Showing 42001 words to 45000 words out of 134406 words

Chapter 15 - SIRRIN MU Complete HAUSA NOVEL

21 Aug 2024

18359

Sheikh yace "is that true?" Shiru Sheikh yay idanunsa na sauya launi Granny tuni tai bayan kujera ganin abinda Sheikh yake, cikin tsawa Uncle Sham yace "dakai nake Imam haka ne? Gsky ne abinda Mama take fa蓷a ko mene? Da gaske ne akwai Aljana jikinka" idanun Sheikh akan Mami yaja ajjiyar zuciya ba tare daya kalli Uncle Sham ba yace "haka ne, kuma ina sane da ita a jikina rayuwa da ita ya fimin rayuwa da Iyayena tunda ta fisu 茩auna ta,bana jin kuma akwai abinda zai rabani da ita sai dai wata sabuwar 茩addarar" kasa mgna Uncle Sham yay sai kallon Sheikh kawai da yake, Arjun ma with much surprised yake bin Sheikh da kallo, sai yanzu abubuwa da dama suka fara dawowa kansa, wato Airahn da yake yawan fa蓷a ba kowa bace face Aljanar dake jikinsa, zanan da yay ba kowa bace a jiki face Aljanarsa, da yawan lokuta yana ganin Granny a jikin Sheikh ashe ba kowa bace face Aljanar dake jikin Sheikh, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wanne irin abu ne haka? Ta maza Uncle Sham yay yace "ita aljanar da ita zaka zauna har 茩arshen rayuwarka kenan?" Kai tsaye Sheikh ya bashi amsa da "Eh" Jinjina kai Uncle Sham yay ba tare da yay mgna ba ya 蓷auki wayarsa ya shiga latsawa harya fice daga parlon not too long time ya dawo ya zauna ba tare kuma da yace komai ba, cikin 蓳acin rai Sheikh ya kalli Mami ya jinjina kansa ita dai ko a jikinta tasan sai an cire Aljanar jikinsa sannan zata samu damar kasancewa da sweet Imam 蓷inta.

茦ara mi茩ewa Uncle yay babu jimawa ya dawo da wani babban Malami wanda yake 蓷auke da babbar jaka da kuma Kur'ani a hannunsa, zama Uncle yay fuskarsa a sake ya kalli malamin yace "Sit Malam" Zama Malamin yay kamar yadda Uncle Sham ya bu茩ata kallon tsaf yaywa Sheikh ya ganu gskyar lamarin, Sheikh wanda ya dur茩osar da kansa ya kalli Arjun yace "let's go" kafin Arjun yay mgna Granny dake bayan sofa tace "me kace?" "Malam ina son a cire Mutanan dake jikinsa yanzun nan" zama Malam ya gyara yana kallon Sheikh wanda yake zaune ko mutsi ba yayi sai sakin ajjiyar zuciya da yake.


A can cikin jeji kam Airah ce kwance tana fitar da numfashi sai Tijama dake gefenta tare da Tu蓳e, cikin mawuyacin hali ta kalli Tijama tace "Nasan bazan tashi ba, na san kin fini sanin suwaye suke farautar rayuwar Sheikh da kuma abinda suke so game dashi, Nakasar Sheikh ba daga Ubangiji take ba magauta ne suka samar da ita tun yana 茦arami,sannan ba Saudat ce ka蓷ai take bu茩atar wani abu game dashi ba,bayan ita akwai wasu, Ya kakata ina son 茩addarar Imam yazo masa da sau茩i, bazai iya 蓷auka ba naso na kasance dashi amma nima bani nake da kai na ba,akwai wanda ya halicci ne wanda a koda yaushe zai iya 蓷aukan rai na,amma ina son kimin wata alfarma Yake Kakata" Tijama da jikin Airah ya fara bata tsoro kuma ta tabbatar wannan karan ba zata tashi ba ta da蓷e da sanin Airah ba zai duguwar rayuwa kamar yadda ake fa蓷a sauran aljanu nayi,rashin Airah a jikin Sheikh ba 茩aramar tawaya bace amma dole tasan abin yi, kallon Airah tayi tace "Me kikeso ya jikanyata?" Sauke ajjiyar zuciya tayi idanunta na janye wa tace "kalli Tijama yadda Rayuwata yake ba茩in cikin rabuwa da ni? Basu san ko basu rabani dashi ba Ubangijin daya ha蓷amu yana gaf da rabamu ba, Tijama ina son Sheikh Imam hamdan Balarabe yay farin ciki a rayuwarsa bana son yay kuka akan rashina kiyi abinda zaki akan cikar muradina, kiyi 茩o茩arin 蓷aukan fansar da nace zanyi akan wanda ya lalata Rayuwar Sheikh Imam hamdan Balarabe, Tijama a koda yaushe numfashi na iya tsawaya ina son ki gayamin abinda kike 蓳oyewa game da Sheikh wanda kikace SIRRIN MU ne ina son sani yanzu" shafa kanta Tijama tayi tace "Tabbas nakasar Sheikh ba lalura bace samar da ita akai ta hanayar a siri tun yana cikin mahaifiyarsa abu guda ne zai dawo masa da 茩afafuwansa har ya fara tafiya kamar sauran mutane" Airah na jan numfashi idanunta na tsiyayar da hawayen ba茩in ciki da kuma takaicin rabuwa da Mijinta tace "Menene shi Yake Kakata?" Tijama ta kalli Tu蓳e tace "Sheikh bazai ta蓳a taka 茩afafuwansa da zumar tafiya ba har sai ya kusanci mace....




馃Hello nace idan an fitar da wannan sai a nemi sanitizer a wanke hannu asa face mars aci gaba da zaman jira



SIRRIN MU isn't free book
Contact to subscribe 08119237616 ga Niger 84506476
10/17/21, 10:23 PM - Mrym: *_NLUV馃挒_*
3锔忊儯1锔忊儯-3锔忊儯2锔忊儯
Zare ido Airah tayi tana 茩ara kallon kakarta ta "Tabbas sai ya kusanci mace yay tarayya ta auratayya da ita sannan 茩afafuwansa zasu warke ya fara tafiya kamar sauran mutane,haka tsarin karyewar asirin yake, komu bamu da ikon da zamu karya wannan sihirin sai dai mu taimaka masa wajan samun macen da zata bashi wannan damar" kuka Airah tasa tace "Mene yasa sai an sama min kishiya kafin Rayuwata ya samu lfyarsa? Bazan iya jurar ganinsa da wata ba koda babu raina please Tijama do something" ri茩eta Tijama tayi sosai sbd rawar da jikinta ya fara cikin 茩aramin lokaci ta fara kokawa da numfashinta, ri茩e hannun Tijama tayi da kyau tace " please i need your help Tijama" shafa kanta tayi tare da danne mata 茩irji tace "zan maki komai zan 茩arasa cika maki muradin ki ko bayan babu ranki, amma dole ki rabu da Imam a dai-dai wannan lokacin domin hakan shima wata damace a garemu, ki fita a jikin Sheikh yanzun nan Airah" kuka Airah tasa tare da juya idanunsa zuwa gefe guda tana hango Sheikh dage gaban Uncle Sham kansa a 茩asa, girgiza kai tayi tace "i can't Tijama dan ki rabu dani na mutu a jikinsa ko zan samu sau茩in abinda na keji a raina, ki barshi yaga mutuwa dan Allah Tijama" tsawa Tijama ta buga mata mai 茩arfin gaske tace "idan baki fita a jikinsa ba yanzu tayaya zan samu damar kawo maki shi nan? Ya zama dole ki hqr da jikin Imam tunda ba tare Ubangiji ya kawo ku duniyar ba, idan kuma taimakon nasa da gaske kike sonyi dole ne ki 蓷auki taki 茩addarar kamar yadda shima sabuwar 茩addara zata riskeshi a tasa rayuwar, rabuwa da Sheikh Imam hamdan Balarabe ya zama dole domin hakan ka蓷ai zai sanya mubawa matar Ubansa kunya a gaban muta nan da suka amince mata,kinga ko gaba ta kai wani zancen ba zasu yarda da ita ba" 茩an茩ame jikinta tayi tana karkarwa tare da danne 茩irjinta dake mata ciwo tace "shikenan zan rabu dashi Tijama amma kimin al'茩awarin babu wata 拼ar macen da zai ra蓳a soyayyata ce kawai zatai ta tasiri a zuciyarsa, da soyayyata zai dauwama ita zata zamu abokin shirarsa, zata zame masa mata 蓷a Aboki, dan Allah kada ki bari wani abu ya raba tsakani na da Rayuwa ta" tsaki Tijama taja duk tana tausayin jikar ta amma hakan bazai sanya ai mata abinda take so ba,ita da zata bar duniyar ta yaya zata bar Mutum kamar mara lfy bayan tafi kowa sanin ingantacciyar lfyar da Sheikh yake da ita, clamly tayi tace "Look! Airah do what is right not what is easy, kada kiyi amfani da damar ki ki cuci bawan Allan da baiji ba bai gani ba, kinsan cewa da bakya jikin Sheikh da bazai ta蓳a kawo iyanzu ba tare da mace ba, yana da 茩arfin sha'awa irin mazan nan ne da basa iya jure abinda suke ji game da mace, Sheikh kaifi 蓷aya ne tayaya kike tunanin duk wannan lafiyar da Ubangiji ya ba shi mu kuma mu zama masu son kanmu wajan da茩oshe sa, wanda suke lalata rayuwar Sheikh kima suke nema ke kuma naki soyayya ce, Kima 蓷auke rayuwa take Soyayya kuma bada rayuwa take,kinga hakan na nufin zaki iya sadaukar da dukkan farin cikin ki akan Imam, to ki 茩arfafa zuciyarki kiyi supporting 蓷ina akan raguwar aikin da baki 茩arasa ba, na shaida kema kin shaida kaima Tu蓳e ka shaida Airah ba zata tashi ba, to why are you wasting your time akan abinda kinsan ba mai yiwuwa ba ne" zuwa lokacin Airah bata fahimtar abinda Tijama take fa蓷a idan Idanunta na kan Sheikh tana tuna yadda zai iya rayuwa babu ita, tana tuna tarin 茩alubale da kuma manyan 茩addarori da zasu hau kansa? Bazai iya ba Sheikh 蓷inta bashi da hayaniya bazai iya 蓷aukan tension 蓷in da zai hau kanshi ba, yaya zatai tabi magnar Tijama ko kuma ta shareta, Ajjiyar zuciya mai 茩arfin gaske ta sauke tana 茩ara dun茩ule wa waje guda yayinda wani jini ya fara biyo bakinta, da 茩arfi kuma ta sanya ihu da kuka, Tu蓳e ne ya ri茩eta yana fa蓷in "Airah kiyi hqr dole ki hqr da Sheikh idan soyayyarki gsky ce ya zama dole ki bamu damar da zamu taimakawa rayuwarsa ya samu lfy sannan mu hska masa ba茩i yansa" cikin fitar hayyaci da 蓷aukewar numfashi tace "What should I do?" Kai tsaye Airah tace "ki sakar masa mazantakarsa frist, sannan ki dawo masu da nutsuwarsa ya fara gani mata a matansu ba kamar yadda yake masu kallon maza ba,ki dawo masa da asalin fa蓷an sa domin wannan shiru shirun da yake dashi duk kece sili duk masifar ABU MALEEK da DEEN Sheikh ya fiso so dole kibar hakan ya faru" cikin kuka tace "idan nayi hakan kina da tabbacin zai samu farin cikin da nake masa burin samu a rayuwarsa?" "Why not? Zai samu farin ciki kafin samuwar farin ciki amma dole sai zu茩ata sun 蓳aci, kin san idan kana son abu 茩alu bale baya hana kaso abu sai dai ka 茩ara kusanta kanka dashi, zaki mmkin Sheikh zai zama Garkuwa ga jama'ar gari, zai zama zaki wanda babu wanda ya isa ya taka shi, zai zama zakara wanda kukan sa ka蓷ai zai tashi al'umma" rungome Tijama tayi a jikinta bata 茩aunar rabuwa da Sheikh 蓷inta amma ya zama dole ta rabu dashi tunda hakan ne ka蓷ai zai sama masa farin ciki, wani gigitaccen ihu da 茩ara ta sanya sai kuma cak numfashinta ya tsaya.


Jikinsa rawa kawai yake tunda Malamin ya bashi ruwan rubutu yasha kana ya fara yi masa karatu ko 蓷aga kai baiyi bare su sanya ran aljanar dake cikin sa zatai magana kuma ta fadi dalilin daya sanya ta shiga jikinsa, gumi kawai yake ha蓷awa jikinsa sai rawa yake idanunsa a lumshe ya sanya dukkan hannayensa ya rungome 茩irjinsa dasu sbd dukan da zuciyarsa take masa, Arjun na can gefe guda a zaune idanunsa ya ka蓷a yay jaa sbd 蓳acin rai harga Allah abinda Mami tai baiji da蓷insa ba, yasan cewa Sheikh yana da matsala sbd shi kansa yasha kamasa yana wasu abubuwa na almara amma bai ta蓳a kawowa kansa akwai wasu mutanan 蓳oye a jikin Sheikh 蓷in ba, kullum yana masa addu'ar Ubangiji ya yaye masa damuwa da kuma 茩unci dake cikin zuciyarsa,Malamin ne ya sauke numfashi yana mai 茩ara 茩arewa Sheikh kallo da idanunsa, kafin yaja numfashi yace "Sheikh Imam hamdan Balarabe kalleni" banza Sheikh yay masa domin shima ya fara fita daga nutsuwarsa ji yake kamar yana shirin rasa wani abu mai matu茩ar muhimmanci a rayuwarsa, Uncle Sham ya kalli Malamin yace "Ya dai Malam?" Jinjina kai Malamin yay yana 茩ara kallon Sheikh kana ya kalli Mami yace "Hajia kin tabbatar da abinda kika fa蓷a gsky ne?" Kai tsaye Mami tace "haka ne Malam" bai 茩ara mgna ba ya 茩ara bu蓷e shafin Alkur'ani yaci gaba da karatu sai dai yay karatu mai yawa amma ko mutsi Sheikh bai ba, gajiya yay yace "gsky ko ba茩in Aljani ko Aljana ce a jikinsa wannan karatun ya isa yasa ya 茩one bama yay mgna ba" cike da gamsuwa Uncle Sham yace "Malam kenan babu batun mutanan 蓳oyen ko?" Kai ya jinjina yace "gsky babu sai dai akwai abu a jikinsa amma bana da ikon aiki a kansa sbd ba huru mina bane" mi茩ewa Uncle Sham yay yace "Ngd Sosai Malam Allah ya 茩ara girma" Malam yace "Kai haba yiwa kaine fa kuma ai aikin mu ne ai so no need to thanks" rakasa yay har waje yana fita Granny ta fashe da kuka tana fa蓷in "Ni daman nasan sharri ne kawai irin na Saudala,banda haka yaya za'ai Alaramma kamar Imamu ace wai Aljana ta auresa fisabilillahi? Aiko makaho ya sha yasan wani zancan bana 蓷auka bane,hankalinki ya kwanta kinci zarafin Imam to wlh keda Allah ha茩茩ina ka蓷ai bazai barki ba bare na Imam,babu ruwana ai Allah gafurur rahimu ne sai kiga Ubangiji ya yafe maki idan kiga nemi ya fiyar mu,amma wlh ba wasa ba kinci mutuncinsa aljani fa ba wasa ba" daga ba茩in 茩ofa Uncle Sham ya tsaya yace "Yaya haka Mama? Meye abin kuka a nan kuma,ai hamdala zaki tunda dai Allah ya 茩aresa" 茩ara rushewa da kuka tai tana fa蓷in "babu ruwana ka barni nai kukan ko zanji da蓷i kaima Imamu yi abunka za nemu maka ruwan wake fuska" Jinjina kai kawai Uncle Sham yay tare da fa蓷in "Toke Saudat kinji me Malam yace dan haka ki sake jikinki babu komai in sha Allah! Allah zai kiyaye" Anut Amina tace "Ameen" Arjun ma ya amsa, Mami kam kasa samun nutsuwa tayi sbd ta tabbatar da Aljanun Sheikh sbd ga shaidar a fuskarta nan, Tayaya za'a ce yanzu kuma babu su? Gsky akwai wani abu akwai dalilin rashin bai yanar su amma ne shi? Shine abinda bata sani amma dole ta bincika, tashin hankali Sheikh ya shiga hankalinsa ya茩i kwanciya da rashin bai yanar Aljanarsa shi zafi kowa farin ciki ba bayyanar ta domin zai samu 拼an cin rayuwa da ita ba tare dasa ido ko kuma wani abu ba,yasan kuma dukkan aljanu suna bai yana yayinda ake masu ru茩iyya where is my fairy? Tana ina? Ina ta 蓳oye, nan da nan idanunsa ya 茩ara birkicewa lura da hakan kuma yasa Uncle Sham cewa Arjun "kuje gida Allah ya tsare" mi茩ewa Arjun yay tare da tura Wheelchair har zuwa compound na gidan kai tsaye kuma ya taimakawa Sheikh ya shiga cikin motar kana ya na蓷e Wheelchair shi kuma ya zauna seat 蓷in driver yaja motar da gudu zuwa gida, suna fita Granny ta mi茩e itama ta nufi waje driver yaja ta zuwa gida, ajjiyar zuciya Mami ta sauke kafin ta mi茩e tsaye tace "Hjy Amina bari naje nima" da Murmushi a fuskar Anut Amina tace "kai haba dai ga lunch ina shirin shirya maki ai ba za'ai haka ba" Murmushin dole Mami tayi tace "kada kiji komai wlh am full Ngd sosai" Sallama sukai Mami ta shiga motar taja ta gudu kai tsaye gidan Fariha ta nufa.

"Ni kam kamar akwai abinda Saudat take 蓳oyewa naga gaba 蓷aya ta茩i sakin harta" Uncle dake juyawa white rice 蓷in gabansa with vegetables source wacce taji cow meat sai 茩amshi take, yace "Wutar mai zargi daban take ki kiyayi kanki Mmn Huda" spoon 蓷in hanunsa ta amsa ta fara basa abincin yana lumshe ido tace "Allah ba wasa ba Uncle na da蓷e da zargin matar nan akan Sheikh, kana kallo a ranar da Mahaiyarsa ta haifesa a ranar kuma Abban Sheikh ya saketa" spoon 蓷in ya amsa yana fa蓷in "kina samun ladar ci da miji kuma kina zobe ladan ta hanyar gulma ko?" Dry tai masa tace "kai dai kawai kace cikinka bai cika ba sai nafi gane karatun" ka fa蓷a ya 蓷aga mata yace "whatever".

Tunda suka 蓷auki hanya ya kifa kansa a a tsakanin cinyoyinsa ya shiga fesar da numfashi da sauri虏 ko Arjun yana iya jiyo yadda Numfashinsa ke fita, kamar wanda zazza蓳in ma sharshara yake shirin kamawa tsoransa 蓷aya kada ciwonsa ya mutsa domin yasan Wannan ajjiyar ziyara da yake ba haka kurum ba ne, yasu shigewa dashi hospital amma yadda yake ganin yanayinsa da kuma abinda ya faru last time yasa yaci gaba da driving a zuciyarsa yana nemawa Sheikh 蓷in sau茩in abinda yake damunsa.

Bayan yayi parking motar ya shiga 茩o茩arin zaro Wheelchair 蓷in daya santa a back seat, da sauri Sheikh cikin zafin nama ya dur茩osa tare da 蓷ura soft fresh hands 蓷insa a 茩asan tarazon gidan, cikin tashin hankali Arjun yace "Buddy mene haka what are trying to do? Idan rai ya 蓳aci nutsuwa ke samu sa" ko inda yake bai kula ba yaci gaba da tafiya kamar yadda guragu suke cikin 茩aramin lokaci guwwar wandonsa tai ba茩i茩茩ir sosai yake jin zafi da kuma ra蓷a蓷in da hannayensa zuwa 茩afafuwansa suke masa sbd bai ta蓳a gwada irin wannan tafiyar ba tunda ya samu kansa a cikin wannan lalurar, ya gwammace ya azabtar da kansa da wani ya azabtar da shi, he need his wife yana bu茩atar Aljanarsa ita kawai zai samu yaji da蓷i a ransa, 蓷umin jikinta da kuma soft lips 蓷inta sune ka蓷ai za suyi tasiri a cikin zuciyarsa har ya samu nutsuwa, shock 蓷in da Arjun ya shiga yasa ya kasa koda mutsi, tausayi da 茩aunar Sheikh suka 茩ara ratsa zuciyarsa. A haka ya 茩arasa har babban parlon gidan ya samu Sa'a babu kowa kai tsaye ya nufi flat 蓷insa yana jan guwwar sa zuwa lokacin har shaddar dake jikinsa ta fara yagewa, yana shiga ya buga 茩ofar da 茩arfi tare da danna mata key, ya saba yiwa Granny kuka amma bai yarda wani wanda ba Granny ko Airah ba yaga zubar hawayensa, yana da rauni amma rauninsa aka abinda yake so ne, ke nan Airah itace weakness nasa, shiru yana sauraran bugun zcyarsa duk yadda idanunsa kuma suka zo zuba da ruwan hawaye ya tauye masu ha茩茩in su ta hanyar hana faruwar hakan rashin Airah a yanzu shine ka蓷ai zai sanya a zubda hawaye, da fasa yaji an sanyin hannunta ka蓷ai ya tabbatar masa da cewa itace da wani mugun saurin ya 蓷aga kansa,tana tsaye a kansa hannunta dafe da saitin zcyarta sai fitar da numfashin wahala take, bai tsaya jiran komai ba yasa hanunsa ya fisgota zuwa jikinsa tare da manna ta a faffa蓷an 茩irjinsa ya 茩an茩ame ta yace "My Airah my Aljana my Fairy Rayuwar Sheikh Imam hamdan Balarabe where are you hiding? Why are you leaving me? You broke my heart, don't

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login