Showing 111001 words to 114000 words out of 117953 words

Chapter 38 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4757

faman bubbuga ƙwanikansu suke a kan ƙwalta suna rera waƙa,
Ita kuma Ƴar Amana tana tsakiyar su sai ɗirkar rawa take tana juyi,
babu hanyar wucewa duk wani mai mota ko napep ko mashin yazo wucewa ta bangaren dama sai dai ya juya baya amma duk sun tushe hanyar wucewa suna zazzaune wasu tsofaffi ne wasu kuma madaidaita, Ƴar Amana ce kawai ta kasance mai ƙaramar shekaru a cikinsu,
haka zalika duk wanda yazo wuce wa ta bangaren hagun shima sai dai su juya kamar yanda su Uncle Deen suka fito suma inda ace shigewa suka zo yi sai dai su kowa baya domin bazasu bada hanya ba, already gomnati ta mallaka musu yankin da gidajensu a ata gefe guda,
Uncle Deen idonsa ne suka sauƙa akan Ƴar Amana wacce take ta shan rawa, su kuma sauran suna zaune suna bada sautin kiɗa tare da rera wakokin gargajiya domin na zamani duk cikinsu babu wacce ta iya,

A hanzarce Marshall ya juyo yana kallon Deen tare da faɗin "Nan ɗin mai akeyi ne haka?"
cike da mamaki yake bin Ƴar Amana da kallo ganin irin rawar da take, a hankali yake motsi da lips ɗinsa ya ce "Nan ne wajen da kace na rakoka...."

Marshall ya ce "amma waje kamar waran ƴan gala?..."

juyowa Uncle Deen ya yi yana kallonsa ya ce "kana ganin tsofaffin mata kace waran ƴar Gala?..."

Ɗaga kafaɗu Marshall ya yi tare da faɗin "naga kamar masu neman temako ne, amma shine zasu tare hanya subar yarinya ƙarama tana musu rawar ƴan China...."

murmusawa Uncle Deen ya yi tare da faɗin "su baka ga aikin da suke yi bane?...."

"Of course naga su suke ƙarfafa mata gwiwa suna tayata kiɗa,
But ina Dreamer ɗinka? Hope ba'a nan take ba...."

ƙayataccen murmushi ya saki a karo na biyu ya ɗago da yatsarsa yana nuna wajen da mutanen suke eyes ɗinsa akan Ƴar Amana ya ce "ita ce yarinyar...."

Dasauri Marshall ya juyo yana kallon Uncle Deen ya ce "Whattttttt! kar dai kace ita ce yarinyar mai rawan?....."

kafin Uncle Deen ya juyo ya bashi amsa har Marshall ya yi saurin buɗe murfin mota ya fice,
kai tsaye waran su ya nufa, yana zuwa ya fara ɗaga musu hannayensa biyu sama tare da dakatar dasu da cewa "ku dakata! Ku dakata!! Ku dakata haka....."

kafin kace mai gurin yayi tsit idanuwansu akansa, sai wata tsohuwa ce tayi ƙarfin halin cewa "meye damuwarka damu? nan yankin mu ne sai muyi abinda muke so...."

wata daga ciki itama ta ce "idan wucewa zakayi yau mallakarka sai dai ka juya baya ai ba nan ne kaɗai hanyar wucewa ba...."

Marshall yasau ajiyar zuciya tareda faɗin "kunga kuyi haƙuri, ba wai dakatar daku zanyi ba nima ɗan uwanku ne mai son kiɗe-kiɗe amma yanzu dai ku ɗan ara mun yarinyar ku zanyi magana da ita....."

wata daga cikinsu ne ta buɗe baki zatayi maganar cewa kurmiya ce!
Ƴar Amana tayi saurin ɗaga mata hannu akan tayi shuru karta sanar masa,
domin duk abinda zai ce zata ji shi mayarwa ne bazata iya ba,
A hankali take taku cikin ƙasaita ta nufi yanda yake ta tsaya dab dashi tana fuskantarsa tare da goya hannayenta ta gaban ƙirjinta,

Marshall haɗiyar yawu yayi wanda bai san ya yi shi ba, gaba ɗaya yarinyar ce ta fara bashi tsoro ganin irin ƙarfin halin da take da shi, still ya tuno da cewa ita ce take wahalar da Major acikin mafarki gaba ɗaya sai yaji wani irin gumi ya yanko masa,
tin daga kan ƙafarta ya fara binta da kallo ganin tana sanye da farin takalmi toes, sai wani gajeren wando wanda ya tsaya mata a iya gwiwarta da rigar Best wanda bai ƙarisa rufe cibiyarta ba daga nan eyes ɗinsa suka sauƙa akan kyakkyawar fuskar ta wanda yake a ɗaure babu wani annuri a tattare da ita,
ga wasu murɗaɗɗun gashi wanda ya baje mata har gadon baya,
yana gama ƙareta da kallo ya juya da gudun gaske ya nufi yanda motarsu take, a cikin motar ya tarar da Uncle Deen zaune yana kallon duk abinda yake faruwa,
ba tareda ya shiga cikin motar ba ya zura kansa ta cikin glass yana haki yake cewa "Major haƙiƙannin gaskiya na yarda cewa wannan yarinyar itace take fito maka acikin mafarki domin zubinta irin na Aljanu ne sak,
Amma sai dai yarinya ce ƙarama domin ko Nono bata fara ba,
bari na koma gurinta yau zanyi magana da Aljana....."

haka ya juya ya koma yanda ya baro ta,
Shi dai Uncle Deen yana jinsa amma ya kasa cewa komai saboda Marshall yana shirin bashi dariyar da rabonsa daya yi tin yana yaro ƙarami....

Marshall tsayawa yayi shima yana fuskantar ta saida yayi gyaran murya kafin ya soma magana kamar haka
"Am da farko dai sunana Marshall Mohandas daga ƙasar U.S,
ke ina son jin sunanki....."

Ƴar Amana gyara tsayuwarta tayi idonta akansa, ta ɗago da hannunta ɗaya tana yiwa mutanenta alamar su gaya masa,
Gaba ɗayansu a tare suka buɗe baki waren faɗin
"ƳA DAGA ALLAH...."

ɗan zaro eyes ɗinsa ya yi cike da mamaki ya ce "kenam daga sama ta faɗo?...."

baki a haɗe wajen cewa "kana tantama ne?...."

Dasauri yake girgiza musu Kai alamar "a'ah..."

sunkuyar dakai yayi ƙasi yana maganar zuci "Tabb Jesus Christ! ban taɓa ganin Aljana ba eyes to eyes ba sai yau...."
bai ankara ba yaji ta ɗago hannu sama ta riƙo haɓarsa sai faman juyar masa da idanu take,
cikin rashin fahimta yake binta da kallo jikinsa har ɓari yake jin Aljana ta taɓa shi,
wata tsohuwa ce ta ce "tana maka alamu ne daka zo kuyi rawa...."

zaro ido waje ya yi tare da faɗin "Rawa kuma?
okay tam ku jirani ina zuwa....."

Juyawa yayi ya nufi motarsu, yana isa ya kuma tsayawa a jikin motar yana fuskantar Uncle Deen ta glass ya ce "wallahi Major tsoronta nake ji kuma tace muyi rawa...."

murmusawa Uncle Deen ya yi sannan ya ce "kar ka damu mutum ce kamar kowa, kaje kayi abinda ta saka...."

Marshall ya ce "okay tam kunna mana waƙa...."

Ba musu Uncle Deen yasa hannu ya kunna Audio domin yana son faranta mata so yake yaga murmushinta ko sau ɗaya ne....

Kafin Marshall ya isa wajen har Ƴar Amana ta fara cashewa da rawa jin sautin ƙida mai daɗi, shima Marshall jujjuyawa ya fara yi yana rawa,
kafin kace mai sauran mabaratan ma duk sun mimmiƙe suma suka fara jujjuyawa da masu ƙarfin jiki da marasa ƙarfin jikin duk rawan suke,
Gurage suma haka suke rawa a zaune, Kutare suma salon rawansu daban yake har da makafi,
a wannan lokacin kowa ya kasance cikin farin ciki da annashuwa,
Ƴar Amana ganin yanda tsofaffi suke cashewa yasata kwashewa da dariya ba tare da sautin ya fito ba, wannan dariyar da tayi akan idon Uncle Deen tayi shi,
Dariyar ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba shima yana zaune ta cikin motarsa bai san lokacin da ya sake wata ƙayatacciyar murmushi ba,
babu wanda yasan da mutum acikin motar domin Black glass gare ta,
Marshall shima lokaci guda ya tsinci kansa cikin farin ciki duk wata damuwa babu ita,
wasa-wasa shima ya zage sai girgizawa yake yana tintsirewa da dariya,
saida sukayi rawarsu mai isarwa sannan yaje ya ɗebo tilin maƙudan kuɗaɗe yazo ya rarraba musu,
ya tafi yana ɗaga musu hannu cikin nuna farin ciki, suma sunyi matuƙar farin cikin kasancewa da shi,
Da haka Uncle Deen yaja mota suka tafi cikin kewar rashin ganin Dreamer sa.....


𝙄𝙉𝙏𝙀𝙍𝙑𝘼𝙇



Da yamma liss misalin ƙarfe 5 Baiwar ALLAH tana zaune a ɓangaren swimming pool wanda ya kasance a bakin ruwan akwai jerukan kujeru na alhurma masu ƙayatarwa da tables, hakan na nufin waran shakatawa kenam, tana zaune akan kujera ita kaɗai tasa ruwa a gaba wanda ya kasance launin blue gare shi,
tayi tagumi da duk kan alamu doguwar tunani ta faɗa,
fuskarta ya nuna tsananin damuwa ƙarara ita kaɗai tasan matsalar dake damunta,
tana cikin wannan tunanin taji an dafa kafaɗarta, a zabure ta miƙe tsaye tare da juyowa tana son ganin wanda yake bayanta,
Ganin Roshan yasa ta kawar da kanta gefe tana faɗin "taya kasan ina nam?...."

dogon numfashi ya sauƙe tareda faɗin "Ummy ce ta sanar mun cewa taga kinyo nan, wai me yake faruwa ne naga kamar bakida lafiya...."

"Lafiya ta ƙalau...." a takaice tayi maganar fuskar ta na kallon gefe,

Murya ciki-ciki ya ce "Ammata me yasa kike gudu na? bakya son haɗuwa dani! Abbah ya ce na ɗauke ku ke da Ummy kuje ku zaɓi kayan furnitures amma ke sam kin ƙi zuwa sai da iya Ummy na tafi,
me yake faruwa?...."

Hawaye ne yake shirin zubo mata tayi saurin sunkuyar dakai saboda kar ya gane a taƙaice ta ce "babu komai, bani da lafiya ne ..."

A ruɗe ya ce "Subhanallahi Ammata bakida lafiya shine baki sanar mun ba? meye amfanin aikin likitanci na indai bazan iya kula dake ta hanyar bada magani ba..."
ya jawo ta jikinsa yana faɗin "gaya mun me yake damunki? bana son ganinki cikin damuwa...."

lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka daman jira take a taɓota tayi kukan da ya tsaya mata a rai,
a firgice ya zaro handkerchief ɗinsa daga aljihu yana ƙoƙarin goge mata hawayen fuskarta,
shima kamar zai fashe da kuka yake faɗin
"Ki daina mun asarar hawayenki mai matuƙar tsada, dan ALLAH Ammata nah,
ina jin zafin haka a raina....."

Sam bata son Auren nan amma gaba ɗaya kamar wanda aka ɗaure mata baki ta kasa sanar masa,
Soyayyar Uncle Deen zai hallakata, ta kamu da matsanancin sonsa bana wasa ba,
inta tuno cewa bashi zata Aura ba sai taji kamar ta hallaka kanta,
cikin takaici da baƙin ciki bata san lokacin data ɗago daga rungumar da yayi mata ba, tasa hannu da iya ƙarfinta ta ture shi baya daman yana dab da ruwa, ƙafarsa ta zame sakamakon tsantsin tiles dake wajen ya yi baya ya tsunduma cikin ruwan swimming pool,
Da sauri ta nufi hanyar fita daga part ɗin tana kuka, har ta fara hawa saman beni zata fita ta waiwayo bayanta jin ko motsinsa bata ji acikin ruwan,
Gaba ɗayansa ya nutse ciki sai saman ruwan da ya shafe,
A tsorace ta juya da gudun gaske ta nufi bakin ruwan tana ƙiran sunansa
"Ya Roshan! Ya Roshan!! Dan ALLAH ka fito kar ka mutu a ciki, na shiga uku na, banaso nayi sanadiyar mutuwarka dan ALLAH Ya Roshan, wayyo Allah nahhh...."

Ganin babu wata mafita yasa itama ta faɗa cikin ruwan, dake bata iya ruwa ba haka ta rinƙa facal-facal a cikin ruwan, tana nutsewa tana ɗagowa da haka itama ta nitse numfashi yana shirin ɗagewa,
Lokaci guda saiga Roshan ya ɗago saman ruwan yana riƙe da kunkumin Baiwar ALLAH, tana fitar da numfashi sama-sama har ta sume akan faffaɗar ƙirjinsa,
Ɗarata yayi saman kafaɗar sa yake yana taka matakalar da zai fidda shi daga cikin ruwan,
Kwantar da ita yayi a ƙasin tiles duk jikinsu a jiƙe jirip, a hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login