Showing 489001 words to 492000 words out of 513411 words

Chapter 164 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16746

?addaro zamanta Abujan ne tunda tuntuni suke son ta koma ta?i hardai yanzu sukai galabar sata ta koma suyi ha?uri ai ba'a rabu ba kenan kamata yay ma su gode ma Allah daya sa ta mi?e, nasiha sosae tayi masu suna ta sharar ?walla daga ?arshe tace suje, har zasu mi?e tace to su basu yafe matan ba wannan magana ba ?aramin ta6a masu zuciya tayi ba duk suka ce mata su wllh ba abunda ta ta6a yi masu ba daidai ba tace duk da haka dai su yafe mata, a tare suka haWa baki suka ce sun yafe mata tare da yi mata Addu'o'i, bin su tayi da ido lokacin da suka nufi ?opa, bayan fitar su ta maido idonta tana kallon gabanta can ta sa hannu ta Waga gilashin idanunta ta goge ?wallan da suka gangaro mata...........

104



~_*
'=؋?BOSS LADIES WRITERS=؋?
'*_~


.........Suna fitowa Tk ya wuce Wakin su Saude kuma ta nufi baya inda Wakinta yake, a bakin gado ya zauna yaci gaba da yin kukan mai cin rai yana haka Husnah ta shigo ciki ma gareta har ya girma, zama tayi a kusa dashi fuskarta Wauke da damuwa ta shiga bashi ha?uri kai kawai yake Waga mata, da yake tasan wurin Hajiya suka je cike da damuwa ta tambayeshi tafiyar dai zata yi da gaske ya Waga mata kai alamar eh ta Wan girgiza kai itama duk wani iri take ji can ta kai hannu ta fara goge mashi ?wallan tana bashi ha?uri, Saude ma tana komawa Wakinta ta faWa gado ta saka kuka mai sauti gwanin ban tausayi, ta Wan Wauki lokaci kafin Officer ya shigo ya isketa a haka, da alamun tashin hankali ya nufi bakin gadon ya zauna ya kai hannu yana ta6ata tare da kiran sunanta yana tambayarta lafiya miya faru, cikin kuka tace mashi da gaske Hajiya tafiya zata yi, cikin sanyin jiki yace mata eh yasani nan da sati guda ya shiga bata ha?uri yana nuna mata ai ba an rabu ba kenan za'a cigaba da zumunci yanzu ma daga wurinta yake tace ma zasu iya cigaba da zama a gidan, ha?uri yaci gaba da bata can ta Wago idanunta sunyi jajir ta saukko daga saman gadon a tunanin shi wani wuri zata ko toilet kawai sai gani yay ta du?a a gabanshi cikin kuka a marairaice tace mashi don Allah tana neman alfarma a wurin shi tana rokon ya dubi girman Allah yayi mata, gaban shi ne ya fara faWuwa yace mata in sha Allah in bata fi ?arfin shi ba zai yi mata, a marairaice tace mashi tunda dama a nan gidan suka haWu har sukai aure kuma Allah bai sa sun samu rabon haihuwa ba don Allah tana ro?on shi ya sawa?e mata Allah ne shaidarta tana jin Hajiya har cikin ranta bata jin zata iya cigaba da zama a gidan nan ba tare da ita ba, shiru yay yana kallonta duk da yaji ba daWi data yi Maganar amman ta bashi tausayi yace mata yanzu in ya sawa?e matan garinsu zata koma kenan tace a'a zata ro?i Hajiyar ne ta tafi da ita, shiru yay yana kallonta ta langa6ar da kai tana mashi magiya can yay yar ajiyar zuciya yace mata shikenan ta bari sai da safe zasu yi Maganar tunda yanzu dare yayi ya kama hannunta ya mi?ar da ita yace suje ta wanke fuskarta. A wannan daren baccin su gaba Waya harda Tk ragagge ne, Washe gari Officer na dawowa daga sallar Asuba part Win Hajiya ya wuce, bayan ya ?wankwasa ?opar daga ciki ya jiyo muryarta tana bashi izinin ya shigo, zaune take kan darduma hannunta ru?e da cazbaha, da hannu tayi mashi alamar ya shigo ya nufi inda take ya du?a a kan carpet, bayan ta shafa Addu'a ta kalleshi da Wan murmushi da sauri ya gaishe da ita ta amsa tayi mashi ya suka tashi ya amsa da Alhamdulillah daga haka yay shiru idon shi akan carpet, daga yanayin shi ta fahimci da wani abu tana Wan murmushi tace mashi tana fatan dai lafiya ko da wani abu, dagowa yay a nutse yace mata dama Saudatu ce jiya da daddare ta ro?eshi kan yay mata wata alfarma to yace ta bari sai zuwa da safe shine yaga ya dace ya fara tuntu6arta gudun yay mata ba daidai ba, kai Hajiya ta jinjina ta tambayi wace alfarma take son ya yi mata ne nan ya faWi mata duk yadda sukai da Sauden,

"Humm, Saudatu Kenan, to yanzu kai ka amince zaka sawa?e matan ne?" Hajiya ta faWa tana Wan murmushi idonta akan shi, Wan shiru yay farko kafin yace tunda ta nuna hakan take so zai mata Hajiyar tace bai son auren ne ko kuwa, da sauri da alamun damuwa yace wllh yana son zamanshi da ita Allah ya sani kawai dai ya fahimci in bai yi mata yadda take so ba ba lalle zaman nasu yaci gaba da yin daWi ba don ta nuna bazata iya cigaba da zama ba tare da ita ba, yar ajiyar zuciya Hajiya ta sauke ta juya ta kai hannu ta Waukko wayarta ta shiga kiran layin Saude bayan ta Waga tace mata tazo dakinta tana son ganinta, ba'a Wau lokaci ba Sauden ta shigo cikin Wakin da sallama tana sanye da doguwar Hijabi duk suka amsa mata ta nufo ciki, gefen Officer Hajiya ta nuna mata alamar ta zauna, bayan ta zauna ta gaishe da Hajiyar tare da yi mata an tashi lafiya da tambayar ?arfin jikinta duk ta amsa mata daga haka Sauden ta sunkuyar da kanta idon Hajiya a kanta tana Wan murmushi, a nutse cikin dattako ta fara magana tace taji yadda sukai da maigidanta saidai sam bata jin daWin jin hakan ya fito daga bakinta ba a matsayinta na wadda take gani mai hankali taya zata tunkari mijinta da zancen ya saketa kenan ta za6i bauta a ?ar?ashin wani fiye da ubangijinta, da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a,

"Aure shine mutuncin kowace mace Saudatu, nasan saboda kauna da sabo yasa kika za6i hakan saidai ni a wurina zaman ki a Wakin mijinki shine abun alfaharina ba kamar in na tuna a gidana kuka haWu har akai auren, kiyi ha?uri don na tafi ba yana nufin shikenan an rabu ba in sha Allahu za'a cigaba da yin zumunci in dai da rayuwar" Wagowa Sauden tayi idanunta sharkaf da ?walla ta Waga mata kai kafin cikin disashshiyar murya tace mata to zata koma Daura,

"To auren fa Saudatu, taya zaki koma can bacin ga mijin ki anan?", shiru ta Wan yi idonta a ?asa kafin tace "Hajiya don Allah ki bari in koma Allah ne shaidata bazan iya cigaba da zama ba a gidan nan in baki nan" shiru Hajiya tayi tana Wan murmushi idonta a kan ta, cikin sigar rarrashi tace mata ta dai yi ha?uri ta zauna saboda aurenta Sauden tayi shiru tana matsar kwalla can Officer yace in hakan take so lafiya lou shi ya amince ta koma Daura din Hajiya tace to ya za'ai hakan yace ba komai indai hankalinta zai fi kwanciya sai ya rin?a zuwa, ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tace shikenan bari ta gani in zata iya neman alfarma sai a maida shi Daura da aiki dama tuntuni abunda yasa ya daWe anan gidan ita ta ro?i alfarmar abar mata shi yanzu abunda za'ayi tunda dama zata siya ma Sauden gida in ta amince sai a siya mata acan Daurar sai su zauna a cikin shi, da sauri Sauden ta Waga kai alamar ta amince Hajiyar tayi murmushi tace to wurin ina take son a siya mata gidan tasa a bincika mata Sauden ta Wago ta faWi mata tace shikenan, kallon Officer tay tace ya jirata Maganar canjin wurin aiki ya yi kuma Addu'a Allah yasa a maida shi can yace Amin ta ?ara ce mashi zata turo mashi sa?on kuWi sai ya juya ya haWa da aikin nashi Allah ya ?ara rufa asiri ya amsa da Amin tare da yi mata godiya da addu'o'i ta amsa tare da cewa shikenan zasu iya tafiya.

Tun bayan da Hajiya tayi magana dasu Tk game da tafiyarta gaba Waya duk sun shiga damuwa gidan ya koma shiru sam basu da wata walwala a haka har ranar tafiyar tata tazo, ranar ta kama Juma'a da safe jirgin Hajiya Maryam ya iso tazo tafiya da ita, bayan zuwan nata nan da nan gidan Hajiyar ya cika da manyan mutane musamman yan siyasa sun zo yi ma Minister sannu da zuwa da kuma yin sallama da Hajiya, da lokacin sallar Juma'a yayi gaba Waya a Masallacin gidan duk sukai salla, misalin ?arfe huWu na yamma ana gama sallar La'asar aka firfito don raka Hajiya Airport tuni an fito da akwatunan kayanta an saka a Mota don iya su kawai zata tafi dasu ba'a dauki komai na gidan ba, a gaban entrance aka jere motocin lokacin da Hajiya ta fito sanye da rantsatstsiyar lifaya tana dogara sandarta ta alfarma Tk na daga can gefe a tsaye idanunshi sunyi ja don tun da safe yake matsar ?walla, har su Gwaggo sun zo suma zasuyi rakiya Amadu ne zai kai su a Motar Fatuu, bayan an fara shiga cikin motoci Amadu ya nufi wurin Tk ya dafa kafaWarshi yana bashi ha?uri yace mashi yazo suje suyi mata rakiya idanunshi cike da ?walla ya girgiza mashi kai yace su je kawai, ganin yanayin shi yana cikin matsananciyar damuwa yasa Amadun ?yale shi ya juya, a tare Convoy Win motocin suka tashi gaba da baya motocin security ne idanun Hajiya na akan Tk dake tsaye har suka isa gate suka ta Wan girgiza kai tare da rufe idonta, lokacin da suka fito kopar gidan cike yake da mutane yan unguwa tun dazu suke son shiga yin bankwana da Hajiya amman Security sun hana, motocin na fitowa suka shiga daga masu hannu suna faWin sunan Hajiyar Sanata ganin haka yasa Hajiya tasa a dakata, bayan Jeep Win da take ciki ta tsaya ta sauke glass aikuwa mutane na ganinta suka nufo ta da sauri nan fa aka shiga tutsetseniyar kama hannun nata ana kiran sunanta harda masu yin kuka daga baya ma sai ta buWe Motar ta fito aikuwa matan unguwa da yara aka shiga rungumeta ana kuka cike da ?arfin hali take basu ha?uri tana kwantar masu da hankali tace ai ba an rabu ba kenan in sha Allahu za'a cigaba da zumunci kuma duk abunda take yi baza'a bari ba tunda ga Tk nan, ganin suna 6ata lokaci yasa Hajiya Maryam tayi ma security magana suka sallami mutanen Hajiyar ta koma cikin Mota, duk yadda ta daure saida ta matse ?walla motocin suka tafi anata cigaba da Waga ma Hajiyar hannu, mutane rahama ko iya haka za'a iya cewa Hajiya ta dace. Hajiya ta tafi ta bar mutane da kewa ba kamar su Tk don tun bayan tafiyarta yake ta zazza6i bawan Allah don ma Allah yasa yana da mata tanata aikin rarrashin shi duk da itama sosae take kewar Hajiya don ba ?aramin sha?uwa sukai ba ita kanta Wiyar su Hauwa'u duk ta damu ko yaushe cikin tambayar yaushe Hajiyarsu zata dawo take sai an kira mata ita ta waya sunyi magana ko Vedio call take kwantar da hankalinta, ta bangaren Saude ma taso tafiya Daura bayan tafiyar Hajiya Officer ya rarrasheta kan tayi ha?uri tunda Hajiya tace zata nema mashi transfer sai su koma can baki Waya da haka ya samu ta ha?ura, su Gwaggo ma duk sun yi kewar Hajiyar duk da su bama gida daya suke da ita ba amman da sun zauna suna hira sai sun yi maganarta, sai bayan wani lokaci Tk ya warware amman ko yaushe cikin jin kewar Hajiyar shi yake.

Bayan komawar Hajiya Abuja da yan watanni Allah ya sauki Farha ta haiho san6aleliyar Wiyarta mace kai kace Wiyar aljanu ce don kyau gaba Waya mamanta da babanta ta biyo, a fuska da Kamalu take kama amman farinta na Farha ne sannan ?wayar idonta ma ta Farha ce gashin kanta kuma ba?i ne wuluk kalar na babanta, cikin sa'a lokacin da akai haihuwar su Fatuu na hutu hakan ba ?aramin daWi yay masu ba, kowa ya ga Babyn sai ya furta ma sha Allah ana ta farinciki Hajiya Maryam ma lokacin data ga Babyn sam kasa rufe bakinta tay sai farin ciki take, bayan sun koma gida daga asibiti da daddare Lokacin da Kamal ya shiga wurin maijegon yana ru?e da babyn yake sanar mata da sunan da yake son sakamata wato sunan Hajiya Maryam Farhar tace mashi ba gara yasa sunan late Mom Win shi ba yace mata tunda Fatuu tasa su bari in ta ?ara haihuwa sai su saka sunan Mom Win nashi, harda yar harararshi tayi tace ita wannan wahalar da tasha ta gama haihuwa yana murmushi tare da yi mata kallo mai cike da tsantsar ?auna yace tayi ha?uri pls ta ?ara mashi yana son su haifi yara tare, itama murmushin tayi ta kai idonta kanshi tana mashi kallon love tace indai irin yaran nan zata rin?a haifa tare dashi to zata ?ara wasu Amman sai ta huta sosae yay murmushin shi mai burgewa tare da jinjina mata kai alamar amincewa da zancenta tana murmushi ta kwantar da kanta a kan shoulder dinshi tana kallon Kyakkyawar Babyn su tana haka taji ya furta "Thank you my lovely wife for loving me for who i am" Wago kai tayi ta kalle shi ta kashe mashi ido tare da furta "i will always love u Babe" yadda tayi maganar har sai da Wumin bakin ta ya bugi fuskarshi saboda kusancin da fuskokin nasu suke dashi, shiru sukai suna kallon juna wani lokacin har mamaki Kamal yake a cikin ranshi irin yadda take nuna mashi ?auna bata ?i a ce koda yaushe suna manne da juna ba, a iya zaman da sukai matsayin ma'aurata ba ?aramar zazzafar soyayya ta nuna mashi ba hakan yasa shima yake ?okari wurin faranta mata a koda yaushe bai ta6a yin wani abu da zai nuna ta takura mashi ba zaman su suke lafiya sam baida matsala da ita kawai dai tana da zafin kishi wannan kuma tun kafin suyi auren ya sani shiyasa yake taka tsantsan da duk abunda yasan zai haifar masu da matsala, lokacin da Hajiya Maryam taji sunanta aka saka ma jaririyar murnarta ninkuwa tayi jin anyi mata takwara, bayan kwana biyar da yin haihuwar aka maida maijegon Villa don acan za'ayi suna, saida Hajiya Maryam tayi ma jaririyar saitin akwatuna ukku masu guda huWu haWaWWun gaske sha?e da kayan jarirai na gani na faWa da sauran kuma abubuwan da suka danganci jarirai ita kanta mai jegon ita tayi mata kayan da zata fita suna harda shi ma Baban jaririyar tayi mashi Winkuna na alfarma abun dai gwanin daWi, ranar suna ta kama Juma'a suna na gani na faWa akayi a Villa maijego ta samu iyayen kaya ita da Baby, mai girma shugaban ?asa kyautar ?aton fili yay ma jaririyar haka dai aka cika su da abubuwan arzu?i kowa yayi bajinta su Gwaggo da Haulat harda Kawu Amadu da Tk da matarshi duk sun zo suna, zo kaga farincikin ganin juna wurin Hajiya da Tk harda rungume shi tayi, suna yayi suna abun sai son barka bayan gama sunan anan Villa apartment Win da Hajiya Maryam take Farha ta zauna sai ta gama wanka zata koma.

A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji gashi President Ali har yayi shekara biyu da komawa kujerar mulki lokacin yaran Fatuu duk sun girma su Twins nada shekara takwas Esha kuma nada shekara bakwai, tun bayan da Esha ta fara girma gaba Waya halayenta sak na Fatuu da tana da ?uruciya ne don sam bata jin magana ga masifa sannan tana da ?arfi sosae don abu kaWan sai ta kai bugu ko su twins bata ?yalesu ba da Wan abu ya haWa su sai ta kama bugun su duk da suna maza bugunsu take har ta saka su kuka kuma duk sun fita tsawo amman tana da jiki bulbul take, kullum cikin rabata faWa ake da yara a gida da kuma makaranta
gashi saboda ansan ko ita wacece yasa ba'a ta6a kai ?orafin halinta ba ga iyayenta har sai watarana data fasa ma wata yar ajin su baki daga ta taka mata colour bata gani ba ta karye tana bata ha?uri amman duk da haka saida ta kai mata bugu saitin bakinta aikuwa bakin ya fashe yay ta jini lokacin Class Aunty Win su ta yanke yin magana da Dad Winta don ai mata faWa ta rage faWa da yara da yake suna da lambobin wayoyin iyayensu, bayan ta kira Haisam cike da girmamawa tayi mashi bayanin dalilin kiran nashi harda bashi ha?uri kan hakan da tayi tace taga abun yana yin yawa ne kada wata rana ta illata wani student sosae, Haisam Win yace mata ba wani abu ya gode da sanar mashi da tayi, a ranar da daddare bayan ya dawo daga sallar isha ya zauna a main parlor dama duk dare in ya dawo daga salla nan yake zama su Twins da Esha din su kawo mashi Assignment Win su ya taya su bayan sun gama sai ya rakasu Wakunansu su kwanta, su Twins Wakin su Waya sai ita kuma Esha a Bedroom Win Fanan take kwana, bai daWe da zama ba sai gasu sun fito duk suna sanye da ?ananun kaya su Twins Jeans da t-shirt sai Esha tana sanye da blouse da Wan gajeran skirt duka kalar pink gashinta na fake a tsakiya ya sauka har kusan tsakiyar bayanta dama kusan koda yaushe sai dai ka ganta da gyaran gashi don bata son kitso, kowannensu ya Waukko ?atuwar jakar Makarantarshi, suna ?arasowa inda Haisam yake zaune Esha ta saki jakarta ?asa ta washe baki duk gefen kumatunta suka lotsa sosae ta nufi Haisam da yar sassarfa tana faWin "My Daddy.." dama ita yar gidan Daddy ce sosae suke shiri kowa ma ya sani daddie's pet ma ake ce mata ko rashin ji take da ance in ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login