwar Allah ta wuce room ɗinta tana kuka...
Duk halin da ake ciki Ummy bata nan taje school ɗinsu karɓo result.....
Razhdeen bayan fitarsa Motarsa ya shiga a fusace yayi tafiyarsa, Sojojin dake escort ɗinsa any way suna tambayarsa akan cewar zasu yi rakiya ne amma ko kulasu baiyi ba haka suka haƙura suka barshi ya yi tafiyarsa,
Kai tsaye ɗaya daga cikin jerukan gidajensa ya nufa wanda saika bi ta layin mabarata road kafin ka ɗau hanyar gidan,
Gudu yake da motarsa amma hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, maganganun Abbah ne suke masa yawo a ƙwaƙwalwarsa, yana cikin wannan halin sauran kaɗan ya buge wata kuturwar dattijuwa tana shirin tsallaka kwalta tana riƙe da ƴar robarta,
Da ƙarfin gaske ya danna burki saida mutanen wajen suka tsorita sun ɗauka yayi kaɗa ne, dake wajen zallar mata ne nakasassu,
Goshinsa ne yayi matuƙar buguwa a jikin sitiyarin motar,
Saida ya ɗau mintuna biyar a haka bai ɗago da kansa ba, still yana nan a wannan halin, yana jin yanda mabaratan suka kewaye motarsa suna faɗin "a temaka mana dana Annabi...."
Dake motar mai baƙin glass ne basa iya gano wanda yake ciki,
zuciyarsa ce take magana "hakan na nufin yazo waran da yazo ranar har yayi rabon kuɗaɗe...."
Jin hayaniyar mabaratar ya ƙara jefa shi cikin wani hali, domin shi sam baya juran jin hayaniya,
jin ƙarar sautin sarewa yasa ya yi saurin ɗagowa sai faman sake nannauyar numfashi yake, jin har yanzu bai daina ji ba yasa ya shiga waige-waige ganin jerukan mabarata yasa bai iya ganin wacce take kaɗa jitar ba,
a tunaninsa mafarki yake, sautin da yake ji a cikin baccinsa ne yake ƙara hura masa ƙwaƙwalwa, a hanzarce ya buɗe murfin motarsa tareda sauƙar da ɗayan ƙafarsa ta dama,
a hankali ya ƙarasa sauƙar da ɗayan ma, yana jin yanda suke shashshafa shi duk a neman temakon amma haka yake sa hannu yana tutture su gefe tareda ratsawa ta tsakiyarsu yanaso ya bi yanda yake jin sautin,
Ita kuwa wacce take kaɗan jitar tana can zaune bayan wata ƙatuwar bishiyar dake kusa da bakin hanya tana ta kaɗa jitar ta,
domin ita koda wasa bata taɓa zuwa yanda mutum yake neman temako saidai a kawo mata har yanda take zaune,
a hankali yake nufan inda take, murɗi-murɗin zirin gashin ta kawai yake gani dake ta juya bayanta,
Haka mutane wajen suma suke bin bayansa saida yazo dab da ita sannan ya tsaya tareda ɗaga musu hannu alamar su dakata,
Ita kuwa Ƴar Amana bata san da mutum a bayanta ba, haka ta cigaba da kaɗa jitar ta hankali kwance ga ƙatuwar jakarta a gabanta na kuɗaɗe yanda ake bata sadaka,
zagayowa yayi ta gabanta yana binta da kallo,
cike da mamaki ya durƙusa a gabanta a yayinda ita kuma take lumshe da idanuwanta, jiki na ɓari yakai hannunsa kan haɓarta ya ɗago da fuskarta suka fuskantar juna,
jin an ɗago da fuskarta yasa tayi saurin buɗe idonta tana ƙare shi da kallo,
Still idanuwansa yakai kan sumar kanta wanda shi zai bada shaidar wacce yake nema ne, wacce yake yawan ganinta a cikin mafarkinsa,
babu abinda ya chanza a duk suffarta, sai dai abinda ya ƙara bashi mamaki kuma yaga yarinya ce,
Da hannunsa yake murza sumar gashin ta wanda ya kasance laushi futus ga wani irin murɗi-murɗi kamar wanda aka tsoma a ruwan zafi,
Ita dai kallonsa take ba tareda tasan ko shi waye ba,
Sai dai abinda ya bata mamaki shine sumar kansa kamar mace har kafaɗa dasauri takai hannu tana shafar sumar kansa da murmushi akan fuskarta,
Bata san lokacin data ajiye jitar hannunta ba.......
*KUYI HAƘURI KUYI MANAGE DA WANNAN ZUWA GOBE DA SAFE DAN ALLAH.....*
𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.
𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦♀️🤦♀️
𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢
𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.
𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈
ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..
𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:
1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.
2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.
3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.
4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.
𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 47 to 48
꧁꧂
A wannan lokacin yana shirin zaucewa domin gaɓa ɗaya tunaninsa baya jikinsa,
kallon Ƴar Amana yake kamar wanda ya yi gamo, ƙwayar idanuwansa ya wurgar kan jitar dake ajiye a gefe guda still ya sake ɗagowa yana binta da kallo, jikinsa har wani zaƙami yake daƙer ya iya buɗan baki ya ce "ke ce? why are you disturb my heart?...."
Cikin rashin fahimta Ƴar Amana take binsa da kallo ba tareda tasan ko shi waye ba, ganin yanda ya zuba mata na mujiya yasa ta gama tsorita, hannu takai kan jitar ta tayi saurin rarimo shi a zabure ta miƙe tsaye da gudu tabar waran, kai tsaye gurin tsohuwar da take kula da ita taje ta zauna kusa da ita tareda maƙala hannunta acikin na tsohuwar,
miƙe wa yayi shima idonsa agun yanda take zaune can bakin titi, yana mamakin yanda ya ganta acikin mabarata sam bata dace da mai neman TEMAKO ba,
yanayin jikinta ya nuna alamun ita ƴar gidan manyan mutane ne,
tin daga kan launin fatar jikinta mai launin madara zuwa kan sumar gashinta fesfes mai laushin gaske haɗi da ƙamshi,
Azo kan kayan jikinta irin na ƴaƴan masu kuɗi doguwar riga fari tas irin party gown, ƙafar ta babu alamun datti ko kaushi, ƙafa ne kamar na jarirai tsantsi da kuma laushi! tana sanye da white toes,
abunda ya ƙara bashi mamaki shine baiga wata nakasa a jikinta ba
"To meya zaunar da ita acikin nakasassu marasa gata?...."
abinda ya furta a cikin ransa kenam,
a hankali yake taku kamar mai tambayar ƙasa ya nufi yanda motarsa yake ya buɗe front seat ta gefen drive ya ɗauko wata baƙar leda mai ɗauke da maƙudan kuɗaɗe,
sannan ya dawo saida ya zaɓo wata daga cikinsu mai ɗan lafiya ya bata rabin kuɗin wanda shi kansa bai san adadin yawan kuɗaɗen ba amma a ƙalla zasu yi karo uku wato 3 millions, abinda ya rage a hannunsa kuma basu fi 1 million ba, nufan yanda Ƴar Amana take yayi,
Ganinsa yasa ta ƙanƙame tsohuwa domin a halin yanzu tsoronsa ne a bayyane saman fuskarta,
yana zuwa ya durƙusa tareda miƙa mata sauran kuɗin hannunsa, ƙin karɓa tayi sai faman girgiza masa kai take,
tsohuwar ce take faman rarrashinta game da faɗin "kar ki damu Allah ne ya turo mana wanda zai rinƙa temaka mana, kuɗin da yake bamu sun isa muyi shekara muna morar su, idan baki manta ba akwai wata rana dana ce miki wani yazo ya raba mana kuɗaɗe mai yawan gaske to ai wannan shine,
ba mai cutarwa bane ki kwantar da hankalinki....."
jin abinda tsohuwa ta faɗa ne yasa ta dawo hayyacinta, kallon kuɗin hannunsa tayi sannan tasa hannu ta karɓe tareda rungumar kuɗin akan ƙirjinta tana bin sumar kansa da