Showing 96001 words to 99000 words out of 99653 words

Chapter 33 - SANADIN ACCIDENT COMPLETE BY FASMA

FASMA   

05 Jul 2024

14103

shekara aman wannan karon ka aza rigima kan a nan kakeson ayi muku patyn anyi rarrashi aman a banza dayake abun kaddararene yasa ka kwallafa rai itama kuma yar renontaka ta biye maka kuka hargitsawa Mom da Dad kwanya babu shiri suka tattataro suka zo nan garin koda mukaji dalilin zuwansu munyi musu fada sosai kan biye muku da sukayi ..

Anan kuma aka shirya muku wani birtday din banzan kuma mantawa da wanan ranar ba rana birday din da safe wajejan goma na safe Fulani da Mom zasu rabon temako ga kauyikan dake kusa damu kamar ko wani bayan wata ukku2 tasoma bari har gobe saboda birtday aman kuma da ta tuna cewa duk bawan dake karkashin su ya kwana da yunwa sun shiga hkkinshi bayan su suna cikin wadata dan haka saboda birtday bazatayi cancel din bada temakon ta ba ..to itama Mom ta kuke seta bita batayi mata musu ba ...itama Maysam na ganin Mom dinta ta shiga kukan seta bisu ..kai kuma kafarta kafarka dan haka kaima ka bisu .lokacin dazaku tafine ka fiddo wani zobe wanda shine gift din da zakayi wa Maysam sosai ya burge mutane dan iri dayane zoben babbaci kawai nata na zinariya ne nashi kuma na azurfa ne wanda tafiyar su wannan haji ya saka Dad ya sa aka kera musu shi ....ku duka a mota daya kuke ..lafiya kukai temakon..se a hanyarku ta dawowa ne tsautsayi ya afka muku wandan kukayi wani Accident a take dreben motar ya rasu a wurin kukam gaba dayanku an wurwurga ku wanda kuka sume a wurin ku duka ... Nan bayin da kuke tare su suka nemi baku temako ..aman abun mamaki shine batan Maysam ko sama ko kasa ..anyi neman duniya aman babu ita babu alamunta ..

Abu kamar wasa aman akayi neman nesa da kusa babu ita ..har kwararu police aka saka nemanta aman jikake shiru ..abu de kamar asiri ..seda aka jera sati anan nemanta aman shiru .....daga baya ma aka tabbatar musu da cewa inde har tana cikin jejin nan to sede wata ba itaba dan akwai namomin daji a wurin da kyar ne idan zata rayu ..shiyasama muka dangana da ita muka dauka da ta mutun..

.to fa nan kuma Murad ya bujiro da nashi sallon rashin Maysam dan bashida aiki se kuka ko kuma ya tisa photonta gaba yana kallo yana magana shi kade ..

Kadan2 ya dawo shiru2 yayi bankwana da dariya fara'a da kuma sakin fuska ga mutane se kuma wata tsabagen fada da masifa ..abu kadan bayi sukayi ze saka ayi musu horo me tsanani . school ma ya dena zuwa kullum kumshe cikin kuryar daki ..abun ba karamin daga hankalimu yayi ba ..ga kuma abangaren Mom itama tun da abun ya faro tayi AVC take zuciyarta ta kamu wanda yayi sanadiyar kullum suna hanyar kasashen waje don neman magani...shima Murad da kyar aka lallabshi yayi candy da weak da izinin Allah ya samu ..ai kuwa muka yanke shawarara turashi turashi England ko ze samu damar sakewa yayi karatun shida Mahmud aka turasu dan ya samu ya kula da shi sosai tare da bayi da dogarai ..acan dinma ansha fama kafin ya dan sauko ya fara karatu aman fa bakar zuciyar nan na nan makalle dashi ..abu kadan ze sakashi fushi .........

Se anan sarki ya ja numpashi yace to kin ji labarin ki Maysam *SANADIN ACCIDENT* ne hakan ta faru... kaf palon in ka dauke parent din kowa se sharbar kuka ya ke bama ya Maysam ba da take ganin abun kamar almara ba..wai itace Sweetbabyn Murad daya ke matukar so ... Ashema shi ya reneta tun tana ciki ..se kawai ta sake fashewa da wani kukan wanda Murad babu ko kumya ya zo ya rumgumeta yana lallashi ..

Sarki ya bukaci M.Musa dake cike da mamakin wannan lamari da yayi mishi bayanin gameda da Maysam din..

Be boye musu komi ba yayi musu bayani yanda ya sameta ..sunyi matukar mamaki jin inda ya sameta dan da wurin da accident din ya faru da kuma inda ya sameta da tazara sosai
Sanan ya basu hakuri kan irin abunda Murza tayi mata ... ..

Kowa na daki murna yake bama ya Maysam da ta samu iyayenta yanzu taji kuma irin so da gatan da suke mata ..ba ..an jima nan ana hira sannan ya aka rufe taro da addu'a .kowa yayi bangarenshi cike da jin dadi da farin ciki....

To fa oga Murad ya aza rigimar sede Maysam ta koma bangarenshi da zama dan yaga Mom na son kaita bangaren da suka sauka ..nan fulani ta shiga yi mishi fada ..to wai ma mi zatayi maka acan bangaren ne dan danyan goyon nan ..aman a memakon ya sauko se cewa yayi Momy ai waccar wifyna ce wanna kuma ai sweetbabyna ce kinga it's two person different ..kuma walahi ni banma gaji da ganin ta ba yana yi yana wani matsawa kusa da Maysam din ..ita kanta Maysam din kunya yake bata bare kuma su fulani ...daga bayama girgiza kai tayi tayi ficewarta ...

Haka yace shikenan Mom kawai muje can naku bangaren dan nima na kwaura kawai ..Mom kam murmushi tayi dan tasan za'a rina dan zeyi fiye ma da haka din..

A bangarenma seda ya danne zuciyar shi ya basu wuri su kara sanin junan su aman bini2 seya leko su ya koma ..

Sha biyu nayi yazo yace to Mom ki ban aron sweetbaby na nima kinga ma dare ya tsala seda safe ko...

Mom harda yar kwallarta don ya tuna mata lokacin da suna yara ma haka yake mata da lokacin baccinta yayi zezo ya dauketa koda kuwa mi take mata ..seda safe su karasa ...dan haka bata musa ba ta sallami Maysam din .wacce take ta zumbura baki kan ita bata gaji da Mom din ta ba..haka ya lallabta aman mi ai kuwa jaririn yace besan dare ba nan ya shiga musu kuka abunka da sabuwar shiga itama kawai ta saka shi gaba tana kukan dan bata son ya zatayi da shi ba ..

Murad kam banda dariya babu abunda yake mata ..can de dayaga da gaske take kukan yasa ya dau baby yana jinjigashi shima dan ayi se yayi shiru ....

Ta kalleshi tace laa only one ya akayi mi kayi mishine ya dena kuka..dariya yayi yaceai ke ya biyo a kukan nan dan kwana kike kina kuka kuma ko ambaki nonon ba wani shiru kike ba ...kuma yanda kika ga yana kuka bakinshi na karkarwa to kema haka kikayi .

Rufe fuskarta tayi tana fadin kai babyna banda sharri fa..

Wani lumshe ido yayi yace 'repete le encore'

Tace mi din?Baby?

Lumshe idon yayi yana murmushi yace Sweetbabyna ina sonki fiye da raina ...ya hada su ya rugume su duka....

Daga nan nima nace bari nayi musu sallama ..ko ba haka bata fans?😆😆😆😜😜....

Baride na dan kara samunku labarin..

Maysam tace baby to miyasa lokacin da aka daura muna aure ka nuna mun tsana da hantara inde har lalle ina kama da sweetbabynka a lokacin ..

Yana mirmushi nan nashi me kashen yan mata yace to ai ko lokacin tsananin kamar ku ce ta saka nayi tayi miki haka dan duk wani kallon da zan miki ina kara tuno da itane wanda yke barazanar tada mun da ciwo na ne..bare kuma fatar jikin mu ta hade senaji zuciya na ta fara Kidan Zut3 shi yasa kika ga bana iya miki muso kan abubuwa da dama na kanyi loosing din controle dina da zarar idon mu sun sarke da juna ..ina sonki da yawa sweetbabyna pls idan kinga zan kauce kiyi kokarin nunamunu hanya dan da rabin zuciya na ne kika bayae gurbin aman yanzu kam gaba dayanta ''elle t'appartienne '' aman am sorry da duk abun da na miki a ba..
Bata bari ya qarasa ba ta hade bakinsu tare da girgiza mishi kai kusan raba daren sukayi suna hira daga karshe ya rumgumeta sukayi baccin su

Ranar suna yaro yaci sunan MUHAMAMAD anyi shagali iri2 ..da walima kai abun ba'a cewa komi se san barka ku ma de kunsani base natsaya baku labarin bikin ba .. .

🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹

Wai ina labarin Inna Murza ne?

Allah ba azalumin bawa ba Murza de ta sake rasa kafarta gudar data rage mata ..yayinda bugan kan da tayi ya haddasa mata tabuwar hankali .hauka turben takeyi (hum jama'a mubi duniya a sannu kana abun kirkin ma ya ka kare bare kana shuka sharri adoran kasa. ..kungade Murza duk abunda tayi nufin su Maysam dashi shine ya kome mata ..dan tayi niyar meda Maysam gurguwa idan baku manta ba aman Allah ya qareta ..taso haukata su nan nan ma batayi nasara ba ....komi zakayi ka yi tawwakalli da Allah ....duk abunda kakeyi ya kamta kasani Allah yana jinka kuma yana ganin ka ..sanan kaji tsoron Allah a duk inda kake ..Allah ya qara karemu mu da zuri'armu baki daya ameen ya kula shiryar da masu hali irin nata) .an kulleta anan cikin masarautar bisa umarnin Maysam dan ita tace ta yafe mata kuma ta nemi alfarmar da abarta nan dan kada ta shiga duniya..Murad ba haka yaso ba to aman Maysam ta zartar da hukunci babu yanda ya iya . sede muce Allah ya shirya masu shiryiwa ya sa sa su gane ga duk masu hali irin na Murza da makarabanta wato waziri da Madina..


🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹

To fa abun na oga Murad ba sauki dan fa ya zama mijin tace ko kuma ma mijin kan tace dama kusan zuciyarshi a rabe biyu take to kuma yanzu Maysam ta mamaye ta duka tunda yasan itace sweetbabyn shi..

Yauma kamar kulum suna zaune a palon fulani ..ya wani tankwashe kafafu yana gyara madarar da za'abawa littlebabyn shi dan baya bari bayi su taba wai acewarshi yafiso suyi renon kayansu da kansu yayinda da Maysam ta saka babyn tana mishi wasa kamar wani babba ...Mom ta fara yi mishi fada akan ya dena sake ma Maysam da yawa haka ..tayaya tana zaune ace shi ze kada madara da kanshi..

Ya wani marece yace kai dan Allah Mom bana son ta wahala da yawa ne walahi a barta da shayarwarshi kade ma jiki take ji ..ita kam Maysam kanta akasa dan ita kanta tana mamakin wannan kaunar da Murad yake nuna mata ..Fulani de batace komi ba. Harkokin gabanta ma take

Mom ta taba hannu tace wai anyya kana cikin hankalin ka kuwa miye na wahala anan wai ayya ma zaka iya mulkar kasar nan kuwa nan gaba ?

Yana dariya yace kai Mom wani mulki kuma ai bazan iya barin Maysam dinta ba dede da yan mintuna bare aje ga zancen awwanin da zanyi a fada ..tab ai da kamar wuya ..

Su duka sakin baki sukayi suna kallonshi ..shikam ko aka ya qara da cewa kunga ma nan da week zamuyi tafiyar mu England abun mu....

Se a sanan fulani tace ka tafide . itada ko arba'in bata yiba ina ita ina zuwa England..

Wata faduwar gaba ta ziyarce shi babu shiri har seda ya dafe baki na karkarwa yace Momy karatun fa?
Walahi satin sama suke komawa kuma kinga can da nan ba daya bane...

Jim Fulani da Mom sukayi suna nazarin maganarshi ..

Fulani tace wai kana nufin da danyan goyon nan zata koma ..to kuwa sede in tare zamu ..

Daga Murad har Mom seda suka dara ..
Mom tace kina da aiki kam ..Momy de shiru tayi tana tunani dan ba karamin tausayawa Maysam take ba duba ga yanda Murad din ke kainenaye ta taso ace se tayi arba'in zata koma to aman ya ta iya ..a ranta tace kada fa yaje ya kuma dibgamata wani cikin da danyan goyon nan (😂😂😂ni kuwa nace to mi naki a ciki ai matarshi ce ki barsu abunsu kawai)ita knta Mom din bataso tafiyar yanzu b badan komi ba sedan basu jima da sanin juna ba taso ta dan jima ko sa shaku. Sosai ...dan haka suka kara himma wajen gyaran yarta su

Haka kuwa akayi sati na zagayowa gaba dayan su suka daga se England wannan karon har da Mahmud dan yace kafar mtarshi kafarshi...

Tunda sukaje suka meda hankalin su ga karatun su kun de sansu ai sede wannan karon kowa yana gidan shi ne dayake Gidan da Murad yake bare biyu ne se Mahmud da matarshi suka shiga dayan..

..haihuwar Maysam da kwana 23 ta samu tsarki ai kam abunda Momy ke gudu shike shirin afkuwa dan Murad kam yanzu ya koyi jaraba babu safe bare ran da kowani loakaci ya medashi lokacin pratical ko a kitchen ya iskota to fa se yayi paratical a kitchen din..don ma ina kokarin tsayawa na kashe gaz din dayayi musu gobara ai😆😉da Maysam tayi magana se yace ai na safen na wify nane yanzu kuma na sweetbaby ne tun abun yana damunta har ta sakin ranta de ..yauma bayan komi ya lafa suna makale da juna Maysam tace baby wai ya akayi sunan ka ya koma Murad ne bayan Mujaheed ne...

Seda yayi murmushi yana shafa kanta yace sunan ya samo asaline bayan batarki wato lokaci da aka medo ni england saboda son da kaunar dana ke miki yasa na cire harufa biyu na fakon sunana ''MU ''sena dauko harrufa na karshen sunanki''RA'' sannan na saka 'D'din karshen sunana se ya bada MURAD kisan don mi na zabi yin haka.
Tana wani kara makalle shi dan wani sonshi take ji yana kara shigarta ta girgiza mishi kai ..

Yace na farko abunda yasa don ina son kullum na kasance inada abun da ze tuna munke ne ..a duk lokacin dana ji MURAD ina tuna harufan sunanki dake ciki ..na biyu zakiga na sa RA din atsakiya to don kin kasance kece zuciyata shiyasa na sakaki a tsakiyar sunana kamar yanda zuciyata ke tsakiyar jiki....se kuma na ukku ma'anar sunan dan MURAD yana nufin MURADINA (mon choix)to kinji yanda akayi sunana ya koma Murad..kuma wani lokacin zakiji su Mahmud na kirana da M² to shima yana nufin MUJAHEED & MUNIRA kar yanda yake a cikin Zoben mu

Wayyo dadi kashe Maysam kai ita bata masan dami zata saka mishi kan irin son da kaunarta ta da yake dan ta tabbata ko makawa babu yafita sonta .....

Bayan wata shida naga su Mufeedah se jan kafa ake don cikin su ya shiga watan haihuwa ....ai kuwa cikin satin su duka biyu suka sambalo yaran su duka maza zo kaga Murna wajen su Mark baki har kunne ..dole anan akayi sunan dan ana tsaka da school babu damar komawa gida....a tsakanin su sukayi yar walimau se yan Uwa da suka zo daga Niger dan sunan ...anci ansha kowa yana cikin murna da jin dadi yara sunci sunnan kakkaninsu na wurin uba dan Mahmud sunanshi MUBARAK yayinda dan Mark sunan shi MANSUR ..inka dauke Maysam dake kwance ba lafiya ...har su Maryam na tsokanarta wai kode wani ciki ne ....

Batade ce musu komi ba dan ita kanta abunda take zargi kenan aman dan ta kwantarwa da kanta hankali se ta ce ai tana shayarwa kuma ma ai malaria ce....


Kai abu de kamar wasa jiki yaki yin sauki shide Murad ya gane komi sede yana son tabbatarwa dan haka yau tun safe suka jeya gwadata..ai kuwa abunda fulani ke gudune wato de Maysam na dauke da cikin wata daya da yan kwanaki ....Maysam suman tsaye tayi ..bazatce bata son cikin ba aman duka duka ma danta watanshi shida ace kuma yanzu tana da wani cikin ...

Murad kam Murna kamar mi ..ya kalleta yace ya naga bakya murna ne da cikin ko bakya sone..
Da sauri ta girgiza kai sega hawaye shar3 tace yanzu duka ma fa Muhammad watanshi shida ace nayi mishi kane ni walahi ina tausayin shi..

Ajiyar zuciya yayi yace inde wanan ne kada ki damu ki ci gaba da bashi nono akwai maganin da zanki baku komi bazeyi ba yana cika shekara daya semu kaywa Mom Ko Momy yaye ko tunda yana cin abincishi?

Dafe kirji tayi tace baby na shiga ukku bade Momy ba dan walahi fada zatayi dan seda ta gwasileni gashi yanzu kayi mun wani cikin dama Momy ta fada..

Haba mi zeyi inba dariya ba seda yaga tana kuka da gaskenta tukon yayi shiru tare da lallabata ya kuma sheda mata se akaishi wurin Mom..


Haka kuwa akayi yana cika shekara guda lokacin sun zo gida vacation sun yanke ranar birtday zata yaye shi ..su duka ukkun ranar birtday din dayane dan haka sosai aka shirya wa wannan birtday din har su Mom seda sukazo ..anci ansha sosai .da daren ranar suna zaune a daki su hudu da cikon Muhammad din na biyar Murad ya dauko jakar kayan Muhammad ya dau keshi da ga cinyar Maysam din ya bawa Mom yace Mom ga da nan mun baki renonshi dan yau aka yayeshi ...

Ba Momy ba har Mom kallon mamaki take binsu dashi..tayide karfin halin cewa da wasa kake yaro duka ma shekara daya yau kace kun yayeshi a ina kuka taba jin haka ...

Maysam kam tuni tayi hanyar waje dan tana jin kunya dan tasan Murad se ya tona asirin...
Ai kuwa bata kai ga huta ba Mom tace dawo ki zauna ...

Sum2 kamar munahuka ta dawo ta sadda kai ..

Momy tace Murad3 walahi ka fita a ido in rufe bana son shashancin banza daga kai har ita kuruciya na damunku walahi..

Sassauta murya yayi yana bawa fulani hakuri tukon ya sanar da ita cikin Maysam din..

Gaba dayansu sakin baki sukayi suna kallon su ..Momy tace haba ni kam daman nasan za a rina koda kuka zo nayi zargin cikin to senaga ita me jariri se kuma tayi shiru da ga haka basu iya cewa komi ba se addu'ar Allah ya raba lafiya sukayi musu....


🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹
Five years later(5ans apres)


Yau ake walimar rantsar da sabbin doctarorin anan jami'ar England inda triple3 aka basu lambar yabo ita Maysam Cardiologist tayi ,Mufeeda gynecologist yayida Mariyam tayi pediatrist...aman fa abun mamaki su duka da nan cikin su kui2 kamar hadin bakin ....duk sun kara girma sun zama wasu mayan mata bulbul dasu a raina nace kai mazajenku sun iya kiwo fa😉😜

Murad ke rike da yaransu su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login