Showing 426001 words to 429000 words out of 513411 words

Chapter 143 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16698

Allah ?ara masu fahimtar juna ya zaunar dasu lafiya yasa mutu ka raba Fatuu ce ta amsa da Amin,

"Yanzu ke ya za'ai da karatun ki gashi ko Ssce ba kiyi ba" Fatuu ta tambaya idonta akan Mino, shiru ta Wan yi tana murmushi kafin tace Nameer Win yace zata yi jarabawar bayan an yi, tambayarta Fatuu tayi bayan an yi mi tayi shiru tana bin ta da ido ta ?ara ce mata bayan an yi wai me zata yi jarabawar, shiru tayi tana kikkafta idanu gwaggo dai murmushi kawai take don ta fahimci mi Fatun ke so ta faWa, ganin ta kafe sai ta faWi mata bayan an yi mi zata yi jarabawar yasa ta tura baki tana yamutsa baki tace "Wayyo Adda Fatuu ba kin gane ba" girgiza mata kai tayi alamar bata gane ba tay shiru can ta saci kallon gwaggo ganin haka yasa Gwaggon ta juyar da fuskarta, juyawa tay ta kalli Fatuu data kafeta da ido ?asa ?asa da murya ta furta "Auren" tana faWin haka ta tashi da gudu ta bar Wakin duk suka saka dariya gwaggo tace ina ruwan Mino sarkin kunya.

Washe gari da safe su Aunty suka tafi a ranar da daddare Haisam da Fanan suka iso, Washe gari Litinin Jidderh ta iso daga Dubai a ranar da yamma Haisam ya taho Katsina don gaba Waya a ?agare yake da ganin Baby Fatuu Win sa, ko gaya mata zai zo bai yi ba saidai ta gan shi yazo sosae taji daWi amman duk da haka saida tayi mashi shagwabar miyasa bai faWi mata zai zo nan ba yace yana son yi mata surprise ne su twins ma sun yi murnar ganin Daddyn su, a daren ranar sun nuna yadda sukai kewar juna sosae, Washe gari aka fara program na Laila a Abuja don su zasu yi abubuwa bayan Dinner da walima da za'ayi in aka kawo Mino su zasu yi Ethiopian Night da Arabian, a ranar yan Adamawa suka iso babbar mota guda nan fa gidan gwaggo ya cika kamar yadda Yaya sukai da innar su Altine duk sun kwaso yan matan gidan a nufin su na suma su samu mazaje a dangin su Haisam, zuwa dare gidan har ya fara fita hayyacinshi don ma Yadikko na Wan tsawatar ma yaran, har bayan isha Fatuu na gidan anata hira su twins tun bayan da aka cika gidan suka fara koke koke sun ?i yarda a Wauke su hakan yasa ta kai su wurin Hajiya don yanzu suna yarda da ita kuma Haisam na nan, suna hirar ne ake tambayar Fatuu inda gidan su yake ta faWi masu ba nisa da an fita ne nan wasu suka ce wai zasu bita suga gidan sai su kwana kan ta basu amsa Gwaggo tace ai Mijinta na nan hakan ba ?aramin daWi yayi mata ba don ?arshe tasan mi zai biyo baya in suka bitan, sai wurin ?arfe goma saura ta baro gidan ta dawo gidan su lokacin data je part Win Hajiya ba kowa a cikin parlon hakan yasa ta wuce Bedroom Winta, da sallama ta shiga Hajiyar har ta kwanta amman bata yi bacci ba jin sallamarta yasa ta Wago Fatun ta shiga, nuna mata bakin gado tayi alamar ta zauna, bayan ta zauna ta gaidata ta amsa kafin tace ai tayi tunanin ta dawo tuni gajiya tasa bata shigo ba Fatun tace a'a yan Adamawa suka zo ta tsaya yin hira dasu ne, tambayar yaushe suka iso tayi ta bata amsa da tun Wazun zuwan nasu ne ma yasa ta aiko dasu twins don suna ta kuka sunga mutane tace "Allah sarki, sun zo lafiya ko?" amsa mata tayi da eh lafiya lou tace to Ma sha Allah, shiru suka Wan yi kafin Hajiyar tace mata su twins Win na wurin babansu ya tafi dasu can part Win nasu ta amsa da to, mi?ewa tay tayi mata sallama har zata juya Hajiya ta dakatar da ita da faWin to maimakon ta taho da wasu nan su kwana tunda ga Wakuna nan ko wanda suka zo Win basu da yawa ne ta bata amsa da suna da yawa tace to ai data rago wasu don su samu walwala gidan, shiru tayi bata ce komai ba a ranta tace ita yaushe zata rakito su suzo suyi ba daidai ba kawai sai gani tayi Hajiyar ta kai hannu gefen pillow ta Waukko wayarta, kiran layin gwaggo tayi bayan ta Waga ta amsa gaisuwar da take mata kafin tace hidima ta fara kankama Gwaggon na murmushi tace eh wllh Hajiyar tayi fatan Allah yasa taron ya tashi lafiya da sauri gwaggo ta amsa da Amin, ce mata tayi Fateema tace waWanda suka zo da Wan yawa to ta turo wasu sai su kwana anan ta amsa mata da to don ba damar ta musa mata, bayan sun gama wayar tace ma Fatuu da tayi tsaye sototo shikenan taje ta ?ara yi mata sallama ta juya ta tafi, sam Gwaggo bata so hakan ba duk da za'a samu sau?in cukowar da aka yi amman tana fargabar tura wasu su kwana can, ?arshe Yadikko ta kira gefe ta sanar mata ta bada shawarar a tura su Yaya da Mero sai innar su Altine sai kuma in za'a ?ara wasu amman su tana ganin lafiya lou bazasu yi ba daidai ba tunda sunje Abuja sun san wasu abubuwan na yan gayu gwaggo ta Wauki sha'awararta, bayan anyi masu magana gwaggo taja Mero gefe don tana da natsuwa ta ro?e ta kan kada ta bari ayi ma Hajiyar ba daidai ba tace to suka tafi tare da Gwaggon ta raka su. Ranar Alhamis Mino tayi Friend's Eve anan part Win su Fatuu akayi decoration mai kyau a cikin harabar part d'in harda kujeru, cikin kuWin da Nameer ya turo mata ta ba Aunty mareeya aka yo abubuwan ci da sha harda wanda zata raba, ba laifi kuma ?awayenta yan makarantar bokon su da islamiyya da na nan cikin unguwa duk sun zo an ci an sha anyi rawa anyi nishaWi sosae, a ranar bayan Magrib iyayen su maza harda Baffan su suka iso a gidan Hajiya Wakin Tk aka sauke su shi kuma ya koma Wakin Kawu Amadu, yan'uwan su Hajiya mata na nan Katsina da Daura duk sun wuce Abuja mazan kuma sun tsaya Waurin aure yan Daura ma sai gobe da safe zasu taho nan Katsina har angwayen da dangin su duk sai gobe in Allah ya kaimu zasu taho, da daddare Hajiya ta kira gwaggo take sanar da ita game da Waukar Amarya ance mutum biyar ake so su bada don a jirgi za'a tafi da ita tunda tafiyar bata kusa bace sosae hakan yayi ma gwaggo daWi Hajiya tace da fatan ba'ai masu ba daidai ba da sauri gwaggo tace a'a wllh hakan yayi ai hidiman da yawa hakan ma ba ?aramin ?okari akai ba, Maganar sauran kayan Wakin Minon da akwatunan lefenta gwaggo tayi ma Hajiyar,

"Wane kayan Waki kuma suka rage banda uwayen kayan da kuka takura kai kuka yi mata, ai dana san haka zaku yi mata kaya da bazan bari ba to bansan irin kayan da akai mata ba sai da akai kai su ake man magana abu duk ba an zama Waya ba sai a kama a matsa ma kai haka" da faWa faWa take Maganar Gwaggo na Wan murmushi ta bata ha?uri tace ba takura ma kai akai ba an samu gudunmawa ne sosae Hajiyar tace "haka dai kika ce tunda ba sanin yadda akai akayi mata kayan nayi ba, yanzu su kayan da suka ragen su minene?" da sauri Gwaggon tace "dama kayan adon Waki ne da zasu iya fashewa sai akwatunan sai kuma kayan gara",

fuska a tur6une Hajiyar tace "dawa yace ayi mata wata gara?" shiru gwaggon tayi Hajiyar tace to ba wata garar da za'a Wauka zata yi Magana yanzu da Senator kan sauran kayan amman kada a sake a kai wasu kayan abinci da sunan gara in kuma ba'a ji Maganarta ba to rai kuwa zai 6aci, Gwaggo na murmushi tace in sha Allahu baza'a kai ba ta bata ha?uri Hajiyar tace ta saurareta yanzu zata yi Magana game da kayan zata kirata cike da girmamawa tace to, bada jimawa ba sai gashi ta sake kiranta ta sanar mata goben in Allah ya kaimu kafin a Waura auren za'a turo Mota da zata kwashe sauran kayan in ma akwae wanda zasu bi Motar lafiya lau su wanda zasu tafi ta jirgin sai su fidda su zuwa da safe zata ?ara kira su yi magana, Sosae Gwaggo tayi mata godiya da Addu'oi kafin suyi sallama saida ta jaddada mata kan kada a sake a saka kayan garar nan suyi amfani da abun su Gwaggo na murmushi tace in sha Allah baza'a saka dasu ba suka yi sallama, bayan sun gama wayar dama Gwaggon ware kanta tayi da suna wayar ta shiga tunanin to suwa za'a bada su tafi ta jirgin bata son wani yaga an yi mashi ba daidai ba, tunanin kiran Fatuu suyi shawara tayi dama tana gidan, bayan tazo ne tayi mata bayanin da Hajiya tay game da Waukar Minon Fatun tace "ni hakan ma wllh yayi man daWi dama ji yadda suka kwaso uban mutane kuma nan nufin su duk gaba Waya za'a dasu kai Amaryar, kawai mutum biyar Win asa Aunty mareeya, Aunty Feenah sai ke sai kuma babbar ?awar Mino sai cikon ta biyar Win asa...." shiru tay tana tunanin wadda za'a sa ta tambayi Gwaggo ko hada Yadikko za'a tace mata a'a ita da take Uwar Amarya tace to wa take ganin za'a sa na biyar Win gwaggon tace "sai ke ko, ai baki sa kan ki ba" Fatun tace shikenan hakan yayi da yanayin yar damuwa Gwaggo tace amman hakan baza'ai ma abun wata fahimta ba ace ba dangin Baffan su da kuma Mahaifiyarta Fatuu tace to su kawai sai a saka su a Motar da aka ce suyi gaba Gwaggon tayi Wan shiru kafin tace ita bata son abunda zai ja rashin fahimta aga tayi ba daidai ba bari dai a kira Yadikko a faWi mata aji mi zata ce, bayan an kira ta faWi mata hannu ta kai ta rufe baki kafin ta cire tace mi zai ja a Waura yan Adamawa a jirgi ai abun kallo da magana zasu ja gara ayi yadda Fatuu tace ala bashshi su Yaya da Mero da innarta wato Kakar Mino sai Yayarta hansai su sai a Waura su a Motar Gwaggo tace tana ganin hakan lafiya lou tace eh in ma wani yayi tsegumi kan hakan sai ace basu da abubuwan da ake bu?ata na yin tafiyar dasu a jirgi, hakan da tace yayi ma Gwaggo akan wannan matsayar suka tsaya, sai wurin ?arfe sha Waya da rabi Fatuu ta koma gida direct part Winta ta wuce ba kowa a parlon ta wuce Bedroom, lokacin data tura ?opar ta shiga a saman gado ta hango haisam yayi shigar bacci haka su twins ma ya saka masu kayan baccinsu da alama ma har wanka yayi masu Abie na a saman ?irjin shi yana bacci Grandpa kuma na a ta gefen shi ya rungumo shi jikinshi da hannun shi guda gaba Wayan su bacci suke yadda sukai kwanciyar abun gwanin burgewa, ta Wan Wauki lokaci tana ta kallonsu tana sakin murmushi kafin ta nufi hanyar laudary, after some minutes ta fito Waure da towel da ?aramin towel tana goge jikinta kanta yasha kitso da Mero tayi mata Wazun, press ta nufa ta fiddo kayan baccin da zata saka Nursing pajamas, bayan ta gama sawa gaban mirror ta nufa tana kallon kitson da aka mata yar yar sosae taga yayi mata kyau ko don bata saba yi bane, mai da take shafawa da daddare ta shafa harda na tafin hannu da yatsu sannan ta goga roll-on bayan ta gama ta feffeshe jikinta da turarurruka masu sanyin ?amshi, wurin gadon ta nufa saida ta gyara ma twins nasu gadon kafin ta kai hannu a hankali don kada ta tada Haisam ta Wauko Abie ta kai shi saman gadon shi, tana ?o?arin daukar Grandpa Haisam Win ya buWe ido slowly suka sauka kanta ta sakar mashi murmushi tare da kashe mashi ido shima yay mata murmushin, shima Adam gadon shi ta kai shi ta juyo tana ce ma Haisam sun ci Abinci ne taga har ta kwantar dasu ba wanda ya farka ya lumshe mata ido kafin a hankali yace ya basu kafin suyi bacci yana gama Maganar ta faWa jikin shi tana faWin thank you Daddy wai a madadin su twins Win ya ?ara faWaWa murmushin shi, bin juna sukai da kallo kowa fuskarshi da annuri can yace yadda ta kwantan baza tayi hurting kan ta ba tace ai bata danne cikin sosae ba ya lumshe ido, tambayarta yay ya hidima tace anata yi gaba Waya a gajiye take don ma Gwaggo na hanata aiki sosae ya jinjina kai kafin ya kai hannu ya fara shafa kitsonta ya furta yayi kyau ta furta thanks tare da lumshe mashi ido irin yadda yake, yana Waya daga cikin abunda take so tattare dashi kenan duk in kayi abunda ke bu?atar yabawa sai ya ya6a sa6anin da yawan wasu mazajen basu iya yaba ma matan su in suka yi kwalliya ko wani ado wasu har sai matan sun tanka sun ce wai baka ga nayi abu kaza ba sannan in an ci sa'a yace yayi kyau wani kuwa saidai yace shi bai ma lura ba irin hakan kaman cin fuska ne ace kana tare da mace a wuri guda amman tayi abu kace wai baka lura ba shiyasa da yawan matan basu yin adon akai akai tunda wanda suke yi domin su basu yabawa sai waWanda ya zamar ma jiki ne sun saba suke cigaba da yi koda mazan basu yabawa, Maza yakamata su gyara yaba kwalliyar mace nasa taji daWi ta ?ara ?aimi wurin yi akai akai sannan yana ?ara soyayya don ita mace abu kaWan kesa a siye zuciyarta, sauketa yay daga jikin shi yace mata yana zuwa ta Waga mashi kai, toilet ya nufa yana shiga wayar Fatuu ta fara ringing har saida gabanta ya Wan faWi ta raya wake kiranta a wannan lokacin sha biyu har ta wuce, saukkowa tayi ta nufi gaban dressing mirror inda wayar take har lokacin ringing take ta kai hannu ta Waukko tana duba mai kiran ta saki murmushi ganin Fauziyya ce,

"?awata Amarya ko kun iso ne?" ta fada bayan ta Waga daga can Wayan bangaren Fauzy ta bata amsa da eh yanzun nan suka sauka Abuja, cikin nuna farinciki Fatuu tayi mata anzo lafiya ta amsa ta sake tambayar Nasarawa zasu wuce tace mata a'a gidan su na Abuja zasu tsaya don gobe yana son zuwa Waurin aure dasu Daddyn Haisam Fatun tace suma goben zasu haWu kenan in suka kawo amarya harda cewa ta ?agara taga yadda ta koma Yaya Sameer ya iya kiwo Fauzyn tay yar dariya mai sauti daga baya sukai sallama, aje wayar tayi ta juya zata koma gado lokacin Haisam ya buWe ?opar laundry ya fito ta juya ta nufe shi suna haWuwa ya rungumeta tana kallon fuskar shi da murmushi ta faWi mashi Fauzy ce ta kirata ta sanar mata sun sauka Abuja yanzu ya jinjina kai kafin yace sun yi waya da Sameer kafin su taho, Waukarta yay ya nufi gado da ita tana ta dariya tana faWin wai sai yaushe zai fara jin nauyin ta yay murmushi kawai, bayan ya kwantar da ita mikewa yay ya kunna lamp ta side Win da yake kafin ya nufi wurin Switch ya kashe hasken Wakin ya dawo gadon ya fara mata tausa cikin salon ?auna tana ta lumshe ido tare da yaba abunda yake matan sun Wan Wauki lokaci yana mata massage Win kafin ya fara canza salo tana ganin haka itama ta fara bashi nata salon daga haka suka lula wata duniya da ma'aurata ke zuwa.

FRIDAY

Alhamdulillah Allah ya kawo mu ranar Waurin aure, ana tashi aka shiga yin hidima ba kama hannun yaro, tunda safe jirgin yan Waurin aure ya sauka daga nan gidan su na G.R.A suka wuce kafin lokacin Waura auren yayi, suna isa gidan ango Nameer ya kira amaryar tashi ya sanar mata gasu sun iso yana son yaga fuskar kyakkyawar amaryarshi ta sanar mashi tana gidan Hajiya part Win su Adda Fatuu yace Ok gashi nan zuwa, yan Abuja basu daWe da zuwa ba suma 6angaren angon Laila convoy Win su ya iso daga Kano, jerin dan?ara dan?aran motoci ne masu numfarfashi tare da na security a gaba da baya da yake wanda zata auran wato bashir Wan sanannan mai kuWi ne a Nigeria, a Vip na haWadWan hotel Hillside Royal Suites suka sauka kafin lokacin Waura auren yayi, tunda wuri Aunty Mareeya ta taho gidan bikin saida ta biya ta Waukko Feenah kamar yadda sukai da ita, bayan isowarsu aka shiga yin aiki ba kama hannun yaro don ma Abincin wasu ba anan za'ai ba abunda za'ai a nan gidan kaWan ne, ganin yadda Fatuu ke ta kujiba kujiba yasa aka fara mata magana kan ta rin?a hutawa saboda halin da take ciki sai lokacin wasu da yawa suka san da ciki gareta har Haulat da Feenah basu gane ciki gareta ba duk an zata ?ibar da ta ?ara ne yasa ta Wan yi tumbi, wuraren ?arfe sha Waya Hajiya ta kira Gwaggo tace a fiddo da sauran kayan Minon ga wanda zai Wauka nan yazo Gwaggo tace to ta sanar da ita akwae wanda zasu bisun sannan akwatunan na nan part Win su Fatuu aka maido su bari tayi mata magana sai tazo a fiddo su Hajiyar tace to ayi ma mutanen magana su fito kar a 6ata lokaci don tafiyar bata kusa bace, suna gama wayar tayi ma su Yaya da sauran wanda Yadikko tace aje dasu magana dama tun jiya ta sanar masu zasu tafi da safe, zo kaga rawar jiki wurin Yaya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login