Showing 432001 words to 435000 words out of 513411 words

Chapter 145 - ASANADIN MAKWABTAKA HAUSA NOVEL

20 Jul 2025

16800

Kamalu yaji don yafi kawu Amadu fari ga sumar shi a kanannaWe take bangaren kyawun fuska kau ba'a magana dama shi Mamarsu ya biyo wato Aysha ita kuma babansu ita da kawu Amadu shi ta biyo hakan yasa Kamalun ya Waukko dogon hancinta ga ?aramin baki dama ba kalar shape Win bakinsu Waya da Fatuu ba ga girarshi ta zanu raWam Wauke da ba?in gashi mai santsi, ganin anata zuwa ana yin li?i yasa shi ce ma Kawu Amadu ya bashi kuWi suma suje suyi Amadun yay yar dariya yace shi ina yaga kuWin da zasu je suyi li?i yana ganin uban kuWin da ake ta li?awa yan kuWin da ke a jikin shi yan kaWan ne, Tk na dariya yace ai masu yin canjin kuWin ana masu transfer sai suba mutum Cash Kawu Amadun yace "kai rabu dasu ba wani li?in da zanyi nima kuWin aure nike tarawa",

"Kaman gaske, kai da har yanzu baka da niyya" Tk ya faWa yana dariya,

"Serious kwanannan zan baka mamaki don mai gaba Waya zanyi saidai kaji Maganar aure kawai da an bani dama" Kawu Amadun ya faWa,

"to Allah yasa, in ba haka ba sai dai kaga na shige na barka don bazan biye maka ba in ?i more rayuwata gashi har mun yi 30yrs",
Amadun yace mashi yasha kurumin shi sai ma ya riga shi yi in sha Allah, hango Fatuu Tk yayi ta dawo daga wurin yin li?i yace ma Kamalu yaje ga Hajiya Fatuu can ya amso kuWin li?in, kai idon shi yay kan Fatun kafin ya mi?e da sauri zai je wurinta Amadu na faWin shima ya amso dashi ya Waga mashi kai, da sauri ya tunkareta don bai son ta koma wurin zaman su saboda akwae mutane, cikin rashin lura yaji ya kai ma mutum karo har abu ya faWi ?asa da sauri ya maido idon shi kan wadda sukai karon ta kai hannu ta dafe goshi tana sanye da irin lace Win su Fatuu anyi mata wasu irin style na riga da skirt kai kace a jikinta aka Winkasu don sun kamata sosae sun fito da suffarta wadda da gani ba ramamma bace kuma tana da shape gaba Waya wuyanta da kafaWunta a bayyane suke farar fatar ta fat ta bayyana, tun daga kunnanta wuyanta zuwa hannunta data dafe goshinta gold ne, sosae hankalin Kamalu ya tashi ya wara ido yana kallonta duk da bai ga fuskarta ba ya shiga motsa baki ya rasa taya zai bata ha?uri da ?yar yay ?arfin halin ce mata don Allah tayi hakuri bai kula bane shiru bata ce mashi komai ba bata kuma Wago face Winta ba, saida ya ?ara bata ha?urin sannan ta janye hannun idanunta suka shiga cikin nashi ta shiga kallon shi fuska a tamke, lokacin da Kamalu ya haWa ido da ita saida gaban shi yay mugun faWuwa tsoro ya kama shi ganin kalar ?wayar idonta, kasa jure ma kallonta yayi ya sauke idon shi ?asa gaban shi na Wan faWuwa ganin yadda ta Waure fuska gashi bai san wacece ita ba,

"Are you blind?" kaman daga sama yaji zazza?ar muryarta ta faWa har saida ya haWiyi abu kafin ya Wago ya kalleta tunanin bata jin hausa yay da yake yayi Secondary kuma yanzu da yake shirin cigaba da karatu Kawu Amadu na koya mashi wasu abubuwan harda turanci dama kuma yana ja don duk yan Wakin su Fatuu ba laifi kan su na rabawa,

"I'm sorry please i bump into you, it was an accident my attention was elsewhere" ya faWa da yar rawar murya sautin turancin gwanin daWi abunka da Bafullatanin Asali, bin shi tay da ido kawai tana ?are mashi kallo ba tare da tace komai ba shikam da ?yar yake jure ma kallon gray eyeballs Winta ganin bata ce komai ba yasa shi ?ara ce mata please he's sorry sai lokacin ta motsa baki a hankali ta furta "is okey" ganin tana ?okarin du?awa ta Waukko haWaWdar purse Winta yasa shi rigata du?awa ya Waukko mata ya mi?a mata still kallon shi take tayi, tana amsa sai ji yay ta furta "Nagode" daga haka ta wuce ta nufi gaban hall Win dama itama li?in zata yi, saida Kamalu yay mamakin godiyar da tayi mashi gashi yay tunanin bata jin hausa ne, juyawa yay ya nufi komawa wurin zaman shi don Fatun tuni ta zauna kuma sai yaji ma yin li?in ya fitar mashi a rai, yana komawa su Kawu Amadu suka tambayeshi miya haWa shi da wadda suka hango su tsaye ya faWi masu ya bugeta ne bai gani ba har jakar hannunta ta faWi Tk yace bata yi mashi masifa ba yace a'a kawai tace mashi shi makaho ne da turanci sai ya bata hakuri ya nuna mata hankalinshi na wani wuri tace shikenan Tk Win yace yayi sa'a don masifaffa ce, tambayar shi yay ya santa ne yace mashi eh itama jikar Hajiyar Senator ce sunanta Farha ?anwar kishiyar Yayar shi Fatuu Kamalun ya jinjina kai Amadu yace ya bai amso kuWin li?in ba ya bashi amsa da ta riga ta zauna cikin mutane a bashshi kawai, Tk na dariya yace yanzu sai ace bazasuyi ma Mino li?i ba gaskiya da basu kyauta ba, ?arshe dai sai tansfer Win Amadu yay aka basu Cash suka haWa dana Tk sukai li?in,

Alhamdulillah an gama Dinner lafiya anci an sha an nishanWu an zubar da galan galan na farinciki an cashe iya cashewa an raba souvenirs iri iri wasu cikin nasu Laila harda hotunansu nasu Mino dai sunan su ne kawai wasu kuma tare aka sa sunan nasu baki Waya dasu Laila, bayan sun koma gida kowa a gajiye yake Fatuu taso tayi fira da Fauzy amman ta gaji sosae hakan yasa tayi wanka su twins ma tayi masu suka kwanta.

Washe gari ana tashi aka fara shirye shiryen Walima don da wuri za'ayi saboda ?arfe ukku na rana za'a tafi da Laila Kano can za'a kaita itama tafiyar Jirgi za'ayi Mino kuma sai bayan Magrib za'a kaita gidanta, bayan sun gama yin Breakfast Gwaggo ta iske Hajiya bayan sun gaisa tace mata dama zata tambaya ne ko za'aje a shirya ma Mino Waki tunda da aka kawo kayan ba'a biyo an shirya ba Hajiyar tace ai tana tunanin kamar ma an shirya mata amma bari ta tambaya, Mom ta kira a waya bayan sun gaisa tayi mata Maganar shirya gidan Minon tace ai ansa an shirya kayan tun bayan da aka kawo su tace to, bayan sun gama wayar ta faWi ma Gwaggo tace saidai ko in suna son zuwa ganin gidan da sauri Gwaggo tace a'a tunda za'a je kaita sun gani, ana yin salar Azahar aka fara yin Walimar Amare sun sha shaddoji da akayi ma tsantsararren Winki kowa kalar tata daban Walimar ma harda ankon Material voile aka yi kowa yayi kyau mutane nata zuwa itama Mino harda kyaututtuka aka rin?a bata, Walima ta ?ayatu anci ansha anata fatan alkhairi ga ma'auratan, Misalin karfe ukku da yan mintuna duk aka fito harabar gidan rakiyar Laila da aka zo tafiya da ita, cikin wanda zasu tafi kaita harda Hajiya Maryam da Aunty da Jidderh da wasu yan uwan su yan Ethiopia sai wasu ?awayenta da kuma wasu yan uwansu na Katsina da Daura harda Fanan Fatuu dai banda ita, anata bankwana da ita ta canza shiga zuwa jigunan lace duk yadda ta daure saida ta matse ?walla lokacin da Mom Win su ta rungumeta haka Hajiya ma, su Kawu Amadu na daga can gefe suna kallon yadda aketa bankwanan, bayan masu tafiyar sun shiga motoci anata Waga masu hannuwa suka tafi sai fatan Allah ya kiyaye, Fatuu na tare da Fauzy har sun juya zasu koma ciki Fatuu taji an kirata hakan yasa ta dakata ta juya don taga waye ya kirata, Kamalu ne ya nufota yana sanye da farar shadda bayan ya ?araso inda suke da murmushi ya gaishe da Fauzy itama tana murmushi ta amsa tay mashi ya hidima, don ta basu wuri yasa tace ma Fatuu ta isketa ciki tace to, tana murmushi tace ma Kamalun da wani abu ne yace eh wllh kuWi yake son ta bashi zasu shiga gari ne shi kuma baida ko sisi ko jiya ma har zai zo ta bashi na yin li?i sai Kawu Amadu ya bashi, wani kallo tayi mashi tace "Duk yadda kai kalar Ya'yan masu kuWin nan amman kake tambayar kuWi"

dariya yay yace "to ai kinsan komai dai ba Wan masu kuWin bane Wan masu shanu ne" yadda yay Maganar ne ya bata dariya tace to ai suma masu shanun suna da kudi yace uhm ayi shiru dai amman ga inda masu kuWi suke nan, tambayar shi tay ya akai baida kuWi yace to ai anyi hidima ya kuma yi Winkuna tace hakane gashi nan ai yanata saka kaya sai kace shima Wan Senator Win ne ya saka dariya, ce mashi tay yaje zata tura mashi yace tunda dai ga wayar nan a hannunta ta tura mashi yanzu zasu fita bazasu ma koma cikin gidan ba,

"Kodai kun yi yan mata ne zakuje siya masu ice cream" tay Maganar tare da yi mashi wani kallon tuhuma yana dariya yace waye zai so su haka basu da ko sisi tana ?o?arin tura mashi tace ai ba'a ganewa, duk wannan abun idon Farha na akan su tun lokacin da Kamalun ya taho wurinta, dubu asharin ta tura mashi tace gashi nan suyi maneji don a Abuja ba wani abun kirki zata siya masu ba bata da kuWi sosae yana murmushin jin daWi yace a hakan ma ya gode sosae Allah ya barta da Baffan su twins tana dariya tace Amin tay mashi sai sun dawo, tana niyyar juyawa ta tafi Farha ta ?araso wurin itama ankon Material Win da kayi ne a jikinta suma riga da skirt ne aka mata tayi Waurin kallabi Zarah Buhari dark ash Win sumarta ta zuba a gadon bayanta, Kamalu na ganinta gaban shi ya faWi don ya ganeta ya bita da kallo, murmushi Fatuu tayi mata tace mata sannu itama Wan murmushin ta mayar mata ta gaishe da ita bayan ta amsa ta maida idonta kan Kamalu suka haWa ido a hankali yace mata sannu ta Waga mashi kai kafin ta maido idonta kan Fatuu tace mata brother Winta ne taga kaman sun yi kama tace mata eh Yayanta ne shi take bi mawa ta jinjina kai sai kuma ta ?ara cewa the same parents suke dashi kenan Fatun tace eh su biyu ne Mom Win su ta haifa kafin ta rasu a hankali tace Allah ya ji?anta Fatuu ta amsa da Amin daga haka Farhar bata ?ara cewa komai ba ganin haka yasa Fatuu ce mata bari ta shiga ciki tace Ok, tana juyawa Kamalu ma ya juya zai tafi da sauri Farhar tace "Hey..." dakatawa yay ya kalleta ta bishi da ido kaman bazata tanka ba bata san daurewa kawai yake yana kallon idonta ba, sai bayan Wan lokaci tace mashi ya bugeta jiya amman bazai iya tambayar ya take ba, sai da ya haWiyi abu sannan cikin kama kai yace tayi ha?uri yaga wurin kaman lafiya lou, Wan yamutsa baki tay tace dole sai wuri ya fashe ne ko yayi alama zai yi ciwo girgiza mata kai yay yace "to kiyi ha?uri fatan wurin bai yi maki zafi" Wan murmushi tay ta Waga mashi kai, shiru suka Wan yi can tace mashi a Yola suke ko yace mata eh,

"kai ya baka zo Katsina ba?",

ya bata amsa da ai yanzu a Katsinar yake zaune, kai ta Waga sai kuma tace "can i know your name?" amsa ya bata da sunan shi Kamalu ta Wan yamutsa fuska tace suna ne haka yana murmushi ya bata amsa da eh, gyaWa kai tayi tace bata ta6a jin sunan ba ko nasu ne na fulani yar dariya yay har ha?oranshi suka bayyana gefen kumatun shi duk ya lotsa kamar yadda na Fatuu ke yi, tambayarta yay to tasan suna Kamal ta jinjina kai alamar ta sani yace to sunan shi kenan tace amman miyasa aka maida nashi haka ya bata amsa da haka ya taso ana ce mashi shiyasa tace ya hana ana ce mashi hakan Kamal yafi, ce mata yay ai an riga an saba yanzu zai wuya a bari tace Ok, wayar shi ce ta fara yin ringing ya Wagota yana kallon mai kiran ganin Kawu Amadu ne yasa bai Waga ba ya kalleta yace bari yaje ana jiran shi ta furta Ok, har zai juya tace ya bata lambar shi idan wurin da ya buge mata na mata ciwo zata kira shi yazo ya kai ta Hospital daga yadda tay Maganar ya gane wasa take yana murmushi yace to, bayan ya bata tace zata kira yanzu sai yay saving yace Ok daga haka yay mata sai anjima ya juya ta bishi da kallo hakanan bata san miyasa ba komai nashi burgeta yake, yana zuwa wurinsu Amadu yace wai mi ya tsaya yi wurin wanccan Kamalun yace mashi ba komai tazo wurin Fatuu ne to shine tayi mata bayanin shi Yayanta ne Amadun yace to kuma shine sukayi tsaye bayan Fatun ta tafi, ce mashi yay ta tambayi sunan shi ne, kafin Amadu ya sake cewa wani abu Tk na yar dariya yace to Kodai ta ?yasa da Wan fillo ne Amadu ya Wan ta6e baki yace da dai wata ba waccan ba har abada bai tunanin zata yi soyayya da talaka,

Tk yace "ka san abun Allah, ai dama irin su ta haka Allah ke kama su, da kuma abun ya bada kala Wan fillo da baturiya"

dariya Kamalu yay ya tambayi baturiya ce Tk yace Babanta ne bature yace ashe shiyasa yaga idanunta wani iri daga haka suka tafi, Bayan Fatuu ta koma ciki part Win data zauna lokacin data haifi twins ta nufa dama acan ta sauka Mino ma da Aysha da Safnah duk suna tare, a parlor ta iske Fauzy zaune dasu Safnah harda Mino ta mi?a mata hannu tace ta taso su shiga ciki, bayan sun shiga cikin Bedroom Win a saman gado suka zauna Fatuu na murmushi tace "Amaryar Ya Sameer bamu samu mun zauna ba inata son in tambaye ki ya amarci" Wan ta6e baki tay tana murmushi tace ai yanzu amarci ya wuce Fatun tace duka wata ukkunne zata ce amarci ya wuce tace Uhmm kawai, hira suka cigaba da yi harda ta makaranta suna cikin yi Fauzy ta kai hannu ta Waukko jakarta dake a saman bedside data aje tun Wazu ta buWe, wata yar farar roba mai kyau ta fiddo tare da farin hanky ta maida jakar bayan ta daidaita zamanta ta latsa saman robar ya buWe Fatuu nata kallonta a zaton ta wani abun ci zata fiddo kawai sai gani tay ta kai bakinta saitin inda ya buWe ta zubda miyau kafin ta saki marfin ya rufe tasa hanky Win tana goge gefen bakinta, sakin baki Fatuu tay tana kallonta da alamun mamaki, kallonta Fauzy tay suna haWa ido tayi murmushi tace mata ya akai ne, hannu Fatuu ta kai ta kama ha6a tace "Ke wai tsaya mi hakan da kikai ke nufi, ni nayi zaton ko Sweet ce zaki fiddo sai inga kin zubda miyau!" Dariya Fauzy tayi tace tun Wazun yake damunta tana ta daurewa ta haWiye saboda mutane, waro ido Fatuu tay ta buWe baki da tsananin mamaki tace "Wai kaddai ciki gare ki Fauzy?" tana murmushi ta Waga mata kai alamar eh, hannu Fatuu tasa ta rufe baki sai kuma ta cire cikin washe baki tace "Ashe shiyasa naga kin ?ara haske sosae saidai kuma baki yi ?iba ba sai ma Wan ramewa da kikai ni na Wauka duk amarcin ne yasa haka wllh" girgiza mata kai tay tace wahala ce don laulayi take sosae tayi mamakin ma yadda da tazo bikin ya rage sosae har abinci take ci acan ai ko abincin bata iya ci ga yawan amai har magani aka bata wanda zai sa ta daina aman in tana sha kullum to in ta sha sai ya rin?a damunta in bata yi aman ba sai kawai wani lokacin ta ?i sha, tambayarta Fatuu tayi watan cikin tace mata Waya da rabi,

"Kenan ma kice da kuka je Honeymoon kika same shi" kai ta Waga mata tace saida yay sati ukku sannan suka san dashi ko Aunty Mareeya bata sani ba sai yanzu tana ganinta ta gane Fatun tace "Ni kinga wllh ban gane ba saboda banyi tunanin Ya Sameer Win zai bari ki samu ciki da wuri ba daga yanayin shi",

"Aikuwa yay farinciki dana samu ni kaina saida nayi mamaki don ko Maganar haihuwa bai yi man nayi zaton bazai so cikin ba sai gashi baki ga yadda yake nan nan da ni ba, dafa wai ma bazai zo bikin nan dani ba Aikuwa nayi ta mashi kuka yace shi tsoron shi kada wani abu ya samu cikin nace mashi ai kema da cikin kika taho bikin ko shine yace to zai taho dani da yake kuma gaskiya bai son yaga damuwata yanzu kinga ya rude",

yar shewar dariya Fatuu tay tace "kice dai kin dam?e ya Sameer a hannu aikin Aunty Mareeya yayi kyau",

tana yar dariya tace "Aikin Aunty Mareeya ko aikin jawo ma mutum wahala ke wllh saida ta kai ina tsoron shi dana ji sallamarshi sai gabana ya faWi har Aunty Mareeya na ta6a kira nayi mata complain taita ?arfafa man gwuiwa daga baya dole na saba tunda naga yana son hakan sosae" Fatuu na dariya tace "kice dai Ya Sameer ya Magantu yadda Aunty Mareeya ke so" Dariya Fauzy ta saka tace wllh ita farko ma yay ta bata mamaki sai kace ba shi ba Fatuu dake ta dariya tace haka suke fa miskilan nan dama Aunty Mareeya ta faWa ta haka ake jin bakin su,

"Amman dai ba wata matsala da kike fuskanta a wurinshi ko" Fatuu ta tambaya bayan sun gama yin dariyar, girgiza mata kai Fauzy

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login