Showing 18001 words to 21000 words out of 117953 words
Bai ankara ba yaji ɗaya daga cikin ma'aikata ta miƙo masa takarda tareda faɗin "Yallaɓai ga wannan saƙo ne daga sama, an canza maka waran aiki zuwa gidan marayu na maza, mu kuma za'a kawo shugaba ta mace zuwa nan da wata ɗaya, yau ake buƙatar ka bar gidan nan Yallaɓai..."
Hannu yasa ya karɓa cike da ɓacin rai, ya ɗago yana bin Ƴar Amana da kallo, shi kaɗai yasan irin muguntar da yake tsarawa a ransa, haka ya juya jiki ba ƙwari ya nufi hanyar gate,
yana jin yanda yaran gidan suke tsokanansa da cewa "Yallaɓai mai gutsurarren tsuriya aje a cigaba da tsarkin ruwan zafi....."
Baiwar ALLAH cike da farin ciki ta juyo tana faɗin "Nagode muku ƴan uwa, kun temake Ni sosai Allah ya bamu mafita..."
suka ce "kar ku damu Baiwar ALLAH ai yanzu mun zama ɗaya, mun kuma haɗe kayuwan mu yanda babu mahalukin da ya isa ya cutar damu, mun ƙwaci ƴancin mu..."
haka suke rungumar juna cike da farin ciki da haka kowa ya koma ɓangarensa, temako kuwa suna samu sosai daga waran al'umma, babu rashin kayan abinci komai akwai...
Bayan Baiwar ALLAH da Ƴar Amana sun koma ɗaki zama sukayi suna fuskantar juna Baiwar ALLAH ta ce "shikenam yanzu babu wani tashin hankali sannan babu fargaban komai, mu kwantar da hankalin mu nasara tana nan zuwa gare mu .."
Ƴar Amana tana kallon cikin idon Baiwar ALLAH nan take tasau wani irin lalataccen murmushi wanda tinda take bata taɓa yin irinsa ba, Baiwar ALLAH bata taɓa sanin Ƴar Amana tanada wannan kyau ba sai yanzu da taga murmushin ta mai ɗauke zuciya, sannan bata taɓa sanin Ƴar Amana tanada dimple ba sai yau domin bata magana balle kaga lotsewarsu sannan bata dariya kuma bata murmushi,
Baiwar ALLAH a ruɗe tace "wow beautiful girl my sister, da ace zaki kasance a haka cikin murmushi da kin wanke mun duk wani tabo dake cikin zuciyata..."
ta ƙarasa maganar tana zubda ƙwallah, lokaci guda Ƴar Amana ta koma yanda take a baya babu alamun Annuri a fuskarta cike da tausayi ta kwantar da kanta saman cinyar Baiwar ALLAH.....
Misalin ƙarfe goma na dare bayan kowa yaci yasha kowa ya nemi makwancinsa, suma Baiwar ALLAH sun kwanta asaman gadonsu kamar yanda suka saba, ita Baiwar ALLAH itace a bakin gado ita kuma Ƴar Amana a can baya take, amma saidai a yanzu Ƴar Amana tana zaune ne akan gado tana kaɗa jitan ta cikin salo da ƙwarewa a yayinda Baiwar ALLAH take kwance tana sauraron wannan sautin mai daɗin sauraro, da haka har bacci ya ɗauke Baiwar ALLAH,
A wannan daren Ƴar Amana bata samu yin bacci ba har waran ƙarfe biyu na dare tana zaune tana ƙiɗan jita, ji tayi ana knocking ƙofar ɗakinsu a hankali waran sau uku, kallon fuskar Baiwar ALLAH tayi taga tanata shan baccin ta, ji tayi kamar ta tashe ta saboda lokacin sallar daren ta yayi amma ta gaza yin haka, a hankali ta sauƙa daga kan gado ta nufi bakin ƙofa zata duba ko waye ne,
babu alamun tsoro a tattare da ita haka tasa hannu ta buɗe sakatar ƙofar ta buɗe,
tana buɗewa kamar jira ake kwatsam taji an jawota waje da ƙarfin gaske,
aka rufa mata wani farin ƙyalle akan fuskarta nan take ta sume a wajen, wani gabjejen mutum ne yasa hannu ya ɗauketa saman kafaɗarsa sannan yayi tafiyarsa da ita, haka yake sauƙa down stairs da sauri-sauri yana sauƙa yabi ta wani ɓoyayyen hanya ya ratsa, lokaci guda aka nemeshi aka rasa....
Can bayan awa guda da faruwar haka Baiwar ALLAH tana motsawa a hankali tana son tashi tayi sallah, ganin hasken ɗakin yayi mata yawa acikin ƙwayar idanuwanta yasa ta buɗesu gaba ɗaya dake basa kwana da haske a ɗaki,
tashi tayi tana addu'o'i ta sauƙar da ƙafarta ƙasin gado kwatsam idanuwanta suka hango mata ƙofar ɗaki a buɗe wangam, a zabure ta zaro ido waje tareda faɗin "innalillahi ya za'ayi Ƴar Amana tabar mana ƙofa a buɗe kalan azo a sace mu.." ta ƙarasa maganar tareda miƙewa tsaye ta nufi bakin ƙofa tasa hannu ta rufe tareda sanya sakata,
juyowar da zatayi taga babu Ƴar Amana akan gado sai iya jitar ta, maida idonta tayi kan ƙofar toilet taji dai babu motsin mutum a ciki, a ruɗe taje ta buɗe ƙofar toilet taga babu kowa a ciki, ta ɗaga kanta sama tana kallon agogon bangon ɗakin ƙarfe uku yanzu har da rabi, cike da fargaba ta kalli yanda jitarta yake, asaninta indai ƴar Amana zata fita to da jitarta take fita, a fili ta furta cewar "yanzu haka tana can waran Lambu, Ni kuwa ba zuwa zanyi ba wallahi, na horu ba Ni ba aljanu...."
ta buɗe sakatar ɗakin yanda inta dawo zata shugo...
haka ta shige cikin toilet tayo alwala sannan ta fito saida ta cire sarƙar Jesus Christ tukun ta sanya hijab ta tsaida sallah,
har ta idar da sallar taga ƴar Amana shuru bata dawo ba, tanata addu'a har aka ƙira sallar asuba ta tashi tayi sallah, nan ma ƴar Amana shuru, taɗan kishingiɗa kafin kace mai bacci ya ɗauketa bata tashi farkawa ba sai ƙarfe goma na safe, nan ma anzo ana bubbuga ɗakin ne aka sanar cewa azo ayi breakfast,
A firgice Baiwar ALLAH ta tashi tana murtsuka ido ta duba waran kwanciyar ƴar Amana bata ganta ba, anan hankalinta yayi matuƙar tashi, saita fara tunanin kodai ta dawo ta fita ne, sai kuma hankalinta ya kwanta, tana jan ƙafa ta shige toilet tayi brush sannan ta fito ta rufa mayafinta ta fice daga ɗakin...
tana sauƙa ƙasin beni ta fara baza idanu ko zataga ƴar Amana amma ko mayafinta bata gani ba, ta dudduba ko ina babu ita, haka ta shiga tambayar mutanen wajen ko sun ganta amma amsa ɗaya ake bata cewar ba'a ganta ba, da gudu Baiwar ALLAH ta nufi can Lambu tana zuwa ta fara ƙwalla ƙiran sunan Ƴar Amana, duk cikin lambun nan babu inda bata duba ba amma ko alamunta babu, tin daga lokacin Baiwar ALLAH ta fara zubda hawaye tareda faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un...."
A ranar wuni akayi ba'aga ƴar Amana ba, ko labarin ta babu, Baiwar ALLAH tasha kuka kamar ranta zai fita, fuskar nan tayi jawur tsabar kuka abunka da farar mace, idanuwanta sun kukkumbura sunyi jawur suma,
ganin wuni guda ba'a ganta ba yasa aka shigar da bayanin ɓatan ƴar Amana can hukumar human right, zasu zo suyi bincike akan al'amarin,
gashi yanzu har ana ƙiran sallar mangarib.....
Human right basu tashi zuwa ba sai washe garin ɓatan ƴar Amana, a daren jiya Baiwar ALLAH kwana tayi bata rintsa ba sai kuka, abinci kuwa ko loma ɗaya batasa a bakinta ba balle ruwa, a ranar da masu bincike suka zo sun bincika ko ina, basu samu wata hujja ba, hatta security masu gadin gidan suma babu wata alamar data nuna cewa an shugo gidan ko kuma an fita, saida sukayi waran sati guda suna bincike kafin suka samo wata ɓoyayyar hanya acikin gidan ta bayan gidan, hanya ce wanda saika bi ta cikin ƙasa kafin ka fice a gidan, wato gidan ƙasa, abun ya bada mamaki a kowa na cikin gidan babu wanda yasan da wannan hanyar, haka sauran mutanen gidan suka fara tsorata...
Bayan an gama bincike an gano hanyar an yanke cewar Ƴar Amana guduwa tayi bawai ɓata tayi ba ko saceta, abun ya bada kowa mamaki sosai, an faɗi hakane saboda a kawar da maganar ɓatan ta, waɗanda suke faɗin hakan sune shuwagabannin masu gidan marayun, mutane da yawa basu yadda da hakan ba, amma saidai babu yanda aka iya, haka maganar ta baza cikin gidan da hukumomi cewar ƴar Amana ta gudu daga gidan marayu..
Baiwar ALLAH jin maganganun da aketa yayatawa yasa ta ɗora hannu akanta ta fara ihu kamar ranta zai fita, kuka take sosai a filin gidan, har tana ƙoƙarin shiɗewa tana kuka tana faɗin "shikenam an ɓatar mun da Ƴar Amana, nasan Ƴar Amana bazata iya tafiya ta barni ba...."
Sauran ƴan matan gidan ne suke rarrashinta suna bata haƙuri,
Baiwar ALLAH gaba ɗaya ta fita hayyacinta idanu sunyi zuru-zuru tsabar rikici da tashin hankali ta faɗi a wajen sumammiya....
Ƴar Amana tinda aka sato ta aka jefar da ita acikin wani ɗaki bata farfaɗo ba yau sati guda domin ba ƙaramin guba aka sheƙa mata a hanci ba,
An ɗaɗɗaure hannayenta da ƙafafuwanta da igiya tana kwance saman wani wantalelen katifa, ɗakin ɗan ƙwaƙwas, amma sai dai ɗakin acikin jeji yake bayan gari, ga masu gadinta wasu zabga zabgan maza su biyar ko wannensu yana riƙe da ƙaton bindiga a gannunshi.....
𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.
𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦♀️🤦♀️
𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢
𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.
𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈
ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..
𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:
1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.
2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.
3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.
4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.
𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (6)
꧁꧂
Bayan sati biyu da ɓatan Ƴar Amana!
Har wannan lokacin Baiwar ALLAH bata samu ƙwanciyar hankali ba, kullum acikin kuka take ba ci ba sha gaba ɗaya ta fita hayyacinta ta rarrame sai kurmin ƙashin wuya, idanu sun kukkumbura sunyi lufu-lufu abinka dame manyan eyes, fuska duk ya kokkoɗe dake farar mace ce kamar ba jini a jikinta tayi fari fatt, tana fama da jinya a jikinta amma babu wanda ya sani ita kaɗai tasan abinda take ji ajikinta, ga damuwar ƙazafin da akayiwa Ƴar Amana cewar ta gudu ne daga gidan marayu!
A gidan marayu kuwa an kawo musu wata shugaba mace Madam Aliya, wannan lokacin sunyi dacen samun shugaba ta gari mai jin tausayi da son temakawa al'umma, Ƴan matan gidan sun samu sauyin yanayi sosai na jin daɗin rayuwa, yanzu wata guda da kawo Madam Aliya kowa yana harkokin rayuwarsa cikin farin ciki, babu tsaro na takurawa, maganar Ƴar Amana kuwa tin tinin an rufe shafinta ba'a maganar ta, tin daga lokacin da Ƴar Amana ta ɓata Baiwar ALLAH bata ƙara fitowa filin gidan ba, daga ɗaki sai ɗaki, iya Aunty Habiba ce kawai take zuwa mata, takan kawo mata flask na ruwan tea saboda iya ruwan tea kawai take iya sha, sannan Aunty Habiba tayi iya kokarinta akan akaita asibiti amma Baiwar ALLAH taƙi yadda kuma taƙi yadda ta haɗu da sabuwar shugabar da aka kawo musu saboda tasan ko bataso dole sai an kaita asibiti, taji labarin matar tanada kirki sosai, a haka take ƙunshe da rashin lafiyarta, hatta sallah a zaune take yinsa tsabar hajijiyan dake ɗinbar ta, ga yawan ciwon ƙirji da take fama dashi,
Ƙarfe takwas bayan sallar isha'i Baiwar ALLAH tana zaune akan sallaya yanda ta idar da sallah tana jan carbi cikin nutsuwa taji an buɗe ƙofar ɗakinta tareda yin sallama, cikin sassanyar murya ta amsa ba tareda ta waiwaya ba saboda tasan Aunty Habiba ce, Aunty Habiba ƙarasa shugowa tayi ta nemi bakin gado dake gefen Baiwar ALLAH ta zauna tare da zabga uwar tagumi idonta akan Baiwar ALLAH,
Baiwar ALLAH kallon Aunty Habiba tayi tare da sau murmushi tace "Aunty lafiya kuwa ki kayi tagumi?..."
Aunty Habiba ta ce "dole nayi tagumi Baiwar ALLAH, kina yarinya dake amma kina so ki sanyawa kanki hawan jini, bakida lafiya kin ƙi sanarwa kowa kuma kin haneni na sanar shin meye dalilin yin haka ?..."
Kasalalliyar murmushi Baiwar ALLAH tayi tana kallon guri guda kamar me yin tunanin wani abu, bayan ƴan mintuna da zurfafa tunaninta sannan ta buɗi baki tareda faɗin "ban san a wani hali take ciki ba, ita ɗin yarinya ce ƙarama kuma Kurmiya, ina tsoron kar wani abu ya cutar da ita, ban saniba ko tana cin abinci ko bata ci shin taya zan iya cin abinci kuma taya zan iya yin bacci alhalin ƴar uwata bata samu yinsu ba aciki...."
kafin ta rufe baki kuka ya kuɓuto mata kamar daman jira take ayi magana tayi kuka, tsabar tausayi Aunty Habiba itama saida ta share hawaye ta sauƙo ƙasan sallaya tareda rungumo Baiwar ALLAH jikinta tana rarrashinta cikin kulawa...
Aunty Habiba bata tashi barin ɗakin ba sai da ta tabbatar da cewar Baiwar ALLAH tayi bacci tukun itama ta tashi ta fice a ɗakin bayan ta kwantar da ita,
Around 1:30AM cikin dare Baiwar ALLAH ta tashi da matsanancin ciwon ciki, wanda a wannan daren ta kasa tashi tayi sallar da ta saba yi koda yaushe, tana daga saman gado ba abunda take sai juyi haɗe da nishin azaba, tana cikin wannan halin bata san lokacin da ta faɗo daga kan gadon ba, ganin ba wani sarki sa ALLAH yasa ta nufi bakin ƙofa da rarrabe tana kuka game da faɗin "wayyo temako! zan mutu wayyo ciki