Showing 51001 words to 54000 words out of 99653 words
bangaren su Maysam kam itada kawayenta sun dage ba kama hannun yaro karatu suke sosai....
Cikin sa'a suka kawo makin da ake so dan haka shugaban makarantar ya ce vacation din 1 month ne kawai garesu dan wani lecture za'a fara yi musu dan kada susha wuya....
Har lokacin Murad be dawo ba kullum intayi mishi zancen se ya katseta da wani zancen ........yanzu kam ciwonshi har tashi yake kadan2 dan kuwa Maysam kuka take saka mishi kan se ya dawo tayi missing dinshi ..
Shi kanshi baze ce ga taka meman abunda yake hana shi dawowa ba ...kullum cikin rarrashi yake ...Fulani ma kullum cikin bata hakuri yake....
A na sakin su Fulani tayi mata booking jirgi ta dawo gida...
Ba karamar Murna sukayi ba itada M.Musa ba da suka juna ..rasa inda ze sakata yayi ..Murza na gefe se tabe baki take tana tsuka kasa2 amma da taga Maysam ta kallota se ta fake da dariyar yake wai ita a dole nan ta shiryu ta fara son Maysam.....
Tun Maysam na dari2 da ita har ta saki jikinta kadan ..
Lokacin da Maysam ta sanarwa da Fulani yanda sukayi da shugaban ba karamar murna tayi ba dan haka tana cika watan ta fara shirye2 komawa. ..
To fa ranar wata samedi(Saturday )ana gobe komawar Maysam .....suna falon Fulani ,Maysam,Murza,da ita Kanta Fulanin ...
Hira suke wacce duk ta karatun Maysam din ce . Murza se wani tarerayar Maysam din take amma fa k'asan zuciyar bakin cikine fal dan ji take kamar ta rufe Maysam din da duka ganin irin yanda take zuba shagwabarta a cinyar fulani ..ita kuma se lallaba ta take. ...
Ganin abun bana karewa bane yasa fulani fadin bari de inkira mijin ki may be shi ya lallabaki ki barni na huta da shagwabar nan.
Gaban Murza yayi wata irin mummunan faduwa ta shiga wuwurga ido ..
Kamar wasa Fulani kuwa ta danna mishi kiran ..
Murza ta kashe kunne kuwa. ..
Bayan ya gaisheta ne ta sake tambayar shi yaushe ze dawo ..nan ya fara yi mata kame2 ..
Fulani tace to ka bude kunnuwanka da kyau kaji ina son ganin ka a week din nan wannan umarni nake baka maza2 ka taho ....
Cike da tashin hankali yace to Momy zan zo ..
Wani farin ciki ya mamaye zuciyar Maysam da ta fulani tace to se kazo Allah yayi maka albarka.
Sabanin Murza datayi mutuwar zaune zuciyar ta cike da wasi2 a ranta tace daman suna waya ko kuma yau ne suka fara kawai. ..bata gama tsinkewa ba seda taji Fulani na fadin pls ka lallaba min yarinyar nan ysa duk ta hanani wali...
Shata da baki Murza tayi ganin Maysam ta karbi wayar tayi cikin kuryar daki tana dariya kasa2 ...wani dunkulelen bakin ciki taji ya to kare mata wuya a ranta tace kada fa Yaron nan ya fara son aljanar yarinyar nan......babu me bata amsa dan haka ta danne bakin cikin ta gaban Fulani ta tashi tana fadin barin koma akwai wasu ayuka da zanyi ...nan tayi ma Fulani sallama ta fice ..
Itade Fulani tana kallonta ne amma bawai ta yarda da tuban Murza ba..
Tana fita kuwa ta fada bangaren Madina ......
[9/2, 10:42 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ππ_*
[9/2, 10:45 AM] A A Dboy: πΉπΉ *SANADIN ACCIDENT* π₯ππΉπΉ
π³πͺStory&Written
by
*FASMA* π³πͺ
π
ΏοΈ 77__78
*FASMA*
_jinjinar ban girma Momyn Mufeedah ,ina tayaki murnar kammala littafinki hakika kin fadadakar da nishadan tar damu Allah yasa sakon da kike son isarwa ya isa ,Allah ya bamu ikon yin aiki da shi ke kuma Allah ya biyaki da mafificin alherinsa ,ya yafe miki kurakuran dake ciki.._
_Up.up.up muna tare dake se mun jiki a sabon littafin ki..._
*congratulation my lovely sis SARAH hakika ina tayaki murna samun Bac din ki Allah ya riqa ya sa ki amfana da* *shi ....ina me kara jinjina miki .*
*Ban manta dake ba kanwata ta kai na Balkissa kema ina taya ki murna samun Bepc ki matuka Allah ya rika ya sanya alheri* ...
*Kai da duk ma wanda suka zana jaraba wa ina muku murna tare da fatan alheri ..*
*Wanda kuma ba su samu ba ne baissent pas les bras ,du courage and wish you bonne chance* ....
_Ilou Ado Safaraou&Rabe Idi Salamatou Magaria ..les fausses jumelles ba ..ina jin dadin yanda kuke nuna kaunarku ga book din nan Allah ya bar kauna Maysam tace ta gaishe ku_
Dedicated to SARAH&BALKISSA
77__78
```Manzon Allah(SAW)ya ce''Musulmi dan uwan Musulmi ne ,kada ya cutar dashi.
Muslim ne ya rawaito shi``` .
Murza na fita ta fada bangaren Madina ..bakin ciki kam kamar ta mutu take ji ...
Tana zuwa ta fara zayyanawa Madina komi har da yar kwalar ta bakin rai ..
Wata zabura Madina tayi tace what?dama suna waya amma bamu sani ba ...
Tirkashi zancen dawowar shi ma bata taso ba kawai abun yi yanzu base gobe ba ki tashi yanzu ki koma wurin yankan wuka ki sanar mishi ..se kuma ki ce mishi ayi mishi asirin da ze manta da zuri'a tashi ma gaba daya ya yanke alakarshi da su ...
Murza bata yi kasa a gwiwa ba ta tashi ta fice bayan Madina ta cika mata jaka da makundan kudi...
A bangaren Maysam kuwa shagwaba wacce tafi ta Fulani ma take zuba ma Murad ..
Shi kuma se lallabata yake kan tazo mishi koda vacance din nan ne..
Se lokaci ta sanar dashi cewa ai wani lecture za suyi dan za ayi musu tsalaken ss2 ..
Shima nan ya tayata murna tare da yi mata fatan samun nasara ...
Hira tayi dadi har take tambayar shi sunan likitar dayake aiki a can ...
Sedayayi murmushi yace to keda ba zowa zakiyi ba miye na wani tambayya...
Kukan shagwaba ta sakamishi .....
Dolen shi shi ya gaya mata kai harda adress din gidan dayake.....
Sun jima suna waya cike da jin dadi ga shi kuma yace zezo cikin sati se murna ta hade mata biyu...
.
Murza ce tayi wani zaman dirshen a gaban boka Yankan wuka tana gaya mishi duk irin makircin da suke so ayi musu tare da kara jadda da cewa arabashi da famylin ma gaba daya ..
Boka ya sheke da dariyar jin dadi yace kai ina jin dadin aikin ki ...raba d'a da iyayenshi abune ne dayake bamu matukar wahalar aiki bare ma Uwa ...amma dole muke jajir cewa muga irin wanna danyan aiki ya yi tasiri badan komi ba se dan mun san yanke zumunta ma bashida kyau ,,bare yanke alaka tsakani da iyaye. ....(kuji wani shedanci )
Dan haka muna bukatar kudi masu yawa dan asiya wa aljanan da zayi aiki jini ..,,kuma ma ba anan garin suke ba se an tafi wani gari wanda ake kira da''DOGON DOUTCHI''ake siyo su wato Aljana 'DOGUWA'....sune masu yin wannan aiki ba tare da an samu matsala ba....ya kwashe da wata dariyar hhhhhh...
Murza se wani washe baki take tace kudi ba matsala bane inde bukata zata biya ...nan ta zube mishi su..
Cike da murna da kwarin guiwa ta koma gida dan Boka ya jaddada mata cewa baze taba dawowa ba..(jifa se kace shi keda ikon duniyar
..Allah de ya shirya in me shiryiwan ne)
Lokacin da Madina taji bayanin boka ba karamar murna tayi ba tace Mulki ne de Murad baza ka taba hawanshi ba...saura shi kanshi sarkin ina nan zuwa lokaci kawai nake jira....
Wannan kenan
.
Washe gari Maysam tayi tafiyar ta Maradi karatu da zumar in Murad ya zo tasan de ze je ganinta tunda ya san tana school.
Amman mi shiru kake ji kamar malan ya ci shirwa ...tun tana tammahani zowarshi har ta dena ...yau har watan su biyu ..
Bayan ta dawo gida ne kafin su koma rentren Ss3 take yi wa Fulani mitar yayanta be zo ba .har yau
Fulani ma dauriya kawai take yi...tana lallashin ta amma mamaki ne fal ranta ....da farko in tayi kira tana samun shi sede baya dagawa .,,kai daga baya ma wayar ta dena shiga..
Ta dau waya ta sake danna kiran shi amman kamar kullum bata shiga .
Maysam kam zuciyar ta banda lugudan zut2 babu abunda take mata ..se kawai ta fashewa Fulani da kuka ..
Da kyar itama ta nutsu ta shiga lallashinta ..
Dama sati biyu ne zatayi ta koma school amma duk ta wani fige ta rame Fulani kam tana tausayin ta ..ganin abun na gaba yasa tace wa Sarki tana son zuwa England wurin Murad.
Da kyar sarki ya lallabata da fadin bari Mahmud ya tafi ya gani..
Cikin satin Mahmud ya shirya ya daga se England ...lokacin da ya tafi akayi rashin sa'a Murad baya nan likitarsu ta tura su qarin karatu kasar Europe kan wata sabuwar cuta data shigowa kasar ..kuma formation din ze dauki 5_6 months....
Murad kam yana can yama manta da wasu wai su Fulani dan kuwa tun bayan kwana biyu dayin hirar shi da Maysam har ya fara shirye2 dawowa amma me kawai rana tsaka ya tsinci kanshi da son rashin dawowar . abun beyi nisa ba seda yaga Fulani tana kiran shi a waya amman ya kasa dauka...wani irin abu yake ji a zuciyar shi se kawai yama canza layi gaba daya ,,,kai da ga karshe ma dayaji tafiyar tura karin karatu se kawai ya saka sunan shi ama su son zuwa ..ya koyi sa'a aka tura sun....
haka nan Mahmud ya dawo ba dan ya so ba tun dade lfyr sa lau aiki ne kawai ya rikeshi......
To fa muje de zuwa
Lokacin da Mahmud ya sanarwa da su Fulani se a sanan suka dan saki ransu .jin an turashi karatu ne ..
Maysam ta koma Makaranta abunta . yanzu kam sun kara girma komi na cikar budurci ya bayyana a jikin su....se wani jiji da kai suke wai su yan matan Ss3 ...yanzu kam sun kara wayo Maysam yanzu bata da wani buri na ta ganta kusa da yayata Murad .. Ga karatu suke babu kama hannun yaro ...
kullum su ke cinye ta daya ,biyu da ta ukku a ajin,,wannan abu ba karamar haushi yake bawa sauran dalibai ba dan ko wata competition se de a zaba cikin su ukku ...gaba daya kansu a hade sun shaku da junan su,,,class,diri ,kyau tsafta ,ilimi duk sun mallake su ..dan ko a islamiya ma kadan ya rage musu su sauke Alqur'ani.......
Kullum zaka gansu cikin walwala da tsokanar junan ,,,har suke kiran kansu da tripleM.. .
amman fa har zuwa lokacin su Mufeedah basu san cewa Maysam matar aure ce dan bata wani nuna musu alama ba...wani lokaci har sukan tsokane ta da fadin sun yi wa yayansu kamu ....
Itade sede ta kallesu tayi dariya..
Bayan 6 months nan ma su fulani suka dinga diba hanyar ganin Murad amma ji kake shiru ...Fulani kullum cikin yi mishi addu'a take ..
Maysam ma kam yanzu bata wani samun isheshen bacci,,,duk dare tana yawaita yin nafilfili da rokon Allah yayi musu zabi na alheri tare da karesu da duk wani me binsu da sharri mutum ko aljan.. Amma fa yanzu idonta ,kunnenta bakinta kai har ma gangar jikinta ba suda wani buri na su jisu tare da oga dan Murad ya rigaye ya koya ma ta sonshi ..dan haka ita da soyyayarshi ta girma cikin ranta ....mafi yawan cin lokaci zata dau photon shi ta saka gaba tana ta zance ita daya (umm su maysam an fada tarkon so ....sede lokaci ya kure miki .)
.
Tafiya tayi tafiya lokaci nata tafiya
Bayan sunyi saukar Qur'ani da sati suka fara final exam ..
Cikin ikon Allah suka gama lafiya suna jiran saka mako..
Gida ta dawo zaman jira.....
Fulani na lura da ita tun dawowarta ta kaura bangaren Murad gashi da ka ganta kasan tana cikin damuwa ...fulani kam ba karami tausaya mata ba take..bz.
Ana haka resulta din su Maysam ya fito ..gaba dayan sun ci harda mention exellente ..
Zo kaga murna wajen su
Harda wata yar kwarya kwarya walima suka shirya su ukkun ...acan gidan Maysam na Maradi akayi ta inda Mahmud ya taka rawar gani wurin yi musu komi dan ganin basu samu wata matsala ba.....
Washe garin walimar su ukku suna ta hira Mariam tace yauwa dama akwai wata magana dana ke son yi muku..
Nan suka nutsu ta ce dama abbana nane yayi mun muji ..
Wani ihu suka kwasa a tare suna fadi wai da gaske dan Allah ..
Tace ee wly wani dan abokin shi ne sunan shi MA'ARUF. Kuma a England yake aiki docteur ne...
murna fal ransu suka yi muta fatan alheri tare da fadin kice kawai da mun sha biki se England ..
Mufeedah ma tace kai nima fa Maysam yayan nan naki ya fara damuna ,,..bakiga jiya daya kaini Super market siyan kayan damuka sa ....ya wani tsareni da surutu kai daga karshe ma seda yayi mun wayo na bashi number ta ..
Maysam ta kwashe da dariya tace kawai kada kija wani aji inya nuna yana so kawai ki amince Mahmud bashi da wata makusa ,kyau ne ,kudi ne,kamala ce, duk ya hada kawai ki yarda musha biki.kemz..
Cike da zolaya Mariam tace kai kede kawai dan yana yayankine kike wani yabonshi ..
Dariya tayi tace haba ba wani nan .gaskiya de na fada.kuma ma abokin MIJINA NE
A tare sukace miji ...
Tace ai koda na shigo makarantar nan da aurena ...kuma wannan wanda yazo lokacin da bani da lfy wato Yaya MURAD shine mijina...gidan nan ma nawa ne ..
Mufeedah tace amman kin san baki kyauta ba ko ace ayanda muke ki kasa fada muna kina da aure...
A tare sukace muna miki fatan alheri tare da zaman lfy me dorewa amman mu kinga tafiyar mu tunda de baki dauke mu ba da mahimmaci...suka tashi zasu tafi
Da sauri tasha gaban su tana basu hakuri kan bata yi haka ba da wata manufa kawai de Allah ne beyi ba zasu ji ...
Nan ta zaunar dasu ta basu tarihin rayuwar ta ...kan ta gama ,ita kuka su kuka ..nan suka rungume junan su ..sun jima a haka sannan Mahmud ya meda su gida ya kai Maysam airport ta dawo gida..
,,,shugaban makaranta su Maysam ya kirayi iyayen su bayan yayi musu barka se kuma yayi musu proposing din a aje musu takardun su inda rabonsu gwamnati zata iya tura su kasar waje karatu...
Da farko fulani bata amince ba amma ganin Maysam ta kwallafa rai yasa ta amince amma fa tace sede in England kusa da mijinta.
Itade Maysam burin ta ta amincen ...
Allah cikin ikonsa suka samu su duka ukkun kuma England duka aka tura su ....dadi kashe su ne kawai beyi ba ....zasu kara hadewa a makaranta daya..
Dan haka fulani tasake tutubar Mahmud da yasake koma wa England ya gani .ya kuma sanar mishi matarshi ta samu gwamnati ta turata England karatu..
Wannan karon Mahmud shi kanshi ya tsorata da lamarin ..dan Murad nunawa yayi da de duniya besan shi ba kwata2 ya manta dashi...
haka Mahmud ya dawo zuciyarshi cunkushe da wasi2 iri2 .....shi be masan ta inda ze fara gayawa fulani cewa ga irin cin mutunci da Murad yayi mishi ba......dan haka tunda ya dawo ya shiga wasan buya da. Fulani....
Ranar wata litinin ana gobe tafiyar su Maysam England dan Mahmud ya cike mata takardun ta.
Bangaren Abbanta ta nufa dan yi musu bankwana shida Murza sun jima Mallam Musa yana yi mata nasiha da kuma ta kare mutuncin ta da na aurenta ...
duk sai jikinta yayi sanyi taji kamar ma ta daina tafiyar amman tuno wa da tayi yayan ta na can sai ta samu kwarin guiwa har zuciyarta tafara azzalzalata dan zumudi
Dakin Murza ta nufa da niyar yimata ban kwana amma mi cak ta tsaya a dede kofar shiga palon banyi aune ba naga hawaye sun fara zarya a kumatunta cike da mamaki na matso na kara kunne na dan ji mi yasata kuka sai naji Murza tana waya tana fadin ee kadan ma suka gani wly ni nan zan zama ajalin Murad de Maysam (kuji fa da allah kamar ran a hannunta yake ) da ba ma rashin sa'a ba da yanzu sun dade da mutuwa ai...,
ke nifa haukata shi naso ayi yabi duniya bama a raba shi ba da dangin ba fadar madina da ga bangaren layi ,
shewa Murza ta kwasa tace wannan shine target din mu na gaba sai kinyi uwar dakina shugaba Madina matar sarki shugaban masarauta gaba daya kai ko makirar Fulani ba ta isa ta taka miki birki ba dole ne ki taka wanda kikeso a garin nan dan duk wanda yayi miki kan kara za kiyi mishi ta itace abuga dake a barki anan waziri ma yayi nashi babin an shafe shi.
Dafe kirjinta Maysam tayi cike da mamaki da kyar ta lallaba ta koma bangaren fulani dede zata shiga taji muryar Mahmud na fadiwa Fulani kaf abunda yafaru shida Murad, yakara da fadin amman fa ina ganin ba a hayyacin shi ba yake dan a gaskia wanan al'amari akwai ayar tambaya a ciki
jim Fulani tayi tana jinjina maganar sai kawa Maysam ta fado ba ko sallama tana gwanjin kuka cinyar Fulani ta fada ta saki wani sabon kuka mai cin rai cike da tashin hankali fulani ke tambayarta miya faru .?
kukan yakasa tsayawa ta shiga fadin Momy kada kiyi fushi da yayana ba laifin shi bane wly sune kuma sunce ma sai sunga bayan mu nida shi
Cike da tsoro Fulani da Mahmud sukace suwa din?
Yanzu nan naji Inna Murza tana waya da wata Madina matar sarki nan ta kwashe kaf abunda taji ta fada musu.
Mahamud dey mamakine ya cika shi har yawun bakinshi ya kafe ya rasa mi zai fadi.
Fulani batayi wani mamakiba dan dama bata yarda da tuban Murza ba kuma ta gane sare Madinar da take fadi sai tayi shiru.
A fusace Mahmud ya tashi yana fadin kafin su kasheku ni bari nakashesu ..
,dakatar da shi fulani tayi da fadin zauna muyi magana
Bayan ya zauna tayi mishi nasiha kan illar a bunda yake son aikata wa takara da fadin ''maintenant on a aucune preuve en notre disposition qui va prouver leur actes. .
Mahmud ya ce''Mais Momy ,Maysam a tout entendu non?.''
Fulani ta sake fadin''Meme si elle a tout entendu c'est sa parole contre celle de Madina kuma ma babu wanda zai yarda saboda iya makircinta dan tana gwada kamar ta goya Murad gaban mutane in baka mantaba waziri ma fa yaka yafada amma babu wanda ya yarda ....
Yanzu de mu fara da kubutar da Murad