Showing 486001 words to 489000 words out of 513411 words

Chapter 163 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16729

biya ma Gwaggo bayan duk Matan shi ya biya masu sunje aikuwa sosae su Fatuu sukai Farinciki itama Gwaggon tayi farincikishi sai hamdala take, bayan gama murnar biya ma Gwaggon Haisam da Nameer sukai ma su wata irin bazata Haisam ya biya ma Baffansu shi kuma Nameer ya biya ma Yadikko wayyo daWi! farincikin yayi yawa saida aka dangana da yan koke koke, bayan tafiyarsu ne ciwo ya tasar ma ArWo sosae har saida su Fatuu da Haisam da Nameer suka je dubashi kafin su baro saida su Haisam Win suka kai shi Yola asibiti aka kwantar dashi ya mi?a kulawar shi a hannun Khalid, bayan kwana biyar aka sallame shi ba laifi ya Wan samu sau?i suka koma gida, gaba Waya hankalin Baffansu Fatuu a tashe yake da jin zancen ciwon sosae yake ma mahaifin nashi Addu'a acan Makka kan Allah ya bashi lafiya, Alhamdulillah Mahajjata sun dawo gida lafiya su Gwaggo an zama Hajiya ma sha Allah, kwana ukku da dawowar su Baffa Allah yay ma ArWo cikawa, akace mahaifi mahaifi ne duk da dama arWon ya tsufa sosae Baffansu Fatuu yaji mutuwar tashi harda kukan shi don yasan mahaifin nashi ba ?aramin son shi yake ba ko kafin ya rasu saida ya bar wasiyyar cewa shi zai gaji mulkin shi na arWo kuma ya ro?e shi kan ya haWa kan iyalin kada ya bari a samu 6araka, lokacin da Fatuu taji labarin rasuwar sosae ta damu harda kukanta sa6anin lokacin da tana yarinya bata da burin daya wuce arWon ya rasu duk da harda ?uruciya, washe gari suka tafi gaisuwa suna can Mom da Aunty suka je dasu Fanan da Jidderh har Aunty Laila ma tazo Lokacin Fauzy basu ?asar shiyasa bata zo ba amman Hajiya Zainab tazo, sosae suka yi ma su Fatun kara har mai girma shugaban ?asa ya turo wakilci an zo anyi masu gaisuwa, duk a ranar dasu Mom suka zo suka koma amman su Fatuu sai da akayi sadakar uku washe gari suka dawo.

?arshe dai kuWin da Fatuu ke tarawa canza ra'ayi tayi tunda an kai Baffan nata makka ta yanke buWe Foundation da zata fara tallafa ma talakawa a Katsina, koda Fanan taji niyyarta nan tace itama tana so su buWe tare Haisam daya ji ya basu goyon baya harda gudunmawa, haka su Mom harda Hajiya Maryam da President duk suma sun basu gudunmawa, daga baya aka buWe Foundation Win mai suna HAIFAT FOUNDATION, bayan buWe shi a hannun Gwaggo suka dam?a kula da shi su kawu Amadu da Tk da matansu su Haulat da Husnah suka zama masu taimaka mata wurin gudanar da ayyukanshi harda Aunty Mareeya da Feenah duk sun shiga cikin masu gudanar da ayyukan shi sai fatan Allah ya sanya albarka,

Bayan komawar President Ali kan mulki da shekara Waya da wasu watanni ne Hajiya ta kwanta rashin lafiya, farko daga zazza6i ranar wata lahadi ta tashi da shi bayan tasha magani ta ji ta samu sau?i, da daddare bayan ta kwanta ciwo ya dawo mata zuwa wayewar gari jikinta yayi zafi sosae lokacin da Tk ya dawo daga Masallaci ya je gaisheta kamar yadda yake yi kullum da ?yar ta amsa mashi sallama, bayan ya shiga a kwance ya isketa saman carpet tana sanye da Hijab da ?yar tayi ?arfin hali tayi Salla, jin yadda ta amsa mashi gaisuwar tana nishi dama gashi ya ganta a kwance ?asa yasa shi tambayarta kamar bata lafiya tace mashi tun jiya take jin zazza6i sama sama tasha magani to da daddare ya idasa rufeta yanzu ma da ?yar tayi salla yana jin haka da alamun tashin hankali yace bari ya fiddo Mota su tafi asibiti, batare daya jira jin mi zata ce ba ya mi?e da sauri ya nufi ?opar fita, bayan ya fito saida ya shiga yayi ma Husnah magana kan taje ta taimaka ma Hajiyar ta shirya sai su tafi asibitin tare, itama hankalinta ya Wan tashi jin Hajiya ba lafiya don da wuya kaji ciwo ya kwantar da ita kaji dai tana cewa bata jin daWi, bayan zuwan su Asibitin wanda suke zuwa ba 6ata lokaci aka dubata tare da yi mata aune aune bayan an turo result likita ya yi masu bayanin zazza6in malaria da typhoid ne ke damunta har saida Hajiya ta Wan yi mamakin jin harda typhoid, da likitan yace ko a bata gado don a dubata sosae ta kuma huta tace a'a adai yi mata abunda ya dace yanzu ta koma gida sai taci gaban da shan magani, bayan anyi mata allura an bata maguguna suka tafi, sai bayan da suka dawo Saude tasan da rashin lafiyar nata nan fa suka shiga bata kulawa kowa ya damu Hajiya ba lafiya Tk yace ko ya kira Haisam ya sanar mashi Hajiyar tace a'a kada a tada masu hankali zata samu sau?i in sha Allah, Amadu ne ya kira Tk kan ya fito su wuce wurin aiki yaga lokaci na niyyar ?urewa ya sanar mashi da Hajiya ce ba lafiya, Gwaggo na jin Hajiya ba lafiya suka taho harda Haulat da Amadun, gaba Waya duk kowa ya shiga damuwa gashi bata cin abinci sai Wan abu mai ruwa shima daga baya aman abunda tasha ta fara yi ganin haka yasa tk yace ko su koma asibitin tace mashi a'a dama haka zazza6i yake da naci ai zata samu sauki, wasa wasa saiga ciwo nata gaba maimakon a samu sau?i cikin kwana biyu sai gashi ya kai komai sai su Saude sun yi mata lokacin da Gwaggo tazo taga halin da take ciki ta tambayi Tk yan Abuja sun san bata lafiyar cikin damuwa yace Hajiyar ta hana a sanar masu Gwaggon tace ai ba biye mata za'ai ba, nan take ta buga ma Haisam waya ta sanar dashi da alamun tashin hankali ya tambayi abunda ke damunta ganin ko jiya sunyi waya da ita amman bai gane bata lafiya ba tayi mashi bayani, ana gama sallar Magrib sai ga Haisam Win ya iso Tk ne yaje ya Waukko shi tun suna kan hanyar zuwa gidan Dad Win shi da Hajiya Maryam suka kira suna tambayar ya isa ya jikin Hajiyar yace masu yana hanyar zuwa gidan, lokacin da yaga yanayin jikin Hajiyar bayan ya iso hankalinshi ya ?ara tashi don duk ta faWa da gani tana jin jiki Haisam Win yace ma Tk tun yashe ne bata lafiya cike da damuwa yace kwananta biyu nan ya sanar mashi yadda sukai da likita harda kwantar da itan da akace za'a yi ta?i, bayan Dad Winshi ya kirashi ya sanar mashi gaskiya tana Wan jin jiki Hajiya Maryam harda Vedio call suka yi taga Hajiyar nan fa hankalinta ya ?ara tashi tace ma Haisam gobe da safe zata zo ta Wauketa, a daren ranar mutanen da suka ji zancen ciwon duk da zullumi suka kwana, washe gari wurin ?arfe bakwai Hajiya Maryam ta iso nan ta hau su Tk da faWan ya tana rashin lafiya zasu ?i kira su sanar tunda ta fara ciwon, bawan Allah harda yar ?wallan shi yace mata Hajiyar ce ta hana don kada a tada masu hankali aikuwa ta ?ara balbale shi da faWa harda cewa ko don ba Mahaifiyarshi bace, wannan kalma ta saka shi fashewa da kuka, cikin halin ciwo Hajiya tace mata don me zata faWi mashi haka bata ji yace ita ta hana ba ko so take yay mata rashin biyayya ya?i jin Maganarta ganin ran Hajiyar ya 6aci ga kuma halin da take ciki yasa ta ba Tk Win ha?uri kan Maganar da tayi, wuraren ?arfe sha Waya suka tafi da Hajiyar Abuja aka bar su Tk da kewa da damuwa sai Addu'ar Allah ya tashi kafaWun Hajiyar suke, su Gwaggo ma duk sun damu haka yan'unguwa da yawanci duk basu san da Hajiyar bata lafiya ba sai yau da aka tafi da ita duk an damu yara da manya anata mata Addu'o'i.

Bayan zuwa da Hajiya Abuja a babban private hospital Win likitansu na Germany wanda yana Waya daga cikin likitocin da Shugaban ?asa ya maido nan wanda yana aiki a Asibitin Gwamnati sannan kuma ya buWe private hospital ya zuba ?wararrun ma'aikata wanda wasu abokan aikinshi ne a can, bayan anyi mata aune aune aka tabbatar da abunda akace yana damunta a Katsina suke damunta kuma ma da sau?i sosae nan aka tabbatar da jikinta yana bu?atar hutu sosae wata?il bata hutawa sosae ko tana yawan yin zurga zurga, ran Hajiya Maryam ne ya 6aci tace ita dama ba son zamanta take a Katsina ba kawai don ta nuna hakan take so tunda basu a kusa da ita dama ai abunda taga dama zatai tayi ba mai hanata ko aikin NGO da take da ?yar aka samu ta daina, ita dai Hajiya jin abunda likitan yace kawai tayi don tasan ita ba wata zurga zurgar da take yi, a Waki na musamman aka kwantar da ita sosae ake bata kulawa hatta zuwa dubata an ware lokacin da za'a rin?a zuwa don kada a dameta, bayan sati Waya sai gashi jikin nata ya fara yin kyau lokacin har massaging jikin ake mata ana kuma bata lafiyayyun abinci da zasu ?ara mata ?arfi da kuzari, bayan tayi satin su Tk da Gwaggo suka zo dubata harda Amadu gaba Waya sunji daWi ganin yadda ta fara samun sau?i ba kamar Tk kullum da zullumin ciwon nata yake kwana duk ya damu kwanansu biyu suka koma, bayan sati biyu aka sallameta suka wuce Villa da ita, zo kaga murna Hajiya ta warke kowa sai farinciki yake duk sun haWu harda su Fatuu, a can Katsina ma sai murnar jin Hajiya ta samu lafiya ake, anan Villa aka cigaba da kula da ita tana shan magunguna, bayan tayi sati biyu ya kama watan ta guda a Abuja lokacin ta warke sosae har Wan ?ara jiki tayi da haske tace ma President tana son komawa Katsina nan fa ya shiga ro?onta kan ta ha?ura da zaman Katsina taci gaba da zama nan amman ta nuna mashi ita tafi son zaman can, koda Hajiya Maryam taji itama zuwa tayi suka haWu da President Win suna ro?onta kan ta zauna nan Hajiya Maryam harda yin ?walla tana faWin su basu son su rasata ne yanzu da basu yi gaggawar Waukkota nan ba da Allah kaWai yasan mi zai faru Hajiyar na murmushi tace abunda Allah ya ?adarro shi zai faru da lokacinta yayi sai ta tafi kuma a tunaninta su suka sa ta warke ne, Hajiya Maryam Win tace eh duk da hakan dai gara ta zauna anan tafi samun kulawa, ?arshe dai saida suka yi nasarar tursasa mata ta dawo nan amman tace masu dole zata koma tayo sallama da mutane Hajiya Maryam harda cewa in don wannan ne ai sai suje rana Waya tayo su dawo tace a'a tana bu?atar lokaci ba wai daga taje zata dawo ba don haka a?alla zata yi wata guda Hajiya Maryam tasa rigimar gaskiya yayi yawa da ?yar aka tsaya kan sati biyu shima saida Hajiyar ta kafe kafin ta amince, kafin su tafi ne tace tana son bar masu wasiyya ko ba yanzu ba in ajali ya risketa tana son kada su tada Tk daga gidanta koda zasu yi amfani da gidan to a ware mashi isasshshen wurin da zai zauna ta bashi halak malak sannan su Saude ma a barsu suci gaba da zama har sai in su suka bu?aci tashi ko kuma su in suna bu?atar su tashi to sai su siya ma Sauden gida, gaba Waya suka haWa baki wurin cewa in sha Allahu zasu yi kamar yadda tace Hajiya Maryam tace amman ta daina faWin wasiyyar nan tana tada masu hankali, Hajiyar tayi yar dariya tace to miye abun tashin hankali abunda ya zama dole da lokacinta yayi kuma su ai yan gata ne tunda sun rayu da ita tsawon lokaci wasu da yawa ma basu san Mahaifiyarsu ba, Hajiya Maryam Win tace duk da hakan dai suna ro?on Allah ya yasa su cigaba da rayuwa da ita tsawon lokaci tana murmushi ta amsa da Amin, bayan kwana biyu ta dawo Katsina harda First Lady da Aunty suka rakota, zo kaga murna Hajiyar Sanata ta dawo kar ma su Tk gaba Waya bakunansu sun ?i rufuwa dama Tk kusan yafi kowa shiga damuwar ciwon nata zuciyarshi tay ta raya mashi kodai mutuwa Hajiyar zata yi shi bama damuwar shi makomarshi ba a'a yadda zai rayu babu ita shine yafi tada mashi hankali don ba ?aramin sha?uwa yayi da ita ba ko Mahaifiyar shi bai jinta a ranshi kamar yadda yake jin Hajiya, Mutane sai so suke su shigo gidan suga Hajiya amman ba dama don ?opar gidan dankam take da Security wasu kuma sun zagaye gidan wanda babu wasa a tattare dasu gasu da manyan makamai, su Gwaggo dai sun shiga har sun gaisa da Mom da Aunty sun masu ya maijiki, haka manyan mutane mata da maza da yan siyasa sun zo duk an barsu sun shiga sun gaisa da su Mom tare da yi masu ya mai jiki har Governor da First Lady Win Katsina sun zo unguwa fa ta Winke ba abunda kake gani sai motoci masu numfashi da jiniya, Washe gari su Mom suka tafi bayan tafiyarsu ne Tk ya faWi ma Hajiyar mutane yan unguwa nata son su shigo su gaishe ta an hana su, tana jin hakan ta bada iznin duk wanda yazo a barshi ya shigo nan fa yan unguwa sukai ta shigowa dubiya manya da yara da dattawa Hajiya tayi amfani da wannan damar duk wanda yazo gaidata sai tayi mashi bankwana ta nemi yafiya, gaba Waya gwuiwar mutane sai tayi sanyi kuma jin Hajiyar zata bar Katsina harda masu yin ?walla tun ma ranar tafiyar bata yi ba, kowa ya nuna rashin jin daWin tafiyar da zata yi tana ta ce masu kada su damu ai ba shikenan an rabu ba indai da sauran rayuwa za'a cigaba da zumunci kuma ga Tukur nan zai cigaba da zama a gidan don haka ba abunda zai fasu tsakaninsu, tunda su Tk da Saude da Husnah suka ji zancen komawar Hajiyar Abuja gaba Waya suka shiga damuwa kowa jikin shi yay sanyi, bayan dawowarta da sati Waya ne ranar Friday da daddare ta kira Tukur da Saude a cikin Bedroom Winta, a kan carpet suka zauna ita kuma tana zaune a bakin gado idanunta sanye a cikin gilashi, sun Wan Wauki lokaci shiru tana ta kallonsu su kuma duk sun sunnar da kai yayin da ?irjinsu ke bugawa tamkar ana masu luguden ta6are can Hajiyar ta nisa kafin a nutse ta fara magana,

"Na bu?aci ganin ku ne don yin maganar da nasan bazaku ta6a jin daWin ta ba kamar yadda nima ba don daWin yasa zanyi maku ita ba, da farko dai ina mai matu?ar godiya a gare ku godiya mara iyaka, gaba Wayan mu bamu da wata dangantaka ta jini face ta kasancewar mu musulmai amman Allah ya haWamu muka zauna tare tsawon lokaci har muka zama tamkar dangin juna, ina son ku sani, ku mutane ne masu matu?ar muhimmanci a gare ni wanda wasu ma da yawa da nike da ala?a ta jini dasu basu da irin muhimmancin a wurina, Tukur, kai tamkar Wan dana haifa kake a wurina duk da kafi kama da jikana amman kallon Wana na jini nake maka, haka kema Saudatu ina m?????&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&'atu?ar jin ki a rai na ba kuma don hidimar da kike man ba sai don ?aunar ki a gare ni wadda nasan ita tasa kika zauna tsawon lokaci kina hidimta man ba tare da gajiyawa ba kuma daidai da rana Waya bazan iya cewa ga lokacin da kika sa6a man ta hanyar yi man rashin biyayya ko makamancin hakan......to, gaba Waya dai ba abunda zance sai dai ince maku Nagode, Nagode Allah ubangiji ya saka maku da mafificin Alkhairinsa ya ji6anci al'amuranku, ina kuma ro?on shi da yadda ya haWa mu a gidan duniyar nan ya haWa mu a gidan aljanna muci gaba da yin rayuwa tare, nasan bazaku rasa jin zancen komawata Abuja ba duk da bamuyi maganar da ku ba kafin yanzu, nasan dole kuji ba daWi amman ina mai baku ha?uri dama haka rayuwa ta gada in har aka haWu to tabbas wata rana sai an rabu koda kuwa ba mutuwa ba, don haka inason ku kwantar da hankalinku dan na tafi ba yana nufin an rabu ba kenan indai da rayuwa dole aci gaba da zumunci, kai Tukur zaka cigaba da zama a gidan nan koda kuwa bayan bani a duniya kana da kaso a cikin sa so nike Hajiyar Sanata taci gaba da wanzuwa ta dalilin ka, haka kema Saudatu zaku cigaba da zama keda mijinki har zuwa lokacin da kuke so ke bazance ki zauna dundundun ba saboda yanayin aikin mijinki a koda yaushe za'a iya canza mashi wuri dama ni na ro?a aka bar man shi tsawon lokaci muna tare ba'a Wauke shi ba saboda ina jin daWin zaman shi sai kuma yazo ya aure ki aka ?ara zama Waya...., akwae gida da nike son siya maki koda bani ba na faWa za'a siya maki in kun bu?aci barin nan, A ?arshe ina mai ?ara godiya a gareku sannan ina ro?on yafiyarku saboda ance zo mu zauna zo mu sa6a indai nayi maku ba daidai ba da sani na ko akasin hakan ina mai ro?on ku da ku yafe man ni dai na yafe ma kowa sannan ina mai ro?on ku da kuci gaba da kyautata ma abokan zaman ku",

Saida ta gama Magana ta fahimci gaba Waya kuka suke jin sheshshekarsu tay shiru tana kallon su dama itama ?arfin hali kawai take, bayan wani lokaci tace "To duk kun tasani a gaba kunata kuka ko nima so kuke Wan ?arfin halin da nike in karaya in sa kukan ne?" a tare suka haWa baki cikin muryar kuka suka ce "a'a......" tace to su daina suyi ha?uri don Allah tun farko tasan dama dole suji ba daWi to amman sai ayi ha?uri wata?il dama Allah ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login