Showing 9001 words to 12000 words out of 99653 words
b'arayi suka tafi da ita..
Cikin tsananin tashin hankali yace wani iri b'arayi ke dakata tun wuri kafin raina ya b'ace ki gayan inda kika kaimun diyata inba hakaba zan d'auki mummunan hukunci a kanki
Ganin ya d'auki abun da zafi yasa tace wanda suka tab'a kad'e tane sukazo suka tafi da ita wai nan bama kula da ita..
Wani mari ya kifeta dashi yace walahi inde dasa hannunki se kin yabawa ayya zakinta ya fice daga gidan kamar ze tashi sama dan sauri ...dayake masarautar sananna ce kuma wancen lokacin sun sanar dashi dan haka mota me zuwa garin direct ya shiga ..bewani wahala ba aka kaishi har kofar masarautar ....
A kofar clinik din ya gamu da jakadiya nan suka gaisa dayakesun shedi juna ..nan ta labarta mishi yanda suka tarar da Maysam da kuma dramar da sukayi da Murza ranshi ba qaramin b'aci yayi ba nan ya bata hakuri tayi mishi jagora har d'akin Maysam d'in ...
Har lokacin bata farka ba nan ya samu wuri ya zauna yana kallonta tare da rafka tagumi..
Yana nan har fulani ta shigo nan ya kwashi gaisuwa ..suna cikin haka Maysam ta farka da wani irin ihu tana fad'in dan Allah inna kiyi hakuri ba da gagan bane..bazan qaraba
Da sauri fulani ta isa kusa da ita ta riqe mata hannu ta kirayi sunanta Maysam Maysam......
Jin murya fulani yasa tayi shiru tana kallonta se kuma ta fashe da wani kukan me tsuma zuciya tace qafata zafi take mun ..
Fulani ta shafa kanta tace yi shiru ze dena kiyi hakuri kinji.....garin yaya kika bari qafarki ta sake karyewa ne ...
Tana hawaye ta labarta wa fulani duk abunda ya faru ta qara da cewa kuma fa a gaban Abba bata nuna ta tsanane aman da zarar baya nan seta yi ta muzguna mini....hakika Abbana yana sona bayason b'acin raina yana faranta min amman bansan miyasa Inna Murza ke yimini haka kodan ba'ita ta haifeni ba ne..har lokacin batasan Malan Musa na d'akin ba ....
Fulani ta share mata hawaye tace kiyi hakuri insha Allah daga yanzu Murza bazata sake muzguna miki ba..kinjiko..
Gyad'a kanta tayi tace to ..se kuma tace dan Allah a sanarwa da Abbana kada yaje yayita nemana besan ina nan ba....
Batayi aune ba taji muryashi yana fad'in Yar Abba sannu da jiki
Cike da jin dadi tace laaa Abba yaushe kazo ne...
Be bata ansa ba se cewa yayi ashe haka Murza ke azab tar dake amman baki tab'a gayamun ba?mesa haka yar Abba kina cutar da kanki ...
Sadda kai kasa tayi tace kayi hakuri Abba ina tsoran kada na gaya maka kuma daga baya Murza ta huce a kainane..
Ai kuwa ta yiwa kanta dan walahi sena d'au mummuna mataki a kanta yanda kika wahala itama seta sha..
Maysam tace a'a Abba ka kyaleta da halinta kuma ai ba'a meda sharri da sharri ....
Duk wanda ya nufeka da sharri to kai ka saka mishi da alheri ..
Nan ya rumgumeta yace shikenan y'ar Abba na hakura Allah ya isar miki ya albarkaci rayuwarki hakika ke y'a ta gari ce ina alfahari dake...ameen tace..
Ba karamin burge fulani sukayi ba bare ma Maysam gata yarinya karama aman da kaifin tunani har taji wani abu ya tsargu mata a rai..
Nan aka dinga bawa Maysam kulawa ta kirki komi se anyi mata kai hatta da cin abinci inde fulani na wurin to itada kanta zata bata wata irin shakuwace ta shiga tsakanin su ..kuyangi har mamakin wannan abu suke sunsa fulani da kirki ga tausayi amman abunda take yiwa Maysam abun azo a ganine musamman Maysam da take y'ar kauye..
Malan Musa ne zaune gaban sarki bayan ya kwashi gaisuwa ..sarki yayi gyaran murya yace to daman wata alfarma mukeso kayi mana ..
da sauri ya d'ago kanshi ya kalli sarkin se kuma ya meda kanshi kasa yace alfarma fa kuma ma a wajena?
Sarki yace ai muna nema alfarmar ka bar mana yar ka ne..
Shiru yayi bece komi ba a ranshi kuwa fad'i yake gaskiya bazan iya bar muku ita ba..
Gani shirun yayi yawa sarki yace dama jiya ne mukayi wata shawara da fulani kan inde bakayi wa yar ka mijiba to muna nemawa yarima Murad auren y'arka Maysam ... .
To fa fans kun ji wata sabuwa kuma .....
Mu had'u a shafi na gaba insha Allah .. .
Ina kaunar ku fans irin sosai d'in nan
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:25 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ππ
[8/17, 1:27 PM] A A Dboy: πΉπΉ *SANADIN ACCIDENT* π₯ππΉπΉ
π³πͺStory&Written
by
*FASMA* π³πͺ
π
ΏοΈ 15__16
*Saudat Farouq na gode sosai da kaunarki ..na ga mesage d'inki kuma in sha Allah zan gyara..Allah ya bar kauna..*
Dedicated to All my Fans
15__16
```Manzon Allah (SAW) ya ce''Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce''
Muslim ne ya rawaito shi``` .*
Malan Musa yace yarima Murad da Maysam? A gaskiya da wani ne dana bashi amman ai yarima ba sa'an auren Maysam bane..
Sarki yace haba Malan Musa dukan mu yan adam ne duk d'aya muke a wurin Allah babu wanda yafi wani babu fifiko se wanda yafi wani tsoran Allah ...hakane Allah ya bani mulki amman wannan ba yana nufin na fika sede ko in bakason had'a Zuri'arka da tawa ne
Da sauri Musa yace wane ni nace bana son had'a Zuri'ata da taku ..tunda hakane ta b'angare na bashi ...bansan ko ita Maysam d'in zata aminci ba amma fa wani hanzari ba gudu ba ya kamata kusan labarin ita Maysam din ..
Da sauri fulani tace a'a eh duk Maysam ta fad'a mana komi har irin sharri da akayi mata wanda tun wancen lokaci nasa aka mata duk wani gwaje2 daya dace kuma alhadulillah duk kariyar mutane ce .....kuma kada ka damu nida kaina zan sanarwa Maysam d'in
Malan Musa a ranshi ya ce kenan ta sanar dasu y'ar tsintuwace ..amman duk da haka suka amince ..to shi inbe basu ba dami ze saka musu da irin son da suke nunawa yar lelen shi..
A fili kuwa se yace shikenan Allah ya zab'a mana abunda yafi alheri ..
Daga haka ya koma clinik...
Waziri kuwa wanda akayi abun a gabanshi ...yayi wa sarki da fulani kirari sannan yace ina neman alfarmar fad'in tsokacin bakina game da wannan had'in da ake son yi ..
Fulani tace fad'i waziri an baka..
Ya kuwa gyara zama yace naga yarinyar nan ba jinin sarauta bace kuma a al'adar masarautar nan dan sarki se yar sarki hakama yar sarki se dan sarki ..amma agafarce ni idan na fad'i badede ba ...
Sarki yace hakane al'ada kace ba addini ba dan haka na rigayi dana zab'awa yarima mata mu hali ,tarbiyya da addini muka bi ,,ina anfanin auren jinin sarautar da ba tada tarbiyya ..daga haka yayi shiru..
Waziri kam kamar ya mutu dan takaici shi yar shi ya so a aurawa yariman sega wata yar qauyen qayau zowar rana tsaka ta samu a bulus ..shida yayi shekara da shekaru yana jira. . ..fakar idon sarki waziri yayi yayi kwafa...
Koda ya koma ya tarar da Maysam tana bacci abunta be tada ita ba ya zauna yana tuna magaganun da sarki......
Har fulani ta riskeshi nan ..bayan ya kwashi gaisuwa se kuma ya fita yana fad'in bari na dan zaga cikin gari ..
Ko minti biyu ba'ayi ba Maysam ta farka .arba da fulani tayi a tare suka sakarwa junan su murmushi ..ga kuyangu wasu tsaye suna mata firfita dukda AC da ke kunne saura kuwa a zube gabanta ...
Fulani tace ya karfin jiki?
Alhadulillah cewar Maysam ...
Fulani ta kuma cewa a zuba miki abicin kici ko?
Gyad'a kai kawai tayi..
Nan kuyangi suka fara zuzzuba abinci kala2 .Maysam ta kalli fulani tace abincin nan yayi yawa fa
Batace komi ba ta dauki plate guda me free rice da miyar zogale wacce tasha naman zabuwa ..spoon ta sa tace ci ko kuma sena baki a baki ne ...
Dariya Maysam tayi tace a'a zan iya ..ansar plate d'in tayi ta faraci ko spon goma batayi ba tace ya ishe ta ...
Fulani ta anshi plate d'in tare da cewa han na baki a baki tunda hakan kika fi so...
Babu yanda ta'iya haka take ansar abincin dan tana jin nauyi cewa fulani a'a.... Seda taci rabin tukon fulani ta kyaleta ..tasha lemun abarba wanda yaji kayan kamshi..bayan ta gama ne fulani ta umarci kuyangi dasu basu wuri jiki na karkarwa suka fice kafin nan seda suka yanyaka fruit kamar pomme(apple) ..pastèque (watermelon) dade sauran su..
Fulani tayi gyaran murya tace Maysam ina son muyi wata magana amman bansan ya zaki dauki abunba..
Maysam ta dauki yanka d'aya na kankanar tace ba komi haba kawai ku fad'i ni na d'auke ki tamkar mahaifiya ta ..
Sosai furuncin nan yayi wa fulani dadi har taji soyyayar yarinyar ta dad'a nimkuwa a zuciyar ta ...tace amince warki nake nema na ki auri d'ana yarima Murad ..
Maysam wacce take shan kankana ai kuwa seta kware ta ringa tari ...da kyar ya tsaya tace yarima Murad fa?ni?gaskiya bazan iya se kuma ta rushe da kuka ta kasa qarasawa tana kunyar cewa bata son jinin fulani kuma ma a gabanta..
Fulani ma sega hawaye shar yana bin kuma tunta tace Maysam bazan miki dole ba kema y'a ce kina da inci ...yarima kad'e Allah ya bani ...ina son ganin jikokina kafin na mutu amma shi yarima aure baya gabanshi saboda wani kuduri nashi ..ina ganin ke kad'e ce zaki iya zama dashi har ki'iya samun soyyayarshi because na yaba da hankalin ki nutsuwarki uwa uba kuma da hakurin ki ...shiyasa nake neman alfarmarki ..
Da sauri ta dago kanta ganin shar d'in hawaye a fuskar fulani da sauri tasa hannun ta ta goge mata t tana kuka tace kiyi hakuri na amince se kuma .. suka rumgume junan su fulani tace hakika ke y'a ta gari ce ..ina son ki dauke ni tamkar nina haifeki .tun lokacin da na fara ganin ki naji kin shiga raina time din daki ban labarinki na tausaya miki matuka ..ina son ki riqe amana ki kula mun da yarima ....
Duk da bata san yanda ake wani kula da miji ba amma seta tsinci kan ta da fad'in insha Allah zan kula dashi kuma bazan tab'a cin amanar ki ba...se bayan ta fa'di kuma se taji kunya tasa hannuta ta rufe fuskar ta .......girgiza kai kawai fulani tayi tana dan murmushi...
Se bayan sallar asar Malan Musa ya shiga d'akin tana lazumi daga zaune abisa gadon da alama yanzu ta idar da sallah....addu'a tayi ta shafa ..
Ta juwo tace Abba sannu da zuwa ..
Yauwa yar Abba ya jiki ..?
Da sauki ta ansa ..
Se kuma sukayi shiru har na tsawo yan mintuna ..
Maysam tace Abba kaji abunda momy fulani tace mun d'azu.....?
Ya san de be huce zancen auren ba amma seyace a'a se kin fad'a dan ya k'arda ..
Nan ta labarta mishi komi tana jiran jin mizece ...
Yace kwarai kuwa y'ar Abba ni suka fara tuntub'a kuma na amince ......dan mutanen nan suna kaunarki suna da kirki da karama ..kuma shi sarkin da kanshi ya nemi auren ki ....ba muda abunda zamu iya saka musu dashi ..kiyi hakuri ki karb'i rayuwa a duk yanda tazo miki. ....na tabbata bazasu cutar dake ba....
Kukan daya zo mata ta shafe tace shikenan Abba Allah yi mana zab'i na alheri..
Ameen ya ansa nan suka ci gaba da hirar su irinta d'a da uba.....har magarib
..
Haka akayi ta kula da Maysam har na tsawon wata biyu .alhadulillah kuwa sauki ya samu har tana taka qafar .....nan suka fara shiryen2 komawa qauyen su ..wanda sati biyu ya rage a daura auren dan haka sarki ya nemi alfarma kuma Musa ya amince ...
Abunka da gidan sarauta nan aka fara kuskus ...
Waziri ne zaune gaban sarauniya Madina yace gaskiya nayi sakaci dayawa dana san haka zata faru baza 'aba y'ata yarima ba dana biyewa shawarar ki da dad'ewa... .shi 'isa yanzu nazo mu gama karfi da karfe dan mu cimma burin mu..
Wata dariya Madina ta kece da ita tace ai daman kwad'ayin ka yaja maka kayi ta jiran gawon shanu ...da kaso ai da yanzu kaine a kadagar Mulkin nan aman wai kai me y'a ..ai ga irin ta nan ..
Waziri yace a bar tuna baya yanzu de na mika wuya...
Da kyau cewar Madina ...yanzu de babu wani plan mu bari se ya dawo kasar...
Nan suka ringa kuskus wanda bana iya jiwo komi..
.
A b'angaren.Murad kuwa besan wainar da ake toyawa ba ..yana zaune a office dinshi kiran Me martaba yashigo ......se kawai ya tsinci kanshi da fad'uwar gaba ....haka ya daure ya d'au kiran....bayan ya kwashi gaisuwa Sarki yace ya zancen mu na zaka kawo mun wacce kake so gashi har time din ya shud'e aman bakace komi ba..
Sosai kai yayi kamar yana gaban shi yace ayi hakuri ban samu ba..
Alhadulillah to ni na samo maka kuma nan da two week ne dan haka seka fara shirin dawowa.
Wani mummunar faduwar gaba yarima Murad yayi ..yace...
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:27 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ππ
[8/17, 1:31 PM] A A Dboy: πΉπΉ *SANADIN ACCIDENT* π₯ππΉπΉ
π³πͺStory&Written
by
*FASMA* π³πͺ
π
ΏοΈ 17__18
*Jinjina ga MAMAN SHUREIM hakika kin cancanci* *yabo na ban girma ...Allah ya* *miki jagora a lamuran ki ....thanks for all .*
. *wannan page d'in* *na kine ke kad'e Fasma tace kiyi* *yadda kike so* *da shi*. .. _Allah ya qara donkon zumunci _
17__18
```Manzon Allah (SAW) ya ce''Sallar jam'i tafi sallar mutum guda daya da daraja ishirin da bakwai''
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi``` .
Wani mummunan fad'uwar gaba yarima Murad yayi dan danan zufa ta karyo mishi duk da AC da ke kunne yace Dady two week fa ?kamar zeyi kuka .
Me martaba yace kwarai kuwa kuma bazan karb'i excuse d'in kin rashin zowanka ba dan haka sati me kamawa ina son ka tattaro ka dawo gida....
Beyi iya cewa komi ba se to in sha Allah zanzo..
Sarki yace yauwa Allah yayi ma albarka ...
Ameen yace lokacin idonshi har sun kad'e sunyi ja kamar wuta ..
Suna gama wayar da Sarki ya kuwa dannawa fulani kiran .
Sallama kawai ya iya yi mata ya fashe mata da kuka..kamar wa'i qaramin yaro
Bata hanashi ba seda yayi me isar shi sanan tace Murad ..
Jin ta kirashi da sunanshi yasa ya nutsu ta wayar kamar yana gaban ta dan bata fiye kiranshi da sunan ba se de inhar maganar dazata fa'da tanada matuka mahimmaci
Fulani tace Murad ina so kayi hakuri ka zama me biyyaya ga iyayen ka ..kasan baza mu tab'a zab'a maka abunda ze tab'a cutar da kai ba.......ina son ka zama me tawakali a rayuwarka .....kaza me karbar da kuma yin imani da kaddarar rayuwa au ta alheri wala ta sharri ....
Na sani ba tun yauba kake kai bazaka tab'a yin aureba .....kasan kuwa aure sunna ce babba ....Manzon Allah SAW ya na ce wanda baya son sunnata to baya tare dani ...shin kana son kasance wa cikin mutanen da basa tare da Manzon tsirane...?
Kamar yana gabanta yake girgiza kai ..yace Astagafirullah....Momy kiyi hakuri daga yau banza sake ba. ....
shikenan Allah yayi mana zab'i na alheri..
Ameeen tace Allah ya maka albarka.....to baza ka tambayyi wacce yarinya ce ba?
A'a Momy duk wacce kuka zab'a min tayi mini dan banida zab'in da ya huce naku....
Shikenan Son Amma ko sunan ta bazaka so sani ba?
Bayason Fulani ta fuskancin wani abun kawai se yace ...ina so mana ..
Sunnata MAYSAM
seda gabanshi ya fad'i jin sunan aman ya dake yace ..shikenan Momy inada aiyuka anan Office ...next week ganinan zowa in sha Allah..
Cike da murna fulani tace Allah ya kawoka lafiya a ganinta ita ya sauko ya amince da auren daga nan bata san qarfin hali kawai yake yana danne zuciyarshi..
Ranar wuni yayi yana tuno zancen auren ..gaba daya ya kasa qarasa aikin dayake se gidanshi ya koma ...yana me bakin cikin wannan al'amari..
.
A b'angaren su Malan Musa sun isa lafiya ...Murza se kaf2 da Maysam take tana tsoron Malan Musa yayi mata maganar karayar Maysam amma se taji shiru hakan yasa ta saki jikinta dan duk a ganinta Maysam bata gaya mishi yanda akayi.ba..
Ai kuwa Malan Musa na fita koda massalaci ne to fa seta san duk yanda zatayi ta muzgunawa Maysam koda rankwashine kuwa...
Bayan kwana biyu da dawo warsu da dare tsakani magarib da isha'i suna zaune suna hira Malan Musa yace Murza dama akwai wata magana danakeson muyi.
Gyara zama tayi tace ina jinka Allah yasa muji alheri ..
Murmushi yayi ya ce alheri babba ma....
Ai kuwa cike da zumud'i tace har na qagauta ka fad'an mana
Yauwa dama Maysam ta samu mijin aure ne .
Wani turnikeken bakin ciki taji ya taso mata aman ta danne tace miji ..a ina dan ita jira take taji yace dan shaye2 ne ko kuma wani dan daba ko barawo wanda de Maysam zatasha wuya..
Ai kuwa yace Yarima MURAD dan Sarkin Mustapha me damagaram..
Kasa boye bakin cikinta tayi har seda tace na shiga ukku ni Murza Yarima Fa?dan sarki kake nufifa?se kuwa ta fashe da kukan bakin ciki..
Shi abun ma mamaki ya bashi..be iya cewa komi ba se girgiza kai dayayi a ranshi yace tsanar da take yimata har takai haka?to Allah ya shiryeki inme shiryiwa ce..
Kiraye2 sallah isha'i aka farayi ..Malan Musa bebi ta kanta ba ya fice mosque..
Tana gani fitarshi ta fad'a d'aki Maysam na sallah lokaci se jin saukar dorina tayi nan ta dinga jibgarta harta kaita kasa ..ita kukan azaba ita kukan bakin ciki..
Ta rasa miza tayi se kawai ta kama dantsen Maysam ta gantsara mata cizo har sau ukku har ta fitar mata da fata tace walahi baza ki tab'a auruwa ba ..senayi duk yanda zanyi na hana wannan ma..
Wani sabon kuka ya zo mata ta d'aga hannun da niyar kaymata mari taji Sallamar Malan Musa da sauri tace yi mun shiru munafuka sauran ki gwada wani alamu har malan ya fahimci nayi miki wanin abun (kuji fa keda yau har da cizo)...
Maysam kam kwna kuka tayi da ga bisani ta dauro alwala ta rinda jero nafilfi tana roqon Allah ta mata zab'i na alheri
Murza kuwa kwana tayi tana neman mafita shawara kawai ta