Showing 501001 words to 504000 words out of 513411 words

Chapter 168 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16708

nan kuma matsayin Wakin ba?in Haisam ne, abun saidai ace Masha Allah kawai komai yayi an narka dukiya ba kaWan ba a wannan gida gashi akwae free internet access wato damar hawa yanar gizo da mutum ya buWe wi-fi shikenan sai yay ta browsing da chat basai kana da Data ba, bayan an gama da ciki bayan gidan aka nufa wanda gaba Wayan shi malale yake da grass carpet, akwae swimming pool wanda aka ?awata tsarin shi gwanin burgewa ruwa har ta sama yake zubowa sannan ta ?asa ma akwae wasu haWaWWun ka?????'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'(n famfuna dake zubo da wani ruwan, daga gaban shi wani wuri ne da aka zagaye da waya ciki kayan wasan yara ne kamar dai park, akwae wurin wasanni guda biyu na ?wallon kwando wato basketball da kuma ?wallon raga wato Volley ball sai wasu rumfuna biyu na sha?atawa ne sai Wayar wadda ta gini ce ita kuma anyi tane don yi ma yara lesson, daga jikin gidan ta baya akwae ?opar fitowa sannan akwai wani Waki mai babbar ?opa cikinshi ma yana da girma nan kuma Gym ne wato Wakin motsa jiki mai Wauke da kayan motsa jikin iri iri harda treadmill irin wanda Fatuu ta ta6a hawa ya wujijjigata har ta suma...

105



~_*
'=؋?BOSS LADIES WRITERS=؋?
'*_~



......... Alhamdulillah Allah yayi mun gama zagaya ko ina sai yaba gidan ake ana an dai kashe kuWi, cike da tsokana Dad Win su Haisam wato Mr President yace mashi anya bazai sa EFCC su bincike shi ba don an kashe ma gidan kuWi da yawa duk akai dariya Hajiya tace in an tashi bincikar tashi sai a haWa dashi tunda ai shine ?arfin nashi, Dad Win na yar dariya yace shi ai gida kawai yasan ya bashi amman ba hannunshi a wannan uban kayan daya zuba ma gidan Hajiyar tace aikuwa shike da hannu tunda ai shiya biya mashi yaje yayi karatun fasahar da yake samun kuWi duk akayi dariya harda Security dake biye dasu, itama Mom yaba ma Jidderh tayi tace bata san kamfaninta sun ?ware haka ba sai yanzu gaba Wayan kayan da aka zuba ma gidan sun hau kuma sunyi kyau nan fa duk aka shiga yaba mata tanata dariyar jin daWi haka mijinta Sadeeq shima yaji daWin yabon nata da ake Dad Win su har yana cewa zai bata kwangilar zuba ma gidan su kaya in ya sauka zasu koma, cike da jin daWi tayi mashi godiya Aunty ma tace zata rin?a samo mata kwangila kuwa tunda sun ?ware haka Hajiya Zainab ma itama tace zata rin?a samo mata dama harda ita aka zo don yanzu sunfi zama a Abuja bayan an ba Dad Winsu Sameer Minister, Fauzy dai basu ?asar kuma har yanzu bata sake haihuwa ba itama don Sameer yace sai ta huta sosae ba kamar daya ga Cs aka yi mata, ganin Dad Winsu na niyyar tafiya yasa Haisam ce mashi please ya bari suci abinci ya Wan buWa mashi ido kafin yace ai baya jin yunwa Jidderh dake murmushi tace ai na murnar sabon gida ne ya kamata yaci yana murmushi yace to tunda hakane a bashi ya tafi da abunshi duk akayi dariya dama ya iya barkwanci, Fanan ce ta nufi cikin gidan da sauri dama sunyi Order Win abinciccika saboda masu rako su sabon gidan, bada jimawa ba ta fito ru?e da manyan ledoji guda biyu ta nufo shi dasu, har rige rigen amsa mu?arrabanshi daya zo dasu suke amman sai yace masu su bari shi zai ru?e abunshi don kada wani ya cinye mashi aikuwa mi za'ai ba dariya ba kuma shi Win ya kar6i abun shi anata ya kawo don Allah a ru?e ya ?i badawa, Addu'o'i yayi masu na Allah ya sanya alkhairi yasa sun dawo a sa'a ya karesu daga dukkan sharri anata amsawa daga baya sukai sallama aka buWe mashi mota duk sauran abokan tafiyar nashi suma suka shiga motocin saida aka ga tafiyar su sannan suka koma cikin gidan harda su Mom, a falo aka zazzauna zaman cin abincin abun gwanin sha'awa su Mom sai kace ba First lady ba sun saki jiki cikin yan uwa ana ta cin abinci ana hirar nishaWi. Sai gab da Magrib Fatuu ta iso Haisam yaje Waukkota tasha gayun doguwar rigar shadda, tun a bakin gate Win gidan ta fara sakin baki don itama ba sanin gidan tayi ba ta dai san shi a hoto, lokacin su Mom duk sun tafi sai su Mino da Aysha da kuma Jidderh da suka tsaya su tarbeta, sosae aka nuna farincikin dawowarta bama kamar su twins, Esha tana ganinta ta ?an?ameta tana mata welcome tare da nuna mata sabon gidan su, sam Fatuu ta kasa 6oye al'ajabinta da kuma farincikin gidan sai faman bin gidan take da kallo idanu waje tana kuma sakin murmushi duk a lokaci guda, zagayawa suka shiga yi da ita harda Fanan Haisam kuma ya tafi Masallaci, bayan sun gama ganin ko ina ciki suka dawo don yin salla, sosae Fatuu tayi godiya ga Allah da yadda yake ta mata ni'imomi da bata ta6a zaton samu ba a rayuwarta, harda kukan daWinta sannan tayi ma Mijinta Addu'o'i sosae shima, bayan sallar isha aka zo Waukar su Mino anata mata Addu'ar Allah ya raba ta da cikinta lafiya haka Aysha amarya ma ba'a daWe da Waukar Mino ba itama angonta Na'eem yazo ya Wauketa, Jidderh ce ta ?arshe da aka Wauka duk saida mazajen nasu sukai ma Fatuu Allah ya sanya alkhairi kafin su tafi don Wazun da suka zo bata nan, bayan Haisam ya dawo a tare gaba Waya suka zauna cin abinci a dining area fuskokin kowannensu cike take da annuri, bayan sun gama cin abincin ne Haisam yace suyi alwala suyi Nafila duk suka ce to harda yaran, anan babban falon sukayi sallar raka'a biyu ta godiya ga Allah bayan sun gama kowa yayi addu'a Esha tana yi tana dariya tana le?en fuskokin su twins, a falo suka zauna nan Fatuu tayi ma Haisam Win godiya da Addu'oin Allah ya ?ara mashi lafiya da arzu?i mai amfani harda su Fanan dasu Esha ake amsawa, kallo suka yi zuwa ?arfe tara da rabi Haisam yace ma su twins suje ya rakasu su kwanta aikuwa Esha na jin haka ta fara tura baki tana ?un?unin ita ba'a yi mata Waki ba a saka mata Wan gadonta itama duk sukai dariya Fatuu tace ita dake da ma Wakuna har biyu ga Wayan na part Winta ga kuma na Momynta sai inda take so zata kwana ta tura baki tace ai duk gadon sun mata ?ato ita kalar nasu twins take so, Haisam dake a tsaye yana murmushi yace mata tayi ha?uri in ta samu sister sai ayi masu Wakinsu suma su biyu ta wani yarfa hannu tace to ba Aunty da Momyn su?i su haihu ba tayi ?anwa duk sukai dariya, jawota Fanan tayi jikinta tana bata ha?uri tace bada daWewa ba zata yi ?anwa da Aunty ta gama karatu,

"To Momy ke ki haihun man younger sister tunda ita sai ta gama karatun" ta faWa a shagwa6e, murmushi Fanan Win ta shiga yi tana Wan kikkifta ido ta kasa ce mata komai, hannu Fatuu ta kai ta dafa kafaWar Esha Win tace "Momy zata haifar maki sister in sha Allahu, daga yanzu duk kikai salla pray for her, kuma su twins ku rin?a yi ma Momynku Addu'ar Allah yasa ta haiho mana Baby mai kyau" ta ?arasa tana murmushi duk suka ce to Haisam nata murmushi bai ce komai ba ya kama hannuwansu bayan sun yi masu saida safe suka tafi yadda ya ru?e su abun gwanin sha'awa, bayan sun haye bene Fanan ta mi?e tana ru?e da hannun Esha tace suje itama ta kwanta ta Waga hannu tana ce ma Fatuu "Good night, Aunty" itama hannun ta Waga mata tace "Goodnight, Esha Darling" ta saki dariyarta mai kyau suka tafi, bin su da ido Fatuu tay har suka shige ta Wan girgiza kai wani irin tausayin Fanan take ji game da rashin haihuwarta don ta san dole tana tsananin son ta haihun, lokacin da su twins suka fara girma duk sun Wauka Fanan Win ce ta haife su saboda yawan jan su a jiki da take, koda ta fahimci hakan don sun fi sakewa da ita da kanta ta sanar masu da cewa Fatuu ce ta haife su Adam har saida yaje ya tambayi Fatun wai da gaske ba Momy bace ta haife su ta tambayeshi waya faWi mashi hakan yace ita, jin haka yasa taje tayi mata magana kan miyasa zata yi masu wannan Maganar tana murmushi tace yakamata su sani ne don uwa ba wasa bace in bata faWi masu ba zasu iya ?in bata muhimmancin daya kamata lokacin har saida su duka sukai ?walla, daga baya ne Fatun tace masu suci gaba da Waukar Fanan matsayin Momyn su ita kuma su rin?a ce mata Aunty, mi?ewa tayi ta nufi Bedroom Winta inda keda royal bed, bayan ta shiga shirin yin wanka tayi dama duk kayan sawarsu an riga an kawo su tun kafin su dawo har ta ware wasu masu yawa zata aika ma Gwaggo a bada su sadaka a Foundation Winsu wanda yanzu sosae ya cigaba ana tallafa ma marasa ?arfi ba kamar yan gudun hijira da akwae su sosae a yankin Katsina, su twins ma da Esha duk an ware kayan su da yawa za'a bada Fanan ma haka, a cikin laundary ta cire kayan jikinta ta Waukko rigar wanka ta saka tana ta kallon kanta ta cikin ?aton madubin wurin, gaba Waya ganin komai take kamar a mafarki gashi sai take ganin komai ya faru da wuri wato dai ashe cin ribar ha?uri haka yake da daWi, lafiyayyan wanka tayi lokacin data fito sai faman sakin wani irin ?amshi take, Bedroom ta shiga ta zauna akan kujerar gaban madubi tana kallon kanta tana goge lemar ruwan jikinta data kanta, tana haka Haisam ya shigo cikin Wakin da sallama ta juya tana kallonshi suna haWa ido ta fara sakar mashi ?ayataccen murmushi shima ya shiga maido mata, tun kafin ya ?araso gareta ?amshin turarenshi ya rigashi isowa yana sanye da kayan bacci riga da wando farare masu taushi wanda da gani sababbi ne, wurinta ya nufo yana zuwa ya tsaya yana kallonta suna sakar ma juna murmushi can ya mi?a hannu ya amshi towel Win da take goge jikin ya cigaba da goge mata sai dai nashi da wani irin salo mai tsuma zuciya yake yi suna yi suna kallon juna ta cikin madubin suna cigaba da sakin ?ayataccen murmushi mai tattare da tsantsar ?aunar juna, bayan ya gama goge mata da kanshi ya shafa mata man da yasan tana amfani dashi da daddare, gaba Waya shi yayi mata shafe shafe da goge gogen da take yi da daddare da yake gashinta bai ji?e ba sosae iya baki baki ne hakan yasa bai busar mata dashi ba, bayan ya gama mi?ewa tayi da niyyar taje ta saka kaya kawai sai ji tayi ya janyota ya haWe jikinsu kafin ya haWe fuskokinsu suka shiga sha?ar numfashi da ?amshin juna, slowly ya kai lips Winshi ya haWe da nata ya shiga bata deep and hot french kiss, tun ?afafunta na Waukarta har suka kasa gaba Waya ta ?an?ame shi, ya Wan Wauki lokaci kafin ya saketa ai da ?yar take iya kallonshi hakan yasa shi yin Wan murmushi mai sauti ya kai hannu ya Wauketa gaba Waya, yana Wauke da ita ya nufi switch ya kashe hasken Wakin kafin ya nufi haWaWWan royal bed Winta daya sha lafiyayyan zanin gadon da ko mutum bai yi niyyar bacci ba ya kwanta sai ya Wauke shi, sosae Fatuu tayi ma Haisam godiya ta hanyar faranta mashi daren ranar ya shiga cikin tarihinta, Washe gari da safe ita da Fanan suka shiga Kitchen don yin Breakfast sai mai aikinsu ta wancen gidan da suka taho da ita ita kuma tana gyara gidan duk da bai wani 6aci ba, suna cikin aiki ne Fanan take ce ma Fatuu yakamata a ?ara masu aiki don yanzu aikin dole zai yi yawa ba kamar wanccan gidan ba tunda shi iya inda suke amfani ake gyarawa Fatun tace mata tana ganin a ?ara guda Waya tunda in ta gama karatunta zata dawo da Asabe mai aikinta ta can
Zaria nan,

"Allah sarki, har na tuna da Aunty Saude mace mai kirki gashi sam bata da son jiki, in mutum ya samu mai aiki kamarta ya more don tana da amana" Fatuu dake juya dankalin turawa cikin mai ta faWa, Fanan na jin abunda tace itama tace gashi ta iya girki kamar me Fatuu tace wllh,

"To ko ayi mata magana in tana da wadda zata turo mana, dama ni ban cika son irin wanda agent ke turowa ba don baka san mutum ba wasu mutanen are evil" kai Fatuu ta jinjina tace to zata mata magana dama basu daWe da sukai waya ba tayi mata barka don ta haihu, Wan buWa ido Fanan tayi "Don Allah fa!" Fatuu tace mata wllh,

"Amman ban samu labari ba ai da nayi mata barka kuwa, ikon Allah, itama tunda tayi aure bata haihu ba sai yanzu duk da bansan ko tana Family planning bane tunda ance tana da wasu yara" Fatuu tace mata eh tana da yara da tsohon mijinta kafin ta ?ara cewa "kema in sha Allahu Aunty Fanan zaki haihu" tana murmushi tace to Amin in tana da rabo in kuma bata da rabo already Allah ya bata ta wata hanyar Fatuu tay murmushi,

"Amman fa in kin mata Maganar mai aiki kada a samo yarinya ko budurwa babba kamarta zaki ce" Fanan ta faWa tana motsa farfesu, cikin rashin fahimta Fatuu tace to dama aikin gidan nan babbar zata fi, yar dariya Fanan tayi don ta fahimci bata gane dalilin da yasa ta faWi haka ba tace mata ita saboda kada a ?wace masu miji ta faWi haka don tana jin labarun faruwar irin haka, dariya sosae Fatuu tay harda Wage kai Fanan dake dariya itama tace Allah, bayan Fatuu ta tsagaita da yin dariyar tace ai Hubby bazai yi hakan ba,

"Uhmm, wani lokacin suna ba mutum mamaki fa ba kamar shi da ya cika tausayi hakan na iya saka shi ya auri mai aiki",

shiru Fatuu ta Wan yi tana Wan murmushi, jin tayi shiru yasa Fanan Win kallonta nan take ta fahimci yanayin fuskarta ya canza da sauri ta kai hannu ta dafata tace "Zarah bafa nayi Maganar saboda ke bane wllh, i just said it as an example, Babe wani irin mutum ne shi yana da kirki sosae, inda kirki yana yin yawa to zance kirkin shi har yayi yawa abunda baka tunanin zai iya yi sai kiga ya yi, kamar yadda ya aure ki da niyyar taimako nima haka ne, gara ke ma don na tabbatar yana son ki kawai bai sani bane, amman ni na tabbatar baya sona lokacin daya aure ni kawai yayi ne don ya faranta man ganin na shiga mawuyacin hali saboda shi, amman saboda kirkin shi tunda nike dashi bai ta6a wula?anta ni ba daidai da rana Waya gashi ko haihuwa bana yi, Babe na musamman ne" ta ?arasa idonta a sama tana murmushi, itama Fatuu murmushin ta shiga yi tana tunano tun daga farkon haWuwar su,

"Amman Aunty Fanan nace mi zai hana mu Wan hada mashi surprised party matsayin godiya da wannan sabon gidan" Fatuu ta faWa tana kallon ta, da sauri Fanan tace wannan shawara ce mai kyau ya take gani za'ai Fatun tace ayi mashi cake sai ai decorating falonta, Jidderh suka yanke zasu kira kan tazo ta shirya falon Fanan Win in zasu yi mashi partyn bazatar, waya Fatuu ta Wauka bayan ta kira Jidderh ta Wauka sun gaisa take faWi mata abunda suke son yi, tambayar ta tayi yaushe suke son yin partyn Fatuu ta kalli Fanan ta tambayeta tay Wan jimm alamar tunani kafin tace ko gobe ko Fatun tace to ai kuma ita gobe zata koma, ce ma Jidderh sukai in zai yuwuwa zuwa da yamma kamar wurin ?arfe biyar tace Ok lafiya lau zata masu ?o?arin hakan,

Misalin ?arfe huWu Jidderh ta iso gidan a Motarta, saida ta fara kiran Fatuu ta tambayi in Haisam bai a babban falo tace mata eh yana Masallaci, tare da wata abokiyar aikinta yare suka zo, bayan sun fito daga cikin Motar suka fara kwasar kayan da suka zo suna shiga dasu, bayan sun kai wasu Fanan da Fatuu suka biyo su suma suka taya su Waukar wasu, ba 6ata lokaci Jidderh da abokiyar aikinta suka fara shirya falon, bayan sunyi nisa ne Fanan da Fatuu suka tafi su shirya,

wuraren ?arfe biyar Fanan ta kira Haisam a waya ta tambayi yana ina ya bata amsa da yana a sama suna yin lesson dasu twins tace pls in ba damuwa ya zo part Winta tana son ganin shi ya furta Ok, ba'a Wau lokaci ba ya turo ?opar yana sanye da ?ananun kaya da suka amshi jikinshi, yana niyyar yin sallama ya dakata sakamakon wani ?yal?yali daya zubo mashi har saida ya Wan runtse ido, bayan ya tsagaita da zubo mashi yasa hannu yana kakka6e wanda ya ma?ale mashi a jiki da saman sumar shi, yana Wagowa ya kalli gaban shi idanunshi suka sauka akan wata yar banner da aka yi rubutu mai walwali an rubuta _"Thank you for our new home, We really love you our Husband"_ ?ayataccen murmushi ya saki ganin rubutun kafin ya juya ya kalli cikin falon wanda aka ?awata shi da baloons wato balo kala kala sannan an aje manyan hotunan bikinsu shida Fanan da kuma wanda akayi mashi da Fatuu a Dinner Win su da akai a Abuja sannan an aje wanda sukai su duka da yaran su harda babban cake mai hawa biyu anyi decoration da hotunan Haisam da zasu kai biyar sannan an yi rubutu in icing an rubuta "Home sweet home" sannan daga saman baki bakin cake Win anyi topping da fresh fruit da suka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login