Showing 114001 words to 117000 words out of 117953 words
ya haɗe hannayensa biyu ya ɗora kan ƙirjinta yana dannawa a hankali daga bisani kuma yakai fuskarsa saitin nata yareda ɗora ɗan lips ɗinsa kan nata yana hura mata iskar bakinsa, cikin lokaci ƙanƙani numfashin ta ya dawo a hargitse,
tari ta fara yi tana amar da ruwan da tasha, daga baya ta buɗe lumshashshun idanuwanta kamar maijin bacci,
yana kwance ta gefenta eyes ɗinsa akanta itama shi take kallo haka suka shiga kallon juna ba tare da wani ya ƙibta a cikinsu ba,
A zabure suka dawo hayyacinsu jin magana kamar daga sama ance "iyyyeee soyayya haka...."
Ummy ce tayi maganar tare da juyawa da gudu tabar wajen,
Suma tashi sukayi, kafin ya ankara harta bar wajen da gudu itama,
tsayawa yayi yana kallon ta har ta ƙule masa,
shima jiki a jiƙe yake shirin barin part ɗin....
Da Daddare misalin ƙarfe 9 bayan an gama dinning,
Roshan ne zaune akan sopa 3 seater hannunsa riƙe da ledar Maganinnuwa har da Allurai, yayi tagumi alamar dogon nazari yake,
Ummy ce ta sauƙo daga upstairs da tarar da shi a cikin wannan halin, a hanzarce ta nufi wajensa tana ambaton sunansa
"Yaya Roshan!.." shuru bai ɗago ba ta ƙara maimaita ƙiran sunansa har sau kusan biyar saida ta bubbugi kafaɗarsa tukun yayi firgitt ya ɗago yana kallon Ummy,
Zama tayi a kusa da shi ta zuba masa eyes cike da mamaki take faɗin "Ango kuma a cikin damuwa?
Yaya Roshan me yake damunka alhalin kana shirin mallakar farin cikinka, kamata yayi a ganka cikin farin ciki...."
Ɗan tsuka yaja acan cikin harshensa yana dafa goshinsa ya ce "bansan me yake damun Ammata ba, gaba ɗaya guduna take bata son kasancewa tare da Ni, duk hanyar da zai haɗamu bata ƙaunar biyo wajen bansan me yasa ba...."
Sauƙe numfashi Ummy tayi tana hararar Roshan ta ce "Ɗazu ba ku na gani a swimming pool ba?...."
Girgiza Kai yayi cikin nuna damuwa ya ce "Ni na bita wannan wajen sannan da hannunta ta tura Ni cikin ruwa tana kuka zata bar wajen, bansan meya dawo da ita a wannan lokacin ba itama ta faɗa ruwan,
Nifa na fahimci kamar ba sona take ba....."
Zaro ido waje Ummy tayi tare da faɗin. "koda wasa kar kayi tunanin nan, domin Aunty Baiwar ALLAH tin kafin ku dawo take muradin son ganinka, idan taga hotonka har wani irin murmushi take saki na farin ciki,
Zai iya yuwa yanzun kunyarka take ji saboda an kusan ɗaura muku Aure, daman indai Amarya tanada kunya toh har ayi Auren bata son haɗa Ido da Angonta....."
kallonta yayi ya ce "wai da gaske kike?...."
cikin fara'a ta ce "sosai ma...."
Sai yanzu yaji zuciyarsa tayi wasarrr, murmushi ya saki tare da faɗin
"Ma sha ALLAH! indai rashin ganina shi zaisa tayi farin ciki to Ni kuwa nayi Alƙawari har a ɗaura Aure bazan ƙara barin mu haɗu ba,
tinda Amaryata kunya gare ta...."
Itama Ummy murmushi ta saki tare da kai hannunta kan ledar hannunsa tana faɗin "meye wannan?..."
Ɗan harararta yayi tareda faɗin "to Sarkin kwaɗayi pharmacy ne na ɗauko a medicine room zan bawa Matata ta ce mun tana jin zazzaɓi,
Kuma na bubbuga ƙofar ɗakinta taƙi buɗe mun...."
Ummy ta ce "ai nasan bazata buɗe ba indai tasan kaine, kawo nakai mata...."
Ya ce "Ok please kiyi ƙoƙarin ganin tasha maganin sannan kiyi mata Allurai tinda kema Doctar ce...."
Murmushi tasau tare da cewa "Insha ALLAH...."
ya miƙe tare da nufan upstairs dazai kaishi part ɗinsa, har yayi nisa ya juyo ya ce yana faɗin "gobe bazaku tashi ku ganni ba saboda da sassafe zamu tafi ƙasar Jidder Ni da twins, na baki Amanar Matata....."
Ta ce "to Allah ya kiyaye hanya My Sweet Bros...."
ta nufi room ɗin Baiwar ALLAH shi kuma ya wuce part ɗinsa,
Ummy a hankali taje tana knocking door tareda ambatar sunanta
"Aunty Daughter! Aunty Daughter ki buɗe ƙofa Ni ce pah......"
Kafin ta ƙara furta wani abu har tazo ta buɗe mata,
murmushi Ummy tayi tana faɗin "wato a Yayana ne baza'a buɗe ba koh?..."
Baiwar Allah ta koma ciki tare da ɗosana mazaunanta a bakin gado,
Itama Ummy zama tayi dab da ita tana kallon ta cike da mamakin ganin yanda ta rame tayi fari sol kamar ba jini a jikinta,
Baiwar Allah kallon front ɗinta take ko annuri babu a fuska,
Ummy ta ce "am daman magani akace na kawo miki, sannan zanyi miki allura..."
Baiwar Allah kallon Ummy tayi ta ce "waya ce miki bani da lafiya?...."
Ummy ta ce "labarin zuciya a tambayi fuska, gashi jikinki ya nuna cewar bakida lafiya..."
ta ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye ta nufi frig ta ɗauki ruwan jarkan ta koma side ɗin Baiwar Allah ta zauna,
buɗe ledar tayi ta curo Maganinnuwan gaba ɗaya tana ɓarewa tareda ƙoƙarin bata,
Girgiza Kai Baiwar ALLAH tayi ta ce "Ni lafiyata ƙalau bazan sha ba....."
Ummy cikin ɓacin rai ta ce "wallahi sai kin sha ko kuma naje na haɗaki da Abbah domin shi yace na kawo miki...."
Jin haka yasa ta karɓa ta watsasu a baki tare da kafa bakin jarkan ta korasu da ruwa,
Bayan ta kammala shan su gaba ɗaya, miƙa hannunta tayi Ummy tayi mata Allurai,
tashi Ummy tayi tace "saida safen ki...." tabar ɗakin domin ta fahimci kwana biyun nan Baiwar ALLAH bata son yiwa kowa magana,
Itama tashi tayi taje ta rufe ƙofar ɗakinta sannan ta shige bathroom tayi wanka, tazo tayi shigar sleeping dress ta ƙwanta zuciyarta cike da tsananin kewar Uncle Deen da son kasancewa tare da shi sannan tana muradin ganinsa.....
Asubar farko Yaya Roshan ya kammala haɗa jakarsa wanda zai tafi da ita domin zai iya kasancewa suyi kwana uku kafin su dawo,
ya kammala shirinsa tsab ya fice daga part ɗinsa zasu je masallaci, a falo ya tarar da Abbah yana zaman jiransa, a tare suka fice....
Shima a ɓangaren Uncle Deen bayan ya dawo daga masallaci zama yayi akan ɗaya daga cikin jerukan kujerun falon farko, zaro wayarsa yayi yana ƙoƙarin kunna shi domin wayar a kashe ta kwana,
yana cikin wannan yanayin saiga Marshall ya sauƙo daga upstairs yana sanye da sleeping dress mai botula ta front ɗin gaba, rigar ta sauƙa masa har gwiwa sai gajeren wandon dake ciki, yana hamma ya ƙarasa sauƙowa falo domin ba ƙaramin yunwa ya tashi da shi ba,
zama yayi beside Uncle Deen yana faɗin "am hungry too...."
Uncle Deen ba tareda ya kalle shi ba ya ce "go and inter kitchen...."
Marshall ya ce "okay kasan dai ina yin girki ko? let me go and find us food...."
ya ƙarasa maganar tare da miƙar hanyar kitchen..
Ba jumawa Uncle Deen ya soma jin knocking,
a hankali ya furta "WHO?..."
ta waje yaji ance "your twins ..."
jin muryar Roshan yasa shi miƙewa ya nufi bakin ƙofa, yana buɗewa saiga Roshan ya kutso kai tare da rungumar Uncle Deen cike da nuna farin ciki,
Shima Uncle Deen yayi farin cikin zuwan Roshan,
A tare suka ƙarasa shiga ciki tare da zama guda ɗaya suna kewar juna,
saiga Marshall shima ya fito daga kitchen yana faɗin "wa nake gani kamar S.D (surgeon doctor)...."
miƙewa Roshan yayi suka rungumi juna yana tambayarsa yaushe yazo...
Marshall ya ce "wallahi jiya isowata,
am glad to see you..."
shima Roshan cikin nuna farin ciki ya ce "me too..."
suka zauna gaba ɗaya cike da kewar juna,
suna cikin tattaunawarsu sai suka ji an buɗe ƙofar falo, dasauri suka waiwaya ganin Minal yasa Marshall saurin miƙewa tsaye,
cike da mamaki Uncle Deen yake binta da kallo,
ƙarasowa tayi ta zauna akan kujera tana gaishe su,
Uncle Deen ne yayi maganar cewa "meya kawo ki da sassafen nan?..."
Roshan yayi saurin taran yawunsa ya ce "sawa tayi nayiwa Abbah ƙaryar da ita zamu tafi ƙasar Jidder, ita kuma ta tsara cewa zata zauna anan gidan ita da Marshall har mu dawo,
kuma nima inaga gwara su fahimci juna akan tsarin yanda zasu gudanar da soyayyar su,
Su samawa kansu mafita...."
Uncle Deen juyawa yayi yana kallon Marshall sannan ya juya eyes ɗinsa kan Minal tare da faɗin
"tayaya iyayen Mohandas zasu barshi ya musulunta and then how comes Minal zata koma christal?....."
Marshall gaba ɗaya ya rasa yanda zai ɓullo wa al'amarin,
Roshan ne ya ce "duk abinda ya kamata na sanar yanzu na riga da na faɗawa Minal,
ita kuma zata sanar wa Marshall idan ya amince toh Ma sha ALLAH! Ni kuma zanyi ƙoƙarin fahimtar da Abbah, idan kuma bai amince ba ya rage nasu, shawara mai kyau dai na bada bayan wannan shawaran bani da ta cewa....."
Uncle Deen cikin rashin fahimta yake bin Roshan da kallo ya ce "wani irin shawara ne haka?...."
Roshan ya ce "gaskiya zai mun nauyin furtawa a gaban Marshall saboda bansan wani irin kallo zai mun ba...."
ya ƙarasa maganar idonsa akan Marshall!
Minal ce ta buɗi baki ta ce "Yaya Roshan ya sanar mun cewa nace wa Marshall idan har ya aminta kuma yana son Aura na toh ya musulunta a ɓoye ba tareda iyayensa sun sani ba, shi kuma zaiyi ƙoƙarin fahimtar da Abbah....."
A ruɗe Marshall ya ɗago yana kallon Minal, cikin ƙanƙanin lokaci damuwa ya bayyana ƙarara akan fuskarsa,
Uncle Deen ya ce "Whattttttt?
kunsan abinda kuke shirin aikatawa kuwa?...."
kafin ya ƙarasa maganar yaji Marshall ya ce "wannan shine mafita, daman na daɗe ina tunanin haka, inhar zaku bani goyon baya Ni kuwa zan musulunta duk da nasan duk randa mahaifina ya gano dole zai kashe Ni ......"
Roshan ya ce "Insha ALLAH babu abinda zai faru dakai, muna tare dakai har abada...."
Minal farin ciki kamar bazata mutu ba,
Uncle Deen kuwa cewa yayi "ba dani za'ayi wannan cin amanar ba...."
Roshan ya riƙo hannun Uncle Deen ya ce "please my Man Kai ɗan hannun daman mahaifin Marshall ne, zaka san yanda zakayi ka fahimtar da shi sannan mahaifiyarsa tamkar ɗa ta ɗauke ka itama zaka fahimtar da ita....."
Uncle Deen yana pressing phone ɗinsa ya ce "Hmmmmm!!!...."
bayan haka bai ƙara cewa komai ba,
Roshan ya ce "ok yanzu dai ba lokaci domin Muna so zamu je ƙasar Jidder Ni da My Man, kai kuma Marshall ka zauna da Minal anan har mu dawo, amma please kar ku fita ko ina domin akwai mutanen Abbah,
Ban taɓa masa ƙarya ba amma yau nayi masa saboda soyayyarku, ina tausayin masoya sosai....."
Gaba ɗayansu murmushi sukayi domin sun san Roshan Romeo ne daman,
Banda Uncle Deen wanda ya tsayar da eyes ɗinsa akan Roshan jin ya furta dashi za'aje Jidder,
Roshan shima kallonsa yayi ya ce "Any problems?...."
Uncle Deen miƙewa yayi tare da faɗin "I'll no go anyway..."
ya ƙarasa maganar tare da miƙar another falonsa wanda zai kaishi har bedroom ɗinsa,
Roshan ya ce "please my Man Abbah ne yace muje...."
"I tell you bazan je ba...." ya yi maganar bayan ya shige falo na biyu...
Roshan ya ce "okay let me go domin lokaci yanata ƙurewa...."
Marshall ya ce "Ni S.D me yake faruwa da Major ne naga ya baro can gidan..."
Roshan ya ce "oh bai gaya maka ba?...."
Marshall ya ce "ka dai san halin mutumin bazai tsaya bani wani dogon labari ba...."
Roshan ya ce "Okay...."
Nan Roshan ya kwashe komai ya sanar wa Marshall,
Marshall Sam baiji daɗin abinda ya faru tsakanin Abbah da Major ba...
Shi dai Roshan tashi yayi ya fice,
yana fita shima Marshall ya miƙe tare da nufan part ɗin Uncle Deen har bedroom ya samo shi yana kwance,
Zama Marshall ya yi a bakin gadonsa yana faɗin "seriously Major baka kyauta ba,
Umarni Abbah ya bada cewa ku