Showing 504001 words to 507000 words out of 513411 words

Chapter 169 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16788

?ara ?awata shi, nufo shi Fatuu da Fanan sukayi sun sha gayun ?ananun kaya riga da wando da suka bayyanar da dirin su gashin kan su gaba Waya sun sake shi kai kace hausa bazata fito daga bakunansu ba, ko a iya matan da Allah ya ba Haisam za'a iya cewa ba ?aramin dacewa yay ba don mata ne da suka amsa sunan mata uwa uba gasu da hali na gari, a gabanshi suka tsaya suna sakin murmushi tare da ?ara yi mashi godiyar yanata murmushi ya ware masu hannuwanshi a tare suka faWa jikinshi suna ta yar dariya Jidderh da abokiyar aikinta ma dariyar suke ta shiga yi masu Vedio, bayan sun Wago daga jikinshi kamo hannuwansu yayi suka nufo ciki, a saman doguwar kujera suka zauna dama a gabanta aka aje cake Win, bayan zaman su Jidderh tace yakamata a kira su twins suzo a yanka cake tare dasu Fanan ta mi?e ta nufi inda wayar landline take ta kira part Win Haisam, Esha ce ta Wauka cikin zazza?ar muryarta tace waye ne ke kiran Dad to bayanan da turanci tayi Maganar Fanan na murmushi tace to Momynsu ce, waro ido Eshar tayi sai kuma tayi dariya ta kira sunanta ta amsa tare da tambayarta ina su twins tace mata gasu nan tace to suzo part Winta yanzun nan akwae surprise da sauri Esha ta maimaita abunda tace tare da waro ido Fanan Win tace mata eh, kife kan telephone Win tayi cike da zumuWi ta faWi ma su twins abunda Momy tace ta nufi hanyar fita da gudu, Esha ce ta fara shigowa da gudu tana sanye da Wan skirt na jeans da farar t-shart bayan ta shigo su twins suka biyo bayanta suma ?ananun kaya ne a jikinsu, koda Esha taga yadda akai ma Falon da tsananin mamaki taja ta tsaya a gabansu ido waje ta furta "Wow! what a surprised!!" hannu Fanan ta mi?o mata ta nufesu tana washe baki, a saman jikinta ta Waurata gaba Waya ta ruWe sai faman tambayar su Dad ake ma Birthday take, saida Adam ya nuna mata rubutun jikin cake Win sannan ta fahimci mi ake, a tare gaba Waya suka kama ma Haisam Win hannu suka yanka cake Jidderh nata masu Video, bayan an yanka kowa ya Wauka ya bashi a baki kafin shima ya basu har shafa mashi icing Win jiki sukai a fuska suna ta dariyar farinciki daga baya Fanan ta kama hannunshi da turanci tayi mashi kalami masu tsuma zuciya kan muhimmancin shi a wajenta da kuma yadda take son shi ?arshe tayi mashi godiya da Addu'oi, bayan ta gama Fatuu ma tayi suma su Esha saida sukai mashi abun dai gwanin burgewa daga baya aka shiga yin hotuna, harda music Fanan ta kunna aikuwa Esha ba ?aramin cashewa tayi ba sosae taba mutane dariya, sosae Haisam ya yaba da abunda sukai mashi shima saidai yay masu kalamai kan yadda suke a wurinshi saida aka kira sallar Magrib suka gama.

A cikin satin akaita zuwa ganin sabon gidan da yi masu Allah yasa Alkhairi har Laila ma tazo daga Kano ita da mijinta da yaranta biyu don ta ?ara haihuwa, ranar Friday su Gwaggo suka zo da Kawu Amadu da Tk da kuma matansu sai yaransu don dukkansu sun ?ara haihuwa ita matar Tk mace ta ?ara haihuwa itama Haulat mace ce mai sunan Gwaggo wato Khadija, zuwan nasu yasa Fatuu ta ?ara zuwa Abujar kowa saida ya jinjina haWuwar gidan akai masu Allah yasa Alkhairi da Addu'oi, a yadda suka shirya zasu bi Gwaggo ne apartment Win da take zama in tazo amman Fatuu ta hana tace anan zasu kwana harda gwaggon tunda ai don su suka zo, ?arshe dai anan suka kwana don Haisam da Fanan duk sun saka baki kan su kwana anan, Washe gari Asabar bayan sunyi lafiyayyan breakfast suka shirya fita harda su Fanan da Fatuu sukai Mota ukku data Fatuu dasu Gwaggo suka zo da ita sai kuma ta Fanan sai wadda Haisam zai hau, Villa suka fara zuwa duk an nuna farincikin zuwansu karma Hajiya sosae tayi murnar ganin su akai masu tarba mai kyau, daga Villa gidan Mino suka wuce zo kaga murna har tana ce ma Gwaggo amman dai bazata koma ba har ta haihu ko Gwaggon na dariya tace a'a abunda da saura amman zata kwana biyu in ta haihun ta dawo, da ?yar ta barsu suka tafi harda ro?onsu kan su dawo su kwana anan suka ce to ?ilan su dawo, daga nan gidan Aysha aka wuce itama taji daWin ganinsu har ta kasa rufe baki gashi tayi masu lafiyayyan abinci don tasan da zuwan nasu, bayan gidan Aysha gidan Kamalu aka nufa nan ma dai sun nuna farincikin zuwan nasu hannu bibbiyu Farha ta kar6e su Babynsu har ta girma tubarkallah, gaba Waya ko ina ro?onsu ake kan su kwana ?arshe saidai rabawa sukai Haulat da Husnah suka koma gidan Mino Tk da Amadu kuma gidan Kamalu zasu kwana Gwaggo kuma gidan Aysha sai dare su Fatuu suka koma gida,

Washe gari gaba Waya suka koma gidansu Fatuu a yadda suka shirya tare da ita zasu tafi Zaria su kwana washe gari Monday da safe sai su wuce Gwaggo dai anan zata tsaya sai ta kwana biyu,

Kwance tashi cikin Mino ya shiga wata na tara lokacin watan su Fatuu Waya da komawa sabon gida kuma Fatun na gida don sun samu hutu, tun ranar litinin ta fara yin na?uda tsaitsaye zuwa washegari talata ciwo ya kankama amman koda aka kaita asibiti sai aka ce da saura su dawo gida taita yin exercise, kan kace mi duk ta fita hayyacinta dama abu ga sabon shiga tuni ido ya raina fata sai mur?ususun azaba take har zuwa Fatuu tay ta dubata itama taga da saura Win haka tay ta ?arfafa mata gwuiwa har tana ce mata kodai dama bata yin exercise da cikin ya tsufa cikin ciwo tace wllh tana yi, sai dare Fatuu ta koma gida Nameer ya dasa yin jinyar, wuraren ?arfe sha biyu ba arzi?i ya kwasheta suka koma asibitin, wannan karon an kwantar da ita a vip wato Waki na musamman ita kaWai ce aciki duk da haka an faWi ma Nameer cewa da sauran lokaci, koda Fatuu ta kira taji ya jikinta Nameer ne ya sanar mata sun dawo asibiti an kwantar da ita amman ance still da saura tana jin haka tace gata nan zuwa, bayan zuwanta Asibitin Auntynsu Nameer ma tazo, shiru shiru ba haihuwa gashi ga dukkan alamu tana cikin azaba wasa wasa sai gashi har asuba bata haihu ba lokacin ta gama jigata ?arfinta ya ?are, gari na wayewa Aunty ta bada umarnin ayi mata Cs, sosae hankalin Nameer ya tashi jin zancen aikin amman ba yadda ya iya haka ya saka hannu, Wuraren ?arfe tara na safe aka shiga da ita Wakin tiyatar lokacin duk yan uwa sun zo harda Mom, Aysha ma tazo sai kuka take ana ce mata tayi mata Addu'a, ita kanta Fatuu hankalinta a tashe yake ?arfin hali kawai take tana ta yi mata Addu'oi, bayan kamar minti ashirin da shiga da ita sai ga likitan ya fito yana ta murmushi ya sanar dasu tama haihu da kanta ba'a riga anyi aikin ba, zo kaga murna Aysha har da tsalle sai ga mai kuka ta koma yin dariya Fatuu da Nameer harda sujjadar godiya ga Allah sukai, lokacin da aka fito da Babyn wanda namiji ne baka jin komai daga bakunansu sai tubarkallah ma sha Allah Babyn kyakkyawan gaske gashi ?ato, daga baya itama Mino aka fito da ita saman gado baiwar Allah har an saka mata rigar aiki, bayan an canza mata Waki duk aka shiga ana mata ya jiki da barka, su Mino an WanWana tun a asibitin ta rin?a faWin ta gama haihuwa aikuwa mi Fatuu zatayi in ba dariya ba tace wasa take ai yanzu ma ta fara sai gata harda kukanta sha6e sha6e tana ta rantsuwar ita Allah ta gama, da yamma aka sallameta ganin lafiyarta lau suka koma gidanta aka cigaba da zaman jego har ranar suna tazo yaro yaci sunan mahaifinsu Fatuu wato Muhammad aikuwa ba ?aramin farinciki su Fatuu sukai ba, bayan suna da kwana ukku ta koma Yola acan zatayi wanka kamar yadda ta bu?ata a wurin Nameer.

Bayan sati biyu da haihuwar Mino ranar Alhamis lokacin hutun su Fatuu na gab da ?arewa tana kwance saman gado da safe wurin ?arfe sha biyu na rana jikinta sanye da turkish dress riga da wando kalar Yellow gyalen kayan na daga can gefe hakan ya bayyanar da kanta da akai ma kitson sunan Mino sati Waya daya wuce, tana cikin yin baccin Esha ta shigo Wakin da gudu koda ta hangota kwance sai ta nufi gadon, hayewa tay ta fara bubbuga jikin Fatuu tana faWin "Aunty, wake up!, wake up pls!! ki tashi" yanayin yadda take Maganar kamar zata saka kuka, buWe ido Fatun tayi ganin Esha ce ke tashinta yasa ta tamke fuska da alamun 6acin rai ta furta "Esha! Why do you always disturb my sleep for God's sake! Banda dama in kwanta sai kin tashe ni kuma bada wani dalili ba kawai baki so ki ganni a kwance!" yamutsa fuska Esha Win ta shiga yi idanunta suka ciko da ?walla, a fusace Fatun ta ?ara cewa "yanzu da kika zo kina buguna haka miye zan maki??" cikin karyayyar murya Esha Win tace "Ba Momy ne bata lafiya ba kuma tayi amai da kuka" waro ido Fatun tay ta maimaita "amai da kuka!" da sauri ta jinjina mata kai aikuwa ba shiri ta wuntsilo daga saman gadon ko ta kan gyalen kayan bata bi ba ta nufi hanyar ?opa Esha data saukko itama tabi bayanta da sauri, lokacin data shiga Bedroom Win Fanan kwance ta sameta a saman gado rabin jikinta lullu6e da duvet sai nishi take su twins sun sakata tsakiya fuskokinsu duk ?walla, a ruWe Fatuu ta nufi bakin gadon ta zauna tare da kai hannu ta ta6a fuskarta tana tambayarta mike damunta haka, cikin nishi tace mata tunda ta tashi bata jin daWin jikinta haka ta rin?a daurewa har sukai breakfast to bayan sun gama ta dawo Waki taji zuciyanta ta fara tashi daga baya kuma sai amai yazo mata bayan tayi ne zazza6i da ciwon kai suka rufeta tana haka su twins suka zo yanzu ma bata daWe data ?ara yin aman ba gashi harda juwa take ji shiyasa tasa a kira mata ita ganin ciwon na gaba, cike da damuwa Fatuu tace ai da tun da taji bata lafiya tasa aka kirata, wayar Fanan Win ta Wauka ta kira Haisam bayan ya Wauka cikin tashin hankali ta sanar mashi da halin da Fanan take ciki Shima hankalinshi ya tashi ba kamar daya ga lafiya lou suka yi breakfast, ce mata yay ko ta kaita Asibitin Villa tunda yafi Kusa zai iskesu yayi wasu ba?i ne daga Lagos amman bada jimawa ba zai sallamesu yazo duk yadda ake ciki pls ta sanar mashi da sauri tace to, suna gama wayar Mom Win shi ya kira ya sanar mata tace bari ta kirasu, bayan ta kira wayar Fanan Win Fatuu ta Wauka ta tambayi yanayin jikin Fanan Win da damuwa Fatun tace to gata nan da gani dai tana jin jiki tana tunanin fever ce ke damunta Mom Win tace Ok su taho nan sai a dubata, dama Fanan Win a shirye take don duk sunyi wankan safe gyale Fatuu ta Waukko mata itama ta Wauki wani cikin nata ta yafa, a tare harda su twins suka kamo Fanan Win yaran duk sun shiga damuwa gwanin tausayi, a Motar Fanan suka tafi, bayan sun isa Mom ta tarbesu aka wuce da ita Asibitin, suna zuwa kwantar da ita akai a Waya daga cikin lafiyayyun dakunan da ake kwantar da marasa lafiya da suka danganci gidan gwamnatin tarayyar, tambayoyi likitan daya kar6eta ya shiga yi mata tana bashi amsa ciki harda rabonta da period ta bashi amsa da tayi last Month sai wannan watan ne bata kaiga yi ba amman dama wani lokacin tana fita daga wata sannan har tsallaken wata ma tana yi nan tayi mashi bayanin lalurar data yi a baya amman tace mashi ta samu sau?i, lokacin da ake mata tambayoyin Mom ta kira Hajiya Maryam ta sanar mata ga Fanan an kawo ba lafiya nan take hankalinta ya tashi ta shiga tambayar abunda ya sameta Mom Win tace ba'asan ta?amaimai ba amman gashi nan likita na bincikawa tace to gata nan zuwa, jininta aka Wiba aka tafi yi mata gwaje gwaje, ba'a jima ba Hajiya Maryam ta ?araso tana ganin yanayin jikin Fanan Win a ruWe ta hau tambayarta abunda ke damunta Fatuu dake zaune a wurin kanta tayi mata bayanin yadda ciwon ya fara sam ba wanda ya kawo komai a ranshi Mom tace su jira likita yazo ya faWi sakamakon gwaje gwajen, bayan wani Wan lokaci Hajiya Maryam Win ta mi?e tace bari dai tabi bayan likitan don ta ?agara taji mike damunta haka, tana niyyar fita likitan ya sako kai da sallama taja gefe, yana shigowa ta hau tambayar shi mike damunta ne fuskarshi Wauke da murmushi yace ta kwantar da hankalinta abun farinciki ne, su Mom na jin haka duk suka mi?e suka nufo shi, tambayarshi Hajiya Maryam ta sake yi miye abun farincikin yace sakamakon gwajin ciki da akai mata ya bayyana tana Wauke da ciki na tsawon sati ukku, yadda kasan wutar jikinsu ta Wauke gaba Waya bin shi sukai da ido ba mai ko ?wakkwaran motsi shi kuma likitan sai murmushi yake,

"Wait Dr, wai abunda kake son faWi mana shine kana nufin ita Fanan Win ke Wauke da ciki?" da tsananin mamaki Hajiya Maryam ta tambaya cikin girmamawa yace mata eh haka sakamakon ya nuna tana dashi na sati ukku yay maganar tare da mi?o mata wata farar takarda da aka naWe, har saura kaWan ta saki wayarta dake a hannunta wurin rawar hannun ta amsa, bayan ta buWe Mom da Fatuu suma suka shiga dubawa nan idonsu ya tabbatar masu, da tsananin farinciki suka shiga washe baki Fatuu harda sa hannu guda ta rufe bakinta alamar mamaki, nan fa aka shiga yin murna su Esha harda tsalle suna faWin Momy is pregnant zata haifa masu baby Allah ya amshi addu'ar su, nan fa aka fara kiraye kirayen waya ana ma yan'uwa albishir, ko ban faWa ba ansan dole ai tsananin farincikin samun cikin, Mom ce ta kira Haisam lokacin ma yana kan hanyar zuwa tayi mashi albishir to shima dai ba ?aramin mamaki da murna yay ba , kan kace mi Wakin ya cika har Hajiya tazo da Farha anata farinciki, kyautar miliyan guda Hajiya Maryam tayi ma likitan daya faWi masu zancen cikin Haisam ma ya ?ara mashi wata miliyan guda Win kakar likita ta yanke sa?a har ya rasa irin godiyar da zai yi, Mom na dariya tace to ai itama yakamata a bata kyautar tunda ita ta kirata ta sanar mata zancen ciwon duk akai dariya Hajiya Maryam Win tana dariya tace to ta bata kyautar Mota duk akai shewar murna, Mom nata dariya tace ita ta yafe Doughter yakamata a ba kyautar tunda ita ta kawota asibitin Hajiya Maryam Win tace to ta ba Fatun Motar, da sauri Fatuu tace a'a ta barta ai duk abun farincikin nasu ne Hajiya Maryam Win tace ta riga ta bata in bata so sai ta bayar, Esha na jin haka ta ru?e ?ugu tace to ai suma tare dasu aka kawo Momyn a basu kyautar, hannu Hajiya maryam ta kai ta Wan ja kumatunta tace ta faWi abunda duk take so da sauri tace stroller take so da zata rin?a tura baby aikuwa mi za'ai in ba dariya ba Hajiya Maryam Win tace an gama in ma guda goma take so zata siya mata ta juya kam Adam tace shi mi yake so yace kayan wasa da zai rin?a yima Baby wasa harda Mota da zasu rin?a shiga tare suna zagaye gida tace to shima za'a siya mashi, juyawa tay kan Abie da yayi shiru kai kace babu shi a wurin tana dariya tace "kai kuma miskilin mu mi kake so?" shiru yay yana bin ta da idanunshi da suke a Wan lumshe duk da idanun nasu manya ne amman wani lokacin sai su lumshesu kamar dai yadda na Haisam ke yi, shiru yay bai tanka mata ba duk idanunsu na akan shi ana son aji mi zai ce don Magana mugun wuya take mashi wannan da alama ma sai yafi Haisam miskilanci dama ance wai kyawun magaji ya zarta, ganin baida niyyar magana yasa tace mashi in fa bai faWi mi yake so ba to in aka haiho Babyn saidai ya rin?a kallonshi do n baza'a bashi ba ya Wauka balle har ya yi mashi wasa, ana jin abunda tace su Mom suka ce mashi ya faWi mata ko so yake su Esha su rin?a Waukar baby suna mashi wasa banda shi, a hankali ya fara motsa baki kafin da ?yar cikin sanyayyar muryarshi ya furta Water Bottle yake so da zai rin?a ba Babyn ruwa aikuwa mi za'ai in ba dariya ba har Haisam saida yayi dariyar Hajiya dake zaune tace ai shine Water Bottle Win aka ?ara yin dariyar, Fatuu dake zaune gefen Fanan ta lura da ita kamar bata farincikin samun cikin don ko uffan bata ce ba duk abun nan tana kwance sai Wan murmushi da take in anyi abun dariya hakan yasa ta dafata tace "Aunty Fanan ya naga kamar baki farincikin samun cikin ko jikinne?" wannan Maganar da tayi ce ta maido hankulan yan Wakin kan su Hajiya Maryam tace itama ta lura don ta Wauka jin zancen cikin zai sa ma ta wartsake, ganin duk sun zuba mata ido yasa tayi Wan faffaWan murmushi tace tana farinciki mana saidai ita a wurinta already tana da yara so bata jin wannan kamar a cikinta na farko, gaba Waya Maganar tayi masu daWi Hajiya dake murmushi tace gaskiya ne Maganarta, Auntyn su Haisam ce tace

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login