Showing 45001 words to 48000 words out of 117953 words

Chapter 16 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4737

zaro ido Ummy tayi rai a ɓace jin an ambaci wanki tasan kayan Yayunta ne tace "wankin kayan uban wa zakiyi acikin gidan nan?...."
Baiwar ALLAH juyo wa tayi tana kallonta jin yanayin furucinta cike da mamaki ta ce "wankin kayan Uba nah....". sannan ta juyo ta cigaba da wanke-wanken ta,
Ummy ganin ran Baiwar ALLAH ya ɓaci yasa tazo dab da ita ta dafa kafaɗarta tace "sorry Aunty Baiwar ALLAH Amma maganar gaskiya baza kiyi wanki acikin gidan nan ba, matsayinki ya wuce wannan kema saidai ki bada naki a wanke...."

juyowa Baiwar ALLAH tayi tana fuskantar Ummy ta ce "please Ummy ki daina shiga shirgin nan, Ni duk abinda akace nayi zanyi iya ƙoƙarina naga nabi doka a zauna lafiya, Meye acikin wankin? duk ba motsa jiki bane? yawan hutu ma illah ne, koda na kasance mai ƴanci acikin gidan nan
I swear to God bazanyi rayuwar irin wannan hutun ba ace komai baza kayi ba saidai ayi maka, bazan iya ba, Inaso ki kwantar da hankalinki ki nutsu, kema ba cewa kikayi kina son aiki ba? so ki barni nima nayi komai lokaci ne, kina ganin kamar cutana suke yi da suke sakayi aiki koh? to wallahi sona suke ba wai ƙiyayya bane, duk wanda zai sakaka kayi abu mai amfani to wallahi sonka yake, shin idan nayi Aure wazai mun? shin idan nayi Aure ban iya aikin gidan miji ba ko girke-girke yazanyi? nidai a gidan mijina bana buƙatar ƴar aiki sam bana so,
shin baki san aikin nan da nakeyi lada nake samu agurin Ubangiji bane? TOH Inaso ki sani Ni ban iya rayuwar hutu ba, motsa jiki kawai na sani, kuma yanzu ne damar da nake dashi yanda zan koyi komai na ayyukan gida da makamancin su,
please ƴar uwa banaso ki ƙara yin magana akan aiki domin rashin yin aikin cutuwa ne a gareni matuƙa....."

Ummy tana zubda ƙwallah ta ce "Nima Insha ALLAH bazan zauna ba, dole tare zamuna aikin gida....."

Baiwar ALLAH tace "ke kam babu halin yin aiki saboda......."
bata ƙarasa ba taji Ummy ta katseta da cewa "wallahi babu wacce ta isa ta hanani ko ita wacece, kuma mata ta taɓani taga ikon ALLAH saidai suyi barazanar su amma babu wacce ta isa ta taɓa mun tsokar jikina...."

tana kaiwa nan tayi ficewarta rai a ɓace kai tsaye upstairs ta haura yanda zai kaita ɗakinta,
Baiwar ALLAH girgiza kai tayi a ranta tana jinjinawa Ummy sam bata jituwa da mahaifiyarta kamar ba ita ta haifeta ba......

Around 4 O'clock na yamma Baiwar ALLAH ta kammala duk wasu ayyukanta tayiwa su twins wanki sannan tayi girke-girke na abincin rana ta sake yin gyaran gidan sannan tayi wanka ta sanya kayan da Ummy ta ɗauko mata wata Abaya mai shegen kyau da duwatsu masu sheƙi da gyalensa ba ƙaramin kyau tayi ba dake kayan milk ne sun karɓeta sosai duk da ba wani kwalliya tayi ba, tana tsaye a jikin mirror tana ƙare kanta da kallo, jira take Ummy tazo ta ɗauketa su fita yowa shopping domin tana fargaban fita falo da kayan Ummy a jikinta, kaya ma masu tsadar gaske....
tana cikin wannan halin tajiyo muryar Ummy daga falo tana masifa tare da yin kuka, muryarta kawai kake ji daga ƙarshe ta fashe da kuka, a tsorace Baiwar ALLAH ta nufi falo da gudu zuciyarta na ɗarɗar gudun ganin abinda zata tarar,
tana zuwa ta tarar da Ummy a durƙushe a ƙasin carpet sai rera kuka take kamar wacce aka mata duka, sai kuma Minal a zaune wacce bata juma da dawowa ba sai ƴan mata twins dake tsaye sunyi cirko cirko suna huci ko wacce ranta a ɓace, Minal ganin Baiwar ALLAH sanye da rigar Abayar Ummy sai kuwa ta miƙe tsaye a fusace ta ce "Keee! Uban wa yace ki saka rigar nan mai bala'in tsada? ....".
Itama Ummy ta miƙe tsaye tana fuskantar Minal ta ce "kada ko wacce ta kuskura tayi mun maganar rigar nan saboda ba taku na ɗauko ba, riga ta ce inada ikon da zan yi kyauta da ita...."

ta kalli Baiwar ALLAH sannan tace "Aunty Baiwar ALLAH kukan da nakeyi kukan baƙin cikin sace kuɗin da Abba ya bani ya ce muje nayi miki siyayyan kayayyaki ne, Million 3 haka ya bani cash amma yanzu naje ɗauka ban gani ba, kuma acikin su ne wata ta ɗauke ko kuma suka haɗa baki suka sace...."

Pinky ta ce "ke Ummy dakata kar ki sake cewa an sace saboda mun fi ƙarfin three millions wallahi, a yanzu haka cikin account ɗina inada kuɗin da sukafi ƙarfin ten millions, kuɗin da kike magana akai kuma Mommy ce tace muje mu ɗauko mata su indai a wannan ƙazamar za'ayo siyayya.....". ta ƙarasa maganar tana nuna Baiwar ALLAH....

Ruky itama tsoma baki tayi tace "ƙwarai mommy ce take buƙatar kuɗin tace indai a wannan ƙwailar zakije yin shopping TOH gwara a ƙona kuɗaɗen domin ba ƙwalisa tazo yi cikin gidan ba...."

Minal zama tayi tana kurɓar coffee domin idan ƙananun ƙwari sunayi ita bata shiga zancen sai sun gama tukun,
Ummy kamar zata haɗiyi ranta tsabar takaici haka take binsu da harara,
suna cikin wannan halin saiga Mommy ta shugo ita da Ƴar Tiny ta dawo daga school itama,
zama tayi tareda jefa handbag ɗinta gefe tana sauƙe numfashi, ta ɗago tana bin yaran da kallo ɗaya bayan ɗaya cikin yamutsa fuska tace "wai meke faruwa ne?...."

kafin su fara yin bayani saida suka mata sannu da dawowa gaba ɗayansu, itama Baiwar ALLAH durƙusawa tayi har ƙasi tace "sannu da dawowa Hajia....."
Mommy ko kallon yanda take batayi ba, idonta akan Ummy wacce ita kaɗaice bata mata sannu da dawowa ba ga hawaye shaɓe-shaɓe a kan fuska,

Hajiya Kilishi tace "ke! kinfi ƙarfin mun magana ne?...."

Ummy tana kallon gefe tace "ai ba kullum nake a haka ba, kema Kinsan idan kika dawo Ni ce first ɗin yi miki magana, yanzu akwai matsala ne...."

Hajia Kilishi ta rigada tasan halin ɗiyarta Ummy idan ta birkice babu kwanciyar hankali kuma daman gado tayi gadon mai sunanta uwar mahaifinta Hajiya Maryama asalin masifaffiyar mata ce ta asali,
tana kallon Ummy tace "Meya faru?..."

Ummy juyowa tayi itama tana kallon Mahaifiyar tatan tace "kuɗin da kika sa aka ɗauko a ɗakina zaki ban...."
Hajia Kilishi tace "me zakiyi dasu?...."

Ummy cike da mamaki ta ce "me zanyi da kuɗin kuma? Ina gidan masu kuɗi ace mai zanyi da kuɗi?..."

Hajia Kilishi cikin ɓacin rai tace "ki kiyayi furucinki domin Kinsan a gaban wa kike a tsaye...."

Ummy tana fari da eyes ɗinta ta ce "eh na sani mana, a gaban matar gidan nake matar ma ta biyu...."

Hajia Kilishi ta miƙe tsaye tare da gyara tsayuwarta domin al'amarin Ummy yana shirin fin ƙarfinta jurewa kawai take ta ce "shin matar farko ce ta haifeki ko ta biyun?..."

Ummy tana karkaɗa yatsu tare da farfara eyes ta ce "ehhh TOH kamar dai mata ta biyu ce ta haifeni amma ina tantama akai saboda sam bata ɗauko halayya irin na uwa ta gari ba, Ni kuma zanso uwata ta kasance cikin nagartattun iyaye kamar dai mata ta farko...."

Hajia Kilishi hajijiya ne yake shirin ɗaukarta tana dafe da goshinta jin maganganun Ummy sun zurfafa,
A fusace Minal ta miƙe tsaye tareda daka mata tsawa ta ce "ya isa haka Ummy, daman rashin tarbiyarki har yakai haka? mahaifiyarki kike gaya mata maganganu son ranki?....."
Suma twins bakinsu a haɗe wajen cewa "kutmeleciii, jar uban nan, anya kuwa Mommy Ummy ƴarki ce kuwa?...."

Ummy tana harararsu ta ce "ai Ni dana fi kowa farin ciki inna kasance ba'a tsatson hajia kilishi na fito ba,
Kunga dallah ku mun shuru bada ku nake maganata ba, ko wacce taja bakinta tayi mun shuru,
Ni yanzu ba wani dogon jawabi ba a ɗauko mun kuɗina a bani ...."

Hajia Kilishi ganin inta biyewa Ummy zatayi sanadiyyar kamuwa da hawan jini domin babu haihuwar data sha wahala kamar haihuwar Ummy amma wai yanzu itace take tsaye a gabanta tana faɗa mata maganganu...
Idon Hajia Kilishi ne yayi jawur cikin sassanyar murya ta ce "Ummy babu Abunda kika rasa a cikin gidan nan shin idan na baki kuɗin me zakiyi dasu?...."

Ummy fuska a yatsine ta ce "temako..."

Hajia ta ce "duk cikin unguwar nan wa kikaga yana buƙatar temako?...."

Ummy ta ce "in babu acikin unguwa ai akwai acikin gari..."

Hajia Kilishi a tsawace ta ce "bazan bada kuɗin ba, ai nasan a wannan yarinyar duk zaki kashe kuɗin, saboda bawai tazo gidan nan saboda ɗaukan fashion bane aiki tazo yi ....."

Ummy a taƙaice ta ce "kika ce bazaki bada ba? Abbah ya bani kuɗi sannan ki karɓa kice bazaki bada ba?...."

Hajia Kilishi ce tayo kan Ummy cikin zafin nama kamar zata rufata da duka ta ce "Ummy nace bazan bada kuɗin ba ki dake Ni, kinji ko dake Ni nace...."

Ummy ja da baya tayi ganin jikinta dana mommynta yana shirin haɗuwa kamar masu dambe,
Murmushi tayi sannan tace "bazan dake ki ba mommy amma ki sani zanyi miki abinda yafi duka zafi, let Abbah come back, u will see what am going to do, I swear to God I'll break the secret,
Sirrin da kike ɓoyewa saina buɗa shi kowa ya sani, saina fasa ƙwai indai baki chanza wannan bad behavior naki ba, mummunan hali da kuma cin amanar wanda ya yadda dake, mommy wallahi tintinin na cireki a raina, bakya raina sam domin bana shiri da maciyi amana......"

Bata ƙarasa maganar ba taji an zabgeta da mari har sau biyu akan fuskarta, ƙanƙame idon tayi tareda dafe fuskar da hannu biyu ta ko wani ɓangare, a hankali take ƙoƙarin buɗe idon ganin ko wacece mai ƙarfin zarrar da ta isa ta mareta, tanason ganin ko wacece shin mommy ce ko Minal ko kuma acikin twins ne, ganin Baiwar ALLAH tsaye a gabanta tana zubda ƙwallah alamun ita tayi marin,
Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "haba Ummy! haba Ummy!! haba Ummy!!! ban taɓa tunanin zakiyi haka ba, ina kallonki mai hankali ashe gwara kowa ma dake, mahaifiyarki ce fa kike gaya mata maganganu son ranki, uwa uwace pah koda ta kasance mai tsinetsine ce akan bolaa......"
Baiwar ALLAH bata ƙarasa maganar ba taji Ummy ta katseta da cewa "uwa uwace amma gwara mun uwar da take yawo tsirara akan titi ta fiye mun wannan uwar....." ta ƙarasa maganar tana nuna Hajia Kilishi da yatsa......
tana ƙarasa maganar tayi gudu ta haura saman Upstairs tayi ɗakinta da gudu tana kuka......


Hajiya Kilishi dokuwa tayi akan carpet ta ɗora hannu aka ta fara rausa ihu tana faɗin "na shiga uku na lalace ɗiyata ta tsane Ni, bansan me nayi Wa Ummy ba ta tsaneni, Ni na haifeta a cikina, na ɗauki tsawon wata tara ina ɗauke ta ita acikin cikina sannan Ni nasan irin azabar dana sha a haihuwarta, nazo na shayar da ita har tayi shekara biyu amma abinda Maryam zatayi mun Kenam?....."

Minal ce ta durƙusa itama ta rungumi mommy tana rarrashinta, Pinky kam cewa tayi "ai Ni banyi mamakin jin hakan ba saboda tin ba yau ba nake cewa Ummy ba ƴar gidan nan bace, chanza mana asalin Ummyn mu akayi da wannan masifaffiyar yarinya...."

Rukky tace "ehhh! ana ce mana marasa tarbiyya ga cikakkiyar marar tarbiyya nan ai...."

Ƴar Tiny fashewa tayi da kuka itama ganin mommynsu tana kuka,
Baiwar ALLAH bazata iya sauraron jin kukan Hajia Kilishi ba yasa itama ta haura upstairs ta wuce ɗakin Ummy, tana shiga ta tarar da ita tanata zuba kaya acikin wata ƙatuwar akwati,
Baiwar ALLAH ƙarasa shugowa tayi ta zauna a bakin gado idonta akan Ummy tace "Ina zakije kuma?...."

Daƙer Ummy take motsa lips ɗinta tace "ina kuwa zanje Ni da gidan ubana...."
Murmushi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "kina ganin kin kyautawa kanki? Mahaifiyarki ta fashe da kuka saboda ke,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login