Showing 495001 words to 498000 words out of 513411 words

Chapter 166 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16699

ya fara bugu da sauri da sauri ta maida idonta ?asa,

"Sunana Na'eem, ni abokin Yayinki Haisam ne, inada mata da yara biyu sannan ina aiki da Central Bank, ban san ko na ta6a ganinki ba kafin yanzu tunda muna yawan kasancewa da Haisam duk wata hidima data danganci Family Win su ina zuwa saidai a wurina yau na fara ganinki zuwan mu nan, kuma cikin ikon Allah ina ganinki naji na kamu da son ki abunda bature ke cewa, Love at first sight, nayi ma shi yayan naki magana kan haka shine yace to in nemi soyayyar ki idan Allah yasa kinga nayi maki to zan aure ki da kin gama School sannan zan barki kici gaba da Karatun ki in sha Allahu" shiru bata ce komai ba bata kuma Wago ba abun ya Waure mata kai sosae don bata yi tunanin zai mata wannan Maganar ba, ganin ta?i tace komai yasa shi kiran sunanta ta amsa ba tare data Wago ba yace tayi shiru bata ce komai ba still ta?i cewa komai Win,

"Ayshat" amsa mashi tayi ba tare data Wago ba yace "Look at me" saida tay Wan jimm kafin a hankali ta Wago idanunta suka sauka akan kyakkyawar doguwar fuskarshi mai Wauke da kwantaccen saje, yanayin fatarshi ba za'a ce mashi fari ba kuma ba ba?i bane yafi kama da a kira shi da wankan tarwaWa, sosae yanayin hutu ya bayyana a jikin fatar ta shi yana da kyawun fuska wadda take a cike Wauke da dogon hanci da kuma madaidaicin baki mai dauke da jerarrun fararen ha?ora harda yar wushirya, a bangaren yanayin jiki sam ba gajere bane don da kaWan Haisam ya Wara shi tsawo sannan kuma ba siriri bane yana da cikar jiki, ganin tanata kallonshi yasa shi ce mata kada taji komai in taji bata son shi ta faWi mashi bazai ji komai ba kuma ko Yayanta bazai faWi ma yadda sukai da ita ba, motsa baki ta fara da ?yar tace mashi shikenan idan Yaya Haisam ya amince to ta yarda, Wan girgiza mata kai yayi yace mata aure ba abu bane da wani zai amince maka tunda bashine zai zauna maka ba sannan aure ana yin shi in ana son juna don haka ita zata amince mashi in taji tana son shi, shiru tayi tana yi tana maida idonta ?asa ya Wan Wage mata gira yana murmushi, sai faman yan kame kame take don taji itama yayi mata don Na'eem ba irin mazan da suke furta ma mace so ta?i amincewa bane kawai dai abun ne taji yayi mata girma ba kamar da yake wannan ne karo na farko da tayi Magana irin haka da Namiji,

"Amman...ita Matarka to zata amince ka aure ni ne?" da ?yar ta furta mashi hakan, gyara zama yay kafin yace "Ayshat ba kowace mace bace ke son a ?ara mata abokiyar zama ba saidai inada kyakkyawar fahimta da mata na nasan zata amince koda hakan bai mata dadi ba amman tasan inada ikon ?ara wata matar kuma dama ban ta6a mata al?awarin zan kasance da ita kaWai ba don haka nasan bazata bani matsala ba in kin amince zaki aure ni" kai ta Waga mashi kafin tace shikenan,

"Kin amince zaki aure ni kenan?" kai ta ?ara Waga mashi ya sake cewa "ina fata dai ba saboda wani dalili ko don ni abokin yayanki bane yasa kika amince man, nafi son ki amince man don kema kinji kina sona" kai ta jinjina mashi yana mata wani kallo yace "nayi maki kina so na?" kan dai ta sake Waga mashi,

"Ok in dai da gaske kike kema kamata yay ki faWi man da bakinki kamar yadda na faWa maki" Wan murmushi ta shiga yi tana motsa baki ya Wage mata gira alamar ta bashi amsa, da kyar ta furta "nima ina son...ka" tana yin Maganar da sauri tasa duka hannuwanta masu Wauke da dogayen yatsu ta rufe fuskarta Na'eem Win ya shiga yin yar dariya, da yake wayayye ne sai gashi yasa ta saki dashi sun shiga yin firar soyayya, suna haka Hajiya Fatuu ta shigo cikin falon tana sanye da riga da skirt na lace da suka amshi jikinta tare da gyale mahadinsu, tana nan yadda take bata ?ara ?iba ba saidai ta ?ara cikowa tay dumdum fatar nan tata har wani sheki take hutu ya zauna mata sosae, ?afafunta na sanye da wasu takalma masu tsini mai Wan gwa6i har yanzu halinta nason takalma masu tudu nan, ta bangaren hips dinta kuwa abun saidai ace tubarkalla don suna nan sai ma ?ara cika da sukai duk da gyalen jikinta babba ne amman kana kallonta zaka san tana dasu, hannunta na hagu na rataye da yar babbar jaka da take Wauke da kayan karatunta sai kuma Wayan hannunta na hagu ta ru?o Lab coat dashi, tana ganin Na'eem ta fara yin murmushi hakan ya bayyanar sa fararen ha?oranta kamar auduga masu Wauke da ha?orin makka daya ?ara ?awata fuskar tata, cikin falon ta nufa sam bata yi mamakin ganin Na'eem Win ba don da sukayi waya da Haisam ya sanar mata tare suka zo, a saman kujera dake gefen wadda suke ta zauna Na'eem daya maido idonshi kanta yana murmushi shima yay mata sannu da dawowa ta amsa tare da gaishe dashi da yi mashi anzo lafiya, bayan ya amsa ya tambayi karatunta tace mashi Alhamdulillah itama ta tambayi matar shi Fadeela da yaransu duk yace mata lafiya lou suke, saida suka gama gaisawa sannan Aysha tayi mata sannu da zuwa ta maida idonta kanta tana murmushi ta amsa ta tambayi ya School tace mata lafiya lou, yar hira sukai da Na'eem kafin ta mi?e tace bari ta Wan shiga ciki yace Ok. Sai bayan sallar Magrib sun dawo daga masallaci suka zauna cin abinci gaba Wayan su Na'eem da Aysha sai satar kallon juna suke suna murmushi, bayan sun dawo daga sallar isha gaba daya a falo suka zauna suna kallo, wuraren ?arfe tara Haisam ya mi?e yace ma Na'eem bacci yake ji ya taso suje ya kai shi Wakin da zai kwanta yana murmushi yace shi da Aysha basu gama yin kallon ba yace Ok yazo suje ya nuna mashi in ya gama sai yaje ya kwanta ya mi?e, bayan tafiyar su ne Fatuu ma ta mi?e tayi ma Ayshar saida safe dama duk in Haisam yazo a Wayan bedroom Win dake part Win Fatuu take kwana tare da mai aikin su Asabe, bada jimawa ba Na'eem ya dawo a saman kujera mai mazaunin mutum ukku ya zauna yace ma Aysha ta dawo nan, a can gefe kamar Wazu ta zauna ya jingina kanshi da jikin kujerar ya shiga sakar mata kallon love da alama dai shima gwani ne ta bangaren soyayya, hirar soyayyarsu suka shiga yi ba laifi ta saki jiki sun Wan Wauki lokaci wurin ?arfe goma saura yace bari ya barta taje tayi bacci kadda ya gajiyar da amaryarshi tayi dariya suka mi?e a tare.

Washe gari bayan Haisam ya dawo daga sallar Asuba itama Fatun tayi sun koma sun kwanta ta tada kanta a saman jikinshi yake mata zancen son auren Aysha da Na'eem keyi ya faWi mata yace mashi ya nemi amincewarta to har sunyi magana kuma ta amince, sosae Fatuu ta jinjina abun don ita koda ta gansu tare bata kawo komai a ranta ba saboda tasan Ayshar nada saurin sakin jiki da mutane ba kamar Mino ba, da alamun damuwa tace mashi amman bai ganin hakan zai iya haifar da matsala tsakaninsu da matar shi taga anyi mata ba daidai ba tunda sun san juna suna gaisawa, yana Wan murmushi yace itama ba sun san juna ba da Fanan kuma ta aureshi, juyawa tay tayi mashi wani kallo tare da Wan tura mashi baki tace to ai ita bata san da Auren ba ko ya Wage mata gira yace data sani bazata amince ba kenan tay shiru tana kallon shi yace ta bashi amsa, yamutsa fuska tay ta sigar shagwa6a tace to tunda dai an riga anyi ya wuce miye na maido maganar, yana murmushi yace Ok tunda itama ya aureta kuma sun san juna da Fanan itama Ayshar ba wani abu bane don ta auri Na'eem, shiru Fatuu ta Wan yi kafin tace ya sani fa Aunty Fanan daban take a cikin mata don da wuya a samu wadda zata iya jarumtar da tayi, shiru yay yana sakin murmushi yayin da zuciyarshi ta shiga dawo mashi da fuskar Fanan. Wuraren ?arfe goma na safe suka zauna yin breakfast, kowa cikinsu yayi wanka Haisam da Na'eem na sanye da ?ananun kaya wando da riga Fatuu kuma da Aysha suna sanye da dogayen riguna masu taushi suna da gajerun hannuwa kowa ya saka hula a kanshi daga bayan hular yay tudu sosae saboda gashin su, bayan sun zauna a kujerun dining Win suka shiga gaishe da juna kafin Fatuu ta shiga yin serving nasu, bayan ta gama a nutse suka fara ci baka jin komai sai ?arar cokulla sai kuma Ac dake a wurin tana ta aiki, bayan sun gama gaba Waya a falo suka zazzauna suna yin hira wadda Haisam da Na'eem sai Fatuu ne ke yi ita dai Aysha tayi shiru tana saurararsu akai akai kuma suke haWa ido da Na'eem su sakar ma juna murmushi, suna cikin yin firar Na'eem yace ma Fatuu "Madam ko in ce Yayata, ina fatan Yalla6ai ya isar maki da sa?ona na naga ?anwarmu tayi man ina neman iri pls, yace man in nemi amincewarta da yake mu indai ta wannan bangaren ne bamu failing tuni har an amince man ance ana sona" ya kai idon shi kan Aysha yace "Ayshanah hakane ko, kin amince zaki aure ni ai ko?" ai tana jin abunda ya faWa tay zumbur ta mi?e da gudu ta nufi hanyar bedroom duk suka bita da ido suna yar dariya, bayan barinta wurin ne Fatuu tace mashi sunyi Maganar da Hubby taji daWi saidai tana gudun hakan ya haifar da matsala tsakaninsu da Fadeela tana iya ganin an yi mata ba daidai ba, yana murmushi yace mata kar ta damu zai faWi mata shi yaga Aysha yaji yana sonta kuma akai sa'a itama tana son shi ba wanda ya haWa su in sha Allah ba wata matsala da zata faru tsakaninsu Fatun tace Allah yasa, tambayar ta yay lokacin da zata gama School Fatun ta faWi mashi yace Ok nan da sati Waya in sha Allah zaije Yola ya gaida Parents Win su Haisam yay mashi wani kallo kafin slowly yace mashi saurin mi yake ne tunda ta amince mashi yabi komai a hankali da sauri Na'eem Win yace ai ba mata irinsu ake bi a hankali ba wurin neman aurensu nan tana gama Secondary zaiga masu son ta suna ta kunno kai ?arshe asamu wani yayi mashi overtaking shiyasa yake son tana gama School Win yayi wuff da ita duk sukai yar dariya, hira suka cigaba da yi bayan wani lokaci Haisam ya tambaye shi yaushe zai je gaida relatives Win nashi Na'eem Win ya duba agogon hannunshi kafin ya bashi amsa da zuwa ?arfe sha biyu zai tafi Haisam yace Ok in lokacin ya ?arasa sai suje ya raka shi,

"No, kai zaman ka kaida kazo Weekend Madam na bu?atar ka a kusa da ita koda yaushe ka ?yale ni in je ni kaWai, ko kuma tunda nima ga Amaryata sai ta rakani kawai kaga ma sai inyi amfani da daman in fara introducing nata ga Family na" Na'eem ya faWa yana murmushi suma duk murmushin sukai basu ce komai ba, ganin lokacin fitar nashi ya ?arato yasashi ce ma Fatuu pls yana neman alfarmar fita da Aysha tana murmushi tace an mashi yay mata godiya kafin yace to ta taimaka tayi ma Amaryar tashi mai kunya magana ta shirya tace to tana dariya tare da mi?ewa shima Na'eem Win ya mi?e yace ma Haisam bari ya shirya ya Waga mashi kai, a bedroom ta iske Aysha kwance saman gado ta nufeta tana faWin kwanciya tayi kenan Ayshar ta Wago tana kallonta, a bakin gadon ta zauna tana kallonta da murmushi tace mata Amaryar Na'eem Ayshar tayi murmushi kawai, shiru Fatun ta Wan yi kafin tace mata ta tabbatar da yayi mata tana son shi don shi da gaske yake aurenta zaiyi tana gama School, shiru Ayshar tayi tana kifce kifcen idanu Fatuu tace mata ta buWe baki tayi mata magana, a hankali tace mata eh in dai baida wata matsala Fatun tace gaskiya Na'eem bata tunanin yanada wata matsala a yadda ita ta sanshi mutumin kirki ne kuma tasan da yanada matsala ma tun Farko Haisam bazai bashi damar ya nemi soyayyarta ba kawai inda take tunanin matsala wurin matarshi ne duk da itama tana da kirki to amman wata baka gane rashin kirkinta sai za'a mata kishiya kawai dai suyi addu'a Allah yasa ta fahimta ta kuma kar6i abun kamar yadda Aunty Fanan tayi Ayshar ta amsa da Amin kafin tace "amman fa Adda Fatuu wllh Aunty Fanan ta daban ce" murmushi Fatun tay tace ta sani samun irinta cikin mata da wuya in ma akwae duk da tasan akwai mata da yawa wanda in mijinsu yaje masu da zancen ?ara aure duk da basu so amman suna karbar abun a matsayin ?addararsu tunda sun san Allah ne ya halarta masu yin jayayya da hakan kuma wahalar da kai ne ?arshe mutum ya jefa kan shi a halaka, faWi ma Ayshar tayi zasu fita da Na'eem Win yana son zuwa da ita wurin danginshi ya gabatar masu da ita, tana jin haka ta Wan zaro ido kafin tace amman da wuri haka, mi?ewa Fatuu tay tana yar dariya tace shifa da gaske yake yace ma nan da sati Waya zaije Yola gaishe dasu Baffa don haka ta fara shiri don ita amarya ce,

"Amman Adda Fatuu ban yi ?arama ba da yin aure" Aysha ta faWa da yar damuwa, Fatuu dake tsaye a gaban wardrobe Win bango tana ?o?arin za6o mata kaya ta bata amsa da "ba wata ?arama da kikai Aysha, ke ai gara kema akan Mino, ita fa ko gama Secondary bata yi ba akayi mata aure gashi ko a jiki ma kin Wan fita kauri lokacin" ta ?arasa Maganar tana dawowa wurin gadon hannunta ru?e da riga da skirt na lace kalar blue da ratsin golden brown, ita ta taimaka ma Ayshar ta shirya cikin kayan ta saka mata yan kunnan zinari da zobe sai kuma agogo golden mai kyau, yar light make up tayi mata ta Waura mata kallabi sai gashi ta fito tayi wani irin kyau, bayan an gama saka kayan ta yafa gyale mahadinsu haka jaka da takalmanta suma duk kalar kwalliyar lace Winne takalman masu dan tudu ne kadan don tana da tsawo don bata cika saka takalma masu tsini ba, lokacin da suka fito falon Na'eem din har ya gama shiryawa ya dawo suna zaune da Haisam, shima shadda ce ya saka brown wadda ta hau da kwalliyar lace Win jikin Ayshar sai baza ?amshi yake, Na'eem na ganin shigarta yana murmushi yace ko daga yanayin shigar su hakan ya tabbatar da sun dace da juna duk akayi yar dariya Aysha ta sunnar da kai, har bakin galleliyar ba?ar Motar Haisam da suka zo da ita suka rako su bayan sun shiga sukai masu sai sun dawo, yana driving suna hira irin ta masoya haka suka shiga zaga gidajen yan'uwan su Na'eem wanda duk mawadata ne, duk inda suka je sai ya gabatar da ita matsayin matar shi ta biyu da zai aura nan bada jimawa ba anata yabata tare da fatan alkhairi, lokacin da suka je gidan Kakarshi wadda ta haifi Mom Winshi shima haWaWWan gidane mai girma don yana da parts da yan'uwan mahaifiyarshi maza ke zaune da matansu haka itama kakar 6angarenta daban an ?awata shi ai kace ba sashen tsohuwa ba, lokacin daya gabatar mata da Aysha matsayin wadda zai ?ara mata cike da zolaya irinta Kaka ta yamutsa fuska tace in baya ga rigima irinta namiji mi zai ci da wannan yar ?aramar bafullatanar bayan yana da mata ?a??arfa kamar ita, ita dai Aysha murmushi kawai take kanta a ?asa haka shima Na'eem Win yar dariya yake yace ina wani ?arfi a tare da ita, sosae ta sake ma Aysha tana ta mata tambayoyi game da ita tana bata amsa da yake tasan Haisam sosae ta yaba da al'amarin tayi Addu'ar Allah ya sanya alkhairi, duk sauran parts Win gidan saida ya kai ta ko ina an yi mata tarba mai kyau, daga baya bangaren Kakar suka koma sai bayan sallar La'asar ya dawo daga Masallaci yace mata zasu tafi tace ma Aysha tunda a garin take zaune ta rin?a zuwa gaishe da ita tana kama ?afa in tana son ta amince ta aurar mata miji in ba haka ba ita dashi saidai kallo, tana murmushi tace mata in sha Allahu zata ri?a zuwa sukai mata sallama cike da tsokana Na'eem yace tunda ita mai ?arfi ce sai ta taso ta raka su bakin mota ko, wurga mashi harara tayi tace Allah ya kyauta tayi ma kishiyarta rakiya duk sukai dariya, bayan sun baro gidan Shopping ya wuce da ita, koda yace mata ta Wauki duk abunda take so cikin marairaicewa tace mashi ai ita tana da komai yana mata wani kallo yace duk da haka ta ?ara so yake daga yau ta fara amfani da kayan mijinta, ba yadda ta iya haka ta fara Waukar yan abubuwa tana sakawa a cart da ya Waukko mata, ganin bata Waukar kayan sosae yasa shi fara za6ar mata da kanshi yana yi yana tambayar wanda take amfani dasu, bayan sun gama da wurin kayan shafa wurin dogayen riguna suka nufa tana ta ro?on ya barsu tana da su da yawa amman duk da haka saida ya daukar mata guda biyar da takalma guda ukku bayan sun gama da nan bangaren undies suka nufa duk yadda take jin kunya saida ya sakata ta Wauka, abunda bata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login