Showing 78001 words to 81000 words out of 117953 words

Chapter 27 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4758

da shinkafa da nama akai ya ɗeba yakai saitin ɗan ƙaramin bakinsa wanda daƙer yake buɗe su,
yana kai abincin cikin bakinsa tauna ɗaya biyu ya sandare guri ɗaya, haka ya tsayar da bakin ya dena motsa shi ƙwayar idonsa akan abincin dake cikin plate.........



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 35 to 36



꧁꧂


Tsabar kiɗimewa da shiga ruɗanin da Baiwar ALLAH tayi gaba ɗaya ta susuce hannunta a sama ta ƙanƙame idanuwanta sosai saboda gudun halin da zata ga Uncle Deen, ta rigada ta saddaƙar yau kashinta ya bushe, haka jikinta yake ɓari kamar wacce take cikin ruwan ƙanƙara....

cikin yanayin rashin jin daɗin bakinsa haka ya burtso da abincin bakinsa cikin plate ɗin abincin yana yamutsa fuska, tinin har fuskar yayi jawur abunka da farin mutum, ba komai ne yasa haka ba illa tsananin ɓacin rai da ya shiga lokaci ƙanƙani,
Ɗagowa yayi a fusace yana wurga mata wani irin la'anannen kallo wanda zaisa mutum sumewa wata ƙil tacan ya rasa rayuwarsa, Allah ya temake ta idanuwanta a rufe suke rub sam bata ƙaunar haɗa ido da shi,

wani irin tsawa ya daka mata cikin fitar hayyaci, kamar daga sama taji sauƙar tsawar a firgice ta zaro da manya-manyan eyes ɗinta tare da ƙafesu guri ɗaya tsabar tsananin ruɗanin data shiga bata san lokacin da ta fara sakin fitsari a jikinta ba, haka jikin yake kakkarwa kamar mai farfaɗiya...

Ganin halinda ta shiga cikin lokaci ƙanƙani yasa ya sassauta muryarsa idonsa akanta ya ce "wani irin dabbanci ne wannan? You want kill me?...."

Baiwar ALLAH dai ido a ƙafe zuwa yanzu ta daina kakkarwar da take sai dai bata motsi kwata-kwata, already ya rigada ya fiskanci halin da take ciki bata cikin hayyacinta, tashi yayi yana jan ƙafa daƙer ya shige bedroom ɗinsa kai tsaye toilet ya shige, yana shiga ya ɗauki brush tare da matsar makilin yayi brush sosai, Saida ya tabbatar baya jin ɗanɗanon gishirin tukun ya wanke bakinsa ya fito,
ya ƙara nufan falo still yanda ya barta anan ya dawo ya sameta a ƙafen bata motsa koda ɗan yatsarta ba ma..
Buɗe frig yayi ya ɗauki farror mai sanyi ya tako har yanda take a durƙushe already ya buɗe murfin robar ba tare da ya tsiyayi ruwan ba haka ya fara kwara mata ruwan da bakin robar a saitin fuskar ta, a razane ta motsa tare da sakin nannauyar ajiyar zuciya haka take fitar da numfashi sama-sama daƙer, har eyes ɗinta sunyi jawur...

Durƙusawa yayi a gabanta yana kallon cikin ƙwayar eyes ɗinta rai a ɓace ya soma faɗin "ba suma zakiyi ba ko mutuwa zakiyi yau sai kin ɗanɗani kuɗanki, sai kin girbi abinda kika shuka, saboda rainin wayo zaki kawo mun abinci mai gishiri?....."

Fashewa tayi da kuka ta soma faɗin "wallahi ban sani ba...." kafin ta ƙarasa faɗin abinda zata ce yayi saurin daka mata tsawa tare da faɗin "shut up! your very stupid, I don't want to breath your smelling mouth,
abinda nake so dake shine yanzu ki tashi kije ki cinye duk abincin nan....."

Baiwar ALLAH tin tinin ta haɗiye kukanta, jin ya ce taje ta cinye abincin yasa ta ɗago a razane tana kallonsa....

zaro mata ido yayi yana faɗin "Now! Now my friend...."

wani irin haɗiyar yawu tayi mai kama da fitar rai, jiki na ɓari ta tashi tana jan ƙafa ta nufi dinning tana kuka,

ya ce "oyah seat down...."
ya nuna mata kujerar dinning, tazo zata zauna anan ya lura da jiƙar kayanta da sauri ya dakatar da ita tare da faɗin "wait! don't seat here, Meya kawo wannan jiƙar a kayanki ?..."

dasauri takai idonta kan kayan jikinta tanata faman dubawa eyes ɗinta ne suka sauƙa akan rigarta ta wajen mazaune ruwa sai faman ɗiga yake,
a ruɗe ta ɗago tana kallonsa cike da tsoro da fargaba, shi kuwa ƙwayar idonsa ya wurgar saitin wajen da ta zauna before, yaga wajen duk jiƙar ruwa,
juyowa yayi ya kalleta tare da faɗin "whattt! kina nufin kice fitsari kika mun a carpet? ....."
jinjina kai ya soma yi domin yau ɗin nan ba ƙaramin ɓata masa rai Baiwar ALLAH take ba, idan ya ce zai ɗau hukuncin abubuwan da tayi masa zai iya raunanata ne, tsabar ya rasa abinda zai yi kuma ya rasa abun cewa
Dogon tsuka yaja sannan ya ce "i hate You wallahi, because of you are an ingratitude fool,
Now ki cire mun wannan ƙazantar da kika mun akan carpet ki fita mun dashi daga room, kije ki wanke sannan ki dawo ki gyara mun room, akwai new carpet in order part from outside ki ɗauko ki saka mun a room, zan shiga nayi bacci sauran kuma ki tashe Ni kiga ikon ALLAH....."

yana kaiwa nan yayi shigewarsa cikin bedroom, yana shiga ya shige toilet domin yin wanka...."

Baiwar ALLAH sauƙe numfashi tayi tana bin ƙofar bedroom ɗinsa da kallo cike da mamakin rashin imaninsa da tausayi, ɗago kai tayi ta kalli agogo taga ƙarfe 3 sauran mintuna,
Ga idanuwanta yanda sukayi lufu-lufu suka kumbura lokaci guda ga wani irin baccin da take ji amma babu halin yi,

Girgiza kai tayi sannan ta nufi tsakiyar filin falon tana ƙare ko ina da kallo, tana nazarin ta yanda zata fara ɗaga kujeru kafin ta samu damar cire carpet ɗin, babu yanda ta iya haka ta fara jan kujerun a hankali tana zamar da carpet, da iya ƙarfinta take janye sopas har tayi nasarar cire carpet ɗin gaba ɗaya, sai dai ɗaukar carpet ɗin ma wahala domin ba ƙaramin nauyi gare shi ba, irin mai gashi nan ne, daƙer take jan carpet har ta fice daga falon, nan ma sauƙa daga kan beni ma aiki ne babba,
cikin ikon ALLAH ta fice da carpet ɗin waje can bakin fanfo waran wanki, sannan ta wuce yanda sabin carpets suke taje ta zaɓo masa carpet mai kyau kalar kujerunsa sannan ta koma part ɗin Uncle Deen, nan ma taje tasha wahalar shimfiɗa carpet ta jejjera kujerun a yanda suke a tsare, sai falon ya ƙara kyau sosai gwanin burgewa,
tana gamawa da wannan ɓangaren ta koma waran dinning tana tura baki acikin zuciyar ta kuwa cewa tayi "wallahi bamai saka Ni naci wannan abincin...."
tasa hannu ta ɗauki kulolin gaba ɗaya ta nufi hanyar waje dasu zata kai can kitchen....

Shi kuwa Uncle Deen bayan ya fito daga wanka iya jallabiyarsa ya zura sannan ya tsaida sallah daman already ya haɗo da alwalarsa,
yayi sallolin lafulfuli sannan ya tashi ya cire rigar jikinsa ya zauna daga shi sai 3 quater da singlet a jikinsa saida ya feffeshe jikinsa da turare sannan yabi lafiyar gado,
duk waɗannan aikace-aikacen da Baiwar ALLAH tayi bai sani ba domin shi tin tinin bacci yayi gaba da shi....

Baiwar ALLAH dawowa cikin room ɗin tayi ta goggoge dinning ɗin da ya ɓaci da maiƙon ferfesu....


Doctor ROSHAN yana kwance saman katafaren gadonsa yana fuskantar ceilling, yanda yaga rana haka yaga dare ya kasa yin bacci, tunanin Baiwar ALLAH ya hana shi sukuni, fuskarta kawai yake gani a saman ceilling,
Ganin ya kasa yin bacci yasa shi miƙewa zaune yana dafe da goshinsa tsabar tsananin ciwo da yake masa, daƙer ya tashi yana jawuwa ya nufi toilet
Ba jumawa ya fito da damshin ruwa a jikinsa alamun wanka yayi haɗi da alwala domin shimfiɗa sallaya yayi ya tsaida sallah bayan ya zura farar jallabiyarsa.....



Baiwar ALLAH bayan ta kammala komai a ɗakin Uncle Deen ta dubi agogon ɗakin ƙarfe huɗu da rabi na asuba,
jiki a sanyaye tasa hannu zata buɗe ƙofar falon ta wuce kafin ta ankara da hakan ta soma jin surutai acikin bedroom ɗin Uncle Deen,
A tsorace ta waiwaya baya tayi tunanin da ita ake, ganin bata ga kowa ba kuma ga maganganun da ake yi kamar ba lafiya ba,
da sauri ta nufi bedroom ɗinsa tasa hannu a hankali ta tura ƙofa ta shige,
zuciyarta na dar-dar abun mamaki gani tayi Uncle Deen gashi nan a kwance ido a rufe amma yana wani irin surutai sai faman juye-juye yake gaba ɗaya ya haɗa gumi jikinsa yayi sharkaf duk da sanyin A.C dake ɗakin,

"Why! Why!! Why!!! I don't like it, ki bayyana kanki please, aina zan same ki, idan har ke mutum ce I need to see you bana so ki rinƙa wahalar dani da wannan sautin naki, ki mun adalci, banaso! banaso!! banasooo!!!!, zan kashe ki i swear, I swear I'll kill you........"

Haka yake haɗa zaƙami yana wannan surutan, hannunsa yakai saitin kansa ya riƙe sosai yana faɗin "Wayyo kaina, Wayyo kaina zai fashe ciwo ku temake Ni ....."

Baiwar ALLAH ganin halinda yake ciki ba ƙaramin tausaya masa tayi ba, kuma duk acikin baccin yake waɗannan maganganun..
Ganin yana shirin zaucewa yasa ta nufi har yanda yake kwance da gudu, hannunta ne ya soma ɓari tana son temaka masa amma sai dai tana tsoro,
idan ya fara wannan abun nashi Allura ake masa ya dawo normal, ita kuma a halin yanzu ta rasa mai zata masa, haka ta fara tunanin ko taje ta sanarwa Abbah ne ko Roshan,
wani dabara ne ya faɗo mata da sauri ta shige toilet taje ta jiƙo towel da ruwan sanyi ta dawo a tsorace ta ɗan haura saman gadon da yake ta ɗora masa jiƙaƙƙen towel ɗin akan goshinsa,
jikinsa ne yake kakkarwa sosai ga jikinsa yanda ya ɗau zafi jin sanyi yana ratsa shi yasa ya sau nannauyar ajiyar zuciya baisan lokacin da ya jawo Baiwar ALLAH saman faffaɗar ƙirjinsa ba tare da rungumarta sosai still jikinsa na kakkarwa kaɗan-kaɗan, a tunaninsa yarinyar da ta juya masa baya tana kiɗan jitarta ita ya runguma domin a wannan lokacin yayi nasarar riƙota sakamakon ruwan da aka saka masa,
basa son ruwa kwata-kwata aljanun yarinyar da suke jefa shi cikin wannan halin a yayinda yake cikin baccinsa,
wani irin sauƙe numfashi yayi cikin lokaci ƙanƙani hankalinsa ya kwanta daga nan ya wuce da ainahin baccin da yake,
Baiwar ALLAH tsoro ne ƙarara a saman fuskar ta, ga yanda ya rungumeta ko kwakkwaran motsi ta kasa yi,
haka jikinta yake ɓari itama saboda tsoro da fargaba ......



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 37 to 38



꧁꧂


Baiwar Allah tana Saman ƙirjin Uncle Deen har aka fara ƙiran sallar asuban farko basu motsa ba,
ta kasa motsawa sai zuciyarta dake bugun uku-uku, gaba ɗaya ta haɗa gumi sharkaf ji take kamar ta haɗiyi ranta tsabar tsoro da fargaban Uncle Deen da zaran ya tarar da ita a haka,
Sam bata runtsa ba gaba ɗaya bacci ya ƙaurace mata,
ƙiran sallah ne ya daki dodon kunnensa a hankali ya fara juyar da kansa Ido a lumshe, hannunsa ya ɗago daga kan Baiwar Allah ya ɗora kan goshinsa yana fitar da numfashi sama-sama, a hankali Baiwar Allah ta ɗago da kanta tana fuskantar sa, manyan idanuwanta ta sauƙar kan kyakykyawar fuskarsa a tsorace take kallonsa ganin yana mutsil-mutsil da eyes ɗinsa yana shirin buɗesu Wani irin juyi tayi bata san lokacin data faɗo daga saman gadon ba har saida ƙafarta ya gurmuɗe, buɗe baki tayi zatayi ihu jin zafin ciwon ƙafar dasauri tasa hannu a saitin bakinta ta rufe ruff tinin ta haɗiye kukan, tana zazzaro Ido...

Shi kuwa jin nauyi a kansa ne yasa ya buɗe eyes ɗinsa gaba ɗaya yana kallo ceiling, jujjuyar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login