Showing 6001 words to 9000 words out of 134406 words
bakwai na safe yana cikin masallacin,sai da ya kammala sannan ya kalli babban abokinsa kuma Amininsa Arjun wanda ya shigo masallacin yanzu "bacci na keji Arjun" mi茩ewa Arjun yay domin yasan indai Sheikh bai Wannan baccin daga bakwai zuwa sha 蓷aya na safe ba to bazai bar kowa ya huta ba, kar蓳ar Kur'anin hannunsa yay ya ajjiye inda ake ajjiye littafan matsallatan,cikin nutsuwa Arjun ya fara tura Wheelchair 蓷in suna tafe Arjun na masa Shira Aliyah sabuwar budurwar da yay a nan garin, Murmushi kawai Sheikh yay yace "Allah yasa albarka" tsaki Arjun yay yace "Buddy a condition 蓷inka yaci ace ka ajjiye matar da zata kula dakai,wacce babu hijabi tsakanin ku zata iya yi maka komai ba tare da jin wani nauyi ba, Granny kullum shekarunta 茩ara jaa yake,wata rana ba zata iya kula da kai ba,kai ka bathroom dawo dakai cikin bedroom, shiryaka,kana ganin hatta mai ita take shafa maka,kaga dole ba zata shafa maka a inda bai dace ace ta gani ba,amma idan matar kace komai zata iya yi maka ba tare da taji nauyinka ba" kamar Imam ba zai magana ba sai kuma ya ce "kai ma ka fara gajiya da taimakon da kake min ne Buddy?" Girgiza kai Arjun yay ya ce "No! At all,kawai da ina ganin abinda yake dai-dai ne, Ni abinda nake maka gaba 蓷aya nawa yake? Tsakani na dakai na kaika gidan redio kana gama program 蓷inka na zo na 蓷auke ka, sai zuwa shopping ko saloon wani lokacin ma baka bari akai ka,sai kuma zuwa Aikin hajji idan lokaci yayi ko Umara" lumshe idanunsa Sheikh yay kafin ya sauke numfashi ya ce "to menene da matanne? Ni bana da interested akan any women wlh,koda ina dashi wa kake ganin zata zauna dani?? Bana da fellings akan wasu mata wallahi gaba 蓷aya shirmammu ne,basa da tausayi?" "Au haba??" Cewar Arjun domin ba 茩aramin haushi Sheikh ya bashi ba, Sheikh na sakin Murmushi domin yana son ya ga Arjun na gaya masa gsky shi kuma ya nuna baya ganewa gaba 蓷aya, Arjun ya ce "Buddy ko dai baka da lafiya ne?? A Wannan zamanin da muke ciki ai kamar da sha'awa ake haifar mutum wallahi,kai sheda ne kana ganin mata kala-kala,dan 茩arya kake kace baka ta蓳a ganin macen da kaji kana sha'awarta ba,indai kaga Manhoon 蓷inka bata mutsa to wlh baka da lafiya" tsaki Sheikh yay ya ce "zamani ya lalace tunda Arjun yasan da蓷in mata" waro ido Arjun yay yace "kai Allah ya sauwa茩e dai,ina tare da babban Malam Alaramma kuma Sheikh Imam Hamdan Balarabe kake tunanin zan san mace indai ba aure nayi ba,kawai dai nasan ina bu茩atar mace kusa dani,domin kullum da ciwon ciki nake kwana wani lokacin sai nayi ta蓳a Arjun 蓷ina nake jin da蓷i" suna gaf da shiga Babban parlour'n daya raba manyan sides 蓷in Sheikh yace "meye Arjun 蓷ina kuma?" Kai tsaye Arjun ya ce "mtwsss! Hajiya ta nake magana be ma'ana Manhoon" ta蓳e baki Sheikh yay yace "Iskanci kawai,ka daina ba kyau is better kai aure idan shi ne salama a gareka" Arjun ya ce "Soon ma kowa ma baka 拼arta ka aura" Sheikh bai 茩ara magana ba,kallo guda yaywa Mami wacce take shirin fita bank dake aikin banki take, Murmushi tayi ta ce "Wlcm my dear" Arjun ya ce "Mrng Mami" wajansu ta 茩arasa tace "Yaya kake Arjun fatan kana kula min da my dear" Murmushi Arjun yay yace "Mami 蓷an naki ai 蓷an rigima ne" bata 茩ara kallon Arjun ba ta kalli Sheikh tare da dur茩osawa dai-dai fuskarsa ta shafa sajensa tace "Me kuma Mother taiwa son 蓷inta ba ko gaisuwa?" Idanunsa a rufe ya ce "Sabahul khairai" Murmushi tai masa ta ce "how're you and how are feeling now?" Ya ce "Allahamdulillah!" Kallon Arjun tayi ta ce "kada ka barshi yay bacci yanzu sai yayi breakfast" Arjun ya ce "In sha Allah Mami" idanunta akan Sheikh tai masa peak a forehead 蓷insa kana tai 茩asa da bakinta ta 蓷ura saman nasa ta sucking lips 蓷insa na 茩asa saurin runtsa idanunsa yay,tana gamawa tai waje tana fa蓷in "bye sweetie" da idanu Arjun ya bita harta fice daga parlour'n.....
10/17/21, 10:22 PM - Mrym: *SIRRIN MU*
*BY*
_鉁嶐煆� NIMCYLUV_
_This book is for sale it's #500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616, ga mutan NIGER sai suyi mgn a wannan number 84506476_
馃啌P
EPISODE7锔忊儯-8锔忊儯
Mami na barin parlourn Arjun ya sauke numfashi, tare da tura Wheelchair suka nufi cikin parlourn. Granny ce kwance saman bed tayi 蓷ai-蓷ai sai bacci take abinta hankali kwance, da sauri Arjun ya juya ya nufi inda Sheikh yake yana shan coffee a parlour, with much shock Arjun yace "Buddy i don't understand what's going on?" A hankali Sheikh ya zame bakinsa daga kan glass cup 蓷in ya ajjiye saman center table 蓷in dake gabansa kafin yace "Meke nan?", Arjun yace "na je flat 蓷inka na ga Granny ciki tana mopping, har muka gaisa yanzu kuma kace na 蓷auko maka zuma a fridge 蓷in Granny nai sallama bata amsa, hakan yasa na shiga cikin bedroom nayi expected wahala take, abun mamaki sai na sameta saman gado tana bacci da alama ko sallah asuba ba tayi ba", ya kai maganar yana kallo reaction 蓷in Sheikh, sai bai ga komai ba sai ma murmushin da ya ga yanayi "Ohh!! Ni ka maida wawa ko?" da blue eye balls 蓷insa ya kalli Arjun yace "Oh! come on dear me zance maka" Arjun yace "More explanation about two of them" ware ido Sheikh yay yace "Laa adaari" cikin fusata Arjun yace "what the you mean by that?,bayan kana gidan kuma Granny ita take maka komai" ta蓳e baki Sheikh yay idanunsa a kan cenema yana kallon labarai a Aljazeera yace "La takaffafuu" kai tsaye Arjun yace "wallahi sai ka fa蓷a min", a 蓷an fusace Sheikh ya kalli Arjun domin ya fara kai shi 茦arshe bai son mita, da kuma nanata magana, calming yay yace "dole ne nasan komai? Ko zaka saka nai bincike akan abinda bana da iko dashi ne? Wallahi Arjun ka kiyayi kanka ka cigaba da shiga sabgar da babu ruwanka, ni nan 茩arya nai maka or what???" SHI ma Arjun yace "Ashe ba zakai hankali ba Imam? Baka tunanin lafiyar ka, ko ka manta situation 蓷in da muke ciki, kullum kai ne zaman gida da tsaron Soldiers saboda gudun abinda zai cuce ka da kuma wanda zai sanya ai maka wani abun, amma kake ganin laifi na, wlh if i find out the truth you'll regret my dear" yana fa蓷in hakan ya nufi flat 蓷in Granny da ido kawai Sheikh ya bisa harya 蓳ace wa ganinsa, Arjun na tafiya ya ci karo da wata farar mage mai kyau gwanin sha'awa 蓷auke kansa yay daga kallon magen yaci gaba da tafiya, wayarsa ce ta fara ringing hakan yasa ya tsaya da tafiya kana yay answering call 蓷in, yana tsaye magen ta huce da sauri ta nufi flat 蓷in Granny, lokacin Granny ta farka tana ta sallami tana fa蓷in "A'a da mutanan gidan nan Arna za ai, babu tsoran Allah a ransu ace nai ta bacci kamar matacciya babu wanda ya kula da sabgata, kamar dai mara gata? To Allah dai yaga zuciyata ba ina sane na茩i sallar safe ba makara nayi wallahi tallahi, daman ita wacce ba'a gama sanin a wanne 蓳angare take ba tuni na sallama ta, shi ma Barista dake gantalalle ne sai ya rabu dani ko na mutu ko nai rai duk uwar ubansu 蓷aya, kai Allah gani gareka ni Fa蓷imatu da miji da mata duk babu na gari gwamma shi 茩arya yake rabtawa, ita kuma ku蓷in jama'a take kwashewa tun da dai naji a banki take aiki, kai amma dai anyi gantalallun mutane wlh" tana fa蓷in hakan tai cikin bathroom, "ni dai wallahi cikina kamar anyi min sata, babu komai sai hanji wannan da shayarwa ne ma sai naji labari", tana shiga bathroom farar magen na shigowa cikin bedroom 蓷in Granny, da ido magen tabi Granny da shi, kafin a hankali magen tai girgiza sai gashi ta koma siffar Granny tatasss babu abinda ya siffanta ta, Arjun ne ya shigo yana fa蓷in "Mrng Granny" kya蓳e Granny tayi tace "bana son gulma da fi'ili meye kuma Munin Ranjun? Kana gani ba'a mai dani komai a gidan nan ba,ai wlh Imamu da babu ni daya shiga uku, bashi da kowa da komai sai ni,Allah gatansan ni ce gatansa bawan Allah kenan", murmushi Arjun yay yace "haka ne fa Granny, kamar yanzu kika tashi ko makara kikai ne??" Wani kallo Granny tayi masa sai kuma tace "Yaushe ka arnantar dani Ranjun? Ka dai dinga jin tsoron Allah wallahj, babu ruwana sharrin da kai min ma ya ishe ka, yoo sharri mana da hankali na da komai shekara wajan 85 ai ba wasa kawai sai na zauna na makara a sallah, ai ni nan lokacin walaha nake jira kawai", jinjina kai kawai yay yace "bari na shige sai anjima na zo kai Buddy gidan Redio", "to to Allah ya kaimu ka gaida Sadiya" yace "za ta ji" yana fa蓷in hakan ya fice daga cikin bedroom 蓷in, da ido ta bisa yana fita ta riki蓷e ta zama magen kamar yadda ta shigo parlon.
Dawowa parlon Arjun yayi ya samu Sheikh yana shan 拼a 拼an inibi masu sanyi yace "am going Buddy sai zuwa anjima" plate 蓷in hannunsa ya ajjiye yace "ok mai dani falt 蓷ina" ba musu Arjun ya kama Wheelchair 蓷in suka nufi flat 蓷in Sheikh, wanda yafi ko wanne flat kyau da kuma tsaruwa a cikin gidan, idan kaga abubuwan da suke flat 蓷in Sheikh saika 蓷auka shi 蓷in wani lafiyayye ne, har cikin bedroom 蓷insa ya shigar dashi komai tsaf Granny da gyara amma a yadda suke tunani, da taimakon Arjun Sheikh ya kwanta saman makeken gadon sa, har Arjun ya juya sai kuma ya dawo,da 蓷an sauri yasa hannu ya zarewa Sheikh jallabiyar jikinsa sannan ya cire masa singlet 蓷in,fresh white skin 蓷insa ya bayyana ga santala-santalan 茩afafuwansa da cinyoyinsa da suka bayyana duk a waje, Arjun na gamawa yace "bye" idanunsa Sheikh a rufe yace "Jazakallah bilkhair" yana fita waje yana fa蓷in "it's my pleasure" Shiru Sheikh Imam yayi domin duk sonsa da bacci a lokacin kasawa yay, sai a yanzu mafarkin da yay ya shiga dawowa cikin brain 蓷insa, idan ya fahimta wacce ta kai shi bathroom da asuba ba Granny bace, domin ya da蓷a fahimtar wani abu 蓷azu,hakan magen data zo kusa dashi ba asalin magensa bace Wannan AIRAH ce, kenan mafarkin da yayi gsky ne yake ganin abun a mafarki ko yaya? Maganar Airah ce dawo masa cikin ransa inda take fa蓷in "Am pregnant with your unborn child Sheikh" ta yaya? Yaushe yayi tarayya da ita da har zata samu cikinsa, yasan cewa koda wasa babu wata halitta ko a jinsin Aljanu da ta ta蓳a ganin Manhood 蓷insa, Lumshe idanunsa yayi yana jin yadda kansa ke masa ciwo ga wani nauyi da yay masa, ji yay gidan yay masa girma dama yace Arjun ya tafi dashi gidansu, ko dai waya zai sanya Abbansa ya sai masa? Idan ya ri茩e waya yayi me da ita, babu abokai family kuma iya Abba da Mami da Granny Fareeq Buhaiyya ya sani sai kuma Arjun daya zame masa komai, mirginawa yayi tare kifa cikinsa ya rungume pillow, iska ya ji tana ka蓷a gashin kansa can kuma ya ji an dafa fresh back skin 蓷insa, bai Motsa ba saboda yayi tunanin Granny ce domin ya san Mami sai 6 zata dawo Abba kuma sai dare, Murmushi Airah tayi saboda farincikin yau zata kasance da mijinta kuma abin alfahari gareta, zama tayi bakin bed 蓷in dai-dai kansa, bai tai kuskuren magana ba sai kansa data kama a hankali ta 蓷aura saman cinyarta, ajjiyar zuciya ya sauke yana 蓳ata fuska yace "Granny!!" Yatsun hannunta ta tura a cikin sumar kansa ta shiga shafa masa sumar tana 蓷an wargatsa ta, sosai Sheikh ya ji da蓷i saboda daman kan ciwo yake masa, 茩ara matsawa yayi jikinta ko zai samu yay baccin gadon da bai samu ya 蓷auke sa ba, kasa yin shiru Airah tayi tace "why kake tsoran fa蓷awa Arjun kana da mata" da sauri ya 蓷aga kansa zuwa fuskarta kasa 蓷auke kansa yay saboda wata 茩yakkyawar halitta daya gani, zai iya cewa bai ta蓳a ganin mace me kyau da kuma tsarin halitta irin ta ba, ba fara bace ba ba茩a bace za'a iya bata Chocolate tana da dugun gashi wanda ta 蓷aura masa siririn veil, duk inda kake neman mace first class Airah ta kai sai yake ganinta kamar ba mutum ba, bakinsa yana rawa "who are you?" Kansa ta mayar saman cinyarta tace "why are you worried Rayuwata?" ji yayi zuciyarta ta buga da 茩arfi amma sam bai nuna a fili ba yace "Uhm" hannunta ta cire a cikin sumarsa tace "So daga juya zuwa yau harka manta dani ko?" Girgiza mata kai yayi yace "No! Kawai am trying to remember you" kallonsa Airah tayi tace "Lemme help you to, Am Airah your wife,Nasan abin zai zo maka kamar a mafarki but is not a dream is reality , tabbas na 蓷auke ka da hannuna har zuwa dajin Sambisa an 蓷aura mana aure Tijama da Tu蓳e da kuma necklaces 蓷in daka bani sune shaida" shiru yay mata ya shiga murza zoben hanunsa wanda tun 蓷azo baya gajiya da kallonsa can kuma yace "what again now?" Tace "na kasa jurewa tun bayan na dawo dakai gida da Asuba,sai ya zamana na kasa bacci, hakan yasa nazo gare ka a suffar Granny bayan na sanya Granny bacci mai nauyi, sannan duk abinda kuka fa蓷a kai da Arjun ina jin ku, hakan yasa na zama mage domin bana son ya fahimci wani abu kamar yadda kai ma baka so, ina zuwa falt 蓷in Granny na samu ta shiga bathroom sai na koma siffar ta da Arjun yazo ban sha wata wahala ba" shiru tayi sai kuma tace "Amma mai yasa kace?" Yun茩urawa yayi, ya mi茩e zaune yana 蓷an yamutsa, 茩afarsa ta kalla da sauri tasa hannayenta ta gyara masa 茩afafuwansa, fuskarta ya kalla yace "Tun Asuba nasan ba Granny bace, duk wanda yasan aljani farin sani ya ganki yasan ke 蓷in ba mutum bace, na 茩ara tabbatar da haka ne ta cikin mirror'n dake ma茩ala a cikin bathroom 蓷ina, kuma Granny bata iya English ba" jinjina kai tayi tace "Ko mugwaye Aljanu ai basu isa su 蓳oye maka ba, bare ni da nake shirin taimaka maka" hannunta ya zame daga nasa kana ya koma ya kwanta can ya 茩ara cewa "i don't have any feelings about women, balle aljana tayaya kike tunanin zan iya rayuwa dake matsayin mata a gare ni? Ta yaya kike tunanin zan baki kulawar daya dace ko wanne namiji ya bawa matarsa? I can't bana son kowa kamar yadda babu mai sona" kamar zatai kuka Airah tace "stop saying that Rayuwata,i promise u, I'll make you happy, ka bani 1week idan har a lokacin kaji baka sona nai baka al'茩awarin zan rabu dakai", hanunsa yasa yaja sajensa yace "sure?" Kai tsaye tace "Yeah" zamewa yayi ya kwanta duk yadda yasu yay baccin daya saba kasawa yayi, har 11 tayi lokacin tashinsa a bacci kallon Airah yayi wacce har yanzu tana zauna tana shafa masa sumar kansa yace "zanyi Sallah" mi茩ewa tayi tare da jawo Wheelchair tana son ta kaisa da kanta amma bata son tai abinda zai firgita da ita, bayan yay alwala yay Sallah ya koma ya kwanta kallonsa tayi tace "Breakfast fa?" Girgiza kai yay yace "No i want to sleep" Yana fa蓷in hakan yana jan duvet ya rufe jikinsa, hawa bed 蓷in tayi tace "i want to sleep with you" bai kulata ba yaja idanunsa ya lumshe yana jin yadda ta ja duvet 蓷in ta shiga ta yadda ta ware hannayensa daya rungome a 茩irjinsa kana ta shige jikinsa tana Murmushin jin da蓷i sosai take farin cikin kasancewa da shi, tsakani da Allah take son Imam bada wata manufa ba, rungomesa tayi sosai ta shiga shafa kansa tana masa wa茩a mai da蓷i a haka har bacci ya 蓷auke sa wanda ya da蓷e bai mai da蓷insa ba, ganin yay bacci yasa Airah mi茩ewa ta cire kayanta kana ta koma wajan Sheikh da yake kwance ta rungume sa sosai tare kissing bakinsa.......
10/17/21, 10:22 PM - Mrym: *SIRRIN MU*
*BY*
_鉁嶐煆� NIMCYLUV_
_Ina ganin masu cewa ko yaya zaman Sheikh Imam hamdan Balarabe da Aljarsa Airah zai kasance??? To kada ko damu you'll be surprised Habibaties kawai a hanzarta payment free pages dai babu yawa馃槏馃憣馃従share And share and share_
Pay #500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment
08119237616 ga 拼an Niger sai su nemi wannan number 84506476
馃啌P
EPISODE9锔忊儯-1锔忊儯0锔忊儯
Sheikh Imam bacci yake mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali, da zarar yay mutsi zai ji an 茩ara shigewa jikinsa ga wani 蓷umi dake ratsa jikinsa seriously zai ce ya da蓷e bai yi bacci mai da蓷i irinsa ba, bai tashi daga bacci ba sai da yaji muryar Granny saman kansa tana fa蓷in "Yau na ga abin da yafi 茩arfina ni Fa蓷imatu, wanne gantalallan bacci ne wannan Fisabilillahi? anayi ana nishi kamar bai zazza蓳in masharshara?" Bu蓷e idanunsa yay da 茩yar yana 蓷an dafe kansa da yaji yana masa ciwo kallo 蓷aya yay wa Granny yay saurin 蓷auke kansa tare da juyawa side 蓷insa,ganin babu kowa a gefensa yasa ya kalli Granny ya ce "Granny where is she?" Ke蓳e baki tayi ta ce "meye kuma Shaa? Kaga Imamu babu ruwana da wannan Ingilishin naka maza tashi ka shirya Ranjun yace min yana hanya,yanzu ya kira a sailolar dake palo" shiru yay kawai yana sauke tagwayen ajiyar zuciya ji yay ransa duk babu da蓷i saboda da rashin ganinta da bai ba, yana da tabbacin tafiya tayi bayan ta sashi ya yi bacci, Granny ta taimakamasa yay wanka tare da 蓷aura alwala, yana gaban dressing mirror Granny na shafawa fatara versiline "haka kurum baka san darajar fata ba kace a shafa maka wani losha,meye ma wani losha fisabilillahi" Shidai bai ce komai ba domin a karo na farko kenan yaji bai ji