Showing 27001 words to 30000 words out of 99653 words
kaleshi yace haba Murad kamar ba Docteur ba zaka bari ciwon ka ya tashi har haka koma ka sani sare irin conséquence din daze biyo baya in har ba'yi intervenir da gagawa ba.....idan ma wani abun ne yayi Sanadin tashinshi to ina baka shawarar idan akwai yuyuwar ka mallakeshi to kayi gaggawa inko ba hakaba ka dangana dashi amma fa zakasha wuya ko kuma ma yayi sanadiyar zama ajalinka...
Murad yayi karfin halin yin dariya yace bazaka gane ba ..tunda de yanzu ganinan ai se kayi abunda ya dace.. A ranshi yace abun dama mallaki nane kawai de bazan so naci amanar my sweetbabyna ba(🙄kaide kasani iya kacinta de in lokacinka yayi ka mutu mu kuma musha gumba da nono atoo....,😎.)
Ya rurubuta mishi magani .sanan yace tode a iya bincike na baccika bashida nasaba da ciwonka mayebe gajiyace ....daga nan ya mishi sallama akan ze tafi siyo maganin da kuma dan abinci dazeci
Gyada kanshi yayi tare da mishi godiya ........
Washe gari kam ras ya tashi har ya tafi wurin aikin shi sede zuciyarshi bata dena yime zogi ba ..aiki ya tarar ba kadan ba.yinin ranar kaf a aiki yayishi se gab da magrib yakoma gida ...bayan yayi isha'i ya dauko wayarshi se alokacin ya ganta ashe a kashe take...yana kuwa kunnawa kiran fulani ya shigo ..
Da sauri ya daga ya gaïda ta tare da jero mata ban hakuri ..
Daga can fulani tayi dariya tace shikenan ya huce da fatan ka isa lafiya ...
Nan suka dan taba hira tace wai ni shi ko ka sanar da Maysam tafiyarka ?
Seda gabanshi ya fadi shi sunan ta kade ma in yaji se gabanshi ya fadi bare yaji muryarta ko kuma ya ganta...gaba daya se yaga kamar yar kanwarshi ya daure de yace to ai Momy batada waya ..
Amma kasan baka kyauta ba ko ko batada waya ai seka biya ta Maradin kayi mata bankwana ko..to yanzu de ba wanan ba ka kirayi offishin makarantar sesu bata ..
To kawai yace amma fa badan ze kira din ba....nan tayi mishi sallama tare da jaddada mishi ya kirayi Maysam din..kuma zata kira taji ko yayi ....
Yayi kicin'2 da fuska shifa gani yake Momy ta takura mishi .... babu yanda ya iya bayan ya kirayi Mai martaba hakade ya kirayi makarantar dayake sun sanshi farin sani koda ya basu sani ya nemi zeyi magana da Maysam ba a wani bata lokaci ba aka kirata....
Tana ansar wayar bata tsaya taji me kiran ba tace ina wuni Momy ya gida? ya.. ....cak ya tseda ita yace ke wai bakida hankali ne bakiji me kiraba kawai ki kama zuba zance yaja tsuka..mtssss...
Shiru tayi can tace kayi hakuri ban san kaine ba..ina wuni..
Se kuma jikinshi yayi sanyi yace lafiya ....yace da fatan de kina karatu dan walahi kinji na rantse idan har baki zo ta daya ba to kada ki kuskura ki dawo gida hutu ...
Tace to..a ranta kuma tace daga kira se masifa
Yace kuma badan kinga na koma ba kice zakiyi abunda kikaga dama zansa a dinga fadamin duk wani motsinki da kamaki da laifi daya sekin raina kanki
Nan ma tace to(a ranta tace kenan ma baya kasar tayi kwafa)
Nan de yayita banbaminshi
Ita kuma komi se tace to ...
Ya kari fadace2n shi ya kashe wayar ...
Maysam ta koma aji amma tunanin fadan Murad ne fal ranta ....tace waishi baya gajiya da yiwa mutum fada ne ....komi shi se yayi fada da mugunta ciki........tana shiga aji ta tatara komi ta watsar tacigaba da karatun ta.....
A bangaren Murad kuwa yana kashe wayar ya dafe zuciyarshi da hannu saboda wani irin zogi da take mishi ...ya daga waya ya kirayi docteur Mark tun yana daukan abun wasa har ya fara ganin dishi2 .kan kace mi tuni ya zube nan kasa .........Mark na shigowa ya tarar da shi cikin wannan halin dataimakon wani abokin aikinshi dayake su biyu sukazo...suka ciccibe shi sukasa a mota suka nufi hospital dashi ...kafin su isa tuni ya sume...direct emergency aka shiga dashi.......
Ta fa fans muje zuwade....
Nikuwa nace amma su waziri sunyi aikin banza da suka tsaya a barin masarauta da ai se susa a shiga tsakaninshi da har mazauna a cikin masarautar tundade gashi ya bar garin amma kuma ya ci gaba da mu'amalal shi da parents dinshi..amma a ganina fa🙃🤔
Fasma ce🖊
Ahmed Gumel
[8/31, 9:56 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/2, 9:49 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
🅿️ 45__46
```Manzon Allah (SAW)ya ce''duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce''
Muslim ne ya rawaito shi
```
Kafin su isa tuni har ya sume ...direct emercency a ka shi ga dashi ..
Nan docteurs suka duqufa dan ceto rayuwarshi a bunka da turai kayan aiki birjik dan haka kan kace mi cikin ikon Allah numfashin shi ya dawo normal ....amma fa idanun sa a rufe da alama bacci yake.....Be farka ba seda ya kwana yayi rabin wuni har wata rama yayi ta kwana daya .......Mark na zaune kusa da shi da yake shi ke jinyarshi ya ga bakin shi ya na dan motsawa kamar me sonyi magana ga kuma idon shi a rufe suke...
Kusanto kunnenshi yayi dede bakin se yaji Murad na ambatan sunan Maysam.... Maysam...
Cike da mamaki Mark ya dago kai yana kallon Murad dake kwance yace Maysam?to ko.....
Kafin ya gama tunanin Murad ya fara bude idanunshi Tar ya bude shi se akan Mark ..yayi karfin halin yin dariya ..
Mark ya kamashi ya kaishi tolet yayi wanka tare da doro alwala ..........yana zuwa ya saka jallabiya ya kabarta sallolin da ake binshi bayan ya gama Mark ya gabatar mishi da abinci ....kadan yaci shima dan ya samu ya kama karfin jikinshi ....
yana tsakada ci . Mark ya kalleshi ya ce .....waccece Maysam ???
Tambayar a bazata tazo mishi dan kuwa har seda ya kware .....
Mark ya tsiyayi ruwa yabashi
Da tarin ya lafa yace Maysam kuma ....''.non je ne la connaît pas ''...(ka ban santa ba)
Mark yayi dariyar gefen baki yace shikenan idan baka santa ba amma ka sani sunan dakayi ta kira kenan ......
Ya mutsa fuska yayi yace nide ban santa ba ..ya kauda fuskar shi...
Mark yace bazan tambayeka abunda ya tado maka ciwon ba amma abunda zance maka kayi gaggawar mallakar ko hakura dashi dan kuwa idan ka bari zuciyar ka ta sake bugawa kamar yanda tayi jiya tofa the best solution se amma ka opération kuma kasan irin ''risque''(hatsari) din dake cikin opération....
Gyad'a kai kawai yayi amma badan ze iyaba dan ko yanzu dayaji sunna ta seda yaji wani zogi a zuciyar shi ....shi yasa tsanar yarinyar yake kara yawa a zuciyarshi.......
kwanan shi ukku aka sake shi ya dawo gida ....ran na hudun ma ya koma aikin shi duk duk dade be wani kama karfin jikinji kamar da ba...
. .
.Abangaren Maysam kuwa karatu take ka'in da na'in ba kama hannu yaro ......dayake kuma ta hadu da masu son karatu Mufeedah da Mariyam ga kuma ilimi ..duk inda bata fahim ta ba suke ganar da ita daya ke su sunyi jss1 ..a duk inda ka gansu to fa zaka tarar suna biya karatun sune na bako ko na arabi........
Akulum kuma Maysam idan ta tuna cewa SANADIN ACCIDENT ne had'uwar su da Fulani har ta samu gatan zuwa école ga islamiyya taci me kyau ta sha me kyau sannan ta saka me kyau ga soyyayar uwa da Fulani ke nuna mata ...se kwai ta fashe da kuka tare yi wa Allah godiya .su Mufeedah de se suyi ta bata baki da hakuri dan su ji suke idan ta tuna rabuwa da yan gida ne take kukan.........
Haka de rayuwa tayi ta tafiya yau da dadi gobe akasin haka inda yau har su Maysam suke zana exam na karshen shekara wato pass to jss1......sun dage karatu suke bana wasa ba ..sati suka jera sunayi se kuma sati me zuwa za'a fada musu résultat se kowa ya tafi gida hutun wata ukku......lfy lau suka gama question din kuma basu bata wahala ba ....tsoran ta daya kada tazo ba ta daya ba saboda har yanzu bata manta da sharadin Murad ba...
A wannan lokacin kuwa Fulani har ta gaji da fadan rashin zuwan Murad tayi fadan tayi fushin ta gaji kullum maganarshi daya ce cewa zezo .....kai daga baya in ta kirashi da sun gaisa seyace mata yana dakin tiyata ko kuma aikin sun mishi yawa ze kirata da ga baya kuma ba kiran zeyi ba..tun abun baya damunta har yazo yanayi....se de kawai ta bishi da addu'a..
Shima anashi bangaren yana so yazo dan yayi missing dinsu barema Maysam zuciyarsa na matukar son ganinta amma besan miyasa baya son dawowa garin ba ba .....gashi har yau zuciyar na mishi zogi lokaci zuwa lokaci......
. .
A bangaren Waziri kuwa duk ya bi ya fige ya rame saboda diyar shi MAHEEBATOU dake cikin mawuyacin halin sakamakon kama mahaifinta wato waziri cewa da sa hannushi akayi wa Murad asiri ya bar kasar ita kuma tunda ta taso ta mallaki hankalin kanta bata da wani buri da ya huce ta ganta a garakal mulki tanayin yanda taso kamar Madina dukda de tanada kuyangi har biyu amma ita tafi so ace gaba daya masarautar a hannunta take........lokacin kuwa hanya daya take ganin zata bi ta cika burinta hanyar kuwa itace ta auri Murad idan sarki ya mutu tana da yakinin yarima Murad shi ze gaje shi tunda shi kade ne danshi na miji ...
Mahaifinta waziri ya daure mata gidin se abunda take so takeyi kasancewar ita daya Allah ya bashi bayan shekara da shekaru da yin aure shi yasa ya dauki karan so ya dora mata .duk abunda zatayi baya ganin laifinta ....koda ta sameshi ta sanar mishi burinta se ya goya mata baya ...a lokacin ya samu me martaba da yanaso akara hada zumunci wato a hada yarima Murad da diyarshi Maheeba aure ...
Sarki ya sa aka kira Murad a lokacin sannan ya sanar masa idan har yana da ra ayin aurenta ..
Bude bakin Murad yace a'aaa kiri2 yace shi baya sonta ...wannan magana tayi matukar batawa waziri rai amman ya danne zuciyarshi...
Koda ya sanarwa da diyarshi yanda sukayi se kawai ta fashe mishi da kuka har dasu birgima ..... .....duk da haka seta fara shigewa tana nuna mishi so ...shi kuwa Murad be masan tana yiba duk inda yayi se taje ........ganin haka yasa ya tattara ya koma England da zama bayan ya sha fama da fulani.....
Wannan tafiyar tashi gaba daya Maheebatou ta fice a hanyacinta dan a rayuwarta ba a saba ce mata a'aa ba dole tasa waziri ya turata kasar Mali karatu wajen dangi mahaiyarta da alkawarin idan ta dawo ze cika mata burinta .....
To fa ranar da tazo ne ta riski Maihaifinta na zancen asirin shida mahaifiyarta ...tun lokacin ba agane mata ba ..dan dama saboda cikar burinta ta dawo....
Ganin abun bana qarewa bane Waziri ya wanke kafarshi ya tafi ya sanarwa Madina halin dayake ciki ..amma Madina fir ta kiya ..babu irin rokon da beyi mata ba kan a karya asirin Murad ya dawo daga baya a san yanda za'ayi aman tace bata san zancen ba ..
Rai a bace ya fito kamar wanda zetashi sama a ranshi yace baki san ko biye miki danake saboda Maheeba bane dan na samu na zama sarki sena barta ta taka wanda take so...
Haka ya isa gida yanata banbami amman mi abunda ya tarar ya kara daga mishi hankali dan kuwa Maheeba numpashinta ya dawo sama2...
Ba shiri ya fita ya kama hanyan se wurin BOKA gobe da nisa ...
Makuddan kudi ya zube mishi nan yace yana son a karya asirin Murad ya dawo gida kuma idan ya dawo kawai a daura aurenshi da diyarshi Muheeba...
to fa fans kunji wata kuma.....
Shin ya luke ganin zata kaya ne?
Fasma ce
Ahmed Gumel
[9/2, 9:49 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/2, 9:50 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
🅿️ 47__48
```Manzon Allah (SAW) ya ce'' ciyarwar mutum ga iyalinsa sadaka ce''
Bukhari ya rawaito shi.```
Makuddan kudi ya zubewa Boka gobe da nisa yace yana son a karya asirin Murad ya dawo gida kuma idan ya dawo kawai a hada aurenshi da yarshi Muheeba...
Boka Yayi wata mahaukaciyar dariya seda waziri ya tsorata can kuma ya daure fuska ya ce ina jin dadin aikin ka ......saboda akwai zubar da jini ...
Waziri ya zaro ido yace jini kuma
Ee na jarirai ma kuwa idan har a nason aikin yayi kyau ...
Waziri yace ayi komi ma idan de har burin er leleta ze cika sannan kuma wani hanzari ba gudu ba ina son abani maganin da zata mallake shi se abunda tace za ayi nan ya sake zube mishi kudi ..
Boka yayi dariya yace an gama ..yayi yan zubace2n shi ..ya dauko wani kullin magani yace wannan a abin ci kona sha za'a zuba mishi amma fa a bari har a daura aure ......sauran aiki mutanen mu zasu cika shi da zarar sun sha jinin jarirai komai ze wakana kaide kawai abunda zakayi shine ka cusawa Murad auren da zarar ya dawo ....
cike da murna ya karbe maganin ..har ze tafi la'anan nan Boka yace kada ka tado zancen auren a kwanakin nan dan kauda duk wani kokwanyo na mutane ka barin a samun koda sati ne da dawowar shi sekace mishi kana so ya auri yar ka ...kafin nan mukuma zamu cusa masa kwar jinin ka da ba ze iya cewa a'a ba ..
Cike da murna ya tafi gida jin harda shawara boka ya bashi ....
Muheeba dake zaune se hirar su suke ita da mahaifiyar ta har da shewa ...ai kuwa ta najin sallamar mahaifinta ta koma ta kwanta ta fara numpashi sama2.......(tab a raina nace ashe gaba ma da gabanta makircin wani yafi na wani)
Da sauri ya isa kusa da ita yace sannu Muheeba .....ki kwantar da hankalin ki wannan karon Murad na kine ...kinga wannan ya fiddo kullin magani yace na mallaka ne..
Caraf ta bude ido aman saboda makirci de taki tashi ta zauna tace Abba zan auri Yarima Murad na hau kadagar mulki ? ........
Waziri yayi dariya ya ce sosai sannan ki shirya wa zowar shi kwanan nan yana kuma zuwa se.aure kawai ...
Ai bata san lokacin da ta tashi zaune ba ...tace wai Allah da gaske?
Yace haba yar lele kin bazan miki wasa da irin wannan batu ba ....
Nan murna ya cika ta har ta fara hangota tana ba kuyangi order se kawai ta fashe da dariyar farin ciki ..
Ganin haka ya waziri fita ya nufi fada ciki da murna yasa yar leleshi farinciki.....
Yana fita suka tafa itada mahaifiyarta tare da yin shewa tace kai mama kin iya hada plan da ba dan nabi shawarar ki nayi cutar karyan nan da baze je a karya a sirin ba ...
Tace kede bari y'ata ai rayuwar ce seda haka ...
Suka sake yin shewa tare da tabawa kamar ba uwa da diya ba ..
.
A bangaren Maysam kuwa yau aka basu vacation bayan an bawa kowa sakama konshi inda Mufeedah tayi ta daya Maysam ta biyu se kuma Mariam ta ukku sunsha kyautikika ..ita de Maysam gaba daya tayi sanyi ta san ba ita ba zuwa hutu gida duk wanda ka gani cike da dauki yau zata tafi gida banda Maysam ...
Mariam aka fara zuwa dauka sanan motar su Mufeedah tazo ...tananan tsaye motocin fulani suka fara zowa daya na bin daya har goma dan kuwa fulani da kanta tazo daukarta ... ......
Maysam na hango fulani ta kuwa zanbad'a da gudu ta rungumeta ....
Sun jima a rungumen fulani ta dagota tace Maysam ya banga kayan ki ba?
Ta dago kai idanun ta har sun kawo ruwa tace Momy banyi ta daya ba ta biyu naci..
Fulani tayi murmushi tace kai amma kinyi kokari fa congrats dauther...
Maysam tace Momy kin manta da sharadin Ya Murad ne....
Fulani tace sharadi kuma?dan ita har ga Allah ta manta
Maysam tace yace idan har banzo ta daya ba to bazan zo vacation ba..
Fulani ta bata rai tace bari batun shi je ki hado kayanki mu tafi...
Da sauri ta zube nan kasa tace Momy ki mun rai ki barni nan dan walahi ko kiranshi na karshe seda yayi mun warning... Sega hawaye shar2 ..
Fulani ta dagota tace kada ki damu zanyi mishi bayani...
Maysam tace kiyi hakuri Momy badan bazan iya bin umarnin ki bane a'a kin huce haka a wurina bana son shiga tsinuwar mala'iku ne dan cewa yayi bada izinin shi ba inde har banyi ta daya ba nazo hutu.....ko satin nan a islamiyya malam ya kara jaddada mana irin sab'awa iyaye ko miji bala'in dake faruwa da mutun
....
Ran fulani ya kara baci a ranta tace ta yaya ma ze gindaya mata irin wannan sharadi kan wani banza dalilin shi da beda tushe ....nan ta zaro waya ta shiga neman layin shi amma a kashe...tayi kira yafi a kirga amman bata shiga...ta kalli Maysam tace shikenan amma bazan iyabarinki a school din nan ba koda kuwa da kuyangi..ki had'o kayan ki na kaiki bade shi garin ne yace bazaki bari ba?
Ta ce eee
Fulani ta bada order a ka debo kayanta aka saka a booth ...suka fice ...
A motan kam fulani tasha surutu har suka iso wani tamtsamemen gida ....tun kofa gidan abun kallo ne bare cikin ba'ama zancen ...katon gidane na gani na fada duk da babu kowa ciki se me gadi da me bawa fleurs (flowers)ruwa amma fa ko ina tsap2 nan kuyangi suka fara goge2 masu shara nayi masu daura abinci ma nayi ..fulani da Maysam kuwa shopping suka tafi kafin su dawo komai is ready.
Se biyar na yamma fulani suka fara shirin tafiya bayan a zube mata kuyangi bakwai dan yi mata komi se digorai biyar ...
Tofa nan ake yinta dan kuwa Maysam kuka take shab'e2 fulani ma daurewa kawai take dan ji take kamar tayi mata kukan sede ga bayinta nan