Showing 420001 words to 423000 words out of 513411 words

Chapter 141 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16769

shiga tunanin miya sa Fanan d'in kuka lokaci guda zuciyarta ta tariyo mata da Maganar da tayi, waro ido Fatuu tay tare da Wan buWa baki da sauri ta shiga faWin "Aunty Fanan wllh ba dake nike ba da nayi Maganar kawai na bashi misali ne ban san abun zai ta6a maki zuciya ba don Allah kiyi ha?uri" idanunta har sun ciko da ?walla, girgiza mata kai tayi tace "No Zarah, baki man laifi ba ai abunda kika faWa gaskiya ne kuma ni ai nasan ba dani kike ba Saboda ni inada yara ko?" Da sauri Fatuu ta jinjina mata kai tare da kai hannu ta fara goge mata ?wallan Fanan Win na Wan murmushi, bayan ta gama goge mata hawayen ta tambayeta itama bata son a fitar da cikin ko farko shiru Fanan Win tayi kafin ta Wan jinjina mata kai alamar eh, juyawa tayi ta kalli Haisam cikin harshen turanci tace mashi Auny Fanan ma bata so don haka koda ita bata son cikin to zata ha?ura ta haife shi, murmushi yay tare da Wan lumshe ido haka ma likitan don yanzu ya fahimci komai da bai gane abunda ke faruwa ba saboda da Hausa suke Maganar sai jefi jefi suke saka turanci, kama hannunta Fanan tay ta d'an girgiza mata kai tace duk da bata ta6a haihuwa ba tasan tun daga rainon ciki akwae wahala in dai itama taji tana son a cire d'in kada Saboda ita ta canza ra'ayi Fatun tace a'a da gaske bata son a cire har cikin ranta ta amince a bar mata suyi mata Addu'a Allah yasa kada ta sha wahala kuma ta haife shi lafiya Fanan na murmushi tace in sha Allah daga yanzu ta fara mata Addu'a kan hakan har zuwa ta haihu ta kalli Haisam dake kallon su fuskarshi a sake tace daga yanzu su fara mata Addu'a ya jinjina kai, tattaunawa Fanan ta shiga yi da Doctor kan maganin daya kamata a bata wanda zai sa ta daina amai ta rinka cin Abinci haka su twins ma suma za'a basu wanda zai k'ara inganta lafiyar su Haisam ya tambayi yanzu zata iya cigaba da breastfeeding nasu doctor din yace k'warae ba wani abu taci gaba da basu koda har zuwa ta haihu ne kuma a rin?a basu maganin da zai basu yay mashi godiya.

Bayan sun baro Asibitin tun akan hanya Fanan ta shiga kiran yan Nigeria su Hajiya da Mom ta sanar masu harda Gwaggo ma kowa yay mamakin jin samun cikin daga baya duk sukai Addu'oin Allah ya inganta ya raba lafiya. Sosae Fanan ke kulawa da Fatuu bayan da suka san da cikin haka su twins ma in dae tana gida bata je aiki ba ita ke duk wata Wawainiya dasu dama tana kulawa dasu sosae yanzu sai ta k'ara don komai ita ke masu kama daga yin wanka shirya su basu Abinci yi masu wasa da sauransu haka Haisam ma in yana a gidan tare dashi ake masu komai koda Fatuu tayi yun?urin yi masu wani abu sai suce ta bashshi ta huta duk da jikin nata da Sauk'i sosae iyakar ta shayar dasu sai kuma in suna zaune tare dasu ta d'auke su har tayi masu wasa, k'arshe ma Haisam cewa yay yakamata a samo masu nanny Saboda in basu nan ba sai ta rink'a wahalar kulawa dasu ba amma sai ta nuna mashi ba sai an samo ba tunda ba wani ciwo take ba zata iya wannan amman ya nuna ta bari dai a samo ganin hakan yake so yasa ta amince amman tace to ya bari tunda sun kusa tafiya biki in suka dawo sai a samu ya amince da hakan.

A kwana a tashi ba wuya a wurin Ubangiji, bikin su Nameer nata matsowa har ya rage saura sati ukku lokacin watan Fatuu biyu da sati guda a Us, a yadda sukai da Haisam in ya rage saura Sati biyu zata tafi shi kuma sai ana saura sati d'aya zasu taho shi da Fanan, gudunmawar miliyan biyu ya bata yace in basu isa ba tayi mashi magana cike da nuna farinciki ta nuna mashi sun isa har ma sun yi yawa, a yadda sukai da gwaggo bayan ta kirata kan Maganar kayan Waki ce mata tayi tana ganin kawai za'a siya mata ne ready made har ma tayi ma Aunty Mareeya magana kan hakan tace in an tashi siya akwae inda zata kai su suna da kaya masu kyau wanda za'a siya ma Minon, Fatuu taji dad'in jin hakan gaba d'aya gudunmawar da Haisam ya bata ta tura ma gwaggo tace saura tata in tazo Gwaggon tace wannan uban kuWi haka da Wanta ya bada anya basu yi yawa ba Fatuu na yar dariya tace mata a haka ma cewa yay in basu isa ba tayi magana ya ?ara da sauri gwaggo tace don Allah kada ta ?ara tambayar shi ko Naira wannan ai Kusan ma shi zai mata kayan Wakin, tambayarta Fatuu tayi kamar ya za'a mata kayan gwaggo tace wai da ita a tunaninta ayi mata saitin gado da kujeru masu kyau wanda da an gani ansan masu kud'i ne tunda Baffan su ma sunyi Magana kan kayan Wakin ta nuna mashi ya turo kuWi kawai a siya sai duk a haWa a siya mata, cewa Fatuu tay gaskiya kamata yay ayi mata komai set biyu kujerun da gadon don tasan gidan da za'a kaita babba ne alabashshi ko sai a siya set Waya masu kuWi sosae sai Wayan koda wanda basu kai su kuWi ba Gwaggon tace to hakan ma bari in aka harhaWa kuWin sai aga kaman ya za'a siya mata don itama tana son a yi mata kaya sosae tunda ita ba'a yi mata komai ba Fatun tace komai kenan sai tazo sai suje a siya in sha Allah ba abunda zai gagara bane, itama Gwaggon tace in sha Allah nan take faWi mata Hajiya tayi mata magana kan inda za'a Waura aure sun ro?i alfarmar in ba takura a Waura a nan Katsina sai a haWa da na Laila a Waura gaba Waya anan sai a tura Mota can Adamawa ta Waukko masu zuwa Waurin auren nan don in akace ayi acan sannan ayi na Laila a Abuja za'a takura mutane don zirga zirgar zata yi yawa to ta kira Baffansu kan hakan shima yayi magana da yan'uwanshi duk sun amince da hakan shi ArWo ma ance ba lalle yazo ba don bai jin daWi Fatuu ta tambayi abunda ke damun shi tace mata kawai harda tsufa wai jikin nashi ne bai jin daWin shi, fatan Allah ya bashi lafiya Fatuu tayi kafin suyi sallama Gwaggo ta tambayi ina Y'ay'anta Fatun tace gasu can wurin Aunty Fanan wai tafiya take koya masu, yar dariya gwaggo tayi tace da wuri haka Fatun tace eh wai daga taga sun fara tsayuwa shine ta fara koya masu Gwaggo na dariya tace ina ruwan Wiyarta tana dai kula da yaran sosae Fatun tace sosae don yanzu har aiki take tafiya dasu ta bada su wurin raino a can har makaranta aka so saka su amman ta hana wai ai a wurin rainon ana koya masu abunda ake koyawa a Makarantar, da alamun mamaki gwaggo tace "wace irin Makaranta kuma yaran da basu wuce wata bakwae ba" yar dariya Fatuu tayi tace mata su nan haka suke yi kamar wurin raino ne to sai a rin?a nuna masu abubuwa don su taso sun sani gwaggon tace ta gane aikuwa bari itama tazo ta koma Makaranta ko ta ?ara sanin abubuwa kada suzo su ?ureta harda ma turanci zata koyo, Fatuu nata Dariya itama gwaggon Dariyar take daga baya ta tambayeta ya jikin nata ta bata amsa da Alhamdulillah tace badai ta laulayi sosae ko Fatun tace mata eh ai maganin da take sha kullum yana hana ta yin amai ko tashin zuciya lafiya lau take cin Abinci saidai wani lokacin tana jin kasala taita kwanciya sai kuma ciwon kai da take yi wani lokacin shima, Addu'ar Allah ya inganta ya sauketa lafiya gwaggon tayi Fatuu na murmushi tace "Amin ya rabbi, Allah ya amsa gwaggota mahaifiyata, ina tsananin son ki da dukkan zuciyata" wani irin murmushin daWi gwaggo tayi itama tace "nima ina ?aunar ki autata Fateema, ina ro?on Allah ya ?ara ma rayuwar ki albarka data zuriyar ki ya ji?an Mahaifiyar ki" wani irin lumshe ido Fatuu tayi nan da nan idanunta suka ciko da kwalla don a lokacin nan koda yaushe Mahaifiyarta na a ranta sosae take jin maraicinta tana jin inama ace tana raye rayuwarta tayi albarka haka, jin tayi shiru yasa gwaggo kiran sunanta ta amsa a hankali tana jin yanayin muryar tata ta gane kuka take, itama zuciyarta karyewa tayi abubuwa suka fara mata yawo a rai tay ?arfin halin ce ma Fatuu ta daina Kuka tayi mata Addu'a in sha Allahu ta dace a sanyaye ta amsa da Allah yasa, kafin suyi sallama gwaggon tace in kusa Fanan take ta bata su gaisa tace to, bayan ta kai ma ta a Nursery ta sanar mata ga gwaggo zasu gaisa cike da nuna jin daWi ta amsa cikin washe baki suka gaisa gwaggo tace ai an faWi mata tana nan tana ta aikin koya tafiya Fanan d'in tay dariya tace eh so take su iya kafin su zo biki yadda in suka zo zasu je ko ina da ?afafun su gwaggon tace lallai kam akwae aiki yanzu nan da sati guda kenan take son su iya tafiyar tana ta dariya tace eh itama gwaggon dariyar take tace to Allah ya taimaka ya bada sa'a ta amsa da Amin kafin suyi sallama harda kara ma Adam wayar wai yace mata Hello sai gashi yace Win cike da jin daWi gwaggon ta shiga yi mashi magana da hausa tana tambayar yadda suke shida Wan'uwan shi yay zuru yana zaro ido Fanan da Fatuu sai yar dariya suke ganin yadda yay ganin sunata dariya yasa shima yin dariyar gefen kumatun shi duk suka lotsa Madarar kyau abun sai dai ace tubarkalla, amsar wayar Fanan tay gwaggo tace ko basu yi masu magana da Hausa ne tace a'a suna yi masu Momynsu ma harda Fulatanci tana masu magana haka Dad d'in su ma yana masu larabci zasu taso suna jin yare hudu Gwaggo tace Masha Allah Allah yay masu albarka da sauri ta amsa da Amin da zasu yi sallama Fanan Win harda cewa "We love you so much granny" gwaggo na murmushi da hausa tace "nima ina son ku Y'ayana, Allah ya ?ara ma rayuwar ku albarka ya ?ara haWa kan ku ya kauda idon ma?iya da mahassada ya kare ku daga dukkan sharri" cike da jin daWi Fanan ta amsa harda lumshe ido daga baya ta ba Fatuu wayar don suyi sallama.

Shirye shiryen biki nata kankama a dukkan 6angarorin angwaye da amaren, Bayan sati guda Fatuu ta taho da wata babbar Mata da zata zo Kano harda iyalinta Haisam ya haWasu don su taimaka mata da su twins dama damuwar shi kenan yadda zata yi dasu shiyasa ma bata wani kwaso kaya ba iya Wan babban trolley ne da yar jaka sauran sai zasu zo su taho mata dasu, bayan sun iso Kano Matar tace mata in ba jirgin da zai je Katsina yanzu sai su tafi gidanta kafin lokacin tafiyar yayi Fatuu na murmushi tace mata ai da Haisam ya siya mata ticket online akwae wanda zai tashi bada daWewa ba yaran Matar suka shiga faWin wayyo ba haka suka so ba sun so su bisu gidansu don basu gaji da ganin su twins ba ita dai Fatuu murmushi kawai take, itama Matar da wani matashin mutum da zai tafi Katsina ta haWa su don ya taimaka mata shima a first class zai zauna inda Fatun zata zauna, lokacin Haisam ya kira don yaji in sun sauka Fatuu taba Matar waya sukai magana sosae yayi mata godiya tana ta fara'a irin tasu ta manyan Hajiyoyi tace ai ba komai duk yima kaine tana fatan wata rana in yazo ?asar zai kawo mata su yace in sha Allah daga baya ta sanar dashi itama ta dam?a su a hannun wani da zasu zauna tare don ta bincika bata samu mace da zata zauna anan ba yace to ba komai ya ?ara mata Godiya kafin sukai sallama, Wuraren karfe sha biyu na rana suka sauka Katsina, cike da Farinciki su Gwaggo da kawu Amadu da Amarya Mino sai Tk daya kai su suka tarbe ta basu zo da Kamalu ba shi Kawu Amadu ya baro ma shago, kowa yay mamakin ganin yadda Fatuu ta canza har sun kasa rufe bakunansu gaba Waya hutu ya zauna mata sosae tayi 6ul6ul da ita ga skin Winta ta ?ara mulkewa ta ?ara haske in tayi dariya abun gwanin burgewa ga cikinta har ya Wan fito, su Twins kam abun ba'a magana su wannan tun a jirgi aketa santin su, sai so suke su Wauke su amman sun ?i yarda dama Adam ne me Wan yarda a Wauke shi shima sai yaga Fatun na a kusa, da ?yar ya yarda Mino ta Wauke shi daga wurin mutumin da ya ru?e shi a jirgi sai faman ta6e baki yake zai yi kuka Fatuu ta shiga rarrashinshi da turanci tana ce mashi itama Minon Mom Win shi ce, shi dai Abie na li?e da ita da alama ma tsoronsu yake don har fuskar shi ta nuna ya waro ido tubarkalla sai bin su da kallo yake, Sosae su gwaggo sukai ma mutumin godiya yana murmushi ya nuna masu ba komai kafin sukai sallama ya tafi, bayan sun fito wurin da aka parker Motar su ukku suka shiga baya kawu Amadu ne yanzu zai tu?a Motar don ya iya bayan tafiyar Fatuun Tk ya koya mashi da Motar tata tare da amincewarta, yana fara driving Fatuu ta shiga yaba mashi ganin har ya iya Tk dake gefen shi yace ai yanzu ba inda bai zuwa da mota, bayan sun bar Airport Win suna ta hira Fatuu ke tambayar Hajiya Tk na murmushi yace tana nan lafiya tana can tana jiran isowar su, lokacin da suka iso ?opar gidansu tsayawa Fatuu tasa akai don ta gaisa da Yayanta Kamalu yana ganinta ya hau washe baki yace bari ya rufe shago yazo su ?arasa gidan tare, a gaban Motar Tk ya matsa mashi suka tafi suna isa gate su officer suka taso suna masu sannu da zuwa daga baya aka buWe masu gate suka shige, a gaban entrance ya parker Motar duk suka firfito lokacin Saude ta fito cikin washe baki ta nufo Fatuu itama tana ganinta ta fara mata murmushi tana zuwa ta Wan rungumota tana mata sannu da zuwa aikuwa Abie na ganin haka ya fashe da kuka da sauri Aunty Saude ta saketa tana faWin ashe ba'a ta6ata ta shiga ba shi ha?uri tana faWin ai ta saketa to yay shiru ai kamar ma tana ?ara tunzura shi sai kukan yake ?ara yi ganin haka yasa Sauden cewa to ko dai tsoron ba?a?en Mutane yake Gwaggo tace taga alama don tun Wazu duk ya bi ya ?an?ame Uwar tashi, ganin Abie Win na kuka yasa Adam shima fashewa da kukan dama ?iris yake jira Mino ta matso dashi wurin Fatun don ta rarrashe shi, Hajiya ce ta fito tana dogara sandarta ta alfarma idanunta sanye cikin glasses ta nufo su tana faWin ita dai tayi gajen ha?uri ta fito, ganin su twins na kuka yasa ta tambayi mi ya faru duk suke kuka Saude ta faWi mata ta jinjina kai tana dariya tace aikuwa aiki ya same su in dai tsoron ba?a?en mutane suke tunda ?asar su suka zo duk akai dariya, gaishe da ita Fatuu tay ta amsa tana ta fara'a tay mata sannu da zuwa kafin tace to a shigo ciki a zauna yadda za'a gaisa sosae suka ce so ta kalli su twins da suka bita da ido tace masu barkansu da zuwa ?asar ba?a?en fata, tambayar ina mai gidan nata yake tay Fatuu ta nuna mata shi a hannun Mino tace wato ita kenan don tana fara ya yarda da ita duk sukai dariya, cikin gidan duk suka nufa a parlor aka zazzauna ana ?ara gaisawa da ?ara yi masu sannu da zuwa Hajiya ta tambayi Fatuu jikinta tana ta murmushi tace Alhamdulillah tay fatan Allah ?ara ingantawa ya sauketa lafiya ta amsa tare da su Saude, sake tambayar ya ta baro su Haisam Hajiyar tay tace lafiya lou duk suna gaishe su suna nan zuwa, Saude nata kallon Fatuu don komai tayi burgeta take can ta kasa ha?uri tace mata har ta canza sosae Hajiya tace ai dole yanayin ?asa ba Waya ba, Maganar Abinci Hajiya tayi ma Fatuu tace gashi can an shirya akan table in kuma a kawo nan to tace eh a kawo nan cikin parlor Saude ta amsa da to ta mi?e, sallama gwaggo tayi masu Hajiya tace ta tsaya sai sun ci Abinci sannan, lafiyayyun Abinci da abun sha aka jere akan carpet duk Saude tay serving nasu abun yay kamar yar Walima har gwaggo na faWin to kada kuma su cinye ma ba?i abinci Hajiya tace ai dama harda yan tarbar ba?in aka yi, a nutse suka fara cin abincin harda Hajiya a kan c-table aka Waura mata bayan ta fara ci tace ma Mino ta kawo mata Adam, kuka ya saka bayan ta kawo mata shi yana mi?a hannu alamar Mino ta Wauke shi Hajiya ta shiga rarrashin shi tana faWin "Haba mai gida yada tsoron Mata inata farincikin tarbarka sai kuma ka?i yarda dani" su Gwaggo nata murmushi Hajiya ta kalli Fatuu tace "to wai ma yana fahimtata ko sai anyi turanci" amsa ta bata da eh suna gane hausa amma sun fi fahimta in akayi turanci, komawa Hajiya tayi tana rarrashin shi da turanci har ya fara yin shiru manyan idanun shi a kanta yana ta6e baki ita kuma tana ta faWin yayi shiru shagwa6a66an maigida, lokacin da suka gama cin Abincin an kira Azahar Kawu Amadu da Tk suka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login