Showing 114001 words to 117000 words out of 134406 words

Chapter 39 - SIRRIN MU Complete HAUSA NOVEL

21 Aug 2024

18361

suyi nisa da juna".
Rungometa Anut Amina tayi tace "In sha Allah I'll try my own Best, ki daina kukan idan kikai sanadiyyar cikin ya zube ko ya samu matsala fa? Kin san shi ne Abu mafi muni dazai ruguza zcyarsa shi ne zai iya rusa farin cikin sa, kiyi addu'a, muje kici abinci kiyi wanka zuwa safiya muga abinda hali zaiyi"
Hannunta taja sukai waje a Parlo suka samu Mami tana Shirin fita suna ha蓷a ido ta watsawa Fannah harara, ita kam ko inda take bata sake kalla ba, da 茩yar ta samu tasha tea 蓷in da fatan dankali wanda yaji bushasshen kifi.
Mami na fita kai tsaye police station ta nufa bata sha wahalar ganin Sheikh ba, yana zaune ya tan茩washe 茩afafuwansa idanunsa a rufe bakinsa na mutsawa a hankali yana Istigifari! Gabansa kuma wani bushasshen abinci ne da ruwan leda guda 蓷aya, domin Barrister yace kada a bashi wani abinci mai kyau..
Hannu ta mi茩a zata ri茩e nasa hannu dake jikin 茩arfan 茩ofar yay saurin zame hannunsa, murmushi tayi tace "Ok! Bazan ta蓳a ka ba idan baka so, nazo maka mafita ne, idan ka yarda ka amshi cikin jikina ni kuma nai al'茩awarin Taimakon ka, domin idan ka bari kaje Court to tabbas za'a rufe ka ne baki 蓷aya za'a ha蓷a maka da sharrin da baka san dashi ba"
Kamar yadda bai motsa ba haka bai bu蓷e bakinsa ba, shi sam bai damu ba ko hukuncin rataya za'ai masa abinda ya keso kawai Jewel tai farin ciki, ta haifa masa abinda yake cikinta yana da tabbacin zata kula dashi bayan ita ga Anut Amina ga Granny, duk zasu iya kulawa da jininsa.
茒an sanda take kanta yace "Hajia lokaci ya kusa fa" Mami tace "Look sweet Imam wlh zan fitar dakai domin koshi Barrister a yanzu idan nayi niyyar 蓷aure sa zan 蓷aure sa, shima yanayin komai a 茩ar茩ashi na ba tare daya sani ba, nasan cewa jikin Fannah naka ne sannan nasan cewa cikin jikina ba naka bane, haka kuma ko nakasar daka samu Mahaifinka shine sila, kuma shine silar rabaka da mahaifiyarka wanda har yanzu ba'a san inda take ba, akwai muhimmin abinda Barrister yake 蓳oyewa a tare dakai wanda har yanzu nima ban sani ba, amma ka yarda ka kar蓳i cikina ka maidani matarka ta kwanciya a 蓷aki, ina sonka Imam ina son komai naka, amma ni duk abinda zanyi babu wanda ya isa ya kamani, Mgna ta 茩arshe kuma mutuwar Uncle Sham ba tsautsayi bane ganganci ana tsane aka shirya hatsarin, kuma anyi amfani da motar Companynka, ko iya wannan zan iya amfani dashi wajan ganin an rufe ka amma bana bu茩atar haka" Mi茩ewa tsaye tayi tace "kayi tunanin kafin mu ha蓷u a court gobe.
Duk inda Arjun da Anut Amina zasu samu evedance na kare Sheikh a Court sun nema sun rasa, time to time kuma suna communicating a waya Shida Moon, itama ta shiga damuwa domin wannan shine karo na farko da Shari'a zata kaita 茩asa, kuma ta 蓷auki alwashin fidda Sheikh amma ba wata hujja da zata nuna haka sai tabi duk ta damu kanta, Murmushi kawai Deen ke mata yasan zatai winning na shari'ar kawai ta takura kanta sbd rigima.
Da daddare Fannah kasa bacci tayi, a daren kuma ta gayawa su Ya Falta komai dake faruwa hakan yasa sukace suma zaso zo goben.
Hankali ya tashi Gashi yanzu har 茩arfe 7 na safe ba hujja ba dalilinta, Barrister kam tunda ya fita cikin daren bai sake dawowa gidan ba, hakan yasa Anut Amina 茩ara gasgata zargin da take masa.
Yana dur茩oshe gaban wani ba茩in Mutum wanda ya cika jikinsa da layoyi kala daban-daban yace "Duk yadda za'ai ayi Sheikh ya ziyarci gidan yari bana son ya fito sai na samu cikar muradin rai na"
Bokan yay dry yace "Kaga wanda ya yarda da duniya ya manta da lahirarsa, ai tun tuni kayi sake 蓷an zaki ya girma kalli nan"
Jikin Barrister na rawa yace "Me zan gani waye wannan kamar Deedat? Bayan an tabbatar min ya mutu"
Dry bokan yay yace "Wannan shi ne babban kuskuren da kayi, ka manta da baya gabanka kawai kake hange"
Dafe kai Barrister yayi yana jin wani gumi na keto masa, kana ya kalli Bokan yace "Mene mafita?" Bokan yace "Kaga ciki mai manta kyautar gobe, kasan abinda muka saba ai idan kana son aikinka yayi".
Ba 蓳ata lokaci Barrister ya zame wandonsa ya juyawa bokan baya, just like yadda maza da maza suke abinsu, suna gamawa Barrister yay waje kai tsaye kuma ya nufi Federal Court of Appeal, domin Lokacin tara da wajan Ashirin, yana hanya Alhj Kamal ya kirasa yake shaida masa babbar lawyern da zata tsayawa Sheikh, tashin hankali ya bai yana akan fuskar Barrister sai kawai ya juya kan motar zuwa wani waje daban.
Court ta cika sosai da mutane domin harda wanda ba'ai tunani ba, Fannah na ganin Ya Falta da Yakura ta saki kuka tana ri茩e su, rarrashinta sukai kana suka nemi waje suka zauna, Anut Amina na gefe Granny sai share hawaye take, Mami da Bahaiyya na can waje guda, Fareeq kam baka iya gane halin da yake ciki. 11 dai-dai Al'茩ali ya buga guduma Court ta zauna, kai tsaye ya bu茩aci ganin wanda ake 茩ara 拼an sanda suka nunawa Sheikh waje yaje ya tsaya, kana akace ana neman mai 茩arar kamar daga sama a kaga Barrister ya mi茩e tsaye ya nufi wajan shima, Al'茩ali ya karantawa Sheikh laifinsa idanunsa cikin na Fannah ya amsa da "Uhm, da cikin da mai cikin duk nawa ne" Al'茩alin yace "Ke nan kana nufin da gske kai ne kayi mata cikin" kafin yay mgn Fannah ta mi茩e tsaye tace "Ba haka bane, 茩arya yake, nice wacce na tilasta masa kwanciya dani bashi da laifin komai, yana son 蓷urawa kansa laifi ne kawai" Guduma Al'茩alin ya buga tare da tsawatarwa Fannah yace "Is an order, Kada wani ya sake mgn ba tare da bashi dama ba" rubuce虏 Al'茩alin yay kana ya bu茩aci ko wanne lawyer ya gabatar da kansa, kai tsaye Alhj Kamal ya gabatar da kansa akan shike kare mai 茩ara, nan fa tunani ya sauya Anut Amina ta fara duba wacce akace itace Lawyer Sheikh, babu ita babu labarin ta, A hankali Deen dake cikin Court 蓷in ba tare da kowa ya lura dashi ba, nan Shima ya fara juya idanunsa yana son yaga ta inda matar tasa zata bayyana, jikin Al'茩alin na fa蓷in "Malam Sheikh Imam hamdan Balarabe ko dai baka da lawyer ne?" Mi茩ewa Deen yay Yana 蓷an covering jikinsa da Al茩yabbar jikinsa, kai tsaye waje yay dan bai son idanun jama'a su dawo kansa, Anut Amina ma mi茩ewa tayi ganin haka yasa Hankalin Fannah tashi zata mi茩e Yakura ta ri茩eta, shi kam Sheikh ko a jikinsa idanunsa a rufe bakinsa na motsa amma rabin tunaninsa yana kanta, da yana da hali babu abinda zai hanashi rungome ta ya rarrashe. Al'茩ali ya hana duk wasu ba yana da aka bashi daga ciki hadda vedio'n hannun Mami wanda Alhj Kamal ya bayar, gyaran murya yay bayan ya 茩ara tambayar Sheikh akan ko yana da hujja dazai kare kansa tunda bashi da lawyer, banza Sheikh yay masa sai bu蓷e idanunsa kawai da yay, yana bu蓷e idanunsa ya sauke a kanta wani tattausan murmushi ya sakar mata yana nuna mata cikinsa sai kuma yay mata nuni da tayi Shiru tsit tayi ta shiga sauke ajjiyar zuciya idanunsa ya juya kamar ance ya juya ya hangi Muhammad Jalal Kabeer bobo shida Jalilerh zaune suna kallonsa.
Guduma Al'茩alin ya buga kana ya mayar da glass 蓷in idanunsa ya shirya takardun gabansa yace "Bisa 茩wararan hujjojin da suka mata da kuma amsa aikin da mai laifin yayi wannan Court mai adalci ta yankewa Sheikh Imam hamdan Balarabe hukuncin....," Shiru yay sbd jin murya daga ba茩in 茩ofa bana fa蓷in "Adakata!!!" Gaba 蓷aya mutanan suka maida hankalinsu Mi茩ewa Barrister yay Sheikh kuma ya 蓷an furzar da iska daga cikin bakinsa yana juyawa a hankali Arjun ne a farko, sai Anut Amina hannunta ri茩e ta dairy, sai kuma Mama kolo da Yagana, daga can baya kuma wani farin mutum ne da alama shima prvt investigation ne, gefe guda kuma wata farar mata ce wacce tasha ado da wani farin lace amma gefen kanta a fashe yake yana zubda jini, sai Deen dake ri茩e da hannunta fuskarsa tai jajir, da sauri aka ware mata rigar ta Deen ya amsa ya sanya mata, hakan na nuni da cewa itace Queen Maimunatou Aliyou Eneye Ahuoyza Deen, kuma lawyer mai kare Sheikh Imam hamdan Balarabe...



SIRRIN MU isn't free contact to subscribe
08119237616


NIMCYLUV鉁嶐煆�
10/17/21, 10:24 PM - Mrym: Who Is The Killer
83-84

Gaba 蓷aya cikin Court 蓷in yay shiru idanun jama'a suka dawo kansu Deen, da Arjun da Anut Amina tare Mama kolo ha蓷i da Yagana.
Gyaran murya ka蓷an Moon tayi wanda yasa Deen fahimtar abinda take nufi, zame hannunsa yay a nata daf da kunanta yace "All the best My Queen" yana fa蓷in hakan yaja baya tare da nufar inda Muhammad Jalal Kabeer bobo yake zaune tare da Jalilerh.
Cikin nutsuwa Moon ta 茩arasa kallo guda tayiwa Alhj Kamal ta 蓷auke kai, kafin ta maida kallonta ga Sheikh, kusan numfashinta ne ya kusa tfy, duk yadda Mijinta yake da kyau da kwarjini amma 茩afar Sheikh Imam hamdan Balarabe Deen bai kama ba, ga wata nutsuwa kamala, da haiba uwa uba kwarjini wanda kallo 蓷aya Mutum zai masa ya cika masa idanu.
Shiru ne ya biyo baya, Arjun da Anut Amina suka nemi wajan zama, Mama kolo da Yagana suka zauna suma, Al'茩ali ya buga guduma Court tayi shiru, jin shiru yay yawa yasa Moon ta mi茩e kamar yadda Al'茩alin ya bata dama, gyaran murya tayi irin tasu ta matan manya da kuma sarauta tace.
"Sunana Maimunatou Aliyou Eneye Ahuoyza Deen, nice lawyern wanda ake a 茩ara Ngd"
Rubuce虏 Al'茩ali yay kafin ya 蓷ago kai yace "Shin Lawyern wanda ake 茩ara tana da hujjar da zata kare wanda Court take tuhuma akan yima matar mahaifinsa ciki?"
Mi茩ewa Moon tayi tana gyara zaman rigar jikinta kanta a 茩asa tana duba wasu takardu kafin tace "Ya mai girma mai Shari'a kamar yadda kace tun farko tuhumarsa ake ba'a tabbatar ba, kuma wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa da dukkan gskyar zcyarsa, to anawa 蓳angaren haka abin yake Tabbas cikin jikin Fannah Baba Baa'na cikin Sheikh Imam hamdan Balarabe ne..," ihun Court ta 蓷auka aka shiga surutai, Barrister kallon Moon kawai yake hakama Alhj Kamal suna jiran suji ta inda zata kare Sheikh daga wannan abun, guduma Al'茩alin ya buga akai shiru da idanunsa ya kalli Moon yace "Muna jinki" gyara tsaiwa tayi tace "Uhm! Hujja ta farko tabbatar da cewa cikin jikinta na Sheikh ne" wata paper ta 蓷auko wani ya kar蓳a kana wani ya amsa ya mi茩awa Al'茩ali, dubawa ya fara yaga gwajin halitta ne, kuma ya tabbatar da jinin Sheikh dana babyn cikin Fannah abu guda ne, ajjiyewa yay kana tace "Sai abu na biyu, wanda ake tuhuma bashi da laifin komai hasali ma ya samar da cikinne ta hanyar da ake so,hanyar da Addinin Musulunci ya shara蓷anta" nan ma shiru tayi kafin ta juyawa sukai ido hu蓷u da Barrister sai kawai ta 蓷auke ganin yadda zufa ke wanke masa jiki, hakama Mami da Alhj Kamal, juyawa tayi idanunta ya sauka akan Deen ya kashe mata idanu, tare da jinjina mata hannunsa, murmushi tayi tace "Bisa dugun binciken dana fara tun jiya zuwa yau, to Allahamdulillah duk wani binciken da nayi ya tabbatar min da cewa Fannah Baba Baa'na halaliyar Sheikh Imam hamdan Balarabe ce, Ma'ana Matarsa ce ta sunna" a hankali ya shiga ware idanunsa yana sauke numfashi ka蓷an虏 bakinsa na mutsawa yana fa蓷in _"Astagafirullah wa'atubu ilaik!! Astagafirullah wa'atubu ilaik!! Astagafirullah wa'atubu ilaik!!"_
Jajayen idanunsa ya sauke akan Fannah wacce itama shi take kallo zuciyoyinsu suka shiga bugawa a lokaci 蓷aya, yayinda numfashinsu ya fara daidaituwa dana juna, idannunsu a manne, suna jin mgnar kamar dirar mikiya, Sheikh taune le蓳ansa yay yana son ya tabbatar da abinda kunnuwansa suke fa蓷a masa amma ya kasa, wani 茩yak茩yawan shock ya kama Sheikh, ya kasa koda mutsi ya zama kamar wani statue.
Moon da take kallonsu tace "You have a right to that, kana da ikon kallanta as much as you can, Fannah is your wife" da sauri Barrister ya mi茩e tsaye yace "茦arya ne, wlh matata ce, 茩arya ne, nina na bada sadakin ta, Ni nace ina sonta ba shi ba, matatace dani aka 蓷aura mata Aure bada Sheikh ba" Barrister ya fa蓷a cike da tashin hankali jikinsa gaba 蓷aya gumi ya wanke sa, Al'茩ali ya buga guduma nan take Court tai shiru cikin bada umarni yace "Is an order Kada wanda ya sake mana magna idan ba haka ba yanzu hukunci ya hau kansa"
Gyara tsaiwa Moon tayi Idanunta na kan Sheikh tace "Ina son Court ta bani damar tambayar Sheikh Imam hamdan Balarabe wasu tambayoyi" kai tsaye Al'茩ali yace "Court ta baki dama" cike da 茩warin qwiwwa Moon tace "Sheikh da gske cikin dake jikin Fannah naka ne?" Jajayen idanunsa ya bu蓷e yana kallon ta kafin ya janye idanunsa ya mayar kan Fannah wacce tai lamo jikin Ya Falta tana sakin ajjiyar zcy sbd kukan da taci ta 茩oshi, ganin da gske bashi da niyyar mgn yasa a hankali Moon tace "Amsar ita zata tabbatar da abinda nake son fa蓷a a gaban jama'a" fesar da numfashi a hankali yasa tattausan hannunsa ya shafa fuskarsa zuwa gemunsa wanda yake ta 茩yalli, kamar bazai mgn ba sai kuma ya janye idanunsa yana fa蓷in _"Ya Allah"_ a zcyarsa, a fili kuma ya fidda wani emotional sound kafin a hankali yace "Da cikin da mai cikin duk Mallakin Sheikh ne" jinjina kai Moon kana ta bu茩aci ganin Fannah, a hankali ta tashi cike da tsoro sbd sam bata sama tsaiwa gaban mutane irin haka ba, bayan ta tsaya kanta a 茩asa tana wasa da yatsun hannunta jikinta duk rawa yake, Moon tace "Shin akwai wata hala茩a ta auratayya data ta蓳a shiga tsakaninki da Barrister Hamdan Balarabe?" Kasa mgn Fannah tayi sbd tambayar tayi mata girma, tsora mata shanyayyun idanunsa yay shima yana so yaji me za tace, domin shi gaba 蓷aya ya manta da wannan tunanin ya manta da cewa wani abu zai iya shiga tsakaninta da Abbansa, a karo na farko tsoro da fargabar abinda zata fa蓷a ya kamasa, addu'a yake idan wani abun ya fara kada Allah ya nufeta da fa蓷a, dan sam zcyarsa ba zata 蓷auka ba, a hankali Fannah ta girgiza kanta cikin sanyin murya wacce ta kama dishewa sbd kuka tace "Babu komai, tun zuwana gidan kawo yanzu" wata 苼oyayyiyar ajjiyar zcy Sheikh ya sauke yana rufe idanunsa wani sanyi ya fara ratsa masa zcy, jinjina kai Moon tayi tace "Idan Court ta amince zan fara gabatar da shaidun da zasu tabbatar da cewa Fannah matar Sheikh ce" Al'茩ali ya bada dama Moon ta bu茩aci ganin Arjun, cike da 茩arfin quiwwa Arjun ya tsaya kana ya gabatar da kansa a gaban Court matsayin mai bada shaida, wayarsa wacce ta samu matsala ya 蓷auko yace "A ranar da Allah yaywa Uncle Sham Kawon Sheikh rasuwa wayata ta samu matsala, kafin rasuwarsa ta riskemu ina tare da matata a kitchen naji shigowar sa茩o wayata, ban samu damar dubawa sbd wayar ta fa蓷a cikin hug 蓷in tea, tun daga rana na cire sim 蓷in na ajjiye ta, na duba ko zanga wanne sa茩o ne ya rage a cikin sim 蓷in amma ba komai duk sun zauna a wayar, to cikin ikon Allah yau na 蓷auko hanyata ta zuwa Court na fara biyawa police station kamar yadda Queen Maimunatou ta bu茩ata, bayan muntattauna da ita, zamu tawo Court 蓷in na samu kira daga matata, tace nai sauri nazo akwai hujja mai 茩arfi dazai kare Sheikh,jin hakan yasa na tafi Queen Maimunatou kuma ta shiga mota ta nufi Court, ina zuwa na samu wayata ta dawo dai-dai kai tsaye kuma ta nuna min sa茩on dake jiki" jinjina kai Moon tayi tace "Ko Arjun zai iya karanta mana sa茩on yadda kowa zai fahimta?" .
Wayar ya bu蓷e yace "ga sa茩on kamar haka;"

_Assalamu Alaikum, Mohd na turo maka wannan sa茩on ne a lokacin da nake jin kamar bazan iya samu damar fa蓷ar wani Sirrin da baki na ba, da farko ka kula da Imam bashi da wanda ya fika, sai Granny ita kuma wannan a Kullum 茩arfinta 茩ara jaa yake, Sheikh yana cikin magauta da ma茩iya, na san halinsa mai 蓷aukan 茩addara da rashi Yadda da mutum, amma kai tsaye bazai fahimci wanda suke son kaisa 茩asa ba, abu mai muhimmanci shi ne FANNAH ba Matar BARRISTER bace, matar SHEIKH, na bu茩aci abun ya zama sirri sbd na fahimci ita zata zama silar samun 茩afafuwansa Kuma Thank God ya samu lfy, haka kuma ya tabbatar min da Sheikh yayi tarayya da mace ne, ka gaggauta sanarwa da Imam wannan mgnar domin akwai gobarar da take shirin tunkaro sa, bayanin Auran sa da FANNAH da kuma bayanin cikakken Tarihin rayuwar Sheikh yana cikin Dairy na kasa Anut Amina ta 蓷auko maka, ka bata hqr sosai ta kula da Huda, ta 蓷auki 茩addarar rashi na, abu na 茩arshe kuma kamar yadda jama'a da kuma ko kuke tunani Sheikh ba 蓷an Barrister ba ne, na barku lfy realy miss you so much Arjun ka kula da Sheikh na baka amanarsa!_

Shiru Court tayi, Barrister ya susuci ga samu ga rashi, tayaya? Yaya akai Uncle Sham ya san da wannan Mgnar? Meyasa bai tunanin 蓷aukan mataki akan Uncle Sham tun tuni ba? Yanzu duk shekarun daya 蓳ata ya tashi a banza kenan ko mene? Da 茩arfi ya furta "Ina it can be possible" kallonsa akai a wannan karan hadda Sheikh a kallonsa, tunanin Sheikh da yawa amma ya rasa wanne zai fara, idan ba Barrister bane mahaifinsa to wanene mahaifinsa, mai yasa Fannah ta zama matarsa bayan bai ta蓳a ganinta ba bare yace yana sonta? Ko kuma 茩addarar ha蓷uwa da Airah ita ta ha蓷asa da Fannah, ada no one replace Airah in his heart, amma yanzu Fannah ta maye gurbin Airah ta samu matsayin da Airah bata samu, wannan da burin samu Allah ya 蓷auki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login