Showing 3001 words to 6000 words out of 117953 words

Chapter 2 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4727

ma ɗayane tin suna yara basu rabu ba.
Yanzu Baiwar ALLAH tanada shekara Ashirin 20 a duniya..
Ita kuma Ƴar Amana tana da shekara sha biyar 15 a duniya...

Kuma duk acikin su babu wacce tasan sunanta,
tin lokacin da aka kawo Baiwar ALLAH ta manta sunanta idan aka tambayeta sunanta sai dai tayi shuru hakan yasa duk wanda zai ƙirata sai dai yace Baiwar ALLAH da haka sunan ya bita kuma har yanzu bata iya tuna sunanta ba....

Ƴar Amana kuma wanda ya kawota aka tambaye shi sunanta yace musu Ƴar Amana sunanta kuma ya sanar musu cewa da haka za'ana ƙiranta har ta girma, shiyasa itama ta tashi babu suna sai dai Ƴar Amana....

Haka rayuwar ƴan mata biyun nan yake gudana acikin gidan marayu, kowa ya raina su ana musu kallon ƙasƙantattu wasu suna zargin cikin shegensu akayi aka zubar dasu, wasu kuma suna faɗin ƴaƴan ƴan gudun hijira ne,

Basu san cewa Ɗaya daga cikinsu Ɗiyar shugaban sojojin ƙasar U.S bane (C.D.S)..

Ɗaya kuma Ɗiyar Mai martaba Sarkin ƙasar JIDDAH bace kuma jikar mai martaba sarkin Niger, Ɗiyar ƙanin Chief of Army's staff na Nigeria....

BAIWAR ALLAH DA ƳAR AMANA STORY BY ASMEETAH
ku cigaba da bibiyata a cikin littafi na mai suna
*MY ENEMY...*


Comments 🙏 And Sharing book,

Ku saurari Chapter two zuwa Monday idan har na samu ƙarancin comment...
Idan kuma na samu comments yanda nake so daga Saturday zan poster kuma,

Bazaku ji Armashin chapter one ba har sai kun shugo chapter two anan labarin zai fara gobara🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢+ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

Asma'u Muhammad Auwal (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
ASMEETAH.
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ᵖˡᵉᵃˢᵉ ᵒⁿˡʸ ᶠᵉᵐᵃˡᵉˢ ᵃⁿᵈ ᵈᵒⁿ'ᵗ ᵃˡˡᵒʷ ᵗᵒ ˢᵉⁿᵈ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ⁱⁿᵗᵒ ᵐʸ ᵍʳᵒᵘᵖ🙏 ⁱᶠ ⁿᵒᵗ ⁱ ʷⁱˡˡ ʳᵉᵐᵒᵛᵉ ʸᵒᵘ, ᵃᵐ ʷᵃʳⁿⁱⁿᵍ ʸᵒᵘ ..

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (2)



꧁꧂


Ƙiran Asubar farko akan dodon kunnen Baiwar ALLAH wacce take zaune akan sallaya tana jan carbi a hankali tin ƙarfe biyu na dare bata koma bacci ba, kullum saita tashi tayi sallar dare...
tashi tayi a hankali ta ɗosana mazaunenta a bakin gado tareda kai hannunta kan Ƴar Amana wacce take lulluɓe da mayafi, cikin sassanyar murya Baiwar ALLAH take ambatar sunanta
"Ƴar Amana! Ƴar Amana!! ki tashi ana ƙiran sallah, kinji koh?.." ganin Ƴar Amana bata motsa ba yasa ta haura saman gadon gaba ɗaya ta ɗagota tareda yaye mata mayafin data rufu dashi, jin yanda jikinta ya ɗau zafi ga rawar sanyin da take yi yasa Baiwar ALLAH tsorita ta zazzaro ido waje tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raju'un Ƴar Amana meya same ki? wayyo zazzaɓi ke samun ki bari na dubo miki magani...."
a ruɗe Baiwar ALLAH ta sauƙo ta nufi waran da jerin kayansu suke nan ta fara fitar da kaya daga cikin jaka tana faɗin "ina tunanin akwai sauran magani, ALLAH yasa na samu wayyo ƴar uwata ba lafiya..."

Ita kuwa Ƴar Amana tana kwance sai rawar sanyi take gaba ɗaya ta fita hayyacinta, Baiwar ALLAH tasowa tayi jiki ba ƙwari tana tsaye takai hannu ta riƙo kunkuminta tana sauƙe numfashi cike da tausayawa tace "Ƴar Amana ban samu maganin ba, gashi yanzu idan naje tambaya ba lallai mu samu ba saboda sau ɗaya ake bamu magani a wata idan ya ƙare kuma shikenam, amma ki kwantar da hankalinki zanje na gwada tambaya ..."
tana kaiwa nan ta juya ta nufi hanyar fita kai tsaye office ɗin shugaban su ta nufa, tana zuwa ta tsaya a gaban ƙofar office takai hannunta a hankali tana knocking, jin shuru yasa ta tura ƙofar ta shige ta kuma rufe ƙofar kar a ganta saboda doka ne wata ta shiga office ba tareda permission ba, anan duk wasu abubuwan da ake buƙata suke nan ta fara bincika ko ina tana neman akwatin maganinnuwa, har gari ya fara washewa daƙer ta samu akwatin ta buɗe a hanzarce ta ɗauki packet na paracetamol da maganin ciwon ciki da kuma maganin olcer domin gaba ɗaya daga ita har Ƴar Amana olcer na damunsu sakamakon rashin samun isasshen abinci,
tana gama jidan magani ta juya zata bar ofishin kwatsam ta tarar da Ogansu yana tsaye ta bayanta wanda yanzu zuwansa, zaro ido Baiwar ALLAH ta soma yi tana haɗiyar yawu daƙer ga wani zufa da yake gangaro mata, buɗan baki tayi zatayi magana a wahalce mutumin ya ɗaga mata hannu alamar tayi shuru, yana mata wani irin kallo yace "Baiwar ALLAH kin shugo hannu, barewar dana daɗe ina farauta yau gashi ta faɗo tarko nah, Baiwar ALLAH! Baiwar ALLAH!! shin kin san hukuncin yin sata acikin Office?..."
Baiwar ALLAH shuru tayi tana kallon ƙasi tana tunanin yanda zata kuɓuce a hannun wannan azzalumin mutumi, ya juma yana nemanta da lalata amma taƙi bashi haɗin kai, daman yana neman yanda zaiyi ya kamata da laifi yau kuma gashi ga ita...
katse ta yayi daga dogon tunanin data faɗa tareda cewa "duk wacce aka kama tayi sata to hukuncin ta shine ayi mata bulala hamsin sannan ayi mata tsirara daga ita sai pant da bra a zagaya da ita cikin wannan makeken gida na marayu kowa da kowa ya ganta..."
yana magana cikin izgilanci ya gyara tsayuwarsa sannan ya goya hannayensa a saman ƙirjinsa ya kuma cewa "toh ya kike gani! shin kin yadda ayi miki wannan tozarcin ne ko kuma dai zaki bani haɗin kai saina ƙyale ki..."

Baiwar ALLAH ɗagowa tayi da rinanan idanuwanta waɗanda tasha kuka dasu ta haɗe hannayenta biyu ta ce "Yallaɓai dan girman ALLAH kayi haƙuri wallahi ba komai nazo ɗauka ba illa magani, Ƴar Amana tana can bata da lafiya ka temaka mun..."
cikin rashin nuna damuwa ya ɗaga kafaɗunsa tareda cewa "i don't care about Damuwata shine ki bani lokacinki mu fake...."
kafin ya rufe baki Baiwar ALLAH ta tafo da gudu ta durƙusa a gabansa tare da riƙe masa ƙafafu tana kuka ta ce "dan ALLAH Ƴallaɓai ka temaka mun, bana son abunda zai zubar mun da mutunci na, inaso na haɗu da iyayena cikin ƙoshin lafiya, inaso na rinƙa alfahari daku koda bama tare saboda tin ina ƙarama kuke riƙe dani, kun zamo mun tamkar iyaye nah, dan ALLAH Yallaɓai Ni ƴa ce a wajenka bai kamata wannan al'amarin ya afku ba..."

Lumshe ido yayi yana sauƙar da numfashi a hankali game da cewa "wayyo daɗi cigaba da rungumar sawaye nahh.."
yakai hannunsa ya cabko nata hannun ya ɗora saitin AK-47 ɗinsa yana hura iskar bakinsa, Baiwar ALLAH ganin haka yasa ta fincike hannunta da ƙarfi tana ja da baya murya na harharɗewa ta ce "A'uzubillahi ALLAH Ubangiji ya toni asirinka yallaɓai...". ta tashi tabi hanyar fita zata gudu yayi saurin riƙota ya mannota saman ƙirjinsa yana zazzaro mata eyes tare da darara mata tsawa ya ce "Keee bari kiji a wannan lokacin ƙarya kike ki tsallake tarko nah, duk ƴan matan cikin wannan gidan babu wacce ban ɗanɗani kalar zumanta ba sai ke da kuma ƴar uwarki Ƴar Amana, don haka ba kowa kuka fi ba dole kuma saina kusance ku kota halin ƙaƙa...."
Baiwar ALLAH jin ya ambaci sunan Ƴar Amana yasa ta dakata dayin kukan tana masa wani irin kallo na ƙasƙanci ta ce "Yallaɓai duk abunda zaka yi kar ka ƙara sako sunan Ƴar Amana acikin maganarka domin banga abunda ta tare maka ba, ita ɗin yarinya ce ƙarama du Da du bazata wuce shekara sha biyar ba a duniya, na zamo mata tamkar uwa don haka kayi komai akaina amma banda ita ..."
Yallaɓai ganin ɓacin rai a fuskar Baiwar ALLAH yasa tayi masa ƙwarjini dai daita muryarsa yayi sannan ya ce "okay fine yanzu acikin biyu ki zaɓi ɗaya, shin zaki amince mun da buƙata ta in yaso duk abunda kike buƙata zaki samu a waje na ko nawa kike so ko kuma kin zaɓi a fitar dake bainar jama'a ayi miki bulala sannan a zagaya dake zigidir...."

Ajiyar zuciya Baiwar ALLAH tayi tana zubda ƙwallah ta ce "ban taɓa jin labarin gidan marayu ana musu wannan mummunan abu ba sai a wannan gidan, Ni bazan bi hanyar da zan saɓawa Ubangiji na ba domin da kunyar lahira gwara ta duniya, na Amince ayi mun hukuncin da aka zaɓar mun, insha ALLAHU idan hukuma taji wannan ƙazamar labarin bazata barku ba domin kunci amanar da aka baku na riƙon ƴaƴan marayu...."
kafin ta rufe baki Yallaɓai ya zage ya zabga mata mari yana huci ga baƙin cikin bata amince masa ba ga kuma ta tsaya masa a gaba sai gaya masa maganganu take...
Baiwar ALLAH kama fuskarta tayi tareda fashewa da matsanancin kuka,
cikin ɓacin rai Yallaɓai ya zaro wayarsa ya ƙira ma'aikatan gidan cikin lokaci ƙanƙani sai ga su sun shugo su biyar duk mata, ganin Baiwar ALLAH yasa suka ce "Baiwar ALLAH meya kawo ki cikin office da sassafe?..."
Yallaɓai ya sanar musu cewa "kuje ku rubuta wannan yarinyar ɓarauniya ce kullum saita shugo cikin office ta saci kuɗin tallafin da ake kawowa marayu, yau nazo na kamata tana kokarin buɗe akwatin kuɗi, saboda haka baza mu ƙyaleta ba, ku fitar da ita waje ku tara duk mutanen da suke gidan za'a yanke mata hukunci...."
duk maganganun da yake yi kuwa idonsa akan kyakykyawar fuskarta, ita kuwa kanta a sunkuye sai zubda hawaye take hannunta kuwa riƙe da maganin data ɗauka,
Acikin ma'aikatan nan kuwa duk basu yadda da abunda Yallaɓai ya faɗa ba dake sun san halinsa mayen mata ne idan mace taƙi bashi haɗin kai haka yake mata wannan sharrin, kuma yana sawa a cirewa mace kayan jikinta ne acikin mutane domin yaga surar jikinta sai yake fakewa da hukunci...
Duk gidan marayun nan babu maza iya zallar mata ne kuma babu mai fita daga gidan saboda kar akai ƙorafi akan yallaɓai duk abunda yakeyi a ɓoye yake yinsa, kuma shine shugaba mai kula da yaran marayu amma yake cin Amana...

Ɗaya daga cikin matan ce ta riƙo hannun Baiwar ALLAH tareda jan ta suka nufi waje, kai tsaye harabar gidan aka fita da ita cikin sa'o'i aka ƙira duk yaran da suke gidan suka fito, lokaci guda har an hallaru a wajen ana son ganin hukuncin da za'a yiwa Baiwar ALLAH, domin har an sanar cewa tana satan dukiyarsu acikin Office, masu jin haushinta suna ji masu tausaya mata kuma har da hawayensu..,

Ita kuwa Ƴar Amana tana can cikin ɗakinsu bata san meke faruwa ba, ganin har yanzu Baiwar ALLAH bata dawo ba yasa ta yunƙura daƙer ta tashi ta nufi toilet, taje ta ɗauro Alwala tazo ta tada sallah, a nutse tayi sallar ta sannan ta jero addu'o'inta acikin zuciya tana zubda ƙwallah,
ganin har an ɗau awanni Baiwar ALLAH bata dawo ba yasa ta yunƙura ta fice daga cikin ɗakin, tafiya take bata ga kowa ba, dake a saman beni suke, saida ta miƙi dogon compound dake saman beni tukun ta fara taka matakala a hankali ta sauƙo ƙasin beni, anan ta fara ganin tarin mutane a cushe guri ɗaya, da gudu ta ƙarisa wajen ganin meke faruwa, abun da ya tada mata da hankali shine ganin Baiwar ALLAH a tsakiyar fili tayi kneel down ga kwantaccen sumar gashi a kwance saman gadon bayanta sai sheƙi yake, ga Kuma wata zankaɗeɗiyar dorina ajiye a gefenta, wata inyamurar mata ce Madam eniola itace mai yin bulala, tazo taza cire wa Baiwar ALLAH riga suka ji daga can bakin get an hura wutsur dake tsakaninsu da get akwai tazara mai nisan gaske, wannan wutsur ɗin da aka wura shine alamar tabbatar da anyi manya-manyan baƙi waɗanda suka kawo ziyara wa marayu,

Yallaɓai yana tsaye takaici kamar zai hallaka shi saboda yaso ace yaga kyakykyawan surar jikin Baiwar ALLAH, domin ALLAH ya yi mata wani irin baiwa ta halitta komai nata a tsare yake, kyakykyawa ce ta asali kamar ba ƴar Nigeria ba, ga surar jiki mai kyau domin ita ba siririya ba sannan ita ba ƴar lukuta ba amma doguwar mace ce fara tass kamar jini zai fito daga jikinta...

A fusace Yallaɓai ya ce "kashhh wayyo ALLAH banso anyi baƙi daga yanzu ba, ku ɗauke mun wannan yarinyar ku kaita can ɗakin duhu ku kulleta kuma kada wacce takai mata abinci da ruwan sha har sai tayi regretting...."

Ƴar Amana ganin an ɗago da Baiwar ALLAH yasa ta tafi da gudu ta rungumeta tana kuka, itama Baiwar ALLAH juyowa tayi tana kuka ta rungumi Ƴar Amana, a ɓoye Baiwar ALLAH ta ware tafin hannun Ƴar Amana ta damƙa mata maganunnuwan sannan ta shafa sumar kanta tareda faɗin "ki kwantar da hankalinki komai mai wuce wa ne, nidai fata na ki kula mun da kanki, ganan magani kije kisha zaki samu sauƙi sosai...."
Ƴar Amana duk taji abunda Baiwar ALLAH take gaya amma saidai ba halin mayar da martani sai kawai ɗaga mata kai data yi...

Yallaɓai ne ya darara wani irin tsawa yana faɗin "ku janye mun wannan kurmiyar anan, kuma kowa ya kama aikin gabansa banason baƙin nan su fahimci akwai matsala...."
Duk suka amsa da TOH...

Baiwar ALLAH can ɗakin duhu aka nufa da ita wanda yake can nesa da bayan ɗaku na,

Ƴar Amana dake ta sulalewa zata bi bayan su Baiwar ALLAH anata riƙeta gaba ɗaya ta fita hayyacinta, saida Yallaɓai yazo har gabanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login