Showing 498001 words to 501000 words out of 513411 words

Chapter 167 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16816

sani ba yana amfani da hakan ne wurin sanin size Winta saboda in zai yi mata lefe, saida ya cika Shopping cart Win taff da kaya sannan suka nufi wurin biya aka saka masu kayan a ledoji bayan an saka a Mota suka tafi.

Kamar yadda Na'eem yace wani ?arshen satin na zagayowa suka shirya zuwa Yola da Haisam, ranar asabar da safe suka bi jirgi zuwa Yola bayan sun isa aka tura Mota ta Wauke su zuwa garin su Fatuu, bayan sun isa sun samu kyakkyawar tarba daga mutan gidan aka sauke su a part Win su Yadikko nan aka shiga zuwa gaishe da su kan kace mi an jere masu kwanonin abinci iri iri koda Yadikko tayi masu Maganar cin abinci cewa sukai a ?oshe suke Baffa dake zaune yana murmushi yace duk da haka yakamata su ci tunda tafiya suka yo, ba wani mai yawa suka ci ba saidai sun sha fura ba laifi, bayan sun gama ne Haisam ya gabatar masu da Na'eem matsayin shine mai son auren Aysha in ta gama School, dama an riga an sanar masu game da zuwansu, sosae suka nuna farinciki da Addu'ar Allah ya sanya alkhairi bayan sun amsa Haisam ya sake cewa yana son a faWi mashi lokacin da zasu turo a saka rana Baffa na murmushi cikin Maganar shi mai tattare da natsuwa yace ai tunda ga shi Haisam Win shima matsayin Mahaifi yake wurin Aysha don haka a nemi aurenta a wurinshi duk yadda ya yanke yayi lafiya lou tunda ba abu bane na kusa kada aita wahalar yin zarya, hakan ba ?aramin daWi yayi ma Na'eem ba shima Haisam yaji daWin yadda ya girmamashi yay mashi godiya da Addu'ar Allah ya ?ara girma da lafiya yana murmushi ya amsa shima yay mashi godiyar abubuwan alkhairi da ake ta masu da Addu'ar Allah ya ?ara girma da arzuki duk suka amsa da Amin, shiru falon ya Wan yi kafin Baffan yace masu bari ya kai su bangaren shi sai su huta Haisam yace ai ba daWewa zasu yi ba zasu koma Yola anjima zasu koma Abuja Baffan yace amman zasu kai azahar ko yana son bayan an gama sallar azahar lokacin duk yan uwanshi sun haWu sai su gaisa dasu yace to, bangarenshi ya tafi dasu don su hutan kafin ayi sallar, bayan gama yin sallar azahar a ?opar gida a fadar dake a cikin soro inda arWo ke zama kafin ya rasu wadda yanzu Baffa ne ke zama don shine arWon suka shiga harda sauran yan'uwan nashi, bayan sun gaggaisa Baffa ya gabatar masu da Na'eem, duk sun nuna farinciki kan al'amarin tare da Addu'ar Allah ya sanya alkhairi, da fulatanci Baffa yay masu bayanin lokacin da Aysha zata gama Makaranta yake son ayi auren ya kuma bada izinin a nemi auren a wurin shi mijin inna wuro kada zaryar tayi yawa, gaba Waya dai sun nuna hakan yayi Baban altine harda cewa ai Haisam Win yanzu shima na gida ne kuma ga abun alkhairi da yake ta kawo masu, bayan sun gama gaisuwar kuWi masu yawa Na'eem ya aje masu yace suyi amfani nan fa suka shiga yin godiya Haisam ma ya ?ara aje masu wasu bandir bandir Win zo kaga godiya da addu'o'i, bayan sun fito bangaren su Baffa suka koma yasa Yadikko ta kaisu su gaisa dasu Yaya, cikin faram faram Yaya ta tarbesu akayi masu shimfiWa suka zauna Yadikko taje tayo ma su Mairo Magana duk suka zo nan Wakin aka shiga gaisawa dasu da tambayar Haisam yadda su Fatuu suke fuska a sake yake amsa masu daga baya ya gabatar masu da Na'eem, duk sun nuna farincikin su suma sunyi Addu'ar Allah ya sanya alkhairi ya kuma nuna masu, nan ma saida suka aje masu kuWi masu yawa kafin su taso, basu daWe ba bayan sun koma falon Yadikko sukai masu sallama suma saida suka aje masu kuWi Baffa yace don Allah su bar shi kada hidiman tayi yawa wanda suka bada sun isa Yadikko tace mashi ko can wurin su Yaya ma saida suka bada masu yawa, duk yadda sukai dasu kan su barshi basu Wauka ba dole sukai masu godiya, har bakin mota duk aka rakosu su suka yi bankwana dasu kafin suka tafi, a kan hanya ne Na'eem ke yabon Baffan su Fatuu yace ya burge shi wllh sosae kai kace ba mutumin ruga ba yana da natsuwa da wayewa in ba don haka ba bazai sake masu ba matsayin su na surukai Haisam yay murmushi yace haka yake ya fita daban a cikin su. Gab da sallar Magrib suka dawo Abuja sosae Na'eem yayi ma Haisam godiya da zasu rabu, saboda tafiyar da su Haisam Win sukai yasa wannan Weekend Win Fatuu ce tazo Abuja, da daddare bayan sun kwanta ne Haisam ke ce mata mi zai hana Baffansu ya baro ?auye ya dawo ko Katsina tunda gasu Gwaggo sai ya siya mashi gida su zauna, itama Fatuu ta nuna tana son hakan tace zata tuntu6eshi kan hakan, Washe gari da safe ta kira Baffan bayan sun gaisa ne take mashi Maganar, farko shiru yayi kafin yace mata zai so hakan saidai barin ruga yanzu ba abu bane mai yuwuwa a wurinshi don arWo ya bar mashi amanar gidan yace kada ya bari kan iyalin ya tarwatse yanzu in yace ya tafi yasan za'a iya samun 6araka kuma shi kan shi yafi sabawa da nan tunda anan ya taso yace taba Haisam ha?uri kuma tayi mashi godiya kan kudirin nashi tace to, koda ta sanar ma Haisam Win ya fahimci Baffan ya nuna mata bakomai, da yamma ta shirya komawa Zaria ta jirgi Esha ta saka rigimar sai ta bita Fanan ta shiga rarrashinta tace ta bari in akayi hutun School sai suje mata hutu kamar yadda suke yi sannan ta ha?ura suka yi mata rakiya gaba Wayansu harda Haisam Airport tabi charter flight zuwa Kaduna daga can driver zai wuce da ita Zaria.

Cikin sa'a Mino ta fara yin bautar ?asarta a Asibiti, wata biyu da farawa kwatsam sai ga ciki ta samu, zo kuga farinciki a wurin Mino duk yadda take da kunya saida ta kasa 6oye murnarta haka kowa ma yayi farincikin samun cikin karma dai Fatuu sosae tayi murnar samun cikin na Mino, ta bangaren Nameer shima yayi farinciki don duk yadda yake nuna bai damu ba yana son yaga Wanshi na cikin shi, bayan samun cikin sai kuma ta fara yin laulayi sosae ta yadda har saida ta daina zuwa Asibitin da take bautar ?asan nata ?arshe ma saida ta kai Nameer ya maidata wurin Mom Win su don bata iya cin komai duk abunda kuma ta samu ta Wan ci sai ta amayar dashi tun lokacin ta gane ciki ba wasa bane, saida tayi wata biyu a Villa kafin ta dawo gidanta lokacin cikin ya kai wata ukku kuma ba laifi ta Wan rage yawan laulayin amman bautar ?asan da take yi saidai aka tsaida shi daga baya tayi, cikin na wata biyar akayi bikin Aysha da Na'eem anan Abuja, a gidansu Haisam akayi hidiman bikin don Haisam su Baffa suka amince mawa ya bada aurenta, yan Katsina da yan Adamawa duk nan suka zo ranar Waurin auren ya kama Juma'a kafin lokacin yin salla su Baffa suka iso, ana gama salla aka Waura masu auren akan sadaki naira dubu Wari ukku sai fatan Allah ya sanya alkhairi ya basu zuri'a Wayyiba, ana gama sallar Magrib jerin motoci suka zo Waukar yan kai Amarya zuwa gidanta dake a Garki, ba'a gida Waya zasu zauna da kishiyarta ba ita tana a gidajen manyan ma'aikatan bankin da yake aiki wato CBN, gidan da aka kai Ayshar babban Flat ne mai kyau, ba laifi anyi mata kaya daidai gwargwado wanda da yawa Haisam ne yayi mata su Fatuu ma da Kamalu dasu Gwaggo sun taka rawa wurin yin kayan Wakin, shi kanshi angon Na'eem ya siya wasu abubuwan na gidan kafin a kawota kamar labulaye dasu carpets sannan part Win shi ya zuba komai, tun kafin ayi bikin Fatuu ta fahimtar da ita komai game da aure gudun kada a maimaita na Mino sai gashi a yadda ta fahimta Ayshar tasan miye auren wanda bata yi mamakin hakan ba don tafi Mino wayewar kai lokacin da aka yi mata aure, an kai amarya Wakinta lafiya tana ta kuka aka barota sai fatan Allah ya basu lafiya.


Ana gama yin bikin Aysha su Haisam suka fara shirye shiryen komawa gidanshi na Asokoro, ?ara sawa a gyara gidan Haisam yayi duk da sabo ne ba'a ta6a shigar shi ba amman za'a ?ara ?awata shi, Jidderh na jin zancen shirin komawar tasu ta ro?i Haisam kan ya bata kwangilar shirya gidan in an gama gyaran sai gashi ya bata aikuwa sosae taji daWi dama yanzu ta ?ware ta fannin shirya wuri har ta buWe Company Hajiya Maryam ma na taimaka mata wurin gudanar da kamfanin harda hannun jari ta zuba kuma da yake ita babbar yar kasuwa ce tana yo mata Order Win kaya daga wasu ?asashen, kafin tayi Odar kayan gidan saida ta fara zuwa ta gano shi don bata ta6a zuwa ba ta dai san da Haisam nada gida, bayan ta gano gidan ta tuntu6i Fatuu da Fanan don taji irin kalar kayan Wakin da suke so duk suka faWi mata sannan ta fara ?o?arin yo Order Win kayan da taimakon Hajiya Maryam. Saida aka Wauki wata ukku wurin ?ara gyara gidan da kuma shirya shi kafin aka gama, ranar da zasu koma ya kama Friday bayan an gama sallar Juma'a akai convoy harda President da Mom da sauran yan uwa da abokan arzu?i aka raka su lokacin Fatuu na kan Hanyar dawowa daga Zaria, lokacin da suka iso tun daga bakin gate Win gidan abun kallo ya fara, dakakken electric gate ne wanda ake amfani da remote wurin buWe shi idan kuma ba wuta akwai inda ake dannawa sannan a zuge shi saidai sai mutum ya iya sannan zai iya buWewa haka saman katangar gidan da aka tsarata nan ma zagaye take da electric fence, daga bakin gate din akwae Security guda ukku ru?e da bindigu, bayan an buWe masu gate Win duk suka kutsa Motocin cikin harabar gidan wadda take mai girman gaske, to Salamu alaikum mun shigo daular su Fatuu, tsaye nan ina kallon ?asan harabar gidan wadda na kasa gane glass ne a ?asanta ko kuwa wani kalar tiles ne da ban sani ba don gaba Waya harabar wani irin sal?i take kai kace in Mota ta taka ?asan zai fashe saidai abun mamaki ko gezo bata yi ba, bayan duk an parker motocin wasu a parking space Win gidan guda biyu dake a 6angaren hagu da dama da zasu Wauki motoci shidda shidda wasu kuma a gaban dan?areren ginin gidan duk aka parker su, akwae shukokin fulawoyi masu ban sha'awa su kansu an tsara su ta yadda sun ?ara ?awata farfajiyar gidan, bayan duk an firfito harabar aka fara tsayawa ana kallo kafin aka nufi shiga cikin ginin wanda yake ?aton ginin bene ne, koda nayi arba da ?opar shiga shiru nayi na shiga tunanin ta yadda za'a buWeta ban gama tunanin ba naga Haisam ya nufi ?opar a wani Wan rami mai glass ya Waura saman babban yatsan shi sai gashi ta buWe ashe ?opar mai fingerprint sensor ce, ganin yadda ya buWe yasa Hajiya dake bayan shi tace yanzu wannan in mutum na gaggawa sai ya tsaya yan ta6e ta6e kuma su yara in tsawon su bai kai ba taya zasu ta6a har ta buWe duk akai murmushi Haisam ya bata amsa da ana cire fingerprint Win a buWe lafiya lou ko kuma in cajin ?opar ya ?are Hajiyar ta jinjina kai, bayan ?opar ta buWe aka fara shiga ciki, wata yar hanya ce zaka fara shigowa tun anan zaka ji wani ni'imtaccen sanyi ya ratsa sassan jikin ka, saman wurin na Wauke da wata irin babbar fitila mai sar?o?i da suka zubo ni dai har saida na Waura hannuwana a saman kai don sai naga kamar zata faWo man, ta cikin wurin matattakalar bene take ta wani lan?waya daga bangon dake kallon mutum kuma nan ma wata dakakkar ?opa ce ita Haisam ya buWe aka bi bayan shi nima na saka kai, a wani irin haWaWWan falo mai sunan falon masu arziki na tsinci kaina, gaba Waya na ruWe na rasa ma ta ina zan fara, falon nada girma ba laifi gaba daya fentin cikinshi fari ne sai walwali yake haka ?asan shi malale yake da tiles, akwae set na jajayen kujeru royal masu ratsin golden brown haka lallausan carpet Win dake tsakiyan kujerun shima kalar kujerun ne, komai na falon mai daukar hankali ne tun daga kan inda kayan kallo suke da sound systems haka Dining area Win dake a can gefe nan ma abun mutum ya tsaya kallo ne akwae dining table da kujeru suma royal kalar na falon da gani mahaWinsu ne akwae glass door deep freezer wadda marfinta na gilas ne kana hango abubuwan dake a cikinta sannan akwae display Carbinet ta glass mai Wauke da cups da dishes da wasu kayan ?awa dake ta walainiya, sosae wurin ya ?awatu harda flower vases masu Wauke da fulawoyi masu ban sha'awa a jikin bangon wurin daga gefe ?atuwar ?opar shiga Kitchen take, babban Kitchen ne U-shape gaba Waya kayan cikinshi kalar ja da fari ne hatta cabinet Win sama da ?asa katakon fentin ja da fari ne sosae Kitchen Win ya tsaru ya sha tsadaddun kayan amfani kama daga masu amfani da wuta zuwa wanda basu amfani da wuta a cikin shi ?opar store take shima sha?e yake da kayan abinci, a jikin bangon falon ba'a li?a komai ba don irin tsarin bangon ba'a fasa shi sai daga wurin adon gidajen da aka saka kayan kallo ne aka aje manyan hotunan masu gidan dana sauran Family Winsu su Dad da Mom da Hajiya da dai sauran su, daga wurin bangaren cin abinci wato dining area akwae wata matattakalar benen da itama zata kai ka sama wato daga nan falon zaka iya bi ka hau sama ka sauka ta Wayan matattakalar dake a waje ko kuma daga ta wajen ka hawo ka saukko ta cikin falon, daga bangaren dama na falon part Win Fanan yake sai na Fatuu na a bangaren hagu, a kowane part Win nasu akwae madaidaicin falo sai Wakuna guda biyu, a falon Fanan komai na ciki blue ne kama daga lumbutsa lumbutsan kujerun ciki wadda suke na fata wato leather chairs zuwa carpet da labulaye duk suma kalar kujerun ne akwae kayan kallo da kuma kayan ?awata falo harda wani haWaWdan console wato madubin falo mai hade da table Win shi anyi masu design masu ban sha'awa, sosae falon ya haWu ba kamar da fentin cikinshi ya kasance fari sai ya ?ara mashi kyau sosae, a Bedroom Waya gadon ciki italian royal ne shima blue da Wardrobe Winshi bango guda sai side drawers da dressing mirror, a Wayan bedroom Win shima gadon italian ne amman mara hayaniya katakon irin mai sal?i ne komai na cikin shi fari da ratsin ba?i ne, a cikin kowanne Waki akwae toilet kalar na zamani komai na cikinshi fari da silver ne, a cikin toilet Win da Royal bed yake har da laundary room wato wurin yin wanki mai Wauke da injin wanki da kuma cabinet mai marfin glass anan tawul suke da rigunan wanka, in muka koma bangaren Hajiya Fatuu itama kamar yadda bangaren Fanan yake haka nata yake wato falo da kuma Wakuna biyu, a falonta itama leather chairs ne maroon sai dai nata L-shape ne, tun daga kan Carpet da labulayen Wakin suma duk marron ne akwae tabur Win tsakiyar falo wato center table na glass haka daga can ?arshen kujerar akwae wani madaidaici an Waura Wan madaidaicin abun saka fulawa shima kalar maroon cikinshi Wauke da fulawoyi green da ja wanda ya ciza yay kamar maroon sai kuma farare, itama akwae kayan kallo kamar na falon Fanan, a Bedroom Win farko itama italian royal bed ne kalar maroon da sauran mahaWinshi sai dayan Wakin simple modern italian ne wato itama mara hayaniya kamar na Fanan amman nata kalar ruwan toka ne suma sai sal?i suke jikinsu nada sul6i, a kowane Waki akwae toilet itama komai na ciki fari ne da silver sosae aka kashe mashi kuWi ba abunda babu na banWakin masu kuWi da suka amsa sunan masu kuWi harda shower cubicle wato ke6antaccen wurin yin wanka na glass, bayan an gama da ?asan benen sama aka hau saidai Hajiya bata hau ba tace suyo mata Vedio Haisam harda cewa bari ya Wauketa ta watsa mashi harara, Mino ma an hanata hawa don cikinta ya tsufa ya shiga wata na takwas itama a falon ?asa ta zauna tare da Hajiya, saman benen 6angaren Oga Haisam ne akwae Wan babban falo mai Wauke da kujeru leathers kalar ruwan madara suma L-shape ne haka carpet da labulayen duk ruwan madara ne akwae kayan kallo daga inda suke anyi adon gidaje an saka hotuna haka daga gefen kujerar an aje Wan tebur na glass an Waura fitila mai kyau haka a tsakiya ma an aje wani tebur Win, akwae bedroom guda biyu a bangaren dama da hagu, a bangaren dama Bedroom Win Haisam yake yana Wauke da saitin italian bed shima mara hayaniya ruwan madara a ciki akwae laundary room da kuma toilet, Wayan Wakin ake kusa dashi nan kuma Wakin daya danganci aikin Haisam ne duk kayan aikin fasaha ne a ciki, daga Wayan bangaren falon nan ma wasu Wakunan ne Waya nasu Twins ne yana da Wan girma an saka yan gadajen katako guda biyu iri Waya harda drawers Winsu sannan akwai wardrobe Win bango daga can gefe kuma wurin karatu ne aka ware masu akwae Wan babban tebur da kujerunshi guda biyu sai kuma daga gefe yar kanta ce mai Wauke da littattafai harda toilet ke akwae a cikin Wakin, a Wayan Wakin kuma nan ma akwae gado kalar coffe brown da drawers Winshi da madubi sai wardrobe Win bango itama kalar coffe brown

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login