Showing 39001 words to 42000 words out of 117953 words
ya ƙara ƙarfafa mata gwiwa tana daddanna jitar tana bada sautin, itama Baiwar ALLAH tana can tana rera waƙar, haka kowa yake jiyo wa ɗan uwansa...
Yana kwance akan lallausar gadonsa mai girman gaske yana lumshe da kyakykyawan idanuwansa ga kyakykyawar fuska kamar mai yin murmushi, a hankali yake shan baccinsa kamar a mafarki yake jiyo sauti mai daɗin gaske da kuma murya mai kashe zuciya suna dukan dodon kunnensa, ganin kamar ba'a cikin mafarki yake jiyowa ba yasa ya fara buɗe eyes ɗinsa a hankali yana lumshe su gwanin burgewa, jin har yanzu bai daina jin sautin da muryan da ake rera waƙar ba yasa ya ƙara miƙewa zaune yana waige-waige, tashi yayi a hankali yana taku har ya isa bakin ƙofar bedroom ɗinsa yana shirin buɗewa yaje falo ko plasman ne a kunne, har yakai hannu zai buɗe idonsa ya sauƙa akan window dake bai gama sauƙar da labulayen ba, wani irin haske yake gani ta waje yanata tashi mai farfatsin wuta kala-kala, cike da mamaki yaje jikin window yasa hannu ya ƙara buɗe labulen yana kallon wannan hasken, ga sautin kiɗa yanda yaketa tashi sannan zazzaƙar murya yana kan dukan dodon kunnensa, wani irin sanyi ne ya fara ratsa shi a hankali yake lumshe idonsa,
Sautin kiɗan da yake ji ba ƙaramin kashe masa jiki yayi ba,
A hankali yake motsi da lips ɗinsa ido a lumshe ya ce "WHO is dis girl? me suke nema a gareni?...."
still bai buɗe idonsa ba ya cigaba da cewa "ƴan mata biyu! ɗaya tana kaɗa jita, ɗaya tana rera waƙa, kullum saikun zo mun a mafarki yanzu kuma sautin kiɗa da kuma sautin Muryar ku sun fara bayyano mun a zahiri shin me kuke nema a gareni? shin ku ɗin aljanu ne ko mutane? ku bayyana mun kanku mana, ku daina azabtar da zuciyata haka, ku daina hanani bacci please, idan wani abu kuke buƙata ku bayyanar mun da kanku,
Ku gaya mun me kuke so! me kuke so!! me kuke so!!!
I said tell me what do you want from meeeee......"
A tsawace ya ƙarasa maganar tare da bugan jikin glass ɗin window da ƙarfin gaske har sai da ya dagargaje glass ɗin, hannunsa yaji rauni sosai daiden lokacin da komai ya ɗauke cakk babu hasken nan sannan babu sautin kiɗa kuma babu Muryar waƙar,
ya faɗa saman gadonsa yana caccakuɗa sumar kansa tare da yin ihu tsabar juyawar da kansa ke yi ga wani irin ciwonda yake yi haka yake ihu har sai da sojoji masu gadinsa suka jiyo ihunsa, da gudu suka turo ƙofar bedroom ɗinsa bayan sun wuce ƙaton falonsa, kamar yadda suka saba haka sukayo kansa suna faɗin "Ogah sorry, what's wrong sorry sorry..."
Saida sukayi masa allurar da ake masa kullum kafin hankalinsa ya dawo jikinsa sai kuma ya wuce da yin bacci...
Daman kullum hakane da ihu yake tashi daga bacci na fitar hayyaci domin ba'a cikin hankalinsa yake ba, sakamakon mafarkin ƴan mata biyu da yake yi kuma sun gagara bayyana masa fuskokinsu wannan karan kuma sai sautin muryar ɗaya da kuma sautin kiɗan ɗaya sun bayyano masa a zahiri, idan ya tashi a wannan halin akwai allurar da ake masa wanda shi yake dawo dashi hayyacinsa daga nan kuma saiya wuce dayin bacci,
Har fargaban kwanciya bacci yake saboda wannan matsalar shiyasa yake so ya koma Nigeria ya samu Abbansu suyi magana akan lamarin ko za'a iya temaka masa,
Bayan ya koma baccinsa Sojojin ne suka fice masa a ɗakin kowa ya koma kan aikinsa.....
Baiwar ALLAH tana kammala waƙar daga nan haske ya ɗauke itama kanta ne ya fara juyawa ta rasa a wani duniya take, daƙer take ja da baya har ta faɗa saman gadonta tana dafe da goshinta nan danan bacci yayi awun gaba da ita.....
Ƴar Amana tana dakatar da kiɗan hasken wajenta ya ɗauke itama dafa kanta tayi sakamakon juyawar da yakeyi nan danan ta faɗi a ƙasin wajen daga nan ta nemi hankalinta ta rasa......
Wannan al'amarin daya faru Aljanun Ƴar Amana ne masu wannan aikin,
a iya mutum uku kawai suka bayyanar musu da wannan sirrin
Daga ƴar Amana sai kuma BAIWAR ALLAH da kuma Major general Razhdeen, bayan su babu wanda zai iya jiyo sautin kiɗa da kuma muryar Baiwar ALLAH, waɗannan hasken sune masu aika saƙo,
Sukan ɗauki sautin kiɗan Ƴar Amana su aikawa Baiwar Allah dake Nigeria sannan su ɗauki muryar Baiwar Allah su aikawa Ƴar Amana dake bakin Teku a ƙasar Misra, su kan ɗauki muryar da kuma sautin su aikawa Major general Razhdeen dake ƙasar Australia,
Kasar Misrah nan Aljanun Ƴar Amana suka kaita bakin Teku....
𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.
𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦♀️🤦♀️
𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢
𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.
𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈
ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..
𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:
1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.
2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.
3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.
4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.
𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 17 to 18
꧁꧂
Washe garin ranar Monday da safe Baiwar ALLAH tana kwance kan gadonta har zuwa wannan lokacin bata samu farfaɗowa ba, da ƙarfin gaske aka turo ƙofar ɗakin cikin zafin nama,
Hajia Kilishi ce ta tsaya tana binta da kallo tare da taɓe baki tace "iyeee ƴar hutu, yarinya an samu guri dole a wataya uhmm hakane...."
Dasauri ta nufi toilet taje ta ɗebo ruwa a bucket tana fitowa ta kwara ruwan nan gaba ɗaya akan Baiwar ALLAH dake kwance tana dafe da goshinta,
a ruɗe ta farfaɗo tana jan numfashi sama-sama, gaba ɗaya a firgice take, daƙer ta iya saita hankalinta ta tsaida shanyayyun idanuwanta akan Hajia kamar wacce tayi shekaru tana jinya duk ta rame ta zamo kalar tausayi,
bata ankara ba taji Hajia Kilishi ta zabga mata mari tare da faɗin "tashi dan ubanki, Ni zaki rinƙa yiwa irin wannan kallon? yau zan ga waye gatanki acikin gidan nan, General ya tafi yanzu kallo ya koma sama, dan haka ki biyo ni falo yanzun nan...."
ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsuka ta fice..
ita kuwa Baiwar ALLAH tana zaune hannu akan fuska, wasu zafafan hawaye ne suka fara gangaro mata, da haka ta tashi ta nufi toilet tayo alwala sannan ta fito tayi sallar asuba domin yau ta makara sosai ƙarfe 7 yanzu haka,
Bayan wasu mintuna ta kammala tare da jero addu'o'inta sannan ta miƙe zatayi hanyar fita da zureren hijab ɗinta saiga Minal ta shugo da bala'inta ganin Baiwar ALLAH yasa ta tsaya tana balbaleta da masifa "ke wato dan kin raina mutane tin ɗazu matar gidan tazo da kanta ta ƙiraki amma ki ƙi zuwa dan buro ubanki! saboda kin mayar mutane Mahaukata koh?....."
Baiwar Allah kamar zata fashe da kuka tace "kuyi haƙuri Sallar Asuba nayi....."
bata ƙarasa maganar ba taji Minal ta kamo kunnenta ta murɗa da ƙarfin gaske tana faɗin "sallo kinji koh, ƴar gidan akharami taho munafuka kawai...."
taja kunnenta suka fice falo, ba ƙaramin murɗe mata kunne tayi ba da haka har suka ƙarasa cikin falon yanda sauran mutanen gidan suke suna isa Minal ta wurgar da ita ƙasin carpet,
Ga Hajia Kilishi tana zaune ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya sai hararar Baiwar ALLAH take, sai kuma ƴan mata biyu twins suma suna zaune a kujera ɗaya ko wacce idonta akan wayar hannunta, sai Minal wacce zamanta Kenam akan kujera idonta akan Baiwar ALLAH,
Ummy ce kawai bata nan tana can ɗakinta bata farka ba ita da ƴar Tiny...
Hajia tana kallon Baiwar ALLAH tace "na ƙira ki shine zaki ɓata mun lokaci koh ?...."
Baiwar ALLAH ɗagowa tayi tace "Hajia Sallah.........". bata ƙarasa maganar ba taji an harba mata baki da ƙafa ɗagowa tayi da rinannun eyes ɗinta tana kallon Minal wacce ita tayi cankin, nan danan lips ɗinta ya fashe sai jini dake takalmi mai tudu ne a ƙafarta, su ko ina zasuje da takalmi a ƙafarsu, kwanciya ne kawai idan zasuyi suke cire takalmi...
"Idan na sake jin anyi magana kema kin buɗe wannan ruɓaɓɓen bakin ki kema kinyi Uhmmm kin san sauran...."
Hajiya Kilishi idonta akan Baiwar ALLAH tace "Meye sunanki?..."
A hankali tace "Baiwar ALLAH...."
cikin zafin rai Hajiya Kilishi tace "kowa ma ai bawan Allah ne dan ubanki..."
Baiwar Allah tayi shuru kai a ƙasi,
Hajia Kilishi ta cigaba da cewa "Inaso ki sani cewa wannan gidan bawai kin shigo shi saboda hutu bane, baccin safen nan dakatar dashi zakiyi saboda bakida ƴancin yin baccin safe sai masu gidan,
wacce take zuwa yi mana aiki a gidan nan yau na sallame ta saboda bana tara ƴan aiki, guda ɗaya nake riƙewa, saboda haka ki ɗaura ɗamaran yin aikin daya dace acikin gidan nan,
aiki na farko shine zaki tashi da asuba ki fara share-share da goge-goge su dinning table da kitchen, kujerun falo da plasman da frig gaba ɗaya zaki goggoge ba saina lissafo miki ba kema kinsan abinda ya dace,
daga nan zaki haura upstairs kije kibi ɗakunan yarana duk ki gyaggyara musu ki wanke musu toilet gaba ɗaya, sannan ki sauƙo ki haura upstairs saman ɗakina ki shiga nan ma ki gyara mun sannan ki wanke toilet,
ɗakin mijina kuma ban baki izinin shiga ba,
Bayan kin kammala sai ki shiga kitchen kiyi mana girke-girken abun breakfast, kuma kece zaki rinƙa mana girki kullum daga safe har rana har na dare sannan ki tattara ki wanke kwanuka,
Still idan kayan yarana sunyi datti zasu tattaro miki kije ki wanke musu tass ki goge musu, ƙarin ayyuka kuma sai matasan gidan sun dawo zakiyi bayani, Kinga can?......"
ta nuna Upstairs part ɗin su Razhdeen ta kuma cewa "wancan part ɗin duk ɗakunan gidan nan baya su girma domin ko wani ɗakinsu akwai falo da kuma bedroom da toilet duk sai kin shishshiga kin gyara musu da zaran sun dawo sannan kina kammala girki ko wanne zaki kai mishi ɗakinsa ne saboda su basa cin abinci acikin mutane, kowa da dining ɗinsa acikin room ɗinsa,
Ki shirya yarinya ba hutu kamar yanda kika tsara yi......."
Hajia Kilishi tana iddasawa ta tashi tayi hanyar fita tare da faɗin "Ni zan wuce gurin aiki saina dawo, sannan ke kuma Minal banaso kina makara a wajen aikin ki, ki samu ki shirya ki tafi....."
Minal tace "toh Mommy sai kin dawo..."
itama tayi maganar tare da miƙewa tsaye zata haura upstairs idonta akan Baiwar ALLAH ta ce "Madam zaman mai kike yi? bazaki fara aikin bane?...."
Baiwar ALLAH tashi tayi tana girgiza kai alamar a'ah...
Dasauri ta miƙe ta fara karkaɗe kujerun falo tana goggogesu,
Suma su Pinky ne suka tashi tare da faɗin "ga can tilin kayan wankin mu idan kin kammala aikin gida saiki hau wanki kuma....". suka ƙarasa tare da haura saman stairs.
tinda Baiwar ALLAH ta fara aiki bata tsaya ba saida ta kammala share-share da goge-goge harda su kitchen da gyaran ɗakunan gidan gaba ɗaya dasu wankin toilet sannan ta shiga kitchen zata girka abun breakfast, tana cikin aikinta saiga Ummy ta shugo tana jinjina kai tace "kinsha aiki sosai Aunty Baiwar Allah, sannu da ƙoƙari...."
juyowa tayi da murmushi asaman fuskarta tana kallon Ummy tace "ai Ni aiki baya ban wahala, yanda kasan wasan yara haka na ɗauki aikatau, ai motsa jiki ne, yawan kwanciya ma illah ne....."