Showing 453001 words to 456000 words out of 513411 words

Chapter 152 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16720

murmushi ya faWi mata ta nufi gefen Fatuu tana faWin ayi ha?uri dasu haka halin su yake ba shareta sukai ba ta zauna kusa da ita tace ma Abie din yace mata Sorry saida ta maimaita mashi kusan sau ukku sannan ya faWi Sorry Win, bayan ta gama ba Adam Win ta amshe shi shima ta fara bashi anan take faWi mata zancen auren Amadu da Haulat itama Fanan Win ta nuna farinciki sosae tayi fatan Alkhairi.

A ranar Gwaggo taje ta sanar ma Hajiya itama tayi farinciki sosae tace Amadu ya kyauta Saude ma ta nuna farinciki, Tk na jin zancen Auren Amadun yace aikuwa bazai riga shi yin aure ba shima zaisa aje a nema mashi aure, da yamma Amadu na shago Haisam ya kira shi a waya cikin girmamawa ya gaishe dashi bayan ya Waga Haisam Win yace mashi yaji abun farinciki Allah yasa Alkhairi Amadun na murmushi ya amsa tare da yi mashi godiya, tambayarshi Haisam Win yay akwae gida na kusa da gidan su yana son sanin wanda ke ciki haya suke ko kuwa nasu ne da alamun rashin fahimta Amadun ya tambayi wanne ciki yace duka na left da right ya bashi amsa da na bangaren dama gidan kansu ne sai na hagu wato gidan su Umar su haya suke Haisam Win yace mashi yasan mai gidan yace mashi eh wani Alhaji Isah ne shima anan unguwar yake daga can ?asa yace mashi yana da lambarshi Amadun yace a'a gaskiya, tambayar shi yay zai iya samo mashi lambar tashi da sauri Amadun yace eh yace Ok ya samo mashi harda ta shi wanda yake hayar gidan Amadun yace ita yana da ita yace to ya fara turo mashi ita kafin ya samo mashi ta mai gidan yace to zai tura mashi yanzu sukai sallama. Da yamma bayan sallar la'asar sai ga Baban su Umar yazo shagon Amadu cikin fara'a suka gaisa kafin cike da farinciki yake sanar dashi Wazun mijin yar'uwar shi ya kira shi yake ce mashi yana bu?atar siyan gidan da yake ciki ne shine yace zai siya mashi gida da zai zauna har ma yace mashi ya nemi gidan da yake so in ya samu sai yayi mashi magana, sam Amadu bai kawo komai a
ranshi ba ya nuna ya taya shi murna sosae, Bayan sallar isha Tk ya samu Hajiya a parlonta daga gefenta ya zauna ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa, shiru yay ya maida kan shi ?asa yana wasa da yatsun hannunshi Hajiya ta lura da Magana yake son yi tace "Ya akai Wan gidan Hajiyar Sanata mi ake son faWi man ne?" Wagowa yay yana murmushi ya kasa mata magana tace mashi ko sun fara yar kunya ne still murmushin yake bai ce mata komai ba tace kar yaji komai ya fadi mata abunda yake son fadi mata da ?yar yana yar in ina yace dama so yake a je a nemo mashi Aure, Wan buWa ido tay tana kallonshi tace "Wato ashe dama kana da wadda kake so shine tuntuni ka?i yin niyya sai yanzu da kaji abokin ka zaiyi kana gudun yayi ya barka ko" yana Wan sosa kai yace a'a yaga bai fara aiki ba shiyasa bai yi niyya ba tace to yanzu aikin ya fara ne yay shiru yana murmushi,

"Ai ganin baka da niyya yasa banyi Maganar a nema maka aikin ba tunda mi zakai da aiki ba iyali amman yanzu tunda kayi niyya zanyi magana sai a nema maka sai kayi Addu'a Allah yasa a dace, Maganar zuwa nema maka aure kuma zan yi ma mahaifinka magana amman tukunna sai ansan wacece kake so tunda ba'a kama nema maka aure ba tare da anyi bincike ba" dakatawa tayi kafin ta tambaye shi sunan yarinyar da kuma yar gidan waye ya faWi mata sunanta Asma'u tare suka yi karatu har ya kwantanta mata ita yace sun ta6a zuwa ta gaishe da ita Hajiyar tace ta ganeta yanzu zata sa ai bincike sosae kafin tayi ma Mahaifin nashi magana sai a turo mutum Waya ko biyu itama zata kira Kawu Mani sai su haWu suje, Godiya yayi mata tare da Addu'o'i tana murmushi tace Allah ya nuna mata bikin Tukur Wan autanta yana murmushi ?asa ?asa yace Amin kafin yayi mata sallama ya tafi.

Washe gari bayan sallar La'asar sai ga Abbas yazo tare da wasu Mutane bayan sun gaisa da Amadu ya tambayeshi Gwaggo na nan ne yace mashi eh, juyawa yay wurin Motar mutanen da suka zo tare su biyu yace masu yana zuwa suka furta Ok ya juyo ya nufi gidan, a bakin ?opar zauren ciki ya tsaya yana sallama Gwaggo ta le?o daga cikin falo tana amsawa tana ganin shine ta washe baki tana faWin "Wana Abbas ashe kai ne ka shigo mana" yana murmushi ya nufo falon Gwaggon ta koma ciki, bayan ya shiga a kujera ya zauna suka gaisa ta tambayi su Abdul yace mata duk suna lafiya kafin yace mata yaji abun murna na auren Amadu Allah ya sanya alkhairi tana fara'a ta amsa da Amin, ce mata yay dama yazo tare da injiniyoyi zasu duba gidan da alamun rashin fahimta Gwaggon tace gida kuma ganin yadda tayi Maganar yasa yace mata basu yi Magana da Haisam bane akan aikin da za'ayi a gidan da sauri ta girgiza kai tace gaskiya basu yi Magana ba sai dai ko Amadu, yar dariya Abbas yayi yace ina ruwan H,Zakee nan ya shiga yi mata bayanin aiki za'a ma gidan don har ma anyi cinikin gidan dake makwabtaka dasu Haisam Win ya siya za'a haWe da wannan ayi sabon gini, zaro ido Gwaggo tayi baki buWe take kallon shi a Wan ruWe tace "anya dai Wana Abbas haka maganar nan take" yana dariya yace mata tabbas haka take ?ilan da Amadu sukai maganar, cike da mamaki tace anya ai daya faWi mata amman bari ta kira shi taji, wayarta ta Waukko ta shiga kiran nashi bayan ya Waga tace mashi ya shigo yanzun tana son ganinshi, bada daWewa ba ya shigo da sallama ya nufi kujera ya zauna yace mata gashi, tambayar shi tayi ko sunyi maganar za'ayi aikin gidanan da Wanta Haisam da alamun rashin fahimta ya girgiza mata kai alamar a'a kafin ya faWi mata yadda sukai dashi game da gidansu Umar da lambobin daya tura mashi sai kuma zuwan da Babansu Umar yayi cike da farinciki ya bayyana mashi sunyi waya da shi yace yana bu?atar siyan gidan da yake ciki shi kuma zai siya mashi wani ya zauna, Abbas na murmushi yace to ai su ya siya ma gidan za'a haWe da wannan a maida shi babban gini shi ya Waura ma kan aikin shine ma yazo da injiniyoyi don su fara duba gidajen, gaba Waya Gwaggo da Amadu idanunsu a waje suke kawu Amadu ya kai hannu ya rufe baki alamar Al'ajabi da alama mamaki ya kashe masu bakuna can da tsananin mamaki kawu Amadu yace "Wai Yaya Abbas yanzu kana nufin saboda mu ya siya gidan su Umar Win kuma har ya siya masu suma gida?" kai Abbas ya Waga mashi yace eh a yadda sukai za'a haWe sai ai babban Flat a fidda ma Gwaggo part Winta sai shima Amadun a fidda mashi nashi da zai zauna da iyalinshi harda ma 6angaren ba?i, nannauyar ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke ta shiga girgiza kai da alamun damuwa tace "Amman gaskiya Wana Abbas wannan hidiman tayi yawa sosae ace ya siya masu gida sannan ya siya wanda suke ciki kuma a haWe da wannan a fara sabon gini yadda gini kede cin kuWi ai gaskiya abun yayi yawa nidai da za'a bi ta tawa don Allah ya barshi in ma dole so yake yayi to a gyara wannan namun kawai ni sai in koma can Wayan Wakin shi kuma Amadun sai su Wauki dakina da nan falon za'a ma iya ?ara girman falon tunda ga Wan sauran wuri nan daga gefe har banWaki ma za'a iya yi masu a ?uryar lafiya lau wannan ma zai ishe mu" fuskarta Wauke da damuwa tayi maganar Abbas na dariya yace "to Gwaggon mu waya ?i cigaba tunda shi yayi niyya yana da halin yi ne karki wani damu tunda daya san zai takura da bazai fara cewa zai yi ba, a yadda ma ya faWi man dama yana ta son a canza ginin gidan to yadda yake son a maida gidan bazai isa ba kuma yasan kun riga kun saba da unguwar bazaku ji daWi ba in ya yi maku ginin wani wuri Hajiya ma yasan bazata so ku rabu ba shine yanzu yay tunanin yin hakan harma anyi cinikin gidan ya biya shi kuma wanda aka siya ma gidan dama can yanada rabo a wurin shi ne, yanzu dai na bar mutane a waje zan iya masu magana su shigo?" duk tayi sukuku da ita ta Waga mashi kai alamar eh ya mi?e yana dariya yana faWin karta wani damu abun farinciki ne don haka tayi farinciki kawai ta Wan yi murmushi ya juya kan Amadu da yayi duruduru yace ya taso yaje gidan su Umar Win yaga in mai gidan na nan yace za'a shigo a duba yace to tare da mi?ewa suka fita, Gwaggo dai tayi zuru tana ta jinjina abun a ranta tasan dole gidan su Umar Win yayi kuWi don yafi nasu girma ga gida kuma da aka siyan masu sannan azo a dasa gini, Bayan duk sun gama dubawa Abbas yace ma Gwaggo za'a kawo hotunan gidaje sai su za6a tace to kawai sukai sallama, zaune sukai falon Gwaggo ta kasa yin magana sai Amadu dake ta faman jinjina abun yana faWin to wai hakanan ya yanke yi masu ginin ko kuwa dai yaji batun gyaran gidan saboda aurenshi shine zai yi masu, wannan Maganar da yayi yasa Gwaggo ta Waukko wayarta ta shiga kiran Fatuu, bayan ta yanke Fatun ta kira suka gaisa nan take tambayar ta wai sunyi maganar gyaran gida da tace mata tana son ayi kafin bikin Amadu da Haisam ne tace mata a'a kawae dai ta sanar mashi zancen shine ya tambayi yaushe za'a saka rana ta fadi mashi yadda sukai da ita na ba yanzu ba sai an yi gyaran gidan Gwaggon ta sauke ajiyar zuciya, da sauri ta tambayeta miya faru ne nan ta kwashe komai ta faWi mata ita kanta Fatun tayi mamaki sosae ido waje ta shiga jinjina Maganar aikin tace gaskiya hidiman tayi yawa sosae Gwaggon tace wllh itama duk ta damu Fatun tace bari tayi mashi magana gaskiya in ma aikin yake son yi masu to a gyara gidan nasu kawai Gwaggo tace itama abunda tace kenan to Abbas yace ai har ya riga ya siya gidan kuma shi Baban su Umar yanzu in aka hana yana iya ganin anyi mashi ba?in ciki, tana cikin yin Maganar Amadu ya mi?a hannu ta bashi wayar bayan sun gaisa da Fatun yace mata kawai a kyaleshi ai mashi godiya yanzu ko anyi mashi magana kan ya bari sun san dai ba fasawa zai yi ba, a sanyaye tace shikenan sukai sallama,

Bayan sun gama yin wayar Haisam ta shiga kira da yake su safiya ce yana wurin aiki, bayan yayi picking tace mashi tana son suyi vedio call ya furta Ok, yana zaune a Office Win shi jikinshi sanye da ba?a?en suit fuskar shi sai annuri take, fuska a tur6une ta gaishe dashi yana Wan murmushi ya amsa ya gane laifi yayi mata daga yanayin face Winta, daga gaisuwar tayi shiru tana ta tura baki, lumshe mata ido yay ya furta "ya akai ne My Baby?" wani kallo tayi mashi a marairaice tace taji abunda yayi amman gaskiya hidiman yayi yawa in aikin za'ayi to ayi iya gidansu basai ya kashe uban kuWi ba haka, murmushi kawai yake ganin har yanzu halinta na rashin son ya kashe kuWi sosae na nan, ganin bai ce komai ba ta tura baki tace bazai yi magana ba,

"Yanzu nayi laifi don zan ma Family ena abu?" ya tambaya tare da Wage mata gira, kaman zatayi kuka tace "a'a ni bance kayi laifi ba Amman gaskiya kashe kuWin zai yi yawa" sigh yay still murmushi yake yace "bazai yi yawa ba akwae kuWin Baby so don't worry" yamutsa fuska tayi tace to in suka ?are fa har saida yayi yar dariya ganin ta?i ta girma har yanzu tana behaving kamar da yarintarta duk da yasan yanzun ma ba wani girma tayi ba tunda yanzu take 20yrs, yana yar dariya yace mata bazasu ?are ba saboda yana dasu da yawa akwae Dollars ya tara cike da tsokana yayi Maganar ta zaro ido ya Wage mata gira,

murmushi tay tace "baka tsoron insa ai kidnapping Winka kana faWi man ka tara Dollars" dariya yay har ha?oranshi suka bayyana yace ai tuntuni ta riga tayi kidnapping Win Heart Winshi yanzu ko duka kuWin dake gareshi tace ya bata zai tattara ya bata, wani kallo tayi mashi tace is he serious ya jinjina mata kai yace amman zai fidda na aikin gidan da za'ai don kar aga yayi magana biyu sai kuma wanda zai ciyar dasu kafin ya sake tara wasu kada Allah ya kama shi ya barsu da yunwa, wani irin kallon ?auna ta shiga bin shi da shi shima kallon nata yake idanu a Wan lumshe cikin sanyin murya ta furta mashi "Thank you for loving me unconditionally Hubby. You have shown me what true love is, and I am forever grateful for that. I couldn't imagine my life without you" tana gama Maganar kwalla suka zubo mata sharrr, lumshe ido yay tare da Wan murmushi yasa yatsa saman screen Win yana yin alamar goge mata ?wallan hakan yasa ta yi yar dariya, Godiya ta shiga yi mashi sosae da Addu'o'i a hankali yake amsa mata daga baya sukai sallama cike da nuna ?auna, a ranar haWaWWun abinciccika suka haWa mashi ita da mai aikin su da daddare kuwa duk da halin da take ciki saida ta tabbatar tayi mashi godiya ta hanyar gigitashi ta yadda har saida suka zubda hawaye su duka..........

101

~_*
'=؋?BOSS LADIES WRITERS=؋?
'*_~



.......Ranar Alhamis Hajiya ta kira kawu Mani na Daura ta tambaye shi gobe Juma'a zai shigo Katsina ne yace mata a'a amman in tanason ganin shi sai yazo tace mashi in bazata takura shi ba tana son ganin shi yace to ba damuwa zai shigo.

Washe gari kafin ayi salla ya iso Ya yi shigar manyan kaya ya fito a dattijo mai kamala anan gidan yayi sallar Juma'a suka ci Abinci tare da Hajiya a dining, bayan sun gama cin abincin ne suka dawo falo yana zaune a kujerar dake gefen ta Hajiya yace "Hajjaju gani na amsa kira Allah yasa na lafiya ne" tana murmushi ta bashi amsa da lafiya lou sai alkhairi ya furta Alhamdulillah shi suke fata a koda yaushe, Maganar zuwa neman auren Tk tayi mashi tace tana son ya shige gaba tasa anyi mata bincike akan gidansu yarinyar an tabbatar mata da basu da matsala shi mahaifin nata asali mutumin Gombe ne aikin custom ya kawo shi Katsina daga nan zaman ya Wore don yanzu har ma yayi retired to tana son ya tuntube shi kan su bada lokacin da za'aje neman auren, jinjina kai yayi yace to ba matsala a yau ma kafin ya tafi sai ya tuntube shin a bashi Address ko kuma lambar wayar shi tace to dama ta amshi lambar a wurin tukur Win, bashi lambar Baban Asma'un tayi yayi saving ya Wago yana murmushi yace ashe sun kusa shan bikin Wan gidan Hajiya itama murmushin take tace aikuwa yay fatan Allah ya sanya alkhairi ya nuna masu,

bayan ta amsa da Amin tace "Kai ma in kana son ?ara Auren akwae mata a ?asa zan baka" waro ido yay ya Wan buWa baki sai kuma yayi dariya yace yasan ai wasa take, Wan ta6e baki tayi tace dama ana wasa da Maganar aure, yana dariya ya tambayeta wacece matar, tace "Kana so ne?"

"To Hajjaju taya zansan ko ina so ba tare dana ganta ba" yana ta dariya yay Maganar,

"To ai in kai baka santa ba ni na santa kuma na yaba da ita ne shiyasa nayi maka maganarta tuntuni ma nake kwaWayin wani cikin Family ya aureta saboda kyawun halinta Allah bai nufa nayi ma wani maganarta ba sai kai da nayi mawa yanzu",

"To ai Hajjaju kyau dai in ganta" still dariyar yake itama haka tace "ai ina ganin ma kasan wacece Kakar matan su Haisam da Nameer ce, ba wani tsufa tayi ba kawai don anyi mata auren wuri ne da yake asalin Fulanin daji ce in ba don haka ba bazata aje ma jikoki kamar su ba don ina ganin ka girmeta kaga kai baka dade daka samu Yan jikokin ba" shiru yay yana ?o?arin tuna ko yasanta can yace gaskiya ya kasa ganeta koda ya santa Hajiyar tace bari taga ai kaman akwai hotonta da akayi da bikin su Nameer anan falonta kuma shima ranar yana nan dashi akai hotunan, hoton gwaggo da tayi tare da Mino a ranar ta buWo mashi ta mi?a mashi ya amsa ya bi hoton da kallo yana Wan murmushi can ya Wago ya tambayi Hajiyar bata da aure ne tace inda tana dashi zatayi mashi tayin auren nata ne ya sake tambayar abunda ya rabata da mijin nata ta faWi mashi aurenta biyu na farko na dole ne akai mata da yake ta taso marainiya shine kawunta da ya ri?eta ya aura mata abokin shi to hardai zaman ya ?are basu haihu ba bayan ta dawo wurin kawun nata Daura tana zuwa tallan nono a kasuwar mashi Allah ya haWa ta da mijinta na biyu data aura shine suka haifi yara biyu kafin ya rasu sanadiyyar haWarin mota tun daga nan kuma bata ?ara yin aure ba kusan shekara ashirin da biyar duk da tana da masu son auren nata itace bata so cikin dangin mijinta daya rasu wani ya samo mata aikin asibiti tana yi farko ma a gidan shi ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login