Showing 441001 words to 444000 words out of 513411 words

Chapter 148 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16793

bayan ta gama ta bata magunguna, cigaba da kwatanta mata rayuwar aure Fatun tay "daga yanzu kada ki ?ara gudun mijin ki kinji yar ?anwata hakan ba kyau indai ya nemi hakkin shi kika hana Allah zai yi fushi dake mala'iku kuma su kwana suna tsine maki saidai idan baki lafiya sai ki faWi mashi, ta hakane zaki kama zuciyar shi ya zama kullum kece a ranshi saboda hakane ma kafin auren kika ga ana baki wasu abubuwa kina sha don ki ?ara daraja a wurin shi ne ki kuma haWa da biyayya ai Gwaggo duk ta maki bayani kan hakan, sannan ki dage da yin ado da kuma kwalliya nasan baki da matsala da wannan dama kin iya shafa jambaki da hoda to yanzun ne zasu yi maki amfani kinga dai mijinki tubarkallah ta ko ina yayi irinsu yan mata rububin su suke don haka sai kin dage ki rin?a yi mashi abunda yake so sannan kisan irin kalar shigar da yafi so kina yi mashi...." da sauri tace mata ?ananan kaya yake so ya faWi mata Fatun tace to ta rin?a yawan saka su in yana gida ko kuma in tasan zai dawo amman kamar in tana sanye dasu tayi ba?i maza sai ta Waura after dress amman suma sauran kayan nata kada tace zata jubge su ta rin?a sakawa akai akai tana cin gayu ba kamar ranar Juma'a Minon nata Waga mata kai bayan ta gama yin Maganar a hankali tace to ko ta canza kayan jikinta yanzu tasa wanda yake so Win fatuu tay murmushi tace a'a ta bar rigar tunda bata jin daWi zata fi sakewa tace to, bayan sun gama yin Maganar tace mata ta kwanta ita kuma ta Wauki tray Win kayan ta nufi ?opa, lokacin data fita ba kowa a parlon ta wuce kitchen, wanke kayan da akai amfani dasu tayi tay tunanin tayi masu girki kafin ta tafi, tana cikin aikin girkin Nameer ya shigo tun yana sawo kai ?amshin turarenshi ya karaWe kitchen Win, da alama wanka yayi yana sanye da ?ananun kaya wanda da gani sababbi ne sumar shi tasha gyara sai sal?i take haka sajen shi, daga gefen ta ya tsaya ya aje tray Win kayan Breakfast Win yana murmushi yace "sannu da aiki Yayata ta kaina" wani kallo tay mashi tana murmushi tace na daWin baki ko,

"Amman kinsan ai tun da kika zama Yayata nike girmama ki ko" Wan ta6e baki tay yana dariya yace yanzu ma zai ?ara girmamata tunda ta mashi aiki tay dariya kafin tace ai biya zai yi da sauri yace ta faWi ko nawa ne zai bata in ma baida su zai samo tace bada kuWi zai biya ba al?awari zai yi na bazai ma Mino kishiya ba yana murmushi yace in don wannan ne dama baida wannan ra'ayin itace kaWai matar shi har ya mutu ta Wan harare shi tace ita zai ma daWin baki,

"Ba daWin baki bane am serious mizai sa in ?ara Aure inada Ameenatu, tamkar rainonta zanyi fa lokacin da zan manyanta lokacin zata ?ara cika mace to mi zai burge ni a wurin wata" murmushi Fatuu tay tace wasa ma take mashi ita ai tana da kishiyar ko yace to shi da gaske yake daga Babynshi ya gama tace Allah ya barsu tare ya basu zaman lafiya da zuriya Wayyiba ya amsa da Amin kafin ya tambayi mi zai tayata da shi tace ba komai duk ta cimma aikin ma sauran ?arashe yace Ok tare da yi mata godiya ya juya ya fita, farar shinkafa da miya tayi sai coleslaw tayi farfesun yan ciki saida ta wanke komai data 6ata ta zuba abincin a cikin warmers masu kyau ta kai kan Dinning table, bedroom Win Minon ta nufa bata yi tunanin Nameer na ciki ba saida ta shiga ta ganshi rungume da Minon suna bacci tay murmushi ta wuce inda ta aje purse Winta ta Wauka kafin ta fito, parlor ta dawo ta fiddo wayarta nan taga missed call Win Gwaggo har biyu, sake kiranta tayi bayan ta Waga sun gaisa tace ta kira bata kusa ne Gwaggon tace eh tayi tunanin hakan dama zasu tafi ne taga bata ganta ba suyi sallama saida suka fito Wanta Haisam ke faWi mata tana gidan Mino tace eh tare da tambayar yanzu sun tafi kenan tace mata eh gasu a Mota, fatan Allah ya tsare tay tace sai tazo, kafin suyi sallama ta tambayi ya Minon tana yar dariya tace lafiya lou dama ta?i kwantar da hankalinta ne tana ta koke koke amman yanzu ta kwantar da hankalin Gwaggo na murmushi tace ina ruwan Mino a hankali zata saba sukai sallama tace tayi ma su Yaya da Safnah Allah ya tsare tace to, bayan sun gama wayar tunanin zaman mi zata zauna yi tay hakan yasa ta shiga kiran Haisam bayan ya Waga tace in bai komai yazo ya Wauketa pls yace Ok, after some minutes ya kira yace mata yana a harabar gidan ta mi?e ta nufi hanyar fita, saida ta buWe kopar gaban Motar taga ashe harda su twins yazo da yake Motar tinted ce gaba Waya an yi masu wanka suna sanye da kaya iri Waya suna ganinta Adam ya washe mata baki Abie kuma yay mata Wan murmushi duk suka miko mata hannu suna son ta Waukesu suna faWin Momy, saida ta zauna sannan ta ru?e su gaba Waya ya tashi Motar suka tafi, bayan sun hau hanya take ce mashi ashe su Gwaggo sun tafi ya Waga mata kai tace ta kirata har sau biyu bata kusa da wayar, shiru suka Wanyi can ya tambayeta lafiya gidan Nameer Win tay faffaWan murmushi idonta akan shi tace mashi laifi yayi ne shine aka kaita rarrashi Haisam Win ya Wan buWa ido tare da Wage gira sai kuma yay murmushi ba tare da yace komai ba, suna cikin tafiyar take tambayar shi yaushe zata je Katsina ya bata amsa da Us zasu tafi tace bazata je sallama ba yace in tana so sai taje amman yana son zasu je Adamawa su duba jikin arWo yaji su Dad Winta suna faWi ma Dad Winshi bai lafiya, sosae taji daWi jin zasu je tace mashi eh bai jin daWi yace Ok cikin next week sai suje.

Bayan sallar Azahar su Aunty yan Kano suka dawo an cika su da abubuwan arzu?i Jidderh harda kukan baro Aunty Laila duk tayi sukuku koda ana Maganar Lailar bayan sun dawo sai ta sake saka wani sabon kukan Hajiya na faWin itama ba Auren zata yi ta tafi ba, Bayan sallar La'asar su Hajiya Maryam suka wuce lagos su Hajiya Zainab ma lokacin suka tafi harda Fauzy.

Alhamdulillah Yan Katsina sun isa lafiya sai fatan Allah ya huta gajiya, a ranar bayan sallar isha duk suna zaune a cikin parlon Gwaggo suna yin hirar bikin baka jin komai sai fullanci dake tashi su innarsu Altine sai zuzuta gidan Mino suke suna faWin ai Aljannar duniya aka kaita, suna cikin yin firar Amadu da Kamalu suka shigo jin firar da suke ne yasashi kunna Vedio Win gidan Minon da yayi lokacin da suke zagayawa ya mi?a ma Yadikko ta fara gani, sakin baki tay da tsananin mamaki take kallon Vedio Win tana faWin yanzu anan Minon take aka bata amsa da eh su Altine da basu je ba duk sun zagayeta sun saki baki galala suma suna kallo, ?arshe dai kukan farinciki Yadikko ta saka ta hau gode ma Allah da kuma Gwaggo tana faWin koda tayi aikatau a Abuja bata ta6a tunanin wani nata zai zauna a can ba balle kuma ?arta, inna Mero matar arWo ce tace hada halin kirkinta yaja mata yadda ta ru?e ?a?an kishiyarta da Amana bata zalunce su ba ta Waukesu tamkar nata gashi nan hakan yayi mata rana tunda data zalunce su ba yadda za'ai Gwaggo ta ru?a mata Wiya har itama tayi aure gidan daula su Kakar Minon suka shiga faWin hakane wllh Yaya kuwa duk tabi tasha jinin jikinta sai murmushin ya?e take, suna haka wayar Kamalu ta fara ringing ya kai idon shi kan screen Win yaga ba?uwar lamba saida ya fito waje saboda hayaniya sannan ya Waga tare da yin sallama daga Wayan bangaren zazza?ar muryar mace ta amsa mashi tare da tambayar ya yake ya bata amsa da lafiya lou kafin ya tambayi wacece, farko shiru tayi kamar bazata tanka ba saida ya ?ara tambaya sannan tace kenan data amshi number Win shi tace zata kira yay saving bai yi ba kenan, jin haka yasa ya ganeta da sauri yace tayi ha?uri ya manta ne da yake lokacin jiran shi ake tace Ok kafin ta tambayi ya suka koma yace Alhamdulillah itama ya tambayeta sun koma ne ko suna Abuja tace mashi No sun koma, Wakinsu ya nufa suka cigaba da yin wayar saidai itace ke fara yin magana sannan yayi harda tambayarshi game da karatunshi ya bata amsa da bayan ya gama Secondary acan garin su bai cigaba ba dalilin da yasa yanzu ya dawo nan kenan don ya cigaba har ma ya siya Jamb zai yi tace Ok tare da yi mashi fatan Akhairi yayi mata godiya daga baya tace mashi tana son zasu zama Friends in ba damuwa har saida ya jinjina Maganar a ran shi don baiyi zaton jin hakan daga wurinta ba jin yayi shiru tace ko bazai yi abota da ita ba, da sauri yace a'a zasu yi suka cigaba da yin wayar kafin daga baya sukai sallama ya tashi ya koma shago.

Ranar Juma'a lokacin sati guda da bikinsu Nameer Jirginsu Fatuu ya tashi zuwa Yola, a yadda Haisam ya shirya masu zasu sauka a gidan wani abokin Dad Win shi wanda shima Senator ne mai suna Buba daga nan sai suje garin su Fatun, bayan sun sauka wurin ?arfe goma na safe Driver ne tare da Wan mutumin mai suna Amir wanda zai yi shekara ashirin da biyar suka je Waukko su, kyakkyawar tarba suka samu daga iyalan mutumin harda shi aka saukesu a part guda cikin ?aton kuma haWaWWan gidan nashi anata so a Wauki su twins sun?i yarda, lafiyayyun abinci da abubuwan sha aka kawo masu bayan sun ci suka huta har lokacin sallar Juma'a yayi Haisam suka tafi Masallaci tare da Senator Buba da yaran shi maza, bayan sun dawo ne ya sanar mashi zasu tafi can garin su Fatuu yace ai yayi zaton zasu kwana su ?ara hutawa ya tambayi zasu kwana acan ne Haisam Win yace mashi ita zai baro ta can ta kwana biyu shi zai dawo nan yace tunda hakane yana ganin kaman yanzu lokaci ya ?ure kar suyi dare ya bari gobe tunda safe sai Driver ya kaisu yadda shima zasu gaisa sosae Haisam Win ya amince da hakan. Washegarin wuraren ?arfe tara da yan mintuna sukai sallama da mutanen gidan suka tafi, tafiyar Awa guda sukai suka iso tun shigowarsu bakin garin Fatuu ta fara murmushin farinciki sosae tayi kewar garin don kusan fin shekara ukku rabonta dashi da yake yanayin damuna ya fara don wasu wuraren sun fara samun ruwa ciki harda nan garin hakan yasa ganyayyaki da tsirrai sun yi kore shar shar gwanin sha'awa ga makiyaya nata koro garken shanaye da tumakai za'a tafi kiwo, Haisam dake zaune seat Win gaba nata kallon garin bayan sun shigo Fatuu ce ke nuna ma Driver hanya yana bi har suka ?araso kopar gidan tace mashi nan ne, wasu dattawan mutane da a ?alla zasu kai biyar na zaune a ?ar?ashin ?atuwar bishiyar dake a ?opar gidan wasu daga cikin su yan gidan ne ciki harda Mahaifin Fatuu daya zauna yana dakon zuwan su da yake da zasu baro Yola ta kirashi ta sanar mashi sai mutum biyu a cikin su duk yayyen shi ne sauran biyun kuma abokai ne, daga can gefen su yara ne ba masu yawa ba suna ta wasa, bayan ya parker suka buWe ?ofofin Motar suna fitowa Mutanen dake zaune suka mi?e a kusan tare suka nufo su, cikin washe baki suka shiga yi masu sannu da zuwa Baffan su Fatuu dai murmushi yake idon Fatun na akan shi itama tana murmushin farincikin ganin shi, bayan sun gama gaisawa da Haisam itama ta gaishe su suna ta fara'a suka amsa mata duk wanda yay yun?urin Waukar su twins sai su ?an?ame jikin iyayen nasu da yake kowa na Wauke da guda Waya, bayan an gama yi masu sannu da zuwa Baffan tare da yayun nashi sukai ma Haisam jagora zuwa ciki, suna shiga cikin soro su Aysha suka shigo da gudu suka nufi Fatuu suka ?an?ameta cike da farinciki suke mata sannu da zuwa da fullanci Adam dake hannunta ya fara ta6e baki zai yi kuka don sun rungumeta Aysha ta Wago tana mi?a mashi hannu ya ?iya sai kallonta yake kaman mai son tuna ta don da bakin su Mino ya yarda da ita Fatuu ta rin?a faWi mashi kowacece da fulatanci sai gashi ya tuno ta ya mi?a mata hannu cikin washe bakin jin daWi ta Wauke shi, ganin an amshi Adam yasa tace ma Haisam yabata Abie kafin suka idasa shiga cikin gidan mutane duk an le?o ana masu sannu da zuwa Fatuu ke amsawa shi kuma Haisam kai yake ta jinjina masu fuskarshi a sake.......


100


~_*
'=؋?BOSS LADIES WRITERS=؋?
'*_~


.........Bangaren da ArWo yake aka kaisu can gefe da inda nasu Yaya yake an kewaye wurin da yar gajeruwar kanta daga cikin wurin harda siminti a ?asa, shiga sukai cikin Wakin wanda yana da Wan matsakaicin girma akwae madaidaicin gado na katako yana da wardrobe mai gida biyu samantaa an Waura wasu tsofaffin akwatuna na fata dana ?arfe akwae yan durowoyi na gadon sai wata yar kanta da aka Waura al'quranai da wasu littafan addini daga jikin bango kuma wanda ke shafe da siminti an rataye abubuwan fulani harda takubba a cikin gidajen su daga saman Wakin anyi ceiling irin na da da ake yi da itatuwa ?asan Wakin kuma gaba Waya a rufe yake da ledar tsakar Waki harda Wan madaidaicin carpet daga tsakiya wannan duk aikin Baffan su Fatuu ne don kullum cikin yi ma mahaifin nasu hidima yake dama kuma yafi duk yan uwan shi wayewa, lokacin da suka shiga ArWon na kwance a saman gadon jikin shi sanye da riga da wando na yadi mara nauyi sai hula ha6ar kada a saman kan shi suna shiga ya fara ?o?arin tashi zaune bayan Baffan su Fatuu ya sanar mashi ga su Inna wuro da maigidan nata sun iso da yake yasan da Maganar zuwan nasu duba jikin shi, saida aka taimaka mashi sannan ya zauna Haisam na niyyar zama a saman carpet da sauri cikin muryarshi data disashe yace kar ya zauna nan Haisam Win bai ma ji abunda yace ba ya dai gane ta hanyar hannu daya Waga mashi hakan yasa ya dakata ArWon ya kalli Baffan su Fatuu da fullanci yace ya Waukko masu darWuman makkan shi a cikin kayan shi, Makkan da ya shekara kusan fin talatin da zuwa wasu ?a?an shi ma basu san da yaje ba balle kuma su Fatuu jikoki, bayan ya Waukko dardumar wadda ba laifi bata ji jiki ba saboda ji yake da ita don ta shiga cikin tarihin zuwa makkan shi tana da girma, shimfiWa masu yay a saman carpet suka ce ma Haisam ya zauna Fatuu ma ta zauna daga gefe suma Yayun Baffan dashi duk suka zauna daga gefe nan aka shiga ?ara gaisawa ya juya suka gaisa da ArWo tare da yi mashi ya jiki a hankali yake amsawa Fatuu ma ta gaishe shi da fullanci tayi mashi ya jiki ya amsa yayi mata sunzo lafiya da tambayar ya suka baro sauran mutane duk ta amsa masu ya kalli su twins yace wannan sune ?a?an nashi da bai sani ba tana murmushi tace eh ya mi?o hannu alamar a bashi su Babban Wanshi wanda yana cikin wanda suka shigo shima ya manyanta sosae yana murmushi yace ai basu yarda da mutane duk da haka Fatuu ta mi?e da Abie tayi ma Aysha dake daga can bakin ?opa alamar ta kawo Adam suka kai mashi su, kamar ma tsoron ArWon suke duk sun waro fararen idanunsu tubarkallah suna bin shi da wani irin kallo daya mi?o masu hannu sai su ?an?ame su Fatun ?arshe saidai a hannun nasu ya gansu ya saka masu albarka harda tofin Addu'a yayi masu yace ma Fatuu kafin su koma zai bada magungunan kariya a rin?a basu tace to, a nutse Haisam cikin cool voice Win shi ya tambayi an kai shi Asibiti ne don asan abunda ke damunshi Modibbo ya bashi amsa da sun kai shi Babbar Asibiti ta Jumeta anyi mashi gwaje gwaje an tabbatar ba abunda ke damunshi kawai shekarune to sun bada wasu magunguna sannan sun ce ya rin?a samun hutu sosae to ya gama shan magungunan kuma yana samun isashshen hutun don ko zama a fadar shi ma bai yi yanzu shiyasa ma jikin nashi da sau?i sosae, kai Haisam ya jinjina kafin yace yana ganin yakamata a kai shi Asibitin ?wararru dake a Yola a ?ara mashi bincike sosae suka ce to shidai Baffan su Fatuu shiru yay saidai a ranshi yaji daWin hakan da Haisam yace don ba yarda baiyi ba a kaishi can amman yayun nashi suka ce kawai 6arnar kuWi ne tunda an tabbatar da lafiyar shi lau, nuna ma Fatuu wata yar ?warya dake a rufe da faifai ArWo yay yace mata ga fura nan taba Haisam da sauri Baffanta yace mashi ya barta tashi ce yasha suma ga ta can an haWa masu yanzu zasu je sai su sha ya Waga kai Modibbo yace yakamata suje an barsu ko ruwa ba'a basu ba Baffan yace to tare da mi?ewa suka ce ma Haisam suje suci Abinci duk suka mi?e harda Fatuu,

Bayan sun fito bangaren su Fatuu suka nufa lokacin da suka isa Fatuu taji daWin ganin yadda aka ?ara gyara wurin kai kace ba'a cikin gidan bane sai ma da suka shiga cikin parlor shima an ?ara gyarashi akan lokacin da tazo da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login