Showing 24001 words to 27000 words out of 117953 words

Chapter 9 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4733

lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka,
ta zura hannunta a cikin rigarta ta ciro ƴar sarƙarta wanda yake ɗaure a wuyanta mai zanen Jesus Christ, tana murza sarƙar tana hawaye kanta na kallon ceilling, tana cikin wannan halin saiga Madam Aliya ta shugo tana ta surutu tin kafin ta shugo
"Daman ai nasan bazata tsaya ta saurareni ba, ita idan aka kawo zancen Amreesh shikenam an rasa hankalinta, Allah dai ya bayyanar mana da ita idan kuma ta mutu Allah ya jiƙanta....."
da haka ta zauna a bakin gado tana wannan surutun daga bisani tayi tagumi tareda sunkuyar da kanta ƙasi tana hura iskar bakinta, itama damuwarta ya isheta na rashin haihuwa tsawon shekara da shekaru amma haka take danne zuciyarta babu yanda ta iya....

Jin shishshitun kukan Baiwar ALLAH yasa ta ɗago da sauri tana faɗin "lafiya kuwa Baiwar ALLAH meya faru dake?...."
Cikin kuka Baiwar ALLAH take faɗin "Mamanaaa! Abbanaaa!! Ina son ganinsu, Mommy and Daddy suna inaaaa? Kowa yana tareda iyayensa amma banda nii, wannan wata iriyar ƙaddara ce haka....."
nan ta ƙara fashewa da kuka sosai mai cin rai,

Daƙer Madam Aliya take rarrashinta cikin kulawa, tana bata haƙuri,
Baiwar ALLAH ce ta rirriƙe hannayen Madam Aliya tana cewa "dan ALLAH ki temaka mun naga iyayena, dan ALLAH Aunty..."
Ita kuwa Madam Aliya ta ƙafar da ƙwayar idonta akan sarƙar wuyan Baiwar ALLAH, cike da mamaki take bin baiwar Allah da kallo tareda sarƙar wuyan, tanaso tayi magana amma ta kasa lips ɗinta har rawa yake, domin tasan a yanda taga irin wannan sarƙar,
Wannan sarƙar kaf Nigeria babu mai irinsa kuma Designer ɗin sarƙar a iya mutum ɗaya kawai akayi shi,
Domin Madam Aliya bazata taɓa mantawa ba, ita da Madam Parveen suka je har ƙasar Maleshiya aka ƙero wannan sarƙar wa Amreesh, dake Madam Parveen su ɗin christal ne hakan yasa aka yi musu mai design ɗin zanen Jesus kuma ba ƙaramin kuɗi aka kashe wa sarƙan nan ba,
Madam Aliya hannu na kakkarwa ta miƙar da hannunta saitin wuyan Baiwar ALLAH tana jujjuyar da sarƙar ata gefe da gefen sarƙar akwai yanda aka rubuta sunanta da ƙananun baƙi wato amreesh,
A razane Madam Aliya tace "Amreesh...." tana bin fuskar Baiwar ALLAH da kallo sai a yanzu kamannun Amreesh lokacinda take ƙarama yake bayyanowa akan fuskar Baiwar ALLAH,
A lokacin ba ƙaramin ruɗewa Madam Aliya tayi ba, muryarta har harɗewa yake gurin faɗin "Please juyo naga bayanki akwai abinda nake son gani...."

Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta take bin Madam Aliya da kallo kamar wata zautacciya,
Haka Madam Aliya ta kwantar da Baiwar ALLAH kan cinyarta ta ɗage mata rigar jikinta saiga drowing photon bindiga ya bayyano, Madam Aliya bata san lokacin da ta fara washe baki ba tsabar farin ciki domin ta tabbata Baiwar ALLAH ɗiyar Madam Parveen ce, domin duk ƴaƴan Madam Parveen sunada wannan tambarin zanen bindiga a gadon bayansu, Yayun Amreesh su biyu Mohandas da Rakesh sai Amreesh hatta ita kanta Madam Parveen tanada wannan tambarin da Daddynsu shima, ba ƙaramin farin ciki Madam Aliya ta tsinci kanta a ciki ba, a zabure ta miƙe tsaye tana faɗin "bari nabi bayan Madam Parveen yau zatayi kwanan farin ciki...." tana kaiwa nan ta fice daga room ɗin da gudu...

Ita dai Baiwar ALLAH sam bata fahimci komai ba sai sake baki datayi tana bin bakin ƙofa da kallo yanda Madam Aliya ta fice, abun ya ɗaure mata kai sosai.....

Ita kuma Madam Aliya tana zuwa ta shige motarta a ɗari ta fice daga cikin hospital kai tsaye airport ta nufa domin Madam Parveen ta sanar da cewar ita komawa ƙasar U.S zatayi baza ta iya aikin da tazo yi ba saboda ɗiyarta Amreesha, kwata-kwata ta tsani nan ƙasar Nigeria.....




Please help me and share dis book 🙏🏼🙏🏼🙏🏼

𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (8)



꧁꧂



Madam Aliya hanyar airport ta nufa tana gudu tana ƙoƙarin ƙiran wayan Madam Parveen akan ta dakatar da ita daga tafiyar da zatayi, dan zai iya yuwa tana zuwa ta samu jirgin da zai tashi, ƙira akan ƙira amma Madam Parveen taƙi yi picking hakan yasa Madam Aliya ta ƙarawa motarta gudu....

Ita kuwa Baiwar ALLAH tana zaune abun duniya duk yabi ya isheta ga bala'in yunwar da take ji bata ci komai ba, idonta ne ya sauƙa akan ledojin da Madam Aliya ta shugo dasu, da sauri ta sauƙa akan gadon ta bubbuɗesu cikin sa'a ledar farko banƙararrun kaji ne a ciki sun sha eggs, sai leda na biyu soyayyun dankali ne da eggs sai shawarma ga lemukan gora da farro na ruwa, haka ta zauna ta fara tura su kamar wanda wani zai ƙwace, taci abinda zataci tabar sauran domin ba ƙaramin ƙoshi tayi ba, ta buɗe murfin gorar lemo tass saida ta shanye su, sannan ta miƙe ta nufi toilet tayi wanka tare da ɗauro Alwala tazo ta shimfiɗa sallaya ta tsaida sallah...


꧁꧂
꧁꧂
꧁꧂


Ɓangaren Ƴar Amana!

tana zaune a bakin gado ta haɗe kai da gwiwa sai sumar gashinta da ya rufe mata kanta gaba ɗaya,
tana jin buɗar ƙofar ɗakin tayi saurin ɗagowa domin ganin ko wanene ya shugo idonta duk yayi jawur tsabar kukan da take sha kullum, ganin wanda yake shugo mata kullum ne yasa ta ƙara fashewa da kuka saboda tasan bazai taɓa jin tausayinta ba balle yayi ƙoƙarin fitar da ita, mutumin koda yaushe fuskarsa a rufe take da baƙar hula, yauma kamar yanda ya saba haka ya shugo da wata ƴar leda wanda ba komai ne a ciki ba sai abinci jallof rice, yana zuwa gabanta ya wurga mata ledar abincin sai pure water da ya kuma jefa mata, da sauri ta rarumi ledar abincin ta buɗe a gaggauce ta wangame ɗan ƙaramin bakinta ta fara turawa ba ƙaƙƙautawa domin ba ƙaramin yunwa take ji ba, abinci ne a rana sau ɗaya ake bata, idan aka bata yanzu sai kuma gobe shiyasa bata wasa waran cin abincin nan danan har ta lashe ta ɗauki ruwan shima ta gwangwaɗe,
Shi kuwa Guest yana zaune ya kafa idonsa a kanta yana jiran ta kammala yayi mata abinda ya saba yi kullum domin bazai iya ganin Nama a gida ya barta ba dole zai ɗan rage zafi,
tana kammalawa yasa hannu a cikin rigar sanyinsa ya ciro wata ƴar ƙaramar allura yana jujjuyata idonsa zuru-zuru acikin hular fuskar yana ƙareta da kallo,
Ƴar Amana ganin allurar yasa ta fara ja da baya domin tasan allurar kullum sai yayi mata daga nan bata sanin abinda yake faruwa da ita saboda hankalinta fita yake daga jikinta sai bayan 24 hours take farfaɗowa,
tana cikin karkaɗa masa kai da hannu bibbiyu tana roƙonsa domin babu bakin magana, bata san lokacin da ya yo sufa ya janyota jikinsa ya caka mata wannan allurar ba, daga nan bata ƙara motsi ba sai kanta da yake kan faffaɗar ƙirjinsa, yafi minti 30 yana kallon kyakykyawar fuskarta, sannan ya kwantar da ita kan gadon yasa hannu yana shafa sumar kanta da gefen fuskarta, yana jin wani abu sosai a ransa wanda shima kansa bai san dalilin hakan ba, yana mamakin kansa sosai abinda yayi niyar yi baya taɓa aikatawa, yana son kasancewa tare da yarinyar amma yana matuƙar jin tausayinta especially idan ya hasasho yawan shekarunta wanda bazata wuce 15yrs ba, sannan gata Kurmiya..
A razane ya miƙe daga kan gadon ya sauƙa kullum acikin haka yake bai taɓa aikata abinda yayi niyya ba saidai kawai yayi mata allurar, kuma daya kasance daman ba manemin mata bane, sam baya shiga harƙar mata wannan ma abinda yasa yake jin hakan a ransa saboda a fake suke kuma yarinyar tana matuƙar burge shi, bai taɓa jin wani abu akan wata yarinya ba sai akan Ƴar Amana, abun yana matuƙar ɗaure masa kai gata yarinya ce bata gama cika cikakkiyar mace ba,

Wannan mutumin shi ake ƙira da GUEST mungu ne na asali akan abinda aka umarce shi, shima yana aiki ne a ƙarƙashin wani mai ƙarfin iko, baya taɓa bayyanar da fuskarsa kuma sannan baya shiga cikin gari sai cikin dare, ya kasance rayuwarsa a cikin daji ne da mutanensa manya-manyan ƴan daba masu kayan yaƙi,
Itama ƴar Amana sashi akayi ya ɗaukota ya cigaba da riƙeta a gurinsa kafin a aiwatar da aiki akanta, shima kansa Guest bai san dalilin da yasa aka ce ya ɗaukota ba, sannan bai san mai za'a mata ba sai dai idan lokaci yayi a sanar masa idan har shine zaiyi aikin akanta,
GUEST baya neman mata sannan baya shaye-shaye, idan kuwa aka bashi aiki akan kisa bayayi saidai shima yasa wani yayi, bashida tsoro sam sannan baya fargaban komai, baya aiwatar da abu da kansa saidai idan an bashi umarni.....



꧁꧂
꧁꧂


Baiwar ALLAH tana zaune akan sallaya kusan awa uku sai faman addu'o'i take tana jiran shigowar Madam Aliya shuru-shuru har yanzu gashi ana shirin ƙiran sallar mangarib, tana zaune taji an turo ƙofar ɗaki, ɗagowar da zatayi taga Nurse tayi tunanin Madam Aliya ce domin ta gaji da zaman asibitin nan,
Nurse tana shugowa tace "am kece wacce Madam Aliya ta kawo?..."
Dasauri Baiwar ALLAH ta ɗaga mata kai tareda faɗin "eh Ni ce..."
Nurse taja dogon numfashi tare da girgiza kai tace "sorry for what am going to say...."

Baiwar ALLAH idonta akan Nurse domin tana son jin abinda zata gaya ita har ranta so take taji Nurse tace an sallame su domin ba ƙaramin gajiya tayi ba,

Nurse tace "Doctor ya ce kada na sanar miki amma naga babu amfanin ɓoye miki tinda naga kinada tawakkali da sanin ƙaddara mai kyau ko akasin haka, kiyi haƙuri dan ALLAH,
ALLAH yayiwa Madam Aliya Rasuwa sakamakon hatsarin mota akan hanyarta na zuwa airport....."

Kafin Nurse ta ƙarasa maganar Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye da sauri ido a zazzare tana bin Nurse da kallo kamar wata zararriya,
Nurse ta ƙarasa maganar ta da cewar "motarta ce ta shige cikin traller, yanzu haka tana nan mutuware zaki iya zuwa ki ganta...."
tana zuwa ƙarshe ta juya ta fice tabar Baiwar ALLAH a sanƙare a wurin...


Mutuwar Madam Aliya ba ƙaramin girgiza mutane yayi ba, domin babu wanda bai santa ba saboda ba ƙaramar mata bace ta sanu sosai, anji mutuwarta sosai especially mijinta,
Innalillahi wa inna ilaihi raju'un,

Sai bayan isar Madam Parveen ƙasar U.S sannan ta biyo ƙiran wayan Madam Aliya ganin yawan miss call ɗin da tayi mata waran 30 missed call, abun ya bata tsoro sosai, kuma bawai taƙi ɗaukar ƙiranta bane wayar ce a silent, bayan ta ƙira jin muryar Namiji yasa ƙirjinta bugawa, a hankali ta furta cewar "where is madam Aliya?..."
Mutumin yace "sorry Madam Parveen baki ganeni ba koh? Ni mijinta ne wayar tana hannuna sakamakon hatsarin motar da Hajia Aliya tayi, yanzu haka bata raye ta riga mu gidan gaskiya, har mun ɗaukota a mutuware tana gida za'a sallaceta...."
duk wannan maganar ta turanci yayi mata,
yana kaiwa ƙarshe ya katse ƙiran,
Madam Parveen kamar a mafarki taji wannan maganganun, jin kanta tayi yana juyawa, a ruɗe ta fara girgiza kai tana faɗin "kai kai Kaiii i can't believe, Madam Aliya she never die, dis is a lie...."
haka ta ƙara dialing number Madam Aliya tana ƙira amma ba'a picking daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login