Showing 456001 words to 459000 words out of 513411 words

Chapter 153 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16815

fara zama daga baya saboda rashin jituwar da suke samu da matarshi ta baro mashi gidan tazo ta gina wannan da take ciki a filin da suka gada, nan ta bashi labarin yadda mahaifiyar Fatuu tayi aure ta haifesu su biyu da yadda Gwaggon ta Waukko su ta ri?e ta kuma shiga nuna mashi kyawawan halayenta, ajiyar zuciya Kawu Mani ya sauke ya sake kallon hoton gwaggon kafin ya mi?a ma Hajiya wayar ta amsa tare da tambayar tayi mashi ko kuwa yana yar dariya yace tunda tayi mata tana son ya aureta in dai zata amince zai auretan,

"A'a ba wani tunda tayi man inason ka aureta salon kaja man matanka su ?ullace ni, kawai in kaji kana son ta zaka aureta to in kuma bata yi maka ba lafiya lau ka fito ka faWi man ai ba wani abu bane dama don naga kana da ra'ayin mata fiye da Waya ne tunda yanzu haka biyu gareka shiyasa nayi maka Maganarta" sosae yake dariya jin abunda tace bayan ya tsagaita yace to yanzu koda tayi mashin in ita ta?i amincewa dashi fa tunda tace tana da masu son aurenta itace bata so Hajiyar tace ai sai suma su jaraba sa'ar su ?ilan Allah yasa ta amince dashi, gyaWa kai yay yace to yanzu ya za'ai tasan dashi,

"Wannan mai sau?i ne in ka shirya haWuwa da ita kuyi magana sai in kirata in mata magana", yar ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi yace abunda za'ai yanzu zai kira mahaifin ita wadda tukur ke so yayi mashi maganar haWuwarsu in ya bashi dama da yayi sallar la'asar sai ya tafi yanzu abunda za'ai tayi ma ita Matar magana in ya fita sai ya fara tsayawa wurinta su gaisa kafin ya wuce, wani kallo Hajiya tayi mashi tace "Humm, su Mani anga farar fata har an zurma da anaso ai man bariki" Dariya ya 6a66ake da ita harda buga ?afa yace "Sai Hajjaju mai dalilin aure, saboda dai kina so ne kawai"

"To tunda hakane a barshi kawai na janye....." da sauri ya katseta "a'a Hajjaju ba'a yi haka ba tunda dai kinyi niyyar haWawa kada kima kan ki bu?ulun lada ki kiratan kawai sai inje mu gwada sa'ar" wani kallo mai kaman harara tayi mashi ya saka dariya, ce mashi tay ya bari ayi sallar la'asar Win zata kirata Kawu Manin harda ce mata to ai kada ta fita unguwa Hajiyar na dariya tace ya dawo wani lokacin,

"gara dai ayi komai yau hajjaju kinsan ance da zafi zafi ake dukan ?arfe" Dariya Hajiya tay tare da girgiza kai, bada daWewa ba aka kira sallar la'asar ya mi?e don yaje masallaci itama Hajiya ta tashi tana ru?e da sandarta ta nufi hanyar Bedroom don taje tayi sallar, bayan ta gama ne ta kira layin Gwaggo wayar na fara yin ringing ta Waga cikin girmamawa ta gaishe da ita tare da yi mata barka da juma'a bayan Hajiyar ta amsa ta tambayi tana gida tace mata eh bata daWe data dawo bama daga wurin aiki, an dawo lafiya tayi mata Gwaggon ta amsa da lafiya lau Alhamdulillah,

"to ga ba?o nan na turo zai zo ku gaisa" Wan jimm Gwaggo tay a ranta ta maimaita abunda Hajiyar tace kafin ta amsa mata da to sukai sallama, zugudum Gwaggo tay ru?e da wayar tana ta nanata zancen zuwan ba?on don abun sai taji shi wani iri saboda basu ta6a haka da Hajiyar ba wai tace mata ga wani nan zai zo su gaisa, Bayan sun gama yin wayar fitowa Hajiya tayi cikin falon kusan a tare suka dawo da Kawu Manin, bayan sun zauna ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa tace yayi na yara duk sukai salla sai sun gaishe da mutum shima murmushin Yay yace ai haka yakamata kafin yace mata yanzu bayan ya fito ya kira Mahaifin yarinyar har ya bashi Address zai je ya same shi daga can zai wuce Daura duk yadda sukai dashi zai sanar mata ta amsa da to tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya, shiru suka Wan yi bai mi?e ba can yace mata bata kirata bane tay dariya tace ai ta zata ya manta yaje ta kirata a waya, tambayar inda gidan yake yayi ta kwatanta mashi da shagon Amadu tace in yaje yaronta ne mai shagon sai yasa shi yaje yayi mata magana ya amsa da to tare da mi?ewa tana murmushi tace Allah yasa taji Alkhairi ya amsa da Amin ta ?ara cewa zata turo mashi kuWi yanzu sai ya zuba mai yayi mata godiya itama tayi mashi da fatan Allah ya kiyaye hanya tace ya gaida iyali daga aka ya fito,

A daidai shagon Amadu ya parker Motar shi lokacin basu daWe da dawowa daga Masallaci ba, fitowa yay bayan ya kulle ?opar Motar ya tunkari shagon, a gaban shagon ya tsaya fuskarshi Wauke da murmushi yayi masu Sallama tunda ya fito Amadun ke kallon shi yana ganin kaman ya sanshi saida ya ?araso gaban shagon ya gane shi shima Amadun murmushin ya mayar mashi bayan ya amsa sallamar cikin girmamawa ya gaishe dashi Kamalu ma dake zaune kan plastic chair yana latsa waya ya Wago kai ya gaishe dashi shima da murmushi ya amsa mashi, tambayar waye Amadu a cikin su yayi Kawu Amadu yace shine ya nuna Kamalu yace to shi kuma wannan fa ya bashi amsa da Wan Yayarshi ne,
"Kenan Wanka ne" Amadu na murmushi ya bashi amsa da eh,

"Ko shine Yayan Matar Haisam" da sauri Amadun yace mashi eh,

"Allah sarki, Allah yayi maku Albarka ya ji?an Mahaifiyarsu da Mahaifin ka" a tare duk suka amsa mashi da Amin,

"Yauwa ka shiga ciki kace ga ba?on ya iso" ya faWa still da murmushi akan fuskarshi, da alamun rashin Fahimta Amadun yace wa zai faWi ma hakan Kawu Manin yace mashi ita mai gidan zaije yace ma ga ba?on da Hajiya tayi mata magana yazo da sauri ya amsa da to ya juyo ya buWe shagon ya fito, lokacin daya shigo gidan Gwaggon na cikin Wakinta tun bayan data yi waya da Hajiya dama tana kan abun salla ne bata tashi ba, da sallama ya shigo ta amsa tare da juyowa ta kalleshi ya sanar mata zancen zuwan ba?on tay Wan jimm kafin a hankali tace mashi ya shigo dashi falo yace to ya juya, shiru tayi a ranta ta shiga tunanin to wane ba?o ne kuma wace irin gaisawa zasu yi kaman yadda Hajia tace, tana jin lokacin da suka shigo Kawu Manin yay sallama, bayan ya shigar dashi yazo Wakin ya sanar mata gashi can a falo kai kawai ta Waga mashi ya juya ya tafi, mi?ewa tayi duk tayi sukuku ganin Hijab Win jikinta lafiya lou dama gogagga ce ta Waukko tayi sallar da ita ta nufi ?opar fita, lokacin data tunkari f????$$$$$$$ $
$ $ $
$$$$$$$$$$$$$$$$$$$ $!$"$#$$$%$&$'$($)$*$+$,$-$.$/$0$1$2$3$4$5$6$7$8$9$:$;$<$=$>$?$@$A$B$C$D$E$F$G$H$I$J$K$L$M$N$O$P$Q$R$S$T$U$V$W$X$Y$Z$[$\$]$^$_$`$a$b$c$d$e$f$g$h$i$j$k$l$m$n$o$p$q$r$s$t$u$v$w$x$y$z${$|$}$~$$?$alon gabanta har Wan faWuwa yake, da sallama ta saka kai cikin falon ?amshin turaren shi ya bugi hancinta yana zaune akan 2 seater ya Wago yana kallonta da murmushi ya amsa mata sallamar suna haWa ido ta gane shi ta nufi kujera mai mazaunin mutum Waya daga can gefen tashi ta zauna idon shi akanta yace mata "Barka da Fitowa", Wan murmushi tayi ta amsa tare da gaishe dashi yana ta murmushi ya amsa, kanta ne ya Waure ganin shine don bata ta6a zaton shi zata gani ba matsayin ba?on don tunda tasan Hajiya tasan shi yana zuwa gidan matsayin ?anin Hajiya tsawon lokacin kuma bai ta6a zuwa nan gidan ba sai yau, mi?ewa tayi ta nufi Fridge ya bita da kallo bayan ta buWe ta Waukko lemu da robar ruwa tare da glass cup bayan ta rufe tana juyowa suka haWa ido ta maida nata ?asa ta nufo inda Wan table yake ta Waura sannan ta Waukeshi ta matsar dashi gabanshi, buWe lemun tayi ta zuba a cikin cup Win ba tare data kalleshi ba tace gashi yasha yana murmushi ya furta "Shukran" Wan murmushi tayi ta koma inda ta taso, Waukar cup Win yayi ya kai baki saida ya kur6a kamar sau uku sannan ya aje tare da furta Alhamdulillah ya Waura idon shi kan Gwaggo dake kallon Carpet yace "Fatan na same ki lafiya, ya gida ya yara ya aiki kuma" Wago ido tayi ta kalleshi da Wan murmushi ta amsa mashi da lafiya lau Alhamdulillah shima ta tambayi ya nashi iyalin da aiki yana sakin ?ayataccen murmushi ya amsa mata, shiru suka yi can ta mi?e tace bari a kawo mashi abinci da sauri ya dakatar da ita yace lemun ma ya isa a ?oshe yake ta koma ta zauna,

"Yauwa, kamar yadda Hajjaju ta sanar maki ita ta turo ni don mu gaisa da juna kuma tunda mu ba yara bane nasan kin gane wace irin gaisawa ake nufi, ni dai na gan ki kuma kin mani don haka in an amince man Aure nike son muyi tunda duk naji duk wani abu dangane dake nima kuma in kina son sanin abunda ya dangance ni zaki iya yi ma ita Hajjaju magana da fatan za'a amince man" tunda ya fara Maganar ta sunkuyar da kanta har ya gama ta kasa Wagowa balle tace mashi wani abu, ganin ta?i yin magana yasashi ce mata ita yake saurare ta taimaka ta bashi amsa, gaba Waya ya Waureta ta rasa amsar da zata bashi don sai taji bata iya ?in amince ma bu?atar daya zo da ita kodan Hajiya gashi ita ta cire sake yin aure a ranta, a hankali ta Wago suka haWa ido tayi saurin kawar da nata kafin tace mashi tana bu?atar yin shawara ya Wan bata lokaci, yana murmushi yace "Har sai anyi shawara kuma, to kodai ban samu kar6uwa bane?" kallon shi tayi da Wan murmushi tace a'a kawai tana bu?atar yin shawara ne tunda tana da babban yaro, Wan buWa ido yay yace "dashi za'ai shawarar kenan karfa yasa a?i amince man don kinsan wasu yaran sukan taya iyayensu maza kishi" yar dariya tayi kawai,

"Yanzu har tsawon wane lokaci zan jira Hajiya" yay Maganar yana mata wani kallo da gani shima za'a dashi ta bangaren soyayya, tana murmushi tace malama dai ya wani Wage gira yace "Ni Hajiya na gani" shiru tay kawai tana murmushi ganin ya kafeta da ido tace mashi ko mi kenan zata sanar mashi ya furta Ok bari ya bata lambar shi amman don Allah kada a Wauki lokaci asa ya kasa samun natsuwa tace uhmm kawai, wayarta ya tambaya yasa mata lambar tashi ta mi?e tace bari ta Waukko tana Waki, bada jimawa ba ta dawo ta mi?a mashi wayar ya amsa yana murmushi ya Wan jujjuyata yace "amman Hajiya sai naga kamar kinfi ?arfin wannan wayar" murmushi tayi tace tafi jin daWin amfani da irinta ne yace to amman ga na zamani ai sai a ha?ura da tsohon yayi gaskiya yakamata a canza ta tace mashi tuntuni yara keson canza mata ita ce bata so,

"To ai yanzu sai aba maigida dama ya canza" da sauri ta kalleshi ganin kallon da yake mata yasa ta kauda fuskarta yace "na cika azar6a6i ko tun ba'a sanar dani matsayi na ba har na yanke hukunci, ayi ha?uri abunda rai ke muradi ne" juyowa tay ta kalleshi tana Wan murmushi, lambar tashi ya saka a tata ya kira kafin yayi mata saving tashi ya mi?a mata yace gashinan ya saka mata Alhaji Mani ya tambayi ita kuma Hajiya wa zai saka mata tace Dije ya Wan yamutsa fuska yace "Wannan na zamanin da ne bari in saka na zamanin yanzu Khadija ko kuma Khadijatul Khubra" Gwaggo bata san lokacin da tayi yar dariya ba shima ita yake yi bayan ya gama saving Win ya Wago ya kalleta yace "to Hajiya Khadija ni bari in zo in wuce inada wani uzuri da zan aiwatar kafin na hau hanya sai naji daga gareki ina fata kuma za'a duba man inji abunda nike fatan ji" murmushi kawai take, mi?ewa yay ya zura hannu cikin yan cikin babbar rigar shi ya fiddo kuWi masu Wan yawa ya Waura akan table Win yace gashi nan a ba Wan shi da jikanshi, da sauri ta kalleshi tace don Allah ya barshi yana mata wani kallo yace bata ji waWanda yace taba bane dole tayi shiru, tafiya ya fara yi zai fita daga cikin falon ta Wan juya tana kallonshi har ya kusa ?opa ya tsaya ganin zai juyo yasa da sauri ta kauda idonta tana haka taji muryarshi yana faWin bazata raka ba?on nata bane tay Wan jimm kafin ta kalleshi suka haWa ido yana mata murmushi, jiki a sanyaye ta mi?e ya furta yauwa ko ita fa ya juya tana biye dashi, saida suka kusa ?opar fita ya juyo yace to ya gode ta koma kada ya wahalar da Hajiya ta Wan yi murmushi tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya ya amsa, falo ta dawo ta zauna kan kujera tayi jugum ta rasa ma tunanin da zata yi ganin abun take kamar ba'a gaske ba duk da ba yau aka fara zuwa neman aurenta ba wannan sai taji yayi mata girma sosae ba kamar daya haWa da Hajiya, tana haka Amadu ya shigo da sallama ta Waga ido ta kalleshi ta amsa a hankali, nufo inda take yayi ya zauna a kujerar dake gefen tata ya Wan yi shiru yana kallonta kamar mai nazarin wani abu ita kuma ta kauda idonta daga barin kallonshi,

"Gwaggota lafiya kuwa?" taji muryarshi yana tambaya, kallonshi tayi da Wan guntun murmushi tace mashi lafiya lou yace amman to ya ya ganta kamar wani abu na damunta ta Wan yi shiru kafin tace mashi ba komai, shiru ya Wanyi yanata kallonta can ya sake tambayarta to lafiya Kawu Mani yazo gidansu yaga bai ta6a zuwa ba tunda suke a gidan, shiru Gwaggo tayi tana tunanin mi zata ce mashi ya kawo shin tunda gashi yasan bai ta6a zuwa gidan ba can zuciyarta ta bata kawai ta faWi mashi abunda ya kawo shi tunda dama ko ba yanzu ba dole zata faWi mashi, ajiyar zuciya ta sauke tare da kallonshi kaman mai zullumin faWi mashi shi kuma ya ?ura mata ido alamar ita yake jira tayi magana can dai tayi ?arfin halin faWi mashi Hajiya ce ta turo shi wai ya nemi aurenta, Wan waro ido Amadun yay kafin da sauri yace "to kin amince mashi zaki aure shin???" a hankali ta girgiza kai kafin tace ce mashi tayi sai tayi shawara amman ita....kafin ta ?arasa abunda take son faWin kawai sai gani tayi ya kamo hannunta yace "Don Allah Gwaggota ki amince mashi kada ki ?i kamar yadda kike yi a baya na ro?e ki, wllh ba wuce kiyi aure kikai ba tsofaffi tukuf ma zaki ga suna da aure tunda shi ibada ne, kinga in kika amince mashi muma a ?alla zai zama muna da Baba a cikin gidan nan" shiru tayi tana kallon shi ta wani bangaren ta Wan ji mamaki don bai ta6a nuna mata ya damu da tayi aure ba irin yanzu yawanci da anzo neman aurenta ta nuna bata so sai yace shikenan tunda haka take so, tana haka sai gani tayi ya saukko daga saman kujerar ya du?a a saman guiwowinshi cikin marairaicewa yace "Don Allah Gwaggota ko don ni ki amince mashi nima dai ace inada wanda zan kira da sunan BABA ba tare dana haWa da sunan shi ba, tun tasowa ta ba wanda nike kira da sunan Baba ba tare da nace Baba wane ba kamar Baba shehu, Baba musa da sauransu kinga yanzu in kika aure shi Baba zan rin?a kiranshi ba yadda za'ai in haWa da sunan shi nima a ?alla in muna hira da wasu zance Babanmu ka za...." kasa ?arasawa yay saboda ?wallan da suka tarun mashi suna niyyar zubowa, wani irin tausayinshi ne Gwaggo taji ya kamata tun yana Wan shekara shidda ya rasa mahaifinshi, girgiza hannunta yay ya furta "Don Allah Gwaggota..." ajiyar zuciya ta sauke tana ?o?arin ?a?alo murmushi tace "baka tunanin ba lalle ya zama kamar uba a garekan ba kamar yadda yake faruwa sau da yawa wasu ma sai kaga sun raba uwa da Wanta..." da sauri ya tari hanzarinta,

"A'a Gwaggo ina da ya?inin bazai yi hakan ba tunda kika ga Hajiya ta turo shi to tasan baida matsala ne, na tabbatar mutumin kirki ne ai ina ganin shi a gidan Hajiyar muna gaisawa, don Allah ki amince?" shiru tay tana kallon shi ?wallan idon shi har sun zubo mashi can tace shikenan tunda haka yake so zata amince mashi, da sauri ya mi?e ya zauna gefenta tare da ?an?ameta cikin tsananin farinciki ya shiga yi mata godiya harda su Kiss ya manna mata a gefen fuskarta ita dae sai dariya take zata iya cewa bata ta6a ganinshi cikin farinciki irin wannan ba in ma ta ta6a gani to ta manta, sakinta yay sai faman washe baki yake ya shiga laluban wayarshi yana faWin bari ya sanar ma Fatuu wannan abun Farinciki, da sauri Gwaggo tace kada ya sanar mata yace a'a yakamata ta sani da zafi zafi, ?o?arin amshe wayar Gwaggon tayi ya mi?e yana dariya ya shiga yin safa da marwa a tsakar falon cikin harshen fullanci Gwaggon ke faWin tana wasa dashi wai sai dariya yake itama yar dariyar take, tana fara yin ringing Fatun ta yanke sai gashi ta kira yana Wauka ko gaisawa basu yi ba da sauri yace mata Albishirinta a ?agauce ta amsa da goro fari ?al yace banda shi ango sun ?ara samun Amarya a gidansu nan ya shiga faWi mata zancen auren Gwaggo aikuwa wata uwar ?arar murna ta saki tana faWin Alhamdulillah abubuwan farinciki sai faruwa suke dasu Amadun yace Wllh kuwa da sauri tace mashi ina Gwaggon ya bata wayar bari ta maida Vedio call taga fuskar amarya yace to, duk Gwaggo na jin su da yake a speaker

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login