Showing 21001 words to 24000 words out of 117953 words

Chapter 8 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4729

na, dan ALLAH temako...." muryarta ba wani fitowa yake sosai ba Saboda tsantsar azaba daƙer take iya motsi da leɓɓenta, da haka tayi nasarar ficewa daga cikin ɗakin tana rarrabe ita kanta bata san ina ta nufa ba, ganin mutum tsaye a gabanta tsargagam ko motsi babu yasa ta dakata ta fara binsa da kallo tin daga ƙafarsa har zuwa ƙarshen kansa, sai dai abun mamaki yana sanye da baƙar hula a kansa da fuskarsa gaba ɗaya, a ruɗe ta juya zata koma daga inda ta fito mutumin yayi saurin cabko sumar kanta ya ɗagota sama yana ƙareta da kallo, ita kuwa ƙoƙarin ta shine taga ta zame masa tana so tayi ihu amma sai dai muryar ya shaƙe,
a hankali ya furta "Baiwar ALLAH kwanakin ki sunzo ƙarshe, ki sani cewar Ƴar Amana tana hannu na, itama na kusan gama wa da ita, ku kukayi sanadiyar tarwatsa mun rayuwata, don haka saina kashe ku, zan fara ne daga kanki...."
Baiwar ALLAH cikin firgici ido a zazzare daƙer ta iya cewa "wanene kai?..."

kafin ta sake cewa wani abu ya haɗe kanta da jikin bango ya gwara nan danan jini kamar da bakin ƙwarya haka yake bleeding, yasa hannu ya toshe mata baki sannan ya kawo bakinsa saitin kunnenta yace "Ni sunana Ɓoyayyen mutum, ki shirya yin bankwana da duniya yanzu..."
cikin zafin nama ya janyo ta saitin tagar beni sannan ya kifar da kanta ƙasin tagar yanda zatana kallon can ƙasin benin,
Ita kuwa ba abinda take sai haki domin ba ƙaramin wahalar da ita yayi ba, ganin yanda ta zubawa ƙasin benin ido yasa ta fara jin hajijiya da jiri ga ido yanda ta zazzaro su tsabar tsoro da firgici game da tashin hankali,
Dariya mutumin ya soma yi irin ta manya manyan mungwaye waɗanda suka shahara wajen yin mugunta, lokaci guda ya dakatar da yin dariyar yana huci yace "shin kinsan ina kike kallo? TOH mutuwarki kike kallo kuma yanzu zaki bita ku tafi...."
kafin Baiwar ALLAH tayi wani motsi har ya ɗago da sawayenta ya dungurar da ita ƙasin beni mai tsayin gaske,
kafin ta ƙarasa faɗawa ƙasi wani irin gigitaccen ihu tayi mai raunana kunnuwa wanda ba iya mutanen gidan Bama hatta masu gadi zasu jiyota......


A firgice ta yaye mayafin data rufe jikinta dashi tana kurma ihu kamar ranta zai fita,
Da gudu wasu mata suka turo ƙofar ɗakin ta suna tambayarta cewar "lafiya kuwa Baiwar ALLAH meya faru dake haka kike ta ihu ko ina ana jiyo ki..."
wata daga ciki ne itama tace "Baiwar ALLAH tinda muke dake bamu taɓa jin kinyi irin wannan ihun ba sai yau, shin me yake damunki haka?...."

Ita dai Baiwar ALLAH haka take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya duk ta haɗa gumi kamar wacce ta watsa ruwa a jikinta, ga idanuwa yanda sukayi jawur sai jan numfashi take daƙer,
abubuwan da suka faru da ita ne a cikin mafarki suke dawo mata ƙwaƙwalwarta, lokaci guda ta suma jin hajijiya da matsanancin ciwon kai, ganin batada ta cewa yasa ta fashe da kuka....

tsabar tsayin mafarkin da tayi bata san gari ya waye ba har ana neman wajen ƙarfe 8 gashi ko sallar asuba bata yi ba...

Suna cikin tambayarta halinda take ciki saiga Madam ta shugo ɗakin ita da Aunty Habiba, tana shugowa taje ta samu bakin gadonta ta zauna cikin tausayawa takai hannu ta jawo Baiwar ALLAH jikinta tana rarrashinta tareda faɗin "kiyi haƙuri kinji koh! Habibah ta sanar mun duk halinda kike ciki, but don't worry I will find something else for you okay..."

Madam ta kalli sauran matan da suke tsatstsaye a ɗakin tace musu "Please kuyi haƙuri ku fita kowa ta kama gabanta tana son hutawa..."
hakan kuwa sukayi sai iya Aunty Habiba ce kawai ta tsaya, Madam ta kalli Aunty Habiba sannan tace "jikinta zafi sosai, Inaso zan kaita hospital yanzu, ki kula mun da Office ɗina duk wacce take buƙatar abu saiki bata Please...."
Aunty Habiba ta amsa mata cikin girmamawa, Haka Madam ta tallafawa Baiwar ALLAH suka tashi tana janta a hankali har suka bar cikin ɗakin, a halin yanzu Baiwar ALLAH bata san a wata duniyar take ba domin ta rigada ta jikkata sosai, kana ganinta kasan babu jini a jikinta domin ba ƙaramin fari tayi ba har wani yellow ² tayi fuskar tayi fattt, da haka suka sauƙa down stairs, suna sauƙa kuwa tasa aka kawo mata motar ta har wajen da suka tsaya saboda majinyaciyar bazata iya zuwa har wajen parking ba domin ya yi mata nisa sosai,
Lokaci guda Madam taji wuyan Baiwar ALLAH ya karye mata a saman kafaɗatar ta, a ruɗe ta kalleta ido a zazzare ganin bata motsi kwata-kwata, a tsorace Madam ta sakata cikin motar ta itama ta shiga ta buƙaci ɗaya daga cikin matan gidan ta shiga motar itama zata raka su, ai kuwa a ɗari Madam ta finciki motarta sai bakin gate......




MA SHA ALLAH
SABODA RANAR FARKO NE YASA NA TURO MUKU PAGE ƊAN KAƊAN SBD WASU NASAN BASU DAWO A HUTUN SALLAH BA
BUT NEXT DA YAWA ZANYI MUKU ....


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (7)



꧁꧂


Ledar jini ne yake ɗiga ɗis! ɗis!! ɗiss!!! a yayin da ita kuma wacce take kwance a saman gadon hospital take bacci ido a lumshe gwanin burgewa, a hankali jinin yake shige mata hannun da aka ɗaura mata,
haka take fitar da numfashi slowly,
jin yanda sanyin A.C yake ratsa jikinta yasa ta ɗan soma mutsil-mutsil tana yatsina fuska still ido a lumshe, daƙer ta iya fara buɗe eyes ɗinta, a cikin tana ganin dishi-dishi har idon ya washe, haka take bin saman ceilling da kallo ko ƙibta idon bata yi, jin wani irin la'anannen ƙamshin turaren da yake bugan hancinta yasa ta ɗan juyar da kanta saitin yanda ƙamshin yake tashi, abinda ta fara gani shine zara-zaran yatsun hannu fari ƙall ga yatsun hannun sun sha zobina da warwaraye na gwal tana ɗauke da wata makekiyar waya wanda a ƙalla zai kai 2millions, ga wani danƙarariyar Abaya mai bala'in tsada wanda duk rigar a jere yake da duwatsu masu ƙalƙali da ɗaukar ido, a hankali take bin zazzafar ƙirar jikin matar dake zaune akan chair da kallo har zuwa kan kyakkyawar fuskar ta, ganin matar yasa ƙirjinta yayi wani irin bugawa a razane take ƙoƙarin tashi zaune ido a zazzare, a yayin da ita kuma matar hankalinta duk yana kan wayar hannunta sai daddannawa take alamun chatting take,
tasha kitson Attach har gadon bayanta sai gyalen rigar da ta ɗora akanta...

Daiden lokacin da Madam Aliya ta shugo cikin room ɗin hannunta riƙe da ledoji guda uku, ganin yanda Baiwar ALLAH take a razane idonta akan Madam Parveen yasa ta ƙaraso da sauri tana faɗin
"Lafiya kuwa Baiwar ALLAH? kin tashi ne? ya jikin nakin?...."

haka take jero mata tambayoyi tsabar yanda take jinta a ranta, domin tinda tayi ido huɗu da Baiwar ALLAH taji ta shiga ranta sosai da kuma tausayinta ,
tana ƙarasowa ta zauna a bakin gadon da Baiwar ALLAH take still idonta akan Madam Parveen,
Madam Parveen jin shigowar Madam Aliya yasa ta ɗago da kanta tana binsu da kallo daga bisani ta tsayar da idonta akan Baiwar ALLAH yanda taga kallon da take mata kamar wacce ta santa...

Madam Aliya tana riƙe da ɗayan hannun Baiwar ALLAH tace "Baiwar ALLAH shin kin santa ne kike kallon ta?...."

A hankali ta soma girgiza kai alamar a'ah!

Madam Aliya ta kuma cewa "ita ɗin Babbar Aminiyata ce, tare mukayi primary school to secondary, sunanta Madam Parveen, jami'ar C.I.D ce wato Agent Madam Parveen, Matar Chief of Defence staff
General Suraj Mahendra Marka shugaban sojojin ƙasar Australia (U.S).
Jiya ta shugo Nigeria domin gudanar da wasu ayyuka na kwana biyu daga nan ta koma can, ta kawo mun ziyara ne taji labarin ina nan hospital tare da ke shine tazo...."

Tinda Madam Aliya ta fara kora jawabai Baiwar ALLAH ta sake baki tana kallonta tareda kasa kunne tana sauraron duk abinda take faɗi, bata ankara ba taji Madam Parveen ta dafa kafaɗarta tareda faɗin "what's ur name?..."

Baiwar ALLAH girgiza kai kawai tayi domin ita kanta bata san sunanta ba...

Madam Parveen ganin bata ba ta amsa ba yasa ta mata magana ta Hausa yanda zata gane, a tunaninta bata iya turanci ba ne,
Ta kuma cewa "Dota Ya ya sunan ki?..."

Madam Aliya ce ta kwashe da dariya jin har yanzu Madam Parveen bata ƙware a Hausa ba,
wani irin harara Madam Parveen ta wurgawa Madam Aliya ganin dariyar da take yiwa Hausar ta,
Ta ce "what are you laughing for?...."

Girgiza kai kawai Madam Aliya tayi ba tareda ta ce komai ba sai ƙunsar dariya take...

Madam Parveen sharar da Madam Aliya tayi ta juyo ta cigaba da tambayar Baiwar ALLAH cewar " wa ne ne ya sameki kike kwanta a hospital? typhoid or maleria?
Ga babu jini a body naki sorry my Dota....."
ɗaga mata kai kawai Baiwar ALLAH tayi domin bata san wani amsa ɗaya zata bata ba....
suna cikin wannan halin saiga Doctor ya shugo da wasu nurses su biyu suna biye da shi,
yazo duba lafiyarta sannan ya cire mata allurar jinin da aka ɗaura mata domin kaɗan ne ya rage,
ya kalli Madam Parveen yace "ke ɗin Mamanta ne ko Auntyn ta?...."
dasauri Madam Parveen ta girgiza kai tana faɗin "No no noo bani santa ba, I have a Daughter but I lost her since 20 years later.....".
tana kaiwa ƙarshen maganar ta tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasi sakamakon hawayen da yake shirin zubo mata....

Doctor ya girgiza kai sannan yace "sorry Madam I think you are her mother because naga kuna kama sosai ...."

yana kaiwa nan yayi ficewarsa tare da nurses dake biye dashi!
jin abinda Doctor ya gaya yasa Madam Parveen ta ɗago tana ƙarewa Baiwar ALLAH kallo tareda share hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata,
Ita kuwa Madam Aliya tinda Doctor yayi maganar nan take bin Madam Parveen da Baiwar ALLAH da kallo domin itama ta tabbatar da suna mungun kama sosai kamar wanda suka haɗa jini, bata lura da hakan ba sai yanzu, komai nasu iri ɗaya, har ta buɗe baki zata yi magana Madam Parveen ta katse ta da cewar " i known my Daughter she's already died since laters,
Omg! inaso zan tafi...."
ta kai hannu ta shafa sumar kan Baiwar ALLAH tana faɗin "take care Dota, Quick recovery okay .....".
tana kaiwa nan ta tashi ta fice daga cikin room ɗin da sauri domin bata son shiga damuwa, saboda idan kana son ganin damuwar Madam Parveen shine ka kawo mata maganar Ɗiyarta Amreesha, nan danan zata rikice ta fara kuka ba ƙaƙƙautawa hakan yasa tayi saurin ficewa...

Ganin haka yasa Madam Aliya itama tabi bayanta da sauri, suka fice a tare.
Baiwar ALLAH jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba, domin taji wani abu a jikinta amma har yanzu ta kasa kawo cewar tanada alaƙa da wannan matar Madam Parveen saboda ita ma ta fara tunanin cewar iyayenta mutuwa sukayi, nan ta shiga dogon tunani tana tambayar kanta "shin meyasa naji wani abu akan wannan matar? sannan meyasa ake cewa munyi kama alhalin bamu da wata alaƙa, amma kuma tace itama ƴarta ta ɓata tin shekarun baya, to me hakan yake nufi?....."
haka zuciyarta take ta magana amma a zahirance girgiza kai ta rinƙa yi tana magana a fili cewar "a'a! a'a!! a'a!!! Bana son kalan dangi, idan iyayena suna a raye nasan wata rana zamu gana da juna amma idan har basa raye to na tabbatar haka zan cigaba da rayuwata cikin ƙasƙanci...."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login