Showing 483001 words to 486000 words out of 513411 words

Chapter 162 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16722

da Saleem, ba ?aramin mutane aka haWa ba kowa yayi shiga ta alfarma kar ma su Mom suji su Fatuu ma ansha rantsattsan leshi iri Waya ita da Fanan wuya da hannu sun sha dan?ararrun gold Haisam ma yasha bugaggun fararen suit sai necktie ba?i haka ?afafunshi na sanye da dakakkun ba?a?en cover suma abokan aikin nashi duk suit ne a jikinsu, yaran su gwanin burgewa duk sun girma su Twins yanzu shekararsu ukku da watanni amman sai kace sun fi hakan don suna da tsawo da kuma kauri suma suna sanye da suit na yara Esha kuma shekarunta biyu itama tana sanye da ?ananun kaya riga da wando an raba mata ba?ar sumarta biyu ta saukko har ta wuce kafaWarta kunnanta na sanye da barimar diamond da yan hannu ba ?aramin kyau yaran sukai ba duk wanda ya kallesu sai ya ?ara yan jarida duk sun zagaye wurin suna ta aikin Waukar rahoto, bayan jin bayanai da suka danganci sabon kamfanin daga bakunan wasu masu ruwa da tsaki a kamfanin ciki harda Chief Executive Officer (CEO) wato Haisam da Mr President da wasu turawa a tare Haisam Win da Fatuu da Fanan suka yanka ribbon Win da aka zagaye ?opar shiga cikin kamfanin mutane suka sa tafi ji kake "raf...raf...raf...) wasu suka shiga faWin "Behind every Sucessiful Man there is woman or women" duk akasa dariya kafin akai bismillah suka sa kai, ginin bene ne hawa ukku akwae Ofisoshi daban daban da bangarorin gudanar da aikin kamfanin ko ina an zuba nagartattun furniture da suka dace da wurin wani abun ma sai Office Win Haisam wata daula ce guda akwae kuma Wakin taro wanda aka sa haWaWWan zunguren tebur aka kewaye shi da kujeru mahaWin shi, haka akai ta zagayawa wurare ana Waukar hotuna da Vedios Mutane sai yabo da sa Albarka suke yan jarida nata yi ma mutanen tambayoyi ciki harda su Fatuu aka tambayesu irin farincikin da suke ciki, bayan an gama duba ko ina saida akayi addu'o'i sannan aka fita daga nan kuma Villa aka nufa don yin lunch event, komai dai ya ?ayatar an ci an sha anyi hani'an sai fatan Allah ubangiji yasa ma kamfanin albarka ake, a ranar kusan kowacce tashar Tv saida aka nuna bikin buWewar haka Social media Maganar sabon kamfanin kawai ake da gidajen radio ana tallata irin ayyukan da kamfanin zai rin?a yi har da tashoshin wasu ?asashen an nuna dasu bbc, a ranar da daddare Khalid na zaune a falon gidanshi yana kallon bikin buWewar a NTA, lokacin da aka nuno Fatuu na magana da turanci tana murmushi shima Wan murmushin yayi saidai nashi yafi kama dana takaici don kuwa shi yasan yayi babban rashi kuma har abada bazata fita a ranshi ba, matarshi Hafsat ce ta dawo cikin falon daga kwantar da Wiyarsu Zarah bayan ta zauna ya nuna mata Fatuu cikin Tv Win yace mata wannan itace Fateema, kallon Tv Win tayi kafin ta juyo ta kalleshi da alamun rashin fahimta tace mashi wace Fateema yay shiru kawai tana ta kallonshi can yace mata ta garinsu yana faWin hakan ta gane don tasan labarin da ita zai aura aka fasa saidai bata san dalilin fasawar ba, maida idonta tayi kan Tv Win lokaci guda taji Fatun ta burgeta ta juya da Wan murmushi tace mashi tana da kyau sosae yay Wan guntun murmushi kawai bai ce komai ba can sai ya mi?e ma ya nufi hanyar Bedroom ta bishi da kallo.

Bayan buWe kamfanin ranar Monday aka fara aiki a cikin shi, a yadda Haisam ya shirya zasu Wan daWe anan daga baya sai su koma America suyo parking Win dawowa Nigeria gaba Waya dama ya aje aikin kamfanin da yake acan saidai ba kwata kwata ya daina aiki dasu ba akwae wanda zai cigaba da yi masu sannan shima akwae aikin da daga can za'a rin?a yi mashi a Companyn shi, bayan wata biyu akayi bikin Jidderh da Saurayinta Sadeeq Wan Minister wanda bayan hawan Senator Ali kujerar shugabanci ya sake ba Mahaifin nashi mu?amin Minister, ba ?aramin shagali aka sha ba auran Wiyar shugaban ?asa da kuma Wan Minister wanda anan Abuja aka Waura ya kuma samu halarta manyan mutane daga ko ina ciki da wajen ?asar nan sai fatan Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a Wayyiba. Tuni aiki ya kankama a kamfanin Haisam anata neman aiki bayan wata ukku da buWeshi lokacin wata guda da yin bikin Jidderh suka koma America, sati biyu sukai suka dawo acan aka baro Nameer da Mino sai sun gama karatunsu nan da shekara Waya da wasu watanni suma zasu baro can, Bayan dawowarsu Haisam Nigeria a yadda ya tsara zasu zauna a gidanshi ne, dama duk mazan gidansu kowa yana da gida da Dad Winsu ya mallaka masu saboda ba zaune suke ba dundundun yasa basu zauna acan ba suke zama a gidansu in sunzo Abuja, shi Nameer wanda yake zaune inda aka kai Mino shine nashi shima Haisam nada nashi shima a Asokoro saidai bayan dawowar tasu Dad Winsu yace mashi su fara zama anan gidanshi inda suka baro suka koma Villa don kar a bar gidan hakanan in aka ?ara wasu shekaru sai su koma nasu, hakan aka yi anan gidan suka zauna duk da yayi masu girma sosae, bayan dawowar su bada daWewa ba Fanan ta samu aiki a National Hospital Fatuu kuma Haisam yay mata magana kan tafiyarta ?asar india yin karatun Medicine amman sai tace mashi tunda anayi anan kawai ya bari sai tayi nan ba sai ta tafi wata ?asa ba, ta yanke hakan ne don bata son yin nisa dashi yace mata amman karatun nan zai iya mata wahala tace lafiya lou in dai za'a koya mata to zata iya ya amince da hakan dama shima kawai don ya cika mata burinta ne zai barta taje India amman ba don yana son yin nisa da ita ba, cikin sa'a ta rubuta Jamb kuma points Winta ya kai yadda ake so don karatun likitancin, ba tare da wata wahala ba ta samu Admission a ABU Zaria Haisam ya kama mata gida mai kyau a zariar harda Security aka aje mata sannan tasa Iya ta samo mata mai aiki yar'uwarsu wadda dattijuwa ce daga can Daura suka zauna tare, lokacin data fara karatun tayi ma Haisam magana kan yasa akawo mata motarta daga Katsina amman sai yace tunda Amadu ke amfani da ita ta bari za'a kawo mata wata daga Kaduna hakan kuwa akai,

Gidan Haisam ya zama biyu Abuja da Zaria, duk Weekend yake zuwa Zaria wani lokacin a mota ko kuma ya hau jirgi zuwa Kaduna daga nan ya wuto Zaria idan kuma bai samu zuwa da Weekend ba cikin ranakun aiki yake ware rana yazo ya kwana sai ya koma wani lokacin kuma Fatun ce ke zuwa can Abujar akwae driver musamman dake kai ta, su Twins da Esha dai duk suna a Villa wurin Mom sai Weekend Fanan ke Waukkosu nan wurinta, sosae Fatuu ke jinjina ?okarin da Haisam ke yi na zaryar zuwa wurinta ta san duk don ?aunarta da yake yi ne, duk in yazo haka zatai ta mashi godiya da Addu'o'i, bayan wasu watanni da fara karatun nata suka ji Yadikko ta haihu abun yazo masu a bazata don basu san da tana da ciki ba aikuwa sunyi murna karma Fatuu da Mino suji don ta daWe bata haihu ba sun ma Wauka ta gama ne duk da Yadikkon bata wani manyanta ba haka shima Baffan nasu ba wani manyanta yayi ba haihuwa ta biyar ce tayi gashi namiji ta haifa dama bata da Wa namiji Fatuu taji daWi data haihu cikin Weekend, da satin suna ya zagayo ranar Friday tana gama lectures ta wuce Abuja washe gari Asabar suna da safe suka bi jirgi zuwa Yola ita da Esha harda Fanan, daga gidan gwamnatin Yola aka tura Motar da zata Waukesu harda ta Security suka wuce garin nasu, lokacin da suka isa tayi mamakin ganin yadda aikin hanyar da ake masu yayi nisa harda rijiyoyin burtsatse aka yi masu Fanan sai yaba garin take tana faWin ya burgeta, anan ta iske Gwaggo da Haulat su jiya suka zo sosae kowa ya nuna farincikin zuwan nasu sai nan nan ake dasu ba kamar Fanan, Yadikko ma sosae tayi murnar zuwansu nan Fatuu ta bata sa?on su Mom harda Aunty kayane masu kyau da tsada atamfofi da laces sai kayan baby wanda yaci sunan ArWo wato Ibrahim, Fatuu sai santin Babyn take harda ce ma Yadikko ta bata shi tana dariya tace ta Wauka Fanan da tunda suka zo tana ru?e dashi tace a'a ita za'a ba sai dariya ake masu, lokacin da Fatuu ta kira Mino Vedio call harda ?walla tayi ganin an haWu banda ita, washe gari da wuri suka fara shirin tafiya saboda bayan sun koma Abuja a ranar kuma Fatuu zata wuce Zaria, tunda Aysha taga suna shirin tafiya ta shiga ro?on Fatuu ta tafi da ita harda ?wallanta Gwaggo tace da kuma tace ita zata bi Ayshar tace a'a yanzu Adda Fatuu take son bi, to itama Fatun taji tana son tafiya da ita dama Mino na niyyar Waukarta tace mata ta shirya kayanta su tafi, Yadikko najin hakan tace ya za'ai ta kama ta tafi da ita ba tare da izinin mijinta ba ai bai kamata kawai ace ta Wauketa taje masu da ita ba Gwaggo tace hakane kamata yay ace sai ta ambayi izinin shi duk da tasan bazai ?i ba amman dai yana da kyau ta tambaye shi izni tace to, lokacin data kira Haisam ta faWi mashi tana son tahowa da Aysha don ta nuna tana son biyota Murmushi yay yace yanzu don zatayi hakan shine sai ta faWi mashi kada ta manta shi da ita abu Waya ne duk abunda yayi mata to shima yayi mashi tana murmushin jin daWi tayi mashi godiya, wurin ?arfe sha Waya na safe aka zo Waukar su suka yi sallama da kowa sai Godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci ake ma Fanan, harda uban naman suna aka basu dana su Mom dama saboda su aka fara aikin naman tunda wuri, kamar kar a rabu haka aka rakosu tare da Aysha dake ta faman washe baki harda su Gwaggo da Haulat su sai gobe zasu tafi suma ta jirgi suka zo kuma tashi zasu koma. Tare da Aysha Fatuu ta koma Zaria Asabe mai aikin Fatun ke kula da ita in ta tafi Makaranta daga baya itama Ayshar Haisam ya sakata a wata private dake anan layout unguwar da suke aka sata aji ukku na Secondary.

Cikin Wan lokaci HAIFAT TechWorld ya samu kar6uwa a faWin ?asar nan, bama nan kaWai ba harda wasu ?asashen don kamfani ne da babu kamar sa a yankin Africa ta bangaren technology dama kuma yanzu harkar fasaha ba ?aramin ci take ba, akwae abubuwa da dama da kamfanin ke samarwa wanda ada sai an dangana da ?asashen turai yanzu kam nesa tazo kusa a kowacce rana ba ?aramar riba Kamfanin ke samu ba. A kwana a tashi ba wuya a wurin Ubangiji gashi har kamfanin yayi shekara Waya da buWewa anyi Addu'o'i da bikin murnar cika shekarar inda aka bayyana irin nasarorin da companyn ya samu da kuma irin ayyukan cigaba da ya kawo ma ?asar nan aka ?ara samun masu son saka hannun jari, an ci an sha an ba ma'aikatan kamfanin masu ?wazo kyaututtuka shima Haisam ya samu lambobin yabo abun saidai ace Alhamdulillah, bayan cikar kamfanin shekara Waya da wasu watanni su Nameer suka dawo Nigeria gaba Waya don duk sun gama karatun su, bayan dawowar su Nameer ya fara aiki shima a kamfanin a matsayin Software engineer, ganin Fatuu na karatu a Zaria kuma tana zaune a can Nameer ya yanke nemawa Mino Admission don ta yi degree kan abunda ta karanta a America wato Nursing dama matsayin diploma ce tayi, ba tare da wata wahala ba aka samar mata itama ta fara karatu a can ta zauna a gidan Fatuu, hakan ba ?aramin daWi yayi ma Fatun ba dama gidan babban gida ne kowacce da part Winta in mazajen su suka zo amman in suka tafi gaba Waya harda Aysha a part Win Fatuu suke zama rayuwar karatun nasu gwanin daWi sam basu da wata matsala.

A bangaren Kamalu har ya shiga shekara ta ukku itama Farha tana cikin yin Master's Degree Winta a jami'ir Lagos, a bangaren soyayyarsu suna cigaba da gudanar da ita sosae saidai matsalar da Kamalun ke fuskanta a wurinta shine ta cika kishin tsiya ba dama ta kirashi taji yana waya ko bai Wauka ba sai ta fara zargin ko da wata yake waya ko kuma ya rage sonta haka dai yake ta ha?uri don yasan saboda son da take mashi ne yasa take mashi hakan kuma shima yana son ta sosae.

Kwance tashi har Kamalun ya gama karatun shi na Degree, cikin sa'a result Winshi yayi kyau sosae saura kuma yin Nysc, result Win nashi na fitowa Fatuu tayi ma Haisam magana kan in zai yuwu ya Wauke shi aiki a company Winshi tunda abunda ya karanta ya danganci aikin kamfanin yace mata lafiya lou zasu Wauke shi daya gama Service sosae taji daWi dama ita abunda bata so shine ace Hajiya Maryam ce ta samar mashi aiki gudun wata rana a goranta mashi, Abuja Haisam yasa aka kawo shi yin bautar ?asan a kamfanin shi ya zauna a gidan su kullum in Haisam Win zai tafi aiki tare suke tafiya hakan kuma ba ?aramin daWi yayi ma Fatuu ba, tun ma kafin Kamalun ya zama ma'aikacin kamfanin Haisam ya yaba da ?wazon shi cikin Wan lokaci Kamalun ya ?ara murmurewa ya zama kalar samarin Abuja, gab da Kamalu zai kammala bautar ?asar aka fara shirye shiryen yin za6e yayin da waWanda ke akan mulki duk suka bayyana muradinsu na yin tazarce ciki harda Dad Winsu Haisam wanda shi tun kafin ma ayi za6en mutane har sun za6e shi kawai don ya zama dole sai anyi zaben amman Al'umma basu ?i kawai yaci gaba ba don a mulkinshi sun shar6i romon demokaraWiyya ba kaWan ba, a cikin shekaru huWun da yayi abubuwa da dama sun inganta kama daga ilimi, lafiya, harkar tsaro, wutar lantarki, ruwan sha hanyoyi da dai sauransu gashi an tallafa ma talakawa ta yadda da yawa sun samu abun yi yanzu tun a makaranta ake koya ma yaro sana'a don ya tashi yana da sana'ar yi haka manoma ma harkar abinci ta inganta sosae ake amfani da abincin nan gida gashi da yawan mutanen mu masu ?wazo dake aiki a ?asashen waje yayi yadda yay suka dawo suna ma ?asa aiki hakan ba ?aramin inganta bangarorin da suke aiki yayi ba ciki harda Asibitoci yanzu saidai don ra'ayin mutum yaje asibitin ?uWi ko ya kai ?a?anshi makarantun kuWi ba wai don rashin ingancin na gwamnati ba don komai ya gyaru haka tsofaffin masana'antu da suka daWe da daina yin aiki duk an farfaWo dasu abun dai sai son barka (Allah ka bamu shuwagabani irin haka Alfarmar Annabin rahama (S.A.W), Amin ya Hayyu ya ?ayyum).

Bayan gudanar da za6e tuni President Ali Adamu Zakee ya koma kan kujerar shi aka ci gaba daga inda aka tsaya, bayan yin za6en Kamfanin Haisam ya cika shekara ukku batun nasarorin da ya samu ko yake samu abun ba'a magana, a yadda suke yi duk ?arshen shekara ake raba ribar da aka samu kuma duk in suka raba sai yaba Fatuu da Fanan wani kaso mai tsoka zuwa shekaru ukkun sai gashi Fatuu ta tara kuWi masu Wan yawa a yadda ta tsara in suka kai kuWin zuwa Hajjin mutum biyu sai ta biya ma Baffanta da Gwaggo. Kamalu na gama bautar ?asar shi aka fara shirye shiryen auren shi da Farha lokacin itama ta kammala karatunta, ba ?aramin shagali aka sha ba bikin Wiyar Minister Wiyar shugaban ?asa, gaba Waya hidimar bikin a Abuja aka yi ta gashi wata gwaninta da Hajiya Maryam tayi ta ban mamaki itace gaba Waya Amaryar da Angon ta haWa tayi masu lefe dama tunda bikin ya taho ta sanar ma Hajiya a faWi ma su Gwaggo kada ayi ma Farhar lefe lokacin har wasu sukai tunanin ko don tasan ba lalle Kamalun yayi lefen daya dace bane sai gashi ta bada mamaki ai kuwa gaba Waya ?asa ta Waukka sai zancen ake na ta ba talaka Wiyarta kuma tayi masu lefe gaba Waya, tun kafin bikin Haisam ya ro?i Dad dinshi kan yaba Kamalun gidan da zai zauna kafin ya mallaki nashi tunda zasu fara aiki tare, Waya daga cikin gidajen shi na Sabuwar Estate Win shi dake a Gwarinpa ya ba Kamalun, ganin babban gidane yasa Haisam Win yace mashi ya faWi mashi yadda zai rin?a biyan haya Dad Win nashi yace dama Wa yana haya a gidan babanshi ne ai Kamalun kamar Wan shi yake don haka bashi yay ya zauna kafin Allah yasa ya mallaki nashi, sosae Haisam yaji daWin hakan yay mashi godiya da Addu'oi, lokacin har Hajiya Maryam tayi niyyar basu gidan da zasu zauna aikuwa hakan da Haisam yayi ba ?aramin daWi yayi ma Fatuu da Amadu ba dama sune masu gudun ayi ma Kamalun abun da za'a iya goranta mashi, ko ban faWa ba kunsan ba ?ananun kayan Waki akai ma Farhar ba wanda in nace zan bayyana to ni kaina wasu abubuwan bansan ya zan faWe su ba gida dai yayi kyau! yayi kyau!! abun saidai ace Ma sha Allah Kamalu anyi auren gata abun na Allah ne, ?arshe dai Farha ta zama matar Kamalu Wan fillo duk wanda yaga hotonunsu da sukai na pre wedding sai ya sake kallo wasu mutanen ma har ?aryata cewa Kamalun Wan talakawa ne suke domin ba kama ba alama, sai fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a Wayyiba Amin, bayan bikin Hajiya Maryam ta basu kyautar motoci masu kyau Kamalun ya fara yin aiki a Kamfanin Haisam ita kuma Farhar Mom Winta ta samo mata aiki a Federal Inland Revenue.

A cikin shekarar lokacin da zuwa aikin Hajji yayi Kawu Mani ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login