Showing 435001 words to 438000 words out of 513411 words

Chapter 146 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16751

tay tace "Wllh baida wata matsala gaba Waya yadda nayi tunanin shi ba haka ba, sosae yake sake man yana bani kulawa dana nuna inason abu sai yayi man in kuma na nuna banso shikenan, kamar farko kinga mata na kiranshi har ya amsa wayar a gabana tunda na nuna 6acin raina shikenan ya daina lokacin harda bani ha?uri don fushi nayi dashi duk ya ruWe tun daga lokacin bai hana ni Waukar wayar shi da kaina nabi na goge duk lambar wata mace da sa?onni kuma bai ce man komai ba, ko tari nayi sai ya tambaye ni lafiya haka in ina wani abun yana taya ni duk da ba wani aiki ma nike ba da nace ya sallami mai mashi girki in rin?a yi to yanzu saboda cikin nan ma yace ba za'a sallame shi ba harda mace ma ya ?aro man da take man aikin gida",

tunda ta fara magana Fatuu keta faman sakin murmushin farinciki har ta gama tace amman taji daWin labarin nan sosae wllh wani hanin ga Allah baiwa ne da bawa yayi ha?uri sai yaga ya kai matakin da bai ta6a zato ba,

"Bari Zarah, kullum cikin gode ma Ubangiji nike wllh don yayi man ni'imar da zatona bai ta6a zata man ba, wani lokacin cikin raina sai in ta raya yanzu da nayi rashin ha?uri lokacin da aka yaudare ni na illata kai na koma na halaka kai na da shikenan nayi asara biyu gata rasa wannan babbar ni'imar ga kuma rasa ta ubangiji" girgiza kai Fatuu tay tace idan mutum yay nazari sau da yawa abubuwa masu daWi suna samuwa ne daga marasa daWi ita kanta ji yadda al'amarinta da Ya Haisam ya kasance data yi ha?uri gashi tanata cin ribar hakan tuni ma ta manta da irin raWaWin data ji a wanccan lokacin, Fauzy tace hakane ha?uri kaWan ke haifar da jin daWi na har abada sannan rashin ha?uri kaWan na haifar da dana sani na har abada, nima dai mai rubutun nace wannan haka yake Allah ya ?ara mana ha?uri Amin, Hira suka cigaba da yi cike da nishaWi har Fatuu na mata Addu'ar Allah yasa ta haifi yan biyu tana dariya tace haka ma Aunty Mareeya tace amman ita tafi son Wayan ma. Ana gama sallar Magrib aka fara shirin kai Mino Fatuu tasa ta canza kaya bayan tayi wanka zuwa lace baiwar Allah duk tayi zuru zuru Gwaggo tazo ta tafi da ita baya wurin danginsu don ayi mata Nasiha,, bayan an kawo motoci bakin entry hall aka sanar a fito Fatuu ce ta kamo ta suka nufo cikin babban parlon gidan lokacin su gwaggo ma duk sun fito suna biye dasu, bayan sun shigo Gwaggo ta kama Minon suka nufi part Win Mom harda su Yaya, a falonta duk suka zazzauna bayan an gaggaisa Gwaggo tace sun kawo amarya ne suyi sallama sannan su dam?a amanarta duk da sun san ko basu bada ba za'a ru?e masu amanarta kamar yadda aka ru?e ta yar uwarta sannan sai anyi ha?uri don zata iya yin wani abu ba daidai ba saboda ?arancin shekarunta in tayi kuskure a nuna mata duk da akwae yar'uwarta saidai itama ba wata babba bace kuma ba lalle su kasance tare ba gaba Wayansu dai duk sukai ba daidai ba a kwatanta masu don su gyara Mom na murmushi tace insha Allahu kada suji komai za'a ru?e amana yadda yakamata sannan yadda suke nuna ma yaransu in sun yi ba daidai ba suma hakan za'a yi masu tunda suma tamkar Ya'yansu ne, sosae suka ji daWin Maganarta sukai ta godiya tare da yi masu Addu'o'i daga baya suka fito don tafiya Mom Win tayo masu rakiya, cikin masu zuwa harda Hajiya Zainab da Hajiya dasu Aunty Mareeya da Feenah kusan duk mutanen da suka rage zasu je Motocin da aka kawo sun kai goma, bayan duk an shishshiga harda akwatunan kayan da Minon tayi amfani dasu waWanda su Yaya suka taho dasu kuma da sauran kayan an kai su can gidanta, a tare Motocin suka fara tafiya suka tunkari gate, ba wata tafiya mai nisa sukai ba suka iso gidan dake a Asokoro dama gidan Senator Win a Maitama yake basu da nisa sosae, tun a bakin gate zaka fara shaida haWuwar shi bayan mai gadi ya buWe masu motocin suka kutsa kai ciki, wuri daban daban akai parking don asamu duk Motocin su shiga wasu a cikin parking space Win gidan mai Waukar motoci huWu aka shigar dasu wasu daga can gefe gefe Motar da Minon take ciki har cikin entry hall aka shigar da ita, bayan an samu duk Motocin sun shigo aka bubbuWe kofofin motocin aka fara fitowa nan fa aka shiga bin gidan da kallo waWanda basu san shi ba, ba laifi gidan yana da girma tunda har harabar shi ta Wauke duka motocin hasken Fitilu ko ta ina ga shukokin fulawoyi wurare daban daban a tsare sun sha gyara, daga bakin gate akwae Wakin mai gadi sai Wayan bangaren nan parking space din yake sannan gaba Waya harabar gidan malale take da interlock daga tsakankanin su anyi adon ratsin grass carpet, bangaren ginin gidan kuwa tun daga cikin entry hall aka malala tiles ga wata babbar fitilar sama mai matukar kyau a saman daga nan zaka shiga cikin gidan ta dakakkar ?opar da ke a wurin, kana shiga Wan passageway ne wurin shima akwae fitila a sama da kuma flower vases sun saka ?opar shiga falon tsakiya ana buWeta za'a shiga cikin parlon wanda babba ne yasha manyan labulai maroon da akai ma wani irin design mai Waukar hankali, gaba Waya parlon tiles ne ruwan madara kalar fentin falon daga tsakiya aka saka kujerun Mino wanda haWaWWun royal ne brown da Wan ratsin maroon an jere throw pillows, daga tsakiyarsu lallausan carpet ne brown tsakiyarsu an aje Ottomon kalar yadin kujerun daga angles Win parlon an aje flower vases da suka hau da kayan ciki sai bangaren wurin kayan kallo an manna babbar plasma Win da aka siya mata a jikin babban Tv stand mai drawers ta kwance da kuma ta tsaye shima cikin saitin kayan yake daga baki bakin shi anyi mashi irin design na adon da aka ma kujerun daga gefe da gefen Tv stand Win sound systems ne, iya wurin kayan kallon abun kallo ne, daga can bayan kujerun matattakalar hawa bene take anyi mata wani irin design ta lan?waya ?arafan jiki silver ne sai Waukar ido suke itama matattakalar anyi mata fenti ruwan madara kalar na cikin parlon sannan an shimfiWa carpet brown yabi jikin stairs Win har sama, daga gefen hagun benen Dining Area ce an aje dining table da kujerun shi guda haWu suma mahaWin kujerun parlon ne, daga can gefen shi nan aka aje standing freezer daga gaban shi anan ?opar shiga Kitchen take daga jikin Wayan bangon wurin wani haWaWWan console ne golden manne daga gefe da gefen shi an aje flower vases sosae wurin yay kyau daga ?asan Dining table Win nan ma lallausan carpet ne maroon da ratsin brown, daga tsakiyar parlon bayan kujerun corridor ne inda bedrooms suke guda biyu suna kallon juna da toilet a tsakiya ba laifi Bedrooms Win suna da girma a Waya Royal Bed ne Milk da wardrobe Win shi mai guda shidda a jikinta anyi adon madubi kana ganin kanka haka a jikin bedside din ma gaba Waya set Win kayan sun haWu ba ?arya wani irin design akai masu mai jan hankali a ?asa an sa carpet milk, a Wayan Wakin kuma Simple Modern Bed ne Coffee brown da wardrobe Win shi mai gida hudu sai nightstands da dressing mirror daga gaban gadon an sa carpet coffee labulayan Wakin ma coffee ne, kowanne Waki akwae toilet irin na zamani irin wanda ya amsa sunan toilet Win masu kuWi komai na cikin shi fari da silver ne, a 6angaren Kitchen kuwa drawers Win ciki L-shape ne dark ash haka cupboards Win sama suma L-shape ne an tsara Kitchen Win shima yayi kyau sosai, Bayan yan kawo Amaryar sun shigo ciki nan fa aka hau jinjina haWuwar gidan Gwaggo sai murmushin daWi take haka Fatuu ma su Yaya da Kakar su Minon mamaki ne shimfiWe akan fuskokinsu ganin wai wannan Aljanar duniyar Mino zata zauna gaba Waya sun kasa rufe bakunansu, yadda aka shirya komai yayi ma su Gwaggo kyau sai yabawa suke, a Waya daga cikin Wakunan aka kai Mino inda keda Royal Bed su Aunty Mareeya suka fito suna ?ara dudduba gidan danginsu Nameer suma suna ta yabawa suna faWin gaskiya anyi ?o?ari da yake sunji Hajiya na magana kan kayan da akayin tana faWin sun kashe kuWi sosae hakan yasa suka gane danginta sukai mata kayan Wakin hatta Hajiya Zainab saida tace gaskiya anyi ?o?ari, har saman bene suka hau wanda nan part Win Nameer ne babban falo ne an zuba luntsuma luntsuman ba?a?en leather chairs da ?aton carpet ba?i da ratsin ruwan toka mai duhu da kuma mai haske sai labulaye suma ba?a?e ne da ratsin ash akwae kuma kayan kallo harda freezer falon baida hayaniya amman yayi kyau sosae, Bedroom guda Waya ne mai Wauke da set Win gado Wan Dubai sai toilet ko ina dai yayi kyau sai yabawa ake, har bayan gidan suka je akwae wurin yin basket ball da kuma Wan madaidaicin Swimming pool daga gefenshi kuma akwai rumfa ta sha?atawa mai Wauke da tebur da folding chairs irin wanda ake linkewa, bayan sun gama zazzagaya gidan Aunty Mareeya da Fatuu suka Waukko kwalin kayan adon da aka kawo suka fara jera su a jikin gidajen Tv stand wasu kwalaben turaren wuta ne an masu ado wasu kuma kayan ?awata wuri ne kowanne aka sashi a inda ya dace sosae falon ya ?ara ?awatuwa suka jona wata jigunannar burner aka saka turaren wuta nan da nan ?amshi mai daWi ya fara karaWe parlon ya haWe da sanyin A.c, su Amadu ne suka shigo da katan katan na lemuna da abubuwan ci suka aje a saman carpet Aunty Mareeya tace sannunsu abokan ango sukai murmushi kafin suka shiga bin falon da kallo suna murmushin daWi don ya burge su Hajiya ce tace masu to su zagaya mana su gani da kyau suka ce to, zama sukai kan kujeru suka fara cin abubuwan da aka kawo ana Wan yin hira Hajiya tasa Fatuu ta Wiba ta kaima Mino da ?awarta dake a cikin Bedroom, suna cikin ci Hajiya ta kalli Gwaggo tace wato Dije kwance kwance ashe kuWi ne daku ko shiyasa kuka zuba ma Ameenatu kaya haka duk aka yi dariya Hajiya Zainab dake cikin cin Shawarma tana murmushinta na manya tace ba Fulani bane su Hajiya tace sune na asali ma tace ai dama kuWi garesu da an saida shanaye sai kaga uban kuWi duk akai dariya Gwaggo dai murmushi kawai take don an kashe bakin, bayan wani lokaci suka mi?e don tafiya wasu suka fita wasu kuma suka je yin sallama da Mino harda Gwaggo da Hajiya dasu Aunty Mareeya, ai tana jin zasu tafi ta ruWe ta saka kuka duk tabi ta ?an?ame Gwaggo aka hau bata ha?uri Hajiya tace Ameenatu sai kace an kawo ki gidan yari, sam ta?i jin rarrashi sai fullanci take tana ce ma Gwaggo don Allah kada a barta ita kaWai su tafi da ita Fuskarta duk tayi jage jage da hawaye har saida tasa idanun Gwaggon suka ciko da ?walla ita Fatuu ma har sun fara zubowa Hajiya ta tambayi Gwaggo mi Minon ke cewa ne ta faWi mata wai su tafi da ita tay Wan murmushi tace ina su ina tafiya da ita ai nan gidantane tazo kenan tayi ha?uri zata saba, ganin ta?i jin rarrashi yasa Hajiya ta kira Nameer a waya bayan ya Waga ta tambayi yana ina yace gasu nan a harabar gidan tace to ya shigo ya samesu a Bedroom yace to, bada jimawa ba sai gashi ya shigo cikin Wakin da sallama yana sanye da riga da wando na Farar shadda fuskar nan sai annuri take ga uban ?amshi dake tashi daga jikinshi, gaishe dasu yay bayan sun amsa mashi Hajiya ta nuna mashi Mino tace gata nan yazo ya rarrashi matar shi ta hana su tafiya wai bin su zatai, kai idon shi yay kan Minon da tabi ta ?an?ame Gwaggo ta kifa Fuskarta a jikinta, tsaye yay kawai yana kallon su Hajiya tace yaje ya kamata ko sun tafi in kuma so yake su kwana to still bai matsa ba don kunyar yaje ya kamata yake sai Wan murmushi yake ganin haka yasa Fatuu ta kai hannu ta Wago da ita suka haWa ido tace mata ya isa ta daina kukan ita zata zauna tare da ita jin hakan yasa ta faWa jikin Fatun Hajiya tace masu su tafi, bayan duk sun fita ya rage saura Fatuu da Safnah sai Nameer da hannu Fatuu tay mashi alamar yazo ya rarrasheta, Moving yay zuwa inda suke ya tsaya a gabansu cikin kwantar da murya ya kira sunanta shiru bata amsa ba bata kuma Wago daga jikin Fatun ba, hannu ya kai ya fara ?o?arin Wago da ita ta turje su Fatuu nata bata ha?uri ganin ta?i rabuwa da jikin Fatuu yasa shi nuna mata ?arfi ya Wagota da ?arfi tana barin jikin Fatun da sauri ta kamo hannun Safnah suka nufi hanyar fita daga Wakin Minon nata rizgar kuka tana ?o?arin kwacewa ta bisu hakan yasa shi haWeta da jikin shi ya rungumeta tightly ya kai bakin shi saitin kunnanta a hankali ya shiga rarrashinta yana faWin ba gashi tare da ita ba, sukuku Fatuu ta dawo duk tausayin Mino ya kamata daga baya ta sake suka shiga yin hira da Fauzy kowa na tuna lokacin da aka kai shi Wakin miji Safnah dai har ta kwanta don itama jikinta yayi sanyi saboda yanayin da suka baro Aminiyarta, suna cikin yin hirar Sameer ya kira Fauzy ta Waga kiran, tambayarta yay tana ina tace gata nan sun dawo gidansu Ya Haisam yace Ok gashi nan zuwa zai dauketa tace to, bayan sun gama wayar Fatuu na murmushi cike da tsokana tace su Fauzy ana waya da miji an wani kwantar da murya dariya tayi tace ai saida hakan, faWi mata tay zai zo ya Wauketa ne Fatun tace maimakon tace mashi zata kwana anan su kwana tare Fauzyn ta Wan buWa ido tare da jinjina kai tace ai tasan ko tace haka ba lalle ya bari ba Fatuu tace bai iya kwana ba tare da ita ba kenan,

"Kusan hakan, kinsan fa koda muna London bayan mun dawo daga Honeymoon in zaije wani wuri indai kwana zai yi dani yake tafiya, ai Honey ba sau?i sai da na samu cikin nan ne ganin ina wahala ake Wan raga man" Fatuu na dariya tace ai hakan ake so a damu da kai sai ta dage taita gyara kanta don ma halin da take ciki ba komai zata iya sha ba Fauzyn tace eh tama daina shan wani magani Aunty ma tace a halin da take ciki ba sai tasha komai ba, bada jimawa ba Sameer Win ya kirata ya sanar mata gashi a gaban entry hall, tare da Fatuu suka fito tayo mata rakiya suna ?arasowa gaban Motar ya buWe Motar tun kafin ya idasa fitowa ?amshin turarenshi ya karaWe wurin, sanye yake cikin ?ananan kaya Fuskarshi tayi wani irin Fresh har yar ?iba ya ?ara da yake wurin fayau yake da haske, bayan ya fito gaisawa sukai da Fatuu fuskarshi a sake yay mata ya hidima ta amsa da Alhamdulillah yace Allah yasa alkhairi, bayan ta amsa ya ambayi ina yaranshi tace suna wurin Mom yace a gaishe mashi dasu, maida idon shi yay kan Fauzy data jingina da Motar ta langa6ar da kai slowly yace "hope u'r Ok?" lumshe mashi ido tay ta Wan Waga mashi kai yace to suje tare da yi mata alama da kai, tare suka zagaya Wayan bangaren ya kai hannu ya buWe mata ?opar saida ta juyo ta kalli Fatuu dake tsaye tana ta murmushi ta Wan Waga mata hannu itama ta Wago mata sannan ta shige ya maida ?opar ya rufe bayan ya zagayo driver side yayi ma Fatuu sallama ya buWe ya shige, saida yaja Motar sannan ta juyo komowa cikin gidan tanata murmushin daWi ganin yadda Sameer yake kulawa da Fauzy harda su buWe mata ?opa abunda bata ta6a zaton zai yi ma mace ba, bayan sun hau titi sosae ya juya ya kalli Fauzy data kwantar da kanta jikin headrest ya kai hannun shi dake gefenta ya kamo nata daga yadda take ta juyo da kan ta kalle shi yace mata ko jikin ne ta girgiza mashi kai alamar a'a ya sake cewa ko tana jin yunwa ne nan ma ta girgiza mashi kai yaci gaba da driving da hannu Waya Wayan kuma yana ru?e da nata can bayan wani Wan lokaci ya sake juyowa ya kalleta ya tambayi ko tana son wani abu ta Wan yi shiru kafin tace tana son ice cream yay Wan shiru tare da maida idon shi kan hanya taji yace tana shan abu mai sanyi sosae ba ba'a son suna sha ba, Wan yamutsa fuska tayi ta sigar shagwa6a tace to ai cikin ne yake mata zafi sai tasha abu mai sanyi take jin sau?i ya jinjina kai, a bakin wani babban cold store ya parker tare da buWe Motar yace mata yana zuwa ta Waga mashi kai, nufar shiga wurin yay tanata kallon shi ta glass wata irin ?aunar shi na ratsata, After few minutes ya fito ru?e da leda mai tambarin wurin ya dawo wurin Motar, bayan ya shiga ya mi?a mata ta amsa tare da furta "thank you Honey" jinjina mata kai yay ya ja suka tafi, bude ledar tayi ta fiddo roba Waya bayan ta buWeta fara sha, tana cikin sha ta Webo ta kai bakin shi idon shi akan hanya ya buWe ta zuba mashi bayan ya shanye ya furta mata "Love you Babes" tana murmushi tace "love you

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login