Showing 1 words to 3000 words out of 99653 words
[8/15, 5:13 PM] A A Dboy: SANADIN ACCIDENT
🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊
( _Home of spécial &extraordinary writers_ )
BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM ....
Godiya ta tabbata ga Allah (SWT)me kowa me komi ..
yanda na fara rubuta littafinan Allah ka bani ikon k'areshi lafiya ...tsira da amincin Allah su k'ara tabbata ga Annabin mu (SAW) da sahabbasa da alayensan ...
Allahouma Salli Ala Sayyidina Mohammadin was Salim...
Ban yarda wani ko wata ya canza min littafina ba inhar bada izinina ba dan kotuce zata rabani da shi dan haka akiyaye🙏
🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
Ina mik'a gaisuwata ga yan kungiyar mu *STAR Writer's Ass ..* Allah ya k'ara had'a kanmu.love you All❤
🅿️ 01__02
Tafe take tana rusa kuka kamar wanda aka ce parent d'inta sun rasu ..hannunta d'aya ta kare fuskarta da shi d'ayan hannun kuwa tana rike da wani fashen2 tulu koda na matso kusa da ita na k'are mata kallo senaga yarinyace qarama fara wacce baza tafi 11ans(11years)duda karanci shekarunta aman bai hana kyan ta fitowa ba tanada hancinta zarot ..bakinta dan madedeci pink ga magana masha Allah amma fa kayan jikintaa dakon2 dasu bakyan gani duk sun kod'e sun cicire ...riga da zanen da d'an kwalin duk daban2 tayi daurin nan irin namu na yan kauye wato ta zaro jelar dan kwalin ta gaban rigarta .....ganin irin shigar yasa nayi zaton tallaka wane amma me..😳 ganin gidan data take shirin shiga yasa nayi mamaki dan kaf kauyen manga gidan daya kaishi ba dan shafe da sumunti gidan yake kuma an kewayeshi da katanga sab'anin sauran gidajen da kusan duka buka ne...
Ta jima tsaye baki kofar gidan ta kasa shiga se tayi kamar zata shiga se kuma ta dawo baya tayi haka yafi sau ukku daga karshe tayi shahada ta shige ganin haka nima na mara mata baya ..
Wata bakar mata nagani zaune bisa kujerar nan tayani tsegumi se girgiza kafa take tayi d'aurin d'an kwali ture kaga tsiyar nan ..
D'an nesa da ita yarinyar nan naga ta durkusa se kame2 take ta kasa magana ga hawaye na tsiyaya bisa ''joue''(cheek) d'inta ...
Matar ta kalleta tace wai miyene kin wanizo kin sani gaba kamar ni d'in bakuwar ganin kice.....ina kuma ruwa dakikaje d'iba ne eee ta fad'i cikin tsawa..
Seda ta firgita yarinyar har tayi baya ta fad'i ragwaf baki na karkarwa tace kiyi hakuri Inna Murza wly mun d'ebo ruwan nida su Ma'u kawai sega su Murtala sunzo fice wa gani suna gigin tseda mu ne . da muka ki tsayawa se kawai suka biyo a guje ina cikin gudu nayi tuntub'e nafad'i tulun ya fashe kuma ma harda ciwo naji ta bud'e gwiwarta idan taji ciwon..tana nuna mata
A maimakon taji tausayi yarinyar se wani uban ashar ta abka tace yoni ina ruwana dajin ciwonki .kuma kice de kin tafi wajen karuwan cin ki da samarinki de.. walahi baki isa tulun nawa zafi fasa sanan wani bani hakuri ... to walahi se kin biyani ko jikin ki ya fanshe ki yanzu nan dan bazan dauki asara ba....
Cigaba da kukan take tana bata hakuri amma ina Murza ita neman ma bugi take ..muciya naga ta d'auko tayi kanta .nanfa ta dinga jibgar yarinyar tun kana jin ihun ta har muryar ta dishe bata barta ba seda ta sumar da ita tayi jifa da muciyar taja kafafun yarintar takaita tsakiyar rana tayi shigewarta daki se mita da zagin yarinyar take ...
Ba'ita ta farka ba se wajejan karfe biyu na rana shima sakamakon ruwan da Inna Murza ta sheka mata...firgit ta tashi se wuki2 da ido take ....
Murza tace shegiya mai kama da aljana tashi ki fice kiwo sauran inkin tafi ki tsaya yawon karuwancin naki dakika saba ...
sum2 ta d'au buta ta nufi rijiyar cikin gidan da niyar yin alwala tayi sallah ..ashe ma akwai rijiya cikin gidan dan tsabar mugunta irin na Inna Murza tace baza'a ja ruwan ba sede taje can cikin rijiyar garin ta d'auko mata..
Wata tsawa ta daka mata tace ke kina hauka ne uwar mi zakiyi min da butana iye..
Cike da tsoro tace Inna alwala zanyi inyi salla..
Shewa tayi tace gaji ladaniya to kokece tabarmar massalaci wacce kullum acikin mosque d'in take baza kiyi sallar ba kamar wacce tafi kowa addini .....maza aje ki fice..
Tace inna to bari nayi fitsari sena tafi ...
Shiga kiyishi hakanan base kin kama ruwan ban ...shasha kawai ..
Fitsarin da batayiba tace Inna abincina fa yunwa ake ji...
Iye i lalle wuyanki yayi kwari kai tsaye tace to ban dafa dake ba
Zata yi magana Murza tace.MAYSAM MAYSAM dige ki fita a idona in rufe tau..tayi shigewarta d'aki
Bayanda MAYSAM d'in ta'iya dole ta d'au sandar kiwon ta kora shanun ta fice....Allah yaso ta cikin shanun akwai masu shayar wa bayan taje idan take kiwon se ta tatsi nonon tasha ta gama.cikin ta dan dama kullum hakace take faruwa idan anbata abincin safe tofa da ranan batada kwanon tuwo idan kuwa bata bata na safe ba to zata bata d'an tsakure da rana...
Bayan tagama sha tayi alwala tayi sallah
Wanan kenan...
Fasma ce✍
Wannan littafin daya daga cikin member din Page din nan ce duk comment din da kuka yi xata na gani in ma gyara kuka mata xata dauka
[8/15, 5:15 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/15, 5:27 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
🅿️ 03__04
```An karbo daga Anas dan maalik R A yace: Manzon Allah( S A W) yace''dukkan d'an adam mai kuskure ne,mafi alkhairin masu kuskure sune wad'anda suke tuba(idan sun aikata kuskuren kuma bazasu sake komawa ba)''
``
Bayan ta gama sallar nan ta zauna tana tunani rayuwarta ita bata san miyasa innarta bata sonta batason dommi yasa ta tsaneta ba ...kullum da iri cin zarafin data ke yimata sab'anin kowace UWA da take nunawa d'anta so da tattali ...ga kuma kalmar da take tsaya mata cikin brain wato Karuwa '' tarasa mi kalmar take nufi so tari Murza zatayi ta kiranta da sunan kuma ba damar tabbayarta ....tana nan har aka kira sallar Asr ,,,bayan tayi sallah ta d'an ringesa kafin a d'an jima ta koma gida...abunka da wanda ta gaji ga wahala da yunwa se kawai bacci me zurfi yayi awon gaba da ita ...ba'ita ta farka ba se gab da magarib ,,,da sauri ta tashi ta kora shanun ta kama hanyar gida tana addu'ar Allah yasa baba MUSA ya dawo ...
Tun daga nesa ta hango Murza a bakin kofar gida tana dube2 da alama jiran isowarta take ,,,..
Dafe kirji tayi tace na shiga Ukku ni MAYSAM yanzu kuma ko wace azaba Murza zatayi mun..Murza na hangota ta juya cikin gida ...
nan Maysam ta fara karkarwa tana matsar kollah ...
Bayan ta d'aure shanun ta shiga gidan ai kuwa tun a bakin zaure taji saukar dorina a jikinta seda ta gantsare ta zube nan ta kama qafar ta tana bata hakuri .....
Hankad'ata tayi da qafa ta dinga zabga mata dorina tana fadin kaji shegiyar yarinya kina son d'auko muna magana a gari wato kiwon ma se kin tsaya wurin karuwanciki.....
Fad'i take wly inna ba'inda natafi bacci ne kwashe ni.....
Iye dan ubanki har kika samu lokacin bacci keda kika tafi kiwo kenan kice hakan kika bar min dabbobi da kishi dan bakin ciki ko....
Tace a'a inna wly ...
Bata bari ta qarasa ba tayi ball da ita wani kara ta saki segata wanwas ta suma a wurin dama sauran yanwa ga duka ai abin yayi yawa(gaskiya na tausaya miki Maysam😭)...
Ana kiran isha'i ta kuma shekamata ruwa a firgice ta tashi se kuma ta saki wani kuka me cin rai ...
Amaimakon taji tausayin ta se kawai naga tana kasa gyad'arta tana qirgawa .bayan ta gama tace idan kin gama kukan munafuncin se kizo ki tafi dandanli kuma wly b'atan daya kikayi jikinki ze fanshe ki..
Ta goge hawayen tace dan Allah ki temakamun da abinci yunwa nakeji ...
Kamar baza tace wani abuba se kuma tace ga zazafen safe can ki d'auka kice ..
Hannu baka hannu kwarya take loma dan ba wani yawane dashi ba amman de ta done wasu kofofi cikin...ta d'au tiren tallar ta fita......
Wajejen goma na dare aka tashi a dandali ..itada kawarta Ma'u suka rako dayake makota ne a hanya tace dan Allah Ma'u ina sonyi miki wata tambayya....
Ma'u tace ina jikin Allah yasa na sani....
Maysam tace wai mi kalmar karuwa ke nufi?
Waro ido Ma'u tayi dayake ta d'an girmeta kad'an tace kada ki bari wani a kauyen nan yaji wannan kalmar a bakin ki ...
Miyasa don ni sunan da innata ta lakaba min kenan...
Ma'u tasa hannuta ta rufe mata baki tace kul kada kibari wani ya san da maganar nan dan karuwa na nufin macen data bada kanta ga maza saboda kud'i wato ta meda yin Zina sana'arta ...ita kuwa zina anyi hani dayinta ga dukka musulmi mumuni dan ko kasanci da ita an hanemu bare yinta .......
Gyad'a kanta kawai tayi amma badan tagane duka abunda Ma'un ta fad'imata ba ...ganin Ma'u ta shiga yanayin damuwa yasan itama tashiga koda bata gane ma'anar kalmar ba amman tasan ba abu ne me kyau ake nufi da ita.....
Bawanda ya sake cewa komi har suka zo kofar gida Ma'u ta kalli Maysam cike da tausayawa kawartata tace kiyi hakuri da abunda Murza take mike wata rana se labari...nan sukayi sallama kawa ta fice gidansu....
Zaune ta tarar da Murza nan ta biqa mata kud'in da ragowar gyadar...seda ta lissafa yafi sau ukku wai ko zataga b'ata amma taga sun cika cif2 ...ta harareta tare da yi mata rankwashi a ka tace Allah ya soki da kinci na jaki....
Sum2 ta d'au buta tayi alwala ta shige wata yar bukka kusa da kitchen da alama store ne dan ga kayan miya nan a ciki ..tattare wuri tayi ta kabarta sallah bayan ta gama ta b'ingire nan bacci ya kwasheta.....
Kiran sallar farko akunnenta akayishi ta tashi ta sand'a tayi alwala ta koma bukkarta tayi sallah...ta salamce kena. Murza ta shiga kwalla mata kira ko azkar na safiyar bata samu damar yi ba ta fito a guje ta durkusa gaban ta tace ina kwana Inna ..
Ya tsine fuska tayi tace da ban kwanaba kya ganin ..ni ba wannan na kira kiyi mun ba maza 2 d'au tulu ki tafi rijiyar cikin gari ki d'auko ruwa sauran ki tsaya yin abunda kika saba....
Tulu da guga ta d'auka amma me har ta kai kofa Murza tace dawo aje mun gugar inki tafi can wani ya baki ki d'iba..
Haka ta fita a ranta tace da rijiya a gida amma ace se an tafi wani wuri d'aukan ruwa ..dan kawai wai kada ruwan rijiyar ya kare...ko a ina ruwan rijiya ya tab'a qafewa.....
Bata dawo gidan ba se bakwai ...
Murza ta kalleta tace issashiya se yanzu kika gama tumb'elen ki ko nan da cikin gari ma sekinyi halin....
Batade ce komi ba ta sauye ruwan ta fara kiciniyar d'aura koko a ranta tace waye ze tafi daukar ruwa da asubar fari kuma kinsan da hakan kika hanani d'aukan goga ...bayan ta gama ta d'umama tuwo sannan ta share tsakar gidan tas ta had'a kayan wanke2 tayi...
Ta zauna zaman jiran a bata kari amma Murza yi tayi ya bata san da halita a wurin ba ta bud'e baki da niyar yin masifa ta tsinkayi sallamar Malam Musa d'up tayi shiru ta fara washe baki tana laale Malam sannu da zuwa...
Da gudu Maysam ta rumgume shi tace sannu da zuwa Abba.....
Rumgume ta yayi shima ya shafa kanta yace yawwa yar Abba da fatan na same ku lafiya ..e tace ya jawo ta suka zauna bisa tabarma yace yar Abba mike damunki naga kinyi wani irin a kwana biyunan da bana nan....
Kasa magana tayi se hawaye da take gogewa ...
Hankalinshi ya tashi yace yar Abba kiyi mini magana mana ...
Karaf Murza tace ayya ai rashin lafiya tayi massasara ke damunta ...jiyan nan na kaita chemist aka bata magani gashi bata son cin abinci ko kad'an har balangon nake sayo mata amman bata iyaci se na matsa mata....ga jikinta wuni take da zazzab'i bata son ruwa ko kad'an ya tab'ata.shiyasa kaga jikinta da d'an datti...kuma kasan marar lfy ba'a matsa mishi diyawa seda lallab'a ...yanzu haka dramar setayi break ne muke nayi2 takici .....
Maysam batayi wani mamaki ba dan inda sabo ta saba da makircin Murza tayi fiye da hakama ...
Malam Musa yace wayoo yar Abba ashe baki ji dad'i ba to Allah sawwake ya baki lfy..
Ameen tace da farar'arta dan ko ba komi zatayi hutun masifar Murza Kwana biyu... Suna had'a ido Murza ta buga mata harara ...ta sadda kanta a ranta tace sede harara dan yau ba wunin yunwa bare zuwa talla da kiwo...
Nan ya bude tsarabar daya kawo musu fruits iri2 nan Maysam ta bud'e sauran qofofin cikinta ta dinga ci ba kyakyautawa...seda taji ba wuri tukon ta sarara...ga wasu d'inki atamfa daya basu kala uku2 ,,,.nan ta ja ruwa a rijiya ta feso wankanta wanda rabonta dashi tun bayan tafiyar Abbanta ..tasa kayanta ta fito tsaf da ita .Murza kamar ta had'e rai dan takaici ...
Abinci rana ta d'aura musu abbanta na gefe se fira suke abunsu gwanin ban sha'awa...dan kuttu Murza kasa zaman wurin tayi ta koma d'aki ..haka tayi musu lunch tare sukaci ..
A kwana biyun nan da Abba ya dawo har wata yar kiba da haske ta qara dama gata da tsapta masifar Murza ce ke sata zama da daud'a dan kuwa batada incin saka kaya masu kyau inde har Malam Musa baya nan...
.
Tofa kuji makirci irin na Murza... ..
Love you all my fans ❤
Fasma ce✍
Ahmed Gumel
[8/15, 5:27 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/17, 1:08 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
🅿️ 05__06
```Daga Abdullahi dan Umar Allah ya yarda da shi yace:Manzon Allah (S A W) yace''mutum bazai gushe ba yana tambayar muta ne(roqo) har sai yazo ranar qiyama fuskarsa babu tsoka d'aya ta nama
,ruwayar Bukhari da Muslim ce_
```
Washe gari Maysam cike da farin ciki ta tashi tayi shirinta na zuwa school tasa uniform d'inta ta fito tsaf da ita ...nan tsakar gida ta tarar da inna Murza da kuma malam Musa suna breakfast ta zauna itama ta gama cikinta lokacin da zata tafi Malam ya dari biyu na break ....ta ansa tanata godiya ...
Wani kallo Murza tayi mata sena ga ta gyad'a mata kai ta fice a gidan ...(ko kallon miyake nufi oho)
Haka Murza tayi wunin aiki a ranar se tsaki da gungunai take ...
Ita kuwa Maysam a school d'inma principal hanata shiga aji yayi dan cewa yayi seta zo da parent d'inta yaji mike hanata zowa akai2 ...
Da kyar ta samu ta shawo kanshi tana kuka ta d'an fad'i mishi abubuwa kad'an daga rayuwarta ....
Nan ya tausaya mata tare alkawari tallafa mata tasamu ta gama primary tunda ma yarinyar Allah yayita da kaifin ilimi dan danan ta haddace duk abunda aka koya mata....
Qarfe biyu na rana suka sauko ta dawo gida Allah ya temaketa Malam yana gida nan ta shari girkin lunch ...qarfe hudu kuma ta tafi islamiyya ....
Malam na fita sallar magrib Maysam na zaune tana biya karatunta se jin rankwashi aka tayi ...koba'a fad'a ba tasan inna ce ...tana d'ago idonta kuwa taga Murza se wani fuci take ta biko mata hannu tace ban ...
dari biyu naga Maysam ta fitar daga bag d'inta ta bata ...
Warcewa tayi tasake yi mata wani rankwashin tace nazata baki ganeba dana ganar dake yanzu munafuka kawai ..
Itade ko A batace ba ta meda hankalinta kan abinda takeyi...a ranta kuwa kukan zuci take ace kud'in break d'inma se an anshe ...
Bayan kwana biyar Malam Musa yayi shirin tafiya dayake kasuwoyin kauyika ya keci shiya sama be cika zama a gida ba...
Kuka kuwa harda na banza Maysam tayi dan tasan tayi bye2 da jin dadi har seya dawo ..
Nan ya rungumeta yana lallashi yace yar Abba kukan nan ya isa haka ...
Murza se wani washe baki take tace ai kasan bata san rabuwa da kaine ...
Maysam aranta tace dole inyi kuka dan nasan lokacin azabata da cin zarafi yayi..
Kudi ya fiddo ya bawa Murza sanna ya bawa Maysam kudin school dinta ..
Ya tafi ya barsu nan Maysam na ta d'aga mishi hannu...
Shigowar su keda wuya Murza tace munafuka annamimiya .. Kwace kud'in tayi tace tundade ba school din zaki ba ..aiki ya dawo sabo..
Haka rayuwa tayi ta tafiya kulum da irin sabuwar muguntar da inna Murza take fito mata dashi ..yau har zasu zana jarabawa shiga secondary Allah yasota Musa na gida dan haka bata samu wata matsalaba ...bayan yan watanni resulta kuwa na fitowa Allah ya temaketa taci fad'ar irin murnar datayi b'ata time ne ....
Inna Murza na gefe se wani murmushi mugunta takeyi a ranta tace e kuma kin gama school daga haka..wannan d' inma dayaya na bari balle har na bari kishiga secondary ee bazama ta sab'u ba....
Bayan kwana biyu da faruwar hakan suna zaune bayan sun gama abincin dare Murza tace Malam dama ina son yimaka wata maganace game da karatun Maysam amma ina tsoron kace nayi mata shishigi..
Malam yace haba Murza wani irin shishigi keda y'arki ki fad'i kawai ina sauraronki..
Dam gaban Maysam ya bada ta kasa kunne tana jiran jin mi zata fad'i
Kalar tausayi tayi tace dama cewa nayi be kamata taci gaba da karatunta ba dan kaga a al'adar garin nan yan mata basayin makaranta gabada primary kuma ka sani kowacce a d'akin mijinta take jinin farko (menstrue)dan abun kunya da tsangwama ne idan har yarinya ta farashi a gida..
Gaban