Showing 57001 words to 60000 words out of 117953 words

Chapter 20 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4752

Roshan ta ce "ur welcome Son..."

Shima yana ɗauke da murmushi ya ce "thank you Hajia, fatan na sameku lafiya..."
kamar baza tayi magana ba can ta ce "we are all fine..."
ya ce "Ok thank God...."

Abbah ya ce "Amm Roshan kaje ka rage kayan jikinka kayi wanka sai kuzo ga kayan abincin da aka tanadar muku, gaba ɗaya zamu haɗu a dinning ne inka fito sai kayi wa Razhdeen magana...."

ya ce "okay Dad..."

Har ya fara haura saman stairs ɗinsu ya dawo yana baza eyes,
Abbah ya ce "lafiya kuwa?...."

yana ɗauke da ƙayataccen murmushi ya ce "where is my love?...."

Abbah murmushi yayi domin duk gidan babu wanda bai san ita kaɗai yake ƙira da haka ba, shima Abbah cewa yayi "Nima sauran kaɗan na tambayeta ka rigani..." ya kalli Pinky ya kuma cewa "wai ina Uwar masu gida ne? ban ganta ba tinda na shugu...."

Pinky ta ce "uhmm tana ɗakin Baiwar ALLAH..."
Abbah ya ce "ha'a toh su fito falo mana, ita uwar masu gida tasan lover ɗinta ya dawo shine bazata zo yi masa oyoyo ba..."

Rukky tayi saurin cewa "Abbah Baiwar ALLAH ganin Uncle Deen yasa ta sume shine Ummy ta tafi kaita ɗakinta...."

Abbah kallon Hajia yayi yaga ko Annuri babu a fuskar nan ya ce "ikon ALLAH, ita kuma ganin Razhdeen ya sata suma, ba shakka indai Razhdeen ne kaɗan Kenam daga aikinsa....."

Roshan ganin bai fahimci maganganunsu ba yasa ya haura upstairs tare da faɗin "saina sauƙo..."

Bayan haurawarsa da mintuna talatin saiga Ummy ta fito tana tura lips cikin sakalci take jumping da sawayenta tace "Ni har yanzu My love bai shugo bane?....".
Pinky tana zaune idonta akan Ummy tana harararta ta ce "ke dillah bama son hauka...."

Ummy turo baki tayi ta ce "Ni bada ke nake ba kiyi mun shuru...."

Rukky ta ce "tselan uwa sakalcin banza dan ma bake bace Autar yau da an shiga uku ...."

Ummy tana nuna Rukky da yatsa tace "Kee nutsu ki kama kanki ai ba'a kanku nake ba...."

Abbah ya katse su da cewa "Kinga uwar masu gida jeki masoyin nakin yana can ɗakinsa,.."
ya kalli su Pinky ya ce "ku kuma babu ruwanku da ita..."
Rukky tace "ai wallahi Abbah kai kake goya mata baya shiyasa ta raina mutane..."

Abbah ya ce "ku kuka jawa kanku raini dai, yanzu da bakuyi mata shishshigi ba ai baza tayi ƙoƙarin gaya muku magana ba...."

Pinky ta kalli Rukky sannan ta ce "zo mu koma ɗaki..."
suka wuce suna turo baki, sai ya rage daga Abbah sai Hajia sai kuma ƴar Tiny wacce itama tashinta kenam wai zataje gurin Uncle Deen.

Abbah ganin har zuwa yanzu Hajia bata saki fuskarta ba yasa ya matsa kusa da ita ya riƙo hannayenta yana murzasu a hankali idonsa akan fuskarta
ya ce "ya akayi ne matar bindiga?..."

Kallonsa tayi sannan ta ƙara kawar da fuska gefe ta ce "babu komai..."
Yace "no kina cikin damuwa ne yakamata ki sanar mun koh? tinda na dawo yau sati guda amma babu walwala kodai nayi miki laifi ne?...."

Girgiza kai kawai tayi alamar a'a tace "bana jin daɗin jikina ne..."
"Meya same ki?"
yayi maganar cikin sassanyar murya,
kamar zata yi kuka ta ce "marata ciwo....."

murmushi yayi domin yasan damuwarta ya kamo hannunta ya ɗago da ita yana faɗin "sorry my dear muje daga ciki ko kafin yaran su fiffito dinning...."

tashi tayi itama tana murmushi suka haura upstairs yanda part ɗinsu yake ....



A Ɓangaren Doctor Roshan yana kwance saman katafaren gadonsa wanda yasha gyara ɗakin sai fitar da ƙamshin turare yake, yana lumshe da ido kamar meyin bacci tsabar zunzurutun gajiya,

Ummy ce ta turo ƙofa cike da zumuɗin ganin masoyinta kuma ɗan uwanta, shugowa falon tayi taga wayam babu kowa sai jerin tsararrun kujeru na alhurma ga plasman a manne a jikin bango sai showing indian Film ake, gefe guda kuma wani ɗan ƙaramin frig ne gwanin burgewa, sai kuma ƙaramin dinning table wanda iya mutum biyu kawai yake ɗauka, falon ya tsaru sosai,
Murmushi Ummy tayi a fili tace "yanzu haka yana cikin bedroom ɗinsa..."
tana zuwa dab da bakin ƙofar bedroom tasa hannu tana knocking a hankali gudun kar ta kutsa masa kai tsaye bata san a wani hali yake ba,

Yana kwance yaji ana knocking ido a lumshe ya furta "Yes come in...."

turo ƙofar tayi ta shugo tana ganinsa a kwance tayi gudu ta nufi yanda yake tayi tsalle ta faɗa masa jikinsa tana dariya....

shima dariyan yake ya ce "kai kai Kaiii my love wannan ai saiki karyani irin wannan tsalle haka...."
Ta ɗago tare da faɗin "oyoyo my love wallahi nayi kewarka sosai, amma kai baka damu dani ba tinda har ka shugo baka nemeni ba......"
ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa

jan kuncinta yayi yace "Ni na isa naƙi damuwa da uwar masu gida wane niii, kina raina sosai kamar yanda nake ranki tinda naga kullum saikin ƙira masoyinki Roshan a waya...."

Dariya tayi ta ce "yawwa Yaya Roshan ina tsaraba taa..."
Saida ya tashi zaune yana fuskantar ta ya ce "tsaraba kam sunanan lodi-lodi sai kin zaɓa kin darje kafin sauran su ɗauki nasu...."

ta ce "wow shiyasa nake ji dakai Yaya Roshan ɗina saboda kaima kana ji dani ...."

yana kallonta fuska ɗauke da murmushi
ya ce "ya za'ayi bazan damu dake ba? kepah kinada darajoji da yawa a gurina...."

zaro ido Ummy tayi tare da bugan ƙirjinsa tace "kaiiii Yaya Roshan toh lissafo mun...."

Saida ya gyara zamansa tukun ya fara cewa "na farko ke mai sunan Hajiyar mu ce marigayiya wato mahaifiyar Abban mu wacce tin muna jarirai take riƙe damu, ita ta sakaltar damu, bata son ko cinyaka ta cije mu, duk abinda muke so zatayi ƙoƙarin yi mana, shiyasa muke matuƙar ji da kakar mu har Allah ya karɓi rayuwarta,
Na biyu kuma again sunan my first lover gareki, Allah sarki Maryama ta mutumiyar kirki ga yawan fara'a, kyakykyawar hallita lokaci guda nayi rashinta, da yanzu na tabbata munada ƴaƴa amma mutuwa tayi mun yankan ƙauna, a waɗanda nafiso a raina daga mahaifiyata wacce ta rasu sanadiyar haihuwar mu sai kuma Kakar mu wacce tayi rainon mu har rai yayi halinsa sai kuma Abar ƙaunata Maryama wacce tayi hatsarin mota tabar duniya....."

Ummy Turi baki tayi cikin shagwaɓa ta ce "Kenam Ni banda Ni acikin sahun masoyanka? daman nuna soyayyarka bai je zuciya baaa...."

Yaya Roshan ya ce "ki fahimce Ni My love! inada waɗanda nake so da yawa, waɗannan wanda na lissafo su sune sukafi soyuwa a cikin zuciyata, in hakane ai ban lissafo da Abbah ba kuma Kinga ai bazance bana sonsa ba...."

Ummy fuska a turɓune ta ce "toh wacece ta huɗu?..." tayi tambayar a shagwaɓe,
ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya ce
"My man! wato twins ɗina Razhdeen sai ta biyar kuma itace Uwar masu gida wato my love...." ya ƙarasa yana jan kuncinta ya cigaba da cewa
"sai na shiga kuma Abbana, sai kuma sauran masoyana waɗanda suke sona nima nake son su....."

Ummy tana jinjina kai ta ce "wato Ni ce ma ta biyar uhmmm hakane...."
tintsirewa yayi da dariya yana jan lips ɗinta domin ba ƙaramin dariya ta bashi ba,
Saida suka gama shan hirarsu sosai kafin ya tashi yana faɗin "uhmmm my love idan na biyeki sai mu kwana muna zance, yanzu dai bari na shiga wanka, naji Abba ya ce gaba ɗaya zamu haɗu a dinning kar su fara jiran mu...."

Itama Ummy tashi tayi ta ce "TOH my love idan ka kammala muna jiranka a ƙasi...."
Ɗaga mata hannu yayi tare da shigewa toilet.....

Bayan fitar Ummy kai tsaye part ɗin Uncle Deen ta nufa tana zuwa ta tsaya a bakin ƙofa tana knocking a hankali domin tasan halinsa muddin ta shiga bada izininsa ba saiya korota duk da baya yawan zama a falonsa sai dai idan wani aiki zai yi a computer yakan zo falo ya zauna akan sopa computer kuma tana kan ƙaramin glass table na tsakiyar falon,
tana cikin knocking taji muryar ƴar Tiny tana faɗin "yeshhh coming..."

Ummy acikin ranta tace "shegen iyeyi har wani yesh coming..."
shugowa tayi da sallama a bakinta ta tarar da Uncle Deen yana zaune sai faman danna computer yake ita kuma ƴar Tiny tana gefensa da wani ƙaton Biscuit mai madara a hannunta, motsa baki kawai Uncle Deen yayi ba tare da anji mai ya ce ba, amma alamu ya nuna cewar amsa sallamar yayi,
zuwa tayi ta zauna gefen ƴar Tiny tace "Uncle Deen your welcome...."
a taƙaice ya ce "Ok" ba tare da ya ɗago ba,
Ɗaga kafaɗa Ummy tayi alamar bata damu ba, domin kaɗan Kenam daga halayen Uncle Deen, inka san halin mutum saika sha maganin zama da shi....

Ummy kallon ƴar Tiny tayi sannan ta ce "Tiny ɗan sammun biscuit ɗin mana, Kinga babu kalar shi a Nigeria na daɗe banci ba...."

Ƴar Tiny hararar Ummy tayi sannan ta ce "wayyayi tayyayi balan bayal ba, ki tambali Unkui Deen mana...."

Ummy cikin ɓacin rai ta ce "shegiya mai tsatstsamar baki....." bata ƙarasa maganar ba taga Uncle Deen ya jefo mata wani irin kallo har sai da ta razana, ga yanayin juyowar nashin yasa sumar kansa wantsilowa zuwa fuskarsa sai dara-daran idanuwa kake gani ta cikin sumar gashin,
Haka ƙirjinta yake bugun uku uku sai yanzu ta tuna ashe ba'a zagin Ƴar Tiny a gabansa saboda takwarar mahaifiyarsu ce wato FATIMA BINTU, sunan mahaifiyarsu Razhdeen da Roshan, shine aka sanyawa ƴar Tiny sunanta,
Amma Razhdeen da Roshan basa ƙiranta da ƴar Tiny saidai Mama...

Ummy tashi tayi suƙu-suƙu zatayi waje yayi saurin dakatar da ita tare da nuna mata wata ƴar jaka wanda cikinsa zallar biscuit ɗin ne, jiki ba ƙwari haka taje tasa hannu ta ɗauka tare da yin godiya,
idonsa akan computer ya ce "tsarabar Mamana ne saboda haka a ita zakiyiwa godiya...."

Ummy ta kalli ƴar Tiny tace "Nagode Tiny..."

turo baki ƴar Tiny tayi sannan ta ce "a shaye zaki yi mun gojiyar? ki durkusha kashi kimun gojiyar....."

wani irin yawu na baƙin ciki Ummy ta haɗiya cike da jin haushin ƴar Tiny ta durƙusa da gwiwowinta ta ce "Nagode sosai Ƴar Tiny...."
ta miƙe idonta akan Uncle Deen wanda yasa hannu yana ture sumar kansa zuwa baya eyes ɗinsa akan computer ko kallonsu bai yi ba,

Ummy taja ƙafa zata fice taji Uncle Deen yayi magana,
Dasauri ta waiwayo tana kallonsa ta ce "na'am!..."
Domin sam bata ji me ya ce ba, amma taji kamar yayi mata magana, murya ne kamar ba'a halitto shi ba bayason fitar da Muryar,
Shi kuwa a ƙa'idarsa magana sau ɗaya yake yi baya maimaitawa,
Jin yayi mata shuru ya cigaba da uzurinsa yasa ta kalli ƴar Tiny ko zata temaka ta maimaita mata abinda ya ce,

Ƴar Tiny tana tura biscuit a ɗan ƙaramin bakinta ta ce "waiii Keee kuymiya ce? aka ce kije ki kiyawo An uwanki shu jo Nam...."

Ɗaga kai Ummy tayi tare da faɗin "tam shikenam...."

Dasauri tabar ɗakin domin ba ƙaramin ƙuluwa tayi da ƴar Tiny ba,
A cikin ranta kuwa cewa tayi "wannan ƴar Tiny saina ci ubanki wallahi, ƴar Banza kawai tsatstsamar bakinki ma ya isheki...."

Da wannan takaicin ta sauƙa falo tana sauƙa kuwa ta tarar da su gaba ɗaya suna zazzaune, tazo ta tsaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login