Showing 447001 words to 450000 words out of 513411 words

Chapter 150 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16767

abunda bata sani ba dana sani kawai yake acikin ranshi don ganinta ya fama mashi babban tabon sonta dake cikin zuciyarshi sai kallon su twins yake yana raya ?ilan da yanzu su yaranshi ne, gaba Waya Abincin ya fice ma Fatuu arai haka shima Khalid Win ba don yana jin daWin shi ba yake ci, Haisam bai daWe ba da tashi itama ta mi?e Dad yace wato Romeo ya ?oshi shine itama Juliet zata tashi Fatun tay yar dariya kafin tace ta ?oshi ne, cikin parlon ta nufa inda Haisam ke zaune yana latsa waya, Bayan sun gama cin Abincin gaba Waya a falon aka zauna ana hira jefi jefi Haisam ke saka baki anan ma Fatuu ta lura da yadda Khalid ke fakaitar idanun mutane yana kallonta cikin sa'a bayan Wan wani lokaci Abie yay bacci ta mi?e tace zata je ta kwantar dashi, bata daWe da tafiya ba shima Adam yayi baccin Hajiya ta bita dashi ya rage saura Alhaji da Khalid sai Haisam suka cigaba da yin hira wadda yawanci akan aikin su ne suna cikin haka Haisam ya ro?i Khalid kan yana son ya shige ma su Baffan Fatuu gaba zasu kai ArWo Asibitin da yake aiki a duba shi sosae yace mashi ba matsala, suna zaunen har lokacin sallar Azahar yayi Dad yace suje suyi kafin su tafi Haisam ya kira Fatuu a waya yace ta shirya da sun dawo daga salla zasu je can ruga suyi bankwana dasu sai su koma Yola ?arfe biyar jirginsu zai tashi zuwa Abuja tace to, suna dawowa sallar ya sanar ma Dad zancen zuwa rugar yace Ok amman zasu dawo ta nan ko sai Driver ya kai su Yola Win Khalid na jin haka yace bari suje rugar tare sai ya duba jikin arWon in sun dawo sai su wuce Yolar tunda shima komawa zaiyi Alhaji yace yauwa to hakan yayi, Part Win da aka sauke su Haisam ya wuce don ya shirya lokacin daya je Fatuu har ta gama shiryawa cikin doguwar rigar shadda ta saka sar?a da yankunnan Diamond su twins ma ta saka masu ?ananun kaya iri Waya, yana shigowa ta nufeshi tana murmushi ya buWe mata hannu yay hugging nata can ?asan ma?oshi ya furta mata "I luv you with every single beat of My Heart Baby" lumshe ido tayi jin yadda hucin Maganar ya bugi kunnanta, shiru yay yana breathing a hankali can ta Wago da fuskarta ta kalle shi sai taga kaman wani yanayi da bata sani ba akan fuskar shi, tambayar shi tayi ko da wani abu a hankali ya lumshe ido tare da Wan girgiza mata kai daga haka yay pecking goshinta ya saketa yace bari yay wanka, juyawa yay ya nufi hanyar toilet tabi bayan shi da kallo can ta Wan Waga murya tace "....Know dat am breathing because of you Hubby" dakatawa yay ya juyo yay mata murmushi itama shi tayi mashi kafin ya juya, zama tayi a bakin gado tay shiru kamar mai nazarin wani abu, bai daWe ba ya fito sanin tafiya zasu yi ita ta taimaka mashi ya shirya yasa brown shaddar cikin wanda Alhaji ya kawo mashi sosae ta hau jikinshi ita ta Waura mashi agogo ta saka mashi links ta feshe shi da turare yanata mata murmushi, bayan sun gama shiryawa sun tattara komai suka fito kowa na Wauke da yaro guda abun gwanin sha'awa, koda su Alhaji da Hajiya suka gansu saida suka yi santin kyaun da sukai Khalid dai murmushin karfin hali kawai yake shi kaWai yasan mike faruwa a cikin zuciyarshi, har bakin Mota su Alhaji suka rako su sukai masu sai sun dawo, tunda suka hawo hanya Fatuu bata bari ta kalli saitin Khalid ba shi ke driving Win Haisam na a kujerar gefe ita kuma tana baya saitin kujerar Haisam, bai wuce sau Waya zuwa biyu ba sukai magana shida Haisam har suka iso, a tare gaba Waya suka je Wakin ArWon bayan sun gaishe shi Khalid Win ya shiga dadduba shi tare da yi mashi tambayoyi da fulatanci yana bashi amsa bayan ya gama ya faWi ma su Baffan su Fatuu ranar da zasu kai shi asibitin suka ce to nan Haisam yayi mashi sallama da fatan Allah ya bashi lafiya ya amsa yana ta mashi godiya da saka mashi Albarka, wani ?umshin leda yasa Baffa ya Waukko mashi yaba Fatuu yace ga magungunan nan ya faWi mata yadda zata masu da yadda zata rin?a ba su twins har itama yace tasha da Haisam sukai mashi godiya, bayan sun fito ?opar gida Khalid ya koma su kuma suka nufi bangaren su Yadikko sai faman le?owa ake ana kallon su, a parlor aka zazzauna suka shiga gaisawa bayan Wan lokaci Haisam yayi ma Yadikko sallama tanata mashi godiya da saka albarka ya kai hannu aljihun rigarshi ya fiddo kuWi masu yawa ya mi?a ma Baffa yace gashi a raba ma mutanen gidan sannan ya tambayi Account Win shi yace zai tura kuWin da za'ai ma ArWo amfani a Asibitin Baffan nata ro?onshi kan ya barshi za'a kai shi yana murmushi yace ba wani abu yayi niyya ne, kuWi masu yawan gaske ya tura har saida Baffa ya jinjina kuWin yace hidiman tayi yawa shidai ba komai kawae yake cewa, Godiya sosae sukai mashi ya mi?e yace ma Fatuu in ta gama yana waje Baffan ma ya mi?e suka fita tare, bayan fitar shi ne Yadikko ke mata tsegumin Khalid don taji dashi suka zo Fatuu ta faWi mata yadda akai suka taho tare tace kuma Haisam bai nuna komai ba tace mata a'a, itama Fatun saida taba Yadikko kuWi harda Baffanta ta bada ta bashi dasu Aysha sukaita Godiya ta Waukko mata wasu magunguna da zasu inganta lafiyar ta data cikin jikinta da kuma wanda zata samu sau?in haihuwa ta faWi mata yadda zatayi amfani dasu, tare da Yadikko suka zazzagaya yi ma sauran mutane sallama nan fa aka shiga ba su twins kyautar abubuwa su kaji, zabbi harda akuyoyi cikin wanda suka basu akoyoyi harda Yaya, duk Yadikko ta amsa tace zata kiwata masu kafin daga baya a aika masu tunda ba'a Mota zasu koma ba, bangaren su Yadikkon ?wai masu yawa suka basu da uban dawon fura da Nono harda zuma mai yawa da man shanu duk akai masu dubara yadda ?wan bazasu fashe ba haka Nonon ma harda ?an?ara aka saka mashi yadda zai tsaya da sanyin shi gaba Waya cikin wata jaka aka saka su a haka ma kayan sunyi ma Yadikko kaWan tace inda da Mota suka zo sai an cika boot Winta da fura da Nono saboda su twins Fatuu nata dariya tace a haka ma ai da yawa, kusan gaba Waya gidan aka fito rakiyar su waje anata masu Allah ya tsare hanya, bayan sun baro rugar gidan su Khalid suka koma anan suka ci abincin rana kafin sukai masu sallama Hajiya Rabi'atu taba Fatuu kyautar atampopi masu kyau guda biyu da lace harda humra masu ?amshi da turarurrukan wuta su twins ma ta basu kaya sosae tayi mata godiya harda Haisam, har bakin Mota suka rako su lokacin da suka baro gidan ?arfe ukku na rana zuwa karfe huWu da wasu mintuna suka iso Yola, har gidan Senator Buba Khalid ya kai su da har yace bari ya jira su sai ya kai su Airport Haisam yace mashi ya bashshi kawai kar su 6ata mashi lokaci akwae Driver da zai kai su yayi mashi godiya kafin ya amshi lambar shi yace zai kira yaji yadda ake ciki dangane da jikin ArWo Khalid Win yace Ok, harda kuWi yaba su twins Fatuu tace ya barshi yana murmushi yace ai ba ita yaba ba yaranshi yaba ta amsa tayi mashi godiya tare da cewa ya gaishe da iyali yace zasu ji daga haka ya tafi, da suka shiga cikin gidan basu daWe ba salla kawai sukai koda aka basu abinci cewa sukai a ?oshe suke sukai masu sallama nan ma saida aka ba Fatuu da twins kaya Senator Buba ma ya basu kyautar kuWi masu yawa zumunci mai daWi, a wata jibgegiyar Jeep aka tafi kai su Airport harda Senator Buba yay masu rakiya, suna akan hanyar ne Fatuu taji ?arar shigowar sa?o a wayarta, lokacin data duba sa?on har saida gabanta yay bugu da ?arfi don ta gane Khalid ne ya turo duk da bata da lambarshi amman daga yanayin sa?on ta gane nashi ne, da turanci ya rubuto mata yana mai bata ha?uri da kuma neman yafiyarta akan abunda ya faru a tsakaninsu a baya yayi nadama da kuma danasanin da yasan har ya mutu bazai daina yi ba sai dai ta wani bangaren yayi farincikin shigowarta rayuwarshi don ta dalilinta Allah yasa ya daina duk wani abu mara kyau a ?arshe yana son ta sani ta zamo wani bangare na rayuwarshi wanda hakan ne ma yasa shi saka ma Wiyarshi sunanta, tana gama karantawa ta Wan saci kallon Haisam dake gefenta taga idon shi na a gaba suna yar hira da Senator Buba dake a seat Win gaba, kamar ta share Khalid Win ba sai ta mayar mashi da amsa ba sai kuma wata zuciyar ta raya mata yana iya cewa zai ?ara turo mata wani sa?on saboda rashin jin amsarta hakan yasa ta maida mashi da amsa, itama da turanci tace komai ya rigada ya wuce don har tama manta kuma tun bayan da aka fasa aurensu ta yafe mashi don haka tana fatan shima ya manta sannan ta gode da karar da yayi mata ya gaida mata da Zarah da Mamanta, tana tura sa?on ta goge duka nashi daya turo mata da nata data tura mashi sannan tayi blocking Win lambar tashi yadda bazai iya sake turo mata sa?o ba ko ya kirata tay shiru zuciyarta ta shiga tariyo mata da abubuwan da suka faru tsakaninsu yadda ya rin?a yi mata a cikin Mota da gidan gonarsu da ya kaita, idanunta ne suka fara tara ?walla da sauri ta fara ?o?arin mayar dasu tare da kawar da tunanin daga ranta.

Bayan sun dawo Abuja Washe gari Fatuu taje gidan Mino kai mata tsaraba Haisam ne ya kawota su twins a gida ta barsu, taji daWin ganin yadda Mino ta saki jiki suna ta shan amarci da Nameer ta sha kananun kaya riga da wando, bayan data je ne Nameer Win ya fita, sosae Mino taji daWin tsarabar data kai mata tace itama bada daWewa ba zata je Yola Fatuu ta Wan harareta tace ba yanzu ba sai ta shekara Minon ta no?e kai tace "kai Adda Fatuu shekara yayi yawa ni dai gaskiya nan bada daWewa ba zanje nasan dana nuna ma My Love ina son zuwa zai bar ni ?ilan ma tare zamu je" Wan buWa ido Fatuu tay ta ru?e haba ta maimaita My Love Win da ta faWa Mino ta saka dariya tare da rufe fuska alamar kunya, hira suka cigaba da yi anan Fatuu ke mata zancen Karatunta tace kar ta bari soyayya tasa ta shashantar dashi koda SSCE ne tayi ta samu result Win gama Secondary Minon tace eh rannan sunyi magana yace zata zana jarabawar sannan in zai tafi yin Master's Degree Win shi US zasu tafi tare sai taci gaba da Karatu a can, sosae Fatuu taji dadin jin hakan anan take sanar mata zancen komawarsu Us Mino ta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace yanzu shikenan tafiya zatayi ta zama bata da kowa a nan Fatun tace mata kada ta damu tasan bazata yi maraicin rashinta ba tunda ga yan gidan su Nameer nan tasan zasu zame mata tamkar yan'uwa, tare suka shiga Kitchen yin abinci suna cikin yin aikin ne Mino ke faWi mata wai Nameer yace in tana so a samo mata mai aiki da sauri Fatuu tace to ya tace mashi Minon tace cewa tayi ba sai an samo ba tunda ba wani aiki sosae sai yace wai ko gyaran gida ne a rin?a yi mata, girgiza kai Fatuu tay tace kada a samo mata wata mai aiki ai gyaran gidan ma zata iya tunda ba wani datti yake yi ba inda take amfani dashi kullum kamar Bedroom, toilet da Kitchen su ta rin?a gyara su kullum shi kuma falon tunda yana da girma in kamar taga bai 6aci ba tana iya bari sai bayan kwana biyu ta rin?a sharewa amman zata iya kullum tasa towel ta goge kayan kallo da kujeru sai ta rin?a saka turaren wuta akai akai koda zata yi mai aiki a bari ba yanzu ba sai kamar in ta samu ciki tayi nauyi kuma mai aikin ma kada ta bari a samo mata yarinya ko budurwa in ba haka ba a kwace mata My Love tana gani, dariya Mino tayi tace ita so take ma Aysha ta dawo wurinta shikenan ma ba sai tayi wata mai aiki ba Fatun tayi Wan jimm alamar nazari kafin tace mata hakan ma yayi amman ta bari ba yanzu zata Waukkota ba tace to, bayan sun gama girkin saida suka gyara ko ina sannan suka zauna suka ci tare, Sai bayan Magrib Haisam yazo Waukarta lokacin Nameer ya dawo ya shigo cikin parlon suka gaisa Mino ta kawo mashi abun ta6awa da lemu daga baya sukai sallama. A ranar da daddare Haisam ke faWi mata nan da sati guda zasu tafi Us, ana saura kwana ukku su tafi taje Katsina yin bankwana, har gidan Aunty mareeya da Feenah taje sannan taje gidansu Aminiyarta Haulat harda abun arzi?in data saba tayi mata taba Kawu Amadu makullin Motarta tace yaci gaba da yin amfani da ita, kwananta biyu ta dawo Abuja Washe gari wurin ?arfe sha Waya suka tafi harda Mino amarya akai masu rakiya Airport daga nan Lagos zasu je wurin Fanan sai da daddare zasu tashi zuwa Us.

Fauzy taso zuwa Funtua bayan zuwan su amman Sameer yace tayi ha?uri ba yanzu ba don tana iya samun matsala in tayi wannan tafiyar a mota dole ta ha?ura anan Nasarawa suka tsaya don zasu Wan kwana biyu kafin su koma London, Bayan bikin Mino da kamar wata Waya lokacin satin su Fatuu biyu da komawa da daddare bayan sallar isha Gwaggo na zaune kan abun salla tun bayan data gama sallar take zaune a wurin kamar mai tunanin wani abu can ta kai hannu ta Waukko wayarta dake ajiye gefen abun salla ta shiga kiran Amadu, bayan ya Waga ta tambayi sun dawo daga masallaci ne yace mata eh ta ?ara tambayar ina Kamalu yace gasu nan tare a shago tace to shi ya shigo tana son ganin shi yace to, bada daWewa ba ya shigo Wakin da sallama ta Waga kai ta kalleshi tana amsawa ya nufi kan kujera ya zauna, gaishe da ita yayi ta amsa yace gashi ta Waga kai, shiru ta Wan yi yanata kallonta can tace "Dama so nike in tambayeka wai kai baka son yin Aure ne?" Wan waro ido yay sai kuma yayi yar dariya yace yana so mana amman miyasa tace haka ta Wan ta6e baki tace taga baida niyya ne gashi yanata girma yanzu har ya fita daga shekara talatin amman bata ta6a jin yayi zancen yana da budurwa ba, yana dariya yace kawai shi soyayyarce ya Wauketa 6ata lokaci don da yawa sai yaga an daWe ana soyayya amman sai kaga anzo ba'a yi aure ba shiyasa Amman daya samu wadda suka fahimci juna zai yi auren, kai Gwaggo ta jinjina ta Wan yi shiru tana kallon ?asa ya fahimci kamar akwae wani abu a ranta hakan yasa shi tambayarta koda wani abu ta Wago tana murmushi tace "Dama wata shawara ce nike son baka nace mi zai hana ka auri Haulatu duk da ba budurwa bace amman bata da wani aibu ina son yarinyar don tanada halin kirki kuma abunda aka fi bu?ata kenan a wurin macen aure na tabbatar duk wanda ya aureta sai yaji daWin zama da ita saboda tana da ha?uri sosae, ka duba yadda aka kasa yin ?awance da Fatuu saboda halinta lokacin kuruciyarta amman haka Haulat ta jure duk da halinta na cika mutum haka taita ha?uri sa ita sukayi ?awance har suka zama tamkar yan'uwa",

Shiru Kawu Amadu yay idonshi a ?asa ganin haka yasa Gwaggon tace ita shawara ce ta bashi ba dole take mashi ba in bata yi mashi ba shikenan tana mashi Addu'ar Allah ya bashi wadda zasu daidaita mai halin kirki, Wagowa yay yana murmushi yace a'a bawai bata yi mashi bane kawai yana mamakin yadda tunaninsu yazo daya ne don tun bayan dawowarta yaji yana son aurenta saida ya bari ta gama takaba sannan kwanaki yaje mata da Maganar amman sai bata yi na'am ba tace wai tursasa mashi akai kan ya aureta kuma tasan bai wuce Fatuu ce tasa saboda tausayinta da take amman in akace ya aureta ai an ?ware shi tunda ita yanzu ba budurwa bace, lokacin ya nuna mata shi ba wanda yasa shi shiya kawo kanshi to sai tace wai ya bata lokaci zata yi shawara to har yanzu zaman jiran amsarta yake ko bayan bikin su Mino saida yayi mata maganar amman sai ta ?ara cewa ya dai ?ara mata lokaci, Murmushi Gwaggo tayi tace ina ruwan Haulatu, duba agogon wayarta tayi taga lokaci kafin ta fara ?o?arin mi?ewa tana faWin bari taje gidan su, mi?ewa yay shima yace suje ya rakata, bayan sun fito Amadu ya kwala ma Kamalu kira ya le?o yace mashi zasu je su dawo yace to ya gaishe da gwaggo ta amsa tana murmushi, suna tafe suna hira gwanin sha'awa har kama Gwaggon yake lokacin da suka iso gidan a waje ya tsaya ita ta shiga, lokacin da tayi sallama innarsu Haulatun na a tsakar gida ta tarbeta da fara'a tana mata sannu da zuwa suka nufi Waki, bakin gado ta nuna mata Gwaggon tace bari ta zauna a kan tabarma dake shimfiWe innar tace ya zata zauna a ?asa don Allah, Gwaggo tana murmushi tace to ai ita ba ba?uwa bace ko kuma ai ba'a ?asa bane tunda kan tabarma ne, itama innar zama tayi gefen gwaggon suka shiga gaisawa ta tambayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login