Showing 42001 words to 45000 words out of 117953 words

Chapter 15 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4742

Ummy girgiza kai tayi sannan tace "Allah Sarki su kuwa suna ganin kamar horaki suke yi, so nake sai Abbah ya sauƙa daga jirgi idan ya huta saina ƙira shi na sanar masa duk abubuwan da suke faruwa..."

Baiwar ALLAH riƙo hannun Ummy tayi sannan tace "please sister kimun wata alfarma...."
Ummy dasauri ta jinjina kai tare da faɗin "Yes inajinki..."

Baiwar ALLAH tace "dan girman Allah duk abinda akayi mun acikin gidan nan karki sanar wa Abbah, haka duk abinda za'ayi mun, wahala ne na rigada na saba tin ina yarinya saboda haka babu abinda zai sha mun kai akan duk aikinda za'a sanyani nayi, wannan shine Alfarmar da zakiyi mun,
Banason Abbah ya rinƙa tayar da hankalinsa akaina naga kamar bashida lafiya, nidai indai zan samu ci da sha kuma idan dare yayi zanyi bacci Alhamdulillah, ki kwantar da hankalinki ki rinƙa kawar da kanki akan duk abubuwan da za'ayi mun...."

Ummy idonta acikin na Baiwar ALLAH cike da tausayawa take kallon ta tace "gaskiya kinada kyakykyawar zuciya kamar yadda fuskarki take da kyau da ɗaukar hankali especially idan cikakken namiji yayi ido huɗu dake....."

Baiwar ALLAH bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba jin abinda Ummy take faɗi tace "ke dai kinada abun ban dariya wallahi....."

Murmushi Ummy tayi sannan ta ce "da zan rinƙa ganinki acikin yanayin farin cikin nan ai dana fi kowa farin ciki...."

Itama Baiwar ALLAH murmushi take ga dimple yanda yake lotsawa gwanin burgewa Lokaci guda ta ɗan sau fuska tana motsi da lips ɗinta idonta akan Ummy tanaso tayi magana amma saita fasa,
Ummy tace "ehen tell me, mai kike son cewa?...."

Da fara'a akan fuskar Baiwar ALLAH tace "Ni daman bayan ku akwai sauran ƴan gidan waɗanda basa nan?...."
Ummy tace "sosai ma suna nan tafe kwanan nan zaki gansu, jaruman gidan, su biyu ne amma tamkar mutane dubu suke,
Razhdeen da Roshan su ɗin twins ne, iya su biyu ne kawai basa nan...."

Baiwar ALLAH zaro ido tayi jin yanda Ummy take yabonsu ta jinjina kai sannan tace "nifah na ɗauka iya ku mata ne kawai babu yaro namiji, amma duk Hajia ce ta haife ku har su?....."

Ummy sauƙe numfashi tayi sannan tace "Kinga Aunty Baiwar Allah Ni yanzu yunwa nake ji, bari na tayaki yin girkin saboda mu gama da wuri munayi muna hirar mu...."

Baiwar Allah cikin nuna farin ciki tace "TOH shikenam...."

Ummy ta ɗauki blander ta fara niƙa kayan miya domin ferfesun chicken zatayi ita kuma baiwar Allah zatayi wainar masa,
Haka suka fara aikinsu gurin yayi tsit
Sai can bayan wasu mintuna Baiwar ALLAH tayi gyaran murya sannan tace "Sis baki bani amsa ta ba...."

Dariya Ummy tayi ganin yanda Baiwar ALLAH take son jin labarin su Razhdeen da Roshan, tace "yawwa kin tambayeni akan cewar Hajia ita ta haifesu koh?..."
tayi ajiyar zuciya sannan ta cigaba da cewa "gaskiya ba Hajiya bace ta haifesu ba, suma mamansu daban Ni kaina bansan mamansu ba, kai ƙarewa ma a yanda naji su kansu twins ɗin basu san mamansu ba saboda a lokacin data haifesu a ranar Allah yayi mata rasuwa, bayan wasu shekaru kuma Abban mu ya Auro Hajiyar mu Kinga itama mommy bata san mamansu Uncle Deen ba....."

Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta tace "Uncle Deen kuma du?...."

Murmushi Ummy ta kuma yi tare da faɗin "Uhm Uncle Deen shine Razhdeen haka muke ƙiransa dashi domin shiɗin ya cancanci sunan baya ɗaukar kansa a matsayin Yaya sai dai Uba hakan yasa ake ƙiransa da Uncle Deen shi kuma ɗayan sarkin Smiling Yaya Roshan muke ce mai, shi wannan a matsayinsa ya zauna na Yaya Kenam...."

Baiwar ALLAH jinjina kai tayi haka kawai sai murmushi take ta sauwa ta ce "amm kar kice na cikaki da surutu shin Yaya Roshan ɗin yanada yawan murmushi ne? Amma kuma zai iya kasan cewar kamar su ɗaya ko kamar yanda ake samun ƴan biyu masu kama ɗaya...."

Ummy ta juyo tana kallonta da murmushi akan fuskarta tace "suna kama amma ba sosai ba, shi Razhdeen yafi Roshan haske sosai kamar balarabe haka yake dake mahaifiyarsu Balarabiya ce ƴar ƙasar Makkah, toh Razhdeen ita ya ɗauko a kyau da farin fata sannan yana tara suma sosai akansa yanda kasan gashin mace macen ma ƴar India domin sumar kansa har gadon bayansa ga laushi kamar Audiga, sannan yanada ƙirar jiki sosai domin yafi Roshan tsayi da faffaɗan jiki da komai yafi Roshan, kasancewarsa shi ɗin Soja ne yana yawan motsa jiki,
Major general Razhdeen yanada matsayi sosai a ƙasar Australia....."
ta dakatar da maganar tare da juyowa ta kalli Baiwar ALLAH taga duk ta haɗa gumi sai faman zazzaro ido take,
Murmushi Ummy tayi sannan tace "jin yanayinsa kaɗai ya sanya ki cikin zulumi, TOH idan kika ganshi sai kinyi kamar zakiyi fitsari a jikinki saboda ganinsa yafin jin labarinsa firgitarwa,
Shi ɗin baya ra'ayin mace ko kaɗan, ko kallon mace baya son yi balle wai soyayya? kaiiiiii ko a mafarki ban taɓa jin ance ganan budurwar Uncle Deen ba, ƴan mata da yawa suna mararinsa amma sai dai suna shakkar kusantarsa, Uncle Deen baya dariya sannan baya son yin magana, baya son zaman cikin mutane bayason hayaniya, sannan baya son raini............"

Ummy bata ƙarasa maganar ba taji Baiwar ALLAH tana faɗin "dan ALLAH Sister ya isa haka, banason jin labarinsa just ki bani labarin Yaya Roshan nasan shi ɗin zamu fi jituwa domin na tsani mutum mai girman kai da jiji dakai....."

dariya Ummy tayi sannan tace "kodai kin tsunduma ne kema?...."

buɗe baki Baiwar ALLAH tayi da sauri ta ce "wa Kenam?..."

Ummy tace "shi Uncle Deen mana..."

Zaro ido waje tayi tana girgiza kai tace "waaaa koda wasa, wane Ni, dan Allah rufa mun asiri ina zaman lafiyata kar kisa na fara jin sauƙar ice a gadon baya na, zan tsaya a iya matsayina na ƴar aikin gidan babu ruwana ..."

Ummy jinjina kai tayi sannan tace "Allah sarki yanzu haka fuskar Yaya Roshan nake hasashowa da wannan kyakykyawar murmushinsa mai ƙayatarwa, shi ɗin na daban ne ga kyakykyawan zuciya ga asalin kyakykyawa ne shima na bugawa a jarida, fari ne shima tass amma bai kai Razhdeen ba, amma shi baya tara suma gaskiya yana yawan ɗora farin glass akan dara-daran idanuwansa masu kyan gaske......."
Bata ƙarasa maganar ba taji Baiwar ALLAH tace "kamar yadda kema kike ɗora glass akan dara-daran idanuwanki masu kyan gaske baaa...." ta ƙarasa tana gyara mata sakun glass ɗinta,

Ummy tace "ai shi Yaya Roshan idanuwansa lafiya lau suke kawai dai yanayin aikinsa na Doctor ne yasa yake yawa saka glass,
Ammm Roshan da Razhdeen sunada ɗan banbanci kaɗan saboda yanayin lips ɗin Razhdeen yaci jaaa sosai shi kuma Roshan lips ɗinsa maroon ne yanda kasan sweet lollipop, kuma gaskiya shima bashida kula ƴan mata amma akwai farin jininsu kam, shi Roshan abinda yasa ƴan mata suke tinkararsa saboda bai iya fushi ba kullum acikin Smiling yake, koda an ɓata masa rai bazai taɓa nuna cewar ransa ya ɓaci ba saidai kawai ya sharar domin baya riƙe mutum a ransa, shiyasa ba'a jin tsoronsa ga yawan wasa da dariya, abu ɗaya ne Yaya Roshan yafi tsana a duniyarsa shine wulaƙanci ya tsani yaga ana wulaƙanta mutum, kuma bashida ƙyanƙyami, ke Yaya Roshan pah yayi a rayuwa duk macen data samu Roshan wallahi tayi dacen samun masoyin gaskiya......"

Sauƙe dogon numfashi Baiwar ALLAH tayi tana riƙe da saitin zuciyarta tace "Wayyo Allah har na ƙagu dana ganshi wallahi...."

Ummy tace "Razhdeen ko Roshan?...."

Baiwar Allah turɓune fuska tayi tana ɗan hararar Ummy tace "wani Razhdeen ana zaune ƙalau, nifah tinda kika fara lissafo mun kalar ɗabi'unsa naji sam jinin mu bai haɗu ba, Ni ina ɓangaren Yaya Roshan ehen...."

Ummy tace "kar daiii...."
Baiwar Allah juyowa ta kuma yi tana kallon Ummy tasan mai take nufi dasauri Baiwar ALLAH ta girgiza kai tare da faɗin "dan Allah Ummy ki daina faɗin haka Kinga jiya-jiya nazo gidan nan banaso a fara samun matsala dani akan wannan al'amarin, kinsan yanda nake a cikin gidan,
wallahi koda wasa bawai inajin soyayyarsa bane kawai dai ɗabi'unsa sun burgeni ne ....."

Ummy ta ja numfashi tare da dafa kafaɗarta tace "na fahimce ki Aunty Baiwar Allah ki kwantar da hankalinki babu wata matsalar da zaki samu Insha Allah, Nima tsokananki nake....."

Gaba ɗayansu murmushi suka sau, suna cikin wannan halin sai suka ji an turo ƙofar kitchen da ƙarfi,
da sauri suka waiwaya suna kallon Minal wacce ta zuba musu ido sai faman harararsu take,
Tace "Inaso zan fita aiki kin kasa kammala mana girki tsabar rashin mutunci...." Idonta akan Baiwar ALLAH
sunkuyar da kai tayi ƙasi tace "kiyi haƙuri yanzu zan zo na shirya akan dinning na kammala....."

taja dogon tsuka sannan ta maida idonta kan Ummy tace "ke kuma uban mai ya kawo ki kitchen? Sarkin shishshigin international, kinada matsalar ido amma kina zuwa waran gass? Let Mommy come back zakiyi bayani...."

tana kaiwa nan tayi ficewarta,
Baiwar Allah tace "Kinga Ummy ki samu ki fita ba'a barinki kina shugowa kitchen ki temake ni, Kinga laifina za'a gani...."

Ummy tace "ai wallahi badan laifinki za'a ganiba babu Abunda zaisa nabar kitchen ɗin nan sai mun ƙarasa, kuma Abbah shima bayaso...."

Baiwar Allah tace "Nima na kammala yanzu zan fito da kayan abincin...."

Ummy ficewa tayi tana turo baki.......



*KAIIII WANNAN PAGE ƊIN KAMM DUK HIRAR BAIWAR ALLAH DA UMMY SUN CIKA MANA GURI 😅😅😅....*



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 19 to 20



꧁꧂


Bayan Baiwar ALLAH ta kammala shirya kayan breakfast akan dinning itama ɗaukan nata tayi ta wuce bedroom ɗinta, kujerar Minal yana fuskantar na Ummy, suma twins suna facing juna sai ƴar Tiny ata gefen Ummy ko wacce tana carkwane plate ɗinta da spoon babu mai kula kowa a cikinsu, har suka kammala, Minal ficewa tayi zata gurin aiki wato Banker anan take aikinta ita ce manager na bank, itama ƴar Tiny fita tayi da gudu tana sanye da kayan uniform hannunta riƙe da lunch bag akwai security da yake kaita school, twins kuma ɗakinsu suka nufa domin har yanzu hutunsu bai ƙare ba da zarar hutu ya ƙare zasu koma ƙasar London, ita kuma Ummy tsaya kwashe plate ɗin dake dining ta tsaya yi domin ta ragewa Baiwar ALLAH aiki, ita kuwa fur taƙi yin karatu tin daga sacondary ita in ba'a Nigeria ba baza tayi karatun ba amma tanason zama Doctor kamar Yayanta Roshan,
tana shirin shiga kitchen da kuloli da plate a hannunta saiga Baiwar ALLAH itama ta fito da plate ɗin data ci abinci, fuska ɗauke da murmushi ta ce "ke dai Ummy bakya jin magana ko? yanzu idan Hajia ta shugo ta tarar dake fah?...."
Ummy tace "to bari kiji kafin kizo ina taya ƴan aikin gidan nan aiki kuma babu yanda aka iya dani, don haka babu abinda zai fasaya, Uhmmm kina wasa da uwar masu gida Kenam...."
Baiwar ALLAH girgiza kai tayi tana dariya ta ce "sannu uwar masu gida, dole a ganki a ƙyale..."
Ummy ta ƙarasa da cewa "ƙwarai kuwa ko matar gidan ce tayi jayayya dani dole zata bar gidan...."
Baiwar ALLAH zaro ido tayi waje ta toshe bakinta da hannu bibbiyu tare da faɗin "naaa shige su, wallahi rufa mun asiri..." ta shige cikin kitchen da sauri, itama Ummy dariya take ta shige kitchen,

Suna shiga Ummy ta kalli Baiwar ALLAH da take shirin yin wanke-wanke tace "Aunty Baiwar ALLAH ki kawo nayi wanke-wanke sai kije ki shirya Kinsan zamu fita yin shopping koh? Abbah ya bani kuɗin da za'ayo miki siyayya..."

Baiwar ALLAH tace "lala kedai jeki fara shirin ki kinga Ni ina gama wanke-wanke zan fara wanki...."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login