Showing 6001 words to 9000 words out of 117953 words

Chapter 3 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4725

yasa hannu ya zabgeta da wani irin gigitaccen mari har saida ta faɗi ƙasi ta kife, ɗagowa tayi hancinta har ya fashe sai ɗigo da jini yake tana ta kar kaɗa masa hannu alamar magiya akan yayi haƙuri ya ƙyale Baiwar ALLAH, ta kama ƙafarsa tana girgiza masa kayi, haka yasa ƙafa ya yi filli da ita gefe nan ma dungura, bakinta yanata kakkarwa kamar zatayi magana amma babu halin yi, a wannan dungurawar da tayi har tsintsiyar hannunta ya karye sakamakon faɗuwar da tayi akan hannun, amma babu wanda yasan hannun ya karye sai mutsil-mutsil take tayi tana ƙoƙarin tashi sai ga wasu zankaɗa-zankaɗan motoci baƙaƙe manya-manya sai sheƙi suke waran motoci guda biyar sun nufo hanyar da zai kawo su har cikin harabar gidan...

wasu ɗirka-ɗirkan sojoji ne suka fara fito wa masu ƙwarjini wanda ko ido baza kaso ka haɗa dasu ba, saida sojojin nan suka gama fitowa duk suka jejjeru kowa da manya-manyan bindigunsu a hannu, ɗaya daga cikin sojojin ne ya buɗe murfin ɗaya daga cikin motocin bayan mintuna ƙalilan saiga ƙafar wanda aka buɗewa gwanin burgewa sai gashi ya fito gaba ɗaya mutumin yana sanye da wata danƙareriyar shadda sky blue da hula kalar shaddan, takalmin ma kalar kayan, yana sanye da wani ɗan siririn farin glass akan dara-daran idanuwansa, mutumin fari ne tass kyakykyawa dashi, dattijo yanada farin gemu amma akwai ɗaukar ido, fuskarsa kuwa yana ɗauke da kyakykyawan murmushi....


Wakilin gidan marayun wato Yallaɓai ganin Chief of Army's ne yau ya kawo ziyara yasa jikinsa ya ɗau kakkarwa, alamun rashin gaskiya ne suka bayyana mishi, yana tunani a ransa cewa "meyasa General zai zo amma ba notice, zuwan ba zata innalillahi, ALLAH yasa dai kar ya kama mu da laifi... "

cikin gaggawa aka kawo wa General gurin zama da lema, haka kowa ya rinƙa zuwa yana gaishe su, saida kowa ya isar da saƙon gaisuwa tukun Chief of Army's
General Muhammad Zaiduddeen Bature yakai idonsa kan yarinya dake zaune a ƙasin floor duk jini ya wanke mata fuska ta ƙura idonta akansa ko ƙibtawa bata yi,

General miƙa mata hannu ya yi alamar tazo yanda yake,
Ƴar Amana ƙoƙarin tashi ta soma yi jin hannunta a karye yasa ta koma ta zaune tana kuka,

General kallon yanda Yallaɓai yake ya yi shi kuwa ganin kallon da akayi masa ne yasa shi cewa "Am amm Ammm yarinyar Kurmiya ce bata ji sannan bata gani amma akwai rigima..."

General ya ce "bashi na tambayeka ba shin meya faru da ita?..."

Muryar Yallaɓai ne ya soma kakkarwa yana faɗin "wallahi General a bishiya ta faɗo, taje wancan bishiyar mangoro ne saboda rigima ta hau ta faɗo, yanzun nan case ɗin da akeyi kenam kuka shugo..."

Jinjina kai General ya yi sannan ya ce "duk ina kuke kallo har yarinya zata hau saman bishiya bazaku dakatar da ita ba? wannan sakaci ne da rashin kula da yara..."

sunkuyar da kansa ƙasi yayi yace "sorry General lokacin babu kowa ata wajen..."

Duk sauran mutanen gidan sun jinjina irin girman ƙaryar da Yallaɓai ya zabga lokaci guda...
General ne ya tura wani soja ɗaya akan yaje ya dubo Ƴar Amana ko akwai ciwo a jikinta bayan fasuwar hanci da bakin...
Sojan saida ya yi checking natan sosai kafin ya gano cewar harda karaya a hannu nan kuwa ya sanar wa General,
General zare glass ɗin idonsa ya yi tareda faɗin "whatt! ta karye kuma? Oya kuyi hanzarin kaita hospital right now..."

Ɗaya daga cikin ma'aikatan ce tazo ta ɗago da Ƴar Amana, idonta kuwa akan General tana ta masa magana da ɗayan hannunta mai lafiya tareda girgiza masa kai tana nuna hanyar da aka kai Baiwar ALLAH...
Shi Yallaɓai ya fahimci abunda take gaya amma sai dai shi ɗin General bai fahimta ba amma shima idonsa akanta yana son gano wani abu acikin zancen zucin da take yi kuma tanata jujjuyar da hannu...

Yallaɓai cikin gidan marayun gudun kar General ya fahimci abunda Ƴar Amana take son aikar da saƙon yasa ya yi saurin cewa "Ammm General yarinyar bata son allura ne shiyasa take ta karkaɗa maka hannu, kuma ga dole za'a ɗora mata hannu zata sha azaba..."

"Okay" abunda General ya furta kenam, nan da nan yasa sojojinsa suka fara sauƙar da buhunan shinkafa da kayan abinci sannan yasa aka rabawa duk matan dake cikin gidan manya-manyan atampopi masu kyau da tsada da kuma kuɗaɗe haka yasa duk aka rarraba musu,
ya bayar aka ajiye wa Ƴar Amana tatan wacce tin ɗazu har sun tafi hospital da ma'aikaciya ɗaya,
saida aka gama rabo tass banda Baiwar ALLAH dake can acikin duhun ɗaki ba haske ko kaɗan sai tarin sauraye....

Suna kammalawa Chief of Army's General Muhammad Bature da sojojinsa suka tafi.....


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (3)



꧁꧂


Bayan tafiyar su General sauƙe ajiyar zuciya Yallaɓai yayi sannan ya ce "Nagode wa ALLAH, na tsallake rijiya ta baya..."
Ganin yanda matan wajen suka zuba masa ido yasa ya turɓune fuska tareda faɗin "me kuka tsaya gani munafukai kawai..."
kafin kace mai duk suka watse a gurin, domin ba ƙaramin tsoronsa suke yi ba.


Ƴar Amana tana hospital tareda ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan, sai kumbura take tayi cike da tsanar Yallaɓai domin a yanzu babu mutumin data fi tsana irinsa, kuma ta ɗaura ɗamarar yaƙansa domin cikin ranta ruruwa yake tsabar takaicin abunda Yallaɓai yayi musu ita da Baiwar ALLAH,
Ga hannu an ɗaɗɗaura mata ƙarafuna ji take kamar daga asibitin nan ta gudu amma sai dai bazata iya guduwa tabar Baiwar ALLAH ba...

Baiwar ALLAH kuwa tana cikin ɗakin duhu a zaune ta kifar da kanta saman gwiwowinta tayi kukan har ta gaji, ga sauraye sun isheta ga kuma wani irin murɗa da take ji tsabar yunwa, a yanzu babu tunanin da take yi illa halin da Ƴar Amana take ciki, ta ƙagu tasa ta a idonta domin ba ƙaramin tausayinta take ji ba,
tana zaune har dare bata yunƙura ba sannan babu alamar motsin mutum, sai can misalin ƙarfe 12 na dare kowa da kowa yayi bacci saita fara jin motsin mutum a tsorace ta miƙe tsaye zuciyarta na bugun 3+3 tana tunanin har ta saddaƙar domin ta tabbatar da Yallaɓai ne, zai iya zuwa mata a kowani lokaci balle yaga ta fake gefe guda...
ji tayi ansa key an buɗe ƙofar a hankali aka shugo, bata iya ganin ko waye ba saboda tsananin duhun ɗakin, saida aka kunna hasken torch sannan taga ashe Aunty Habiba ce wacce take kula dasu, murya na kakkarwa Baiwar ALLAH ta ce "Aunty Habiba kece 🥹..."
Dasauri Aunty Habiba tasa hannu ta toshe mata baki alamar tayi shuru, a hankali ta soma cewa "Yallaɓai ya ce kada wanda yazo gurin da kike balle a kawo miki abinci ko ruwan sha, kuma ba'a san ranar fitar dake daga cikin wannan akurkin ba, nima a ɓoye nazo Ni domin na tabbatar Yallaɓai ya tafi gidansa zuwa anjuma zai iya dawowa ya bincike ki, yanzu abinda nakeso dake shine zan fitar dake a ɓoye ki gudu ki bar wannan gidan domin rayuwarki tana cikin hatsari Baiwar ALLAH..."

Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "Aunty Habiba yanzu idan kika fitar dani shin baza kiyi laifi ba?..."
Aunty Habiba ta ce "kar ki damu dani babu wanda zai san Ni na fitar dake..."
Baiwar ALLAH taja dogon numfashi sannan ta ce "a gaskiya bazan iya tafiya nabar Ƴar Amana ba, ban san a wani hali zata kasance ba..."
Aunty Habiba ta dafa kafaɗarta ta ce "Baiwar ALLAH kar ki damu zan kula da Ƴar Amana sannan itama zuwa wani ɗan lokaci zan fitar da ita..."
Girgiza kai Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "a'ah gaskiya ki bar Ni kawai, insha ALLAHU zuwa gaba ALLAH zai kawo mana mafita ta wani hanya, domin nasan idan na fita bansan ina zan nufa ba, rabon dana leƙa cikin gari tin zuwana wannan gidan ina ƴar yarinya ta, yanzu bansan ya kalar garin yake ba, zan iya fita na tarar da waɗanda zasu kashe Ni ko su sace Ni, zan cigaba da zama tareda ƴar uwata Ƴar Amana...."

Aunty Habiba ta ce "shikenam Baiwar ALLAH duk yanda kika yanke Ni dai ina tare da ke, kuma bazan iya barinki da yunwa ba dole kullum zan rinƙa kawo miki abinci kuma kinsan yau da gobe sai ALLAH asiri na zai iya tonuwa shiyasa naso ki gudu, amma tinda kin ƙi bazan gajiya ba, ga wannan leda abinci ne a ciki idan kin ci saiki jefar da ledar ta cikin wancan ƙofar sannan ga pure water..."

Baiwar ALLAH rungumar Aunty Habiba tayi tana kuka ta ce "Nagode sosai Aunty Habiba amma ina tsoron kar a kama ki, da kin barni hakan nan idan ALLAH yaso zan rayu zan cigaba da rayuwata..."
Aunty Habiba tace "hakane amma bazan iya barinki da yunwa ba Baiwar ALLAH, yanzu dai zan tafi kar azo a ganni..."
har Aunty Habiba ta juya zata tafi Baiwar ALLAH ta tsayar da ita tareda faɗin "Aunty Habiba banyi sallah ba, dan ALLAH ki temaka mun zanyi sallah..."

Aunty Habiba ta ce "tashin hankali yanzu ya zanyi? Amma jira Ni ina zuwa..." Da sauri Aunty Habiba tabar wajen ba tareda ta rufe ƙofa ba, cikin ƴan mintuna sai gata ta dawo hannunta rinƙe da butar Alwala tana zuwa ta shiga cikin akurkin ta kunna light, ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin babu Baiwar ALLAH ta fice, waige-waige ta soma yi tana faɗin "ina kuma taje? Na shiga uku...."

ajiye butar hannunta tayi sannan ta nufi compound ɗin ɗakunan yaran dasauri zata hau upstairs gida na sama sai taji ana buɗe gate ɗin gidan Yallaɓai ya dawo da mota zai shugo, gaban Aunty Habiba ne yayi wani irin yanke wa addu'o'i kawai take jerowa domin tasan halin Yallaɓai bashida mutunci, da gudu ta ƙarasa hawa saman beni kai tsaye ɗakin da Baiwar ALLAH suke ta nufa domin zata iya cewa zata gano Ƴar Amana, tana buɗe ɗakinsu kuwa saiga Baiwar ALLAH tana rungume da Ƴar Amana sai kuka suke ta sha,

Aunty Habiba ƙarasa shugowa tayi a ruɗe tana faɗin "yanzu Baiwar ALLAH abunda zakiyi mun kenam? so kike asirina ya tonu to Yallaɓai ya dawo kuma nasan zai iya zuwa yanda kike ya dubo ki..."
Baiwar ALLAH a ruɗe take kallon Aunty Habiba ta ce "bazan iya wuni guda banga Ƴar Amana ba..."
Aunty Habiba bazata iya jin abunda Baiwar ALLAH zata ce ba
a gaggauce tasa hannu zata jawota su koma kwatsam Ƴar Amana ta riƙe Baiwar ALLAH sosai tana girgiza kai alamar babu yanda Baiwar ALLAH zata je...

Aunty Habiba ta kalli Baiwar ALLAH sannan ta ce "ki sani cewa zaman ki a cikin ɗakin duhu shine zai ceceki daga tozarcin da za'ayi miki, yanzu kuwa idan har Yallaɓai ya ga kin fito toh kuwa zai iya ƙudurta abunda yayi niyar yi miki, saboda haka ki temaki kanki kizo mu koma kafin ya ankara dake..."
Baiwar ALLAH jin abunda Aunty Habiba ta faɗa yasa ta fara janye jikinta daga na ƴar Amana tana ƙoƙarin zamewa ita kuwa Ƴar Amana ta ƙanƙameta sosai da hannu ɗaya taƙi sakinta, Baiwar ALLAH tana binta a hankali saboda kar ciwon hannunta ya fame amma ita Ƴar Amana fur taƙi sakinta daƙer Aunty Habiba tasa hannu suka fincike hannun ƴar Amana wanda ta riƙe, da gudu suka fita itama ƴar Amana tabi bayansu kafin ta iso bakin ƙofar Aunty Habiba taja ƙofar ta rufe ta kulle ta baya...
a hankali suke bin jikin gini suna tafiya, da haka har suka sauƙa daga saman beni kafin su wuce dole sai sun bi ta gaban bakin ƙofar office ɗin Yallaɓai kuma gashi ƙofar a buɗe take haske ta ko ina, ƙafewa sukayi a gurin suka rasa yanda zasuyi, Aunty Habiba ce ta ɗan leƙa cikin office ɗin taga yanata bincika wasu takardu, ganin haka yasa ta kamo hannun Baiwar ALLAH suka wuce da gudu kafin ya ɗago,
Daiden lokacin da Yallaɓai ya ɗago gani yayi kamar wurgawar mutum, tsaya kallon bakin ƙofar ya yi kafin daga bisani ya miƙe tareda nufan bakin ƙofar ya fice, waige-waige ya tsaya yi amma baiga alamun mutum ba ga haske ta ko ina, girgiza kai ya yi sannan ya koma ciki a tunaninsa mutanen ɓoye ne suke wasa saboda yanzu misalin ƙarfe 1 ne na dare, kuma babu wanda zai iya shugo gidan saboda security dake can bakin gate, kuma babu wanda zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login