Showing 3001 words to 6000 words out of 99653 words

Chapter 2 - SANADIN ACCIDENT COMPLETE BY FASMA

FASMA   

05 Jul 2024

14082

Maysam cigaba da fat3 yayi tana jiran taji mi Malam ze fad'i..
D'an jim yayi yace nikaina abunda nake dubawa kenan dan d'azun nan Mai gari damuka gama yin sallah bayan yayi min barka nasararta se kuma yace d'anshi Murtala yaga y'ar wurina kuma yana so ..na de cemishi zanyi shawara da iyalina tukon..yakike gani kenan
Wasu sirarrun hawayene suka zubowa Maysam tayi sauri ta gogesu a ranta tace aure kuma..
Wani malolon bakin ciki ya tokare mata wuya aman seta cije tace kawai ka bashi tunda Mai garin da kanshi ya nema kaga be dace ba ka hana d'anshi ko...ta kuma cewa kaga jiya2 nan aka saka ranar qawarta Ma'u ..a ranta kuwa cewa tayi yanzu de matsalar cigaban karatunta ce a gabana tunda nayi nasara daga baya kuma sena ji da auren dan walahi bazan barta ta aurin d'an me gari ba .
Malam yace shikena Allah ya zab'a mafi alheri...
Kasa2 Murza tace ba Ameen ba..
Ya kalli Maysam yace y'ar Abba kinji duka abunda mukace in har bakya son Murtalan ki fad'an bazan miki dole ba..
Kanta a kasa tace Abba zab'inku shine nawa kuma ai dama Uwaye ya dace su zab'awa yar su budurwa miji .. Allah yayimana zab'i mafi alheri
Ameen y'ar Abba hakika ina alfahari dake Allah yayi miki albarka ..
Ameen tace ta shige d'aki dan wani kuka yazo mata..a ranta tace yanzu a rasa wanda za'a had'ani dashi se marar mutunci nan meyiwa y'ay'an mutane fyad'e ..ta d'aga hannu sama tace Allah gani gareka kayi mini zab'i na alheri ..tana kuka ta shafa ..nan bacci ya kwasheta....
Tofa fans anya Murza zata bari ayi auren nan kuwa?
Ina sonku masoyana irin dayawan nan
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:08 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/17, 1:10 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

🅿️ 07__08
```Mazon Allah (SAW) yace''lallai mamaci anayi masa azaba saboda kukan masu rai''
Ruwayar Bukhari da Muslim ce```
Washe gari da matse nanci ciwo kai ta tashi saboda kikan datayi dayake babu school tayi shara da wanke2 gidan tana kiciniyar d'ora break Malam da Murza suka fito da alama tafiyar kasuwancin shi zashi bata san lokacin da hawaye suka zubo mata a ranta tace yau kuma ko wata azabar zansha ....nan ya bawa Murza kud'in cefane ita kuwa Maysam dari biyar ya bata tunda yanzu ba school ..ko fita daga gidan beyiba Inna Murza ta kwace kud'i tayi shigewarta d'aki ashe Malam Musa ya gani dan yayi mantuwa ya dawo ....bece komi ba ya d'auki abunda ya manta ya sake yiwa Murza sallama sekuma yace Maysam ta biyoshi ze aiketa wani gu......Murza bata kawo komi a ranta ba..
Bayan sun fita ya kalleta yace yar Abba ki zanki hakuri da Innarki wata rana se labari ki qara hakuri da ita kinji ko...ina sane daduk abunda take miki dan qawarki Ma'u tana sanar dani komi yayi zafi maganinshi Allah dan baze yuyu na dinga tafiya dakene ba ..
Wani hawaye taji ya zubo mata magana ma kasayi tayi se gyad'a kai kawai ta iya'yi ...
Share mata hawayen yayi ya rumgumeta yana lallashi har ta fasa kukan ..ya ciro dubu biyu ya bata yace ki sayi duk abunda kike so kada ki bari innarki ta gani bare har ta kwace miki kinji kuma daga yanzu zan ringa baki kud'in da zakina kashewa ...
To tace Abba na gode Allah ya kara bud'i ya bada sa'ar abunda aka tafi nema...
Sosai yaji dadi addu'ar yace ameen yar Abba Allah ya albarkaci rayuwarki....
Ameen tace ..
Nan ya tafi ya barta tana d'aga mishi hannu har ya bace ganinta...a bakin zaninta ta kulle kudin ta koma gida...
Tana shiga taga inna da tulu a hannunta tasan mi hakan yake nufi dan haka da duka da niyar karb'ar tulun ai kuwa ta daka mata duddu tace shegiya annamimiya har da wani kukan munafurci dan Malan yayi zaton ina cin zarafin ki in bayanan ko.....
Itade batace mata komi ba ..
Dungura mata tulun tayi tace saura kitsaya inda kika saba tsayawa .....
Biyawa Ma'u tayi sukatafi tare ..a hanyarsu ta dawo ne suka gamu da Murtala shida abokanan shashacin shi....
Nan suka taresu har sun tatare zanin su zasu arce Murtala yace wly in kuka gudu kun jawowa kanku ..cak suka tsaya ...
Ya matso daf da Maysam yace matana ya kike ...kin san banso kina daukan ruwan nan bara natayaki ..yayi niyar sauke tulu daga kanta nan taja baya da sauri ..ma'u tace wai miye hakane kun wanizo kun tsare mu a hanya har kana wani kiranta da matarka kota ina ma...
Daka mata tsawa yayi yace ke kuwa asuwa ...kinci darajar kece yarinyar da abokina ze aura wly da yanzu na keta miki haddi...tsit kake ji Ma'u tayi...
Suka kwashe da wata arniyar dariya ya sake matsowa daf da Maysam wadda ita alokacin tuni hawaye keta zuba....yace haba tawan nan yasa hannu ya share mata hawaye se kuma yayi niyar rumgumeta wai azuwan lallashi ..
Efa nan ake yinta nan kokowa ta barke har rigarta ta cire daga gefen ai bata san lokacin da yarda tulun anan ta arce a 60.....zasu mara mata baya Murtala yace a'a ku barta ku muje idan zamu kawai ....
Seda ta isa kofar gidan su tukon ta tsaya duk jikinta karkarwa yake ...se kuma ta sake fashewa da kuka ...ga abunda Murtala yaso yimata ga kuma tulun Inna ya fashe wanda jiya2 nan ta sayeshi ta jima nan tsaya sannan ta shiga gidan se rarab'ewa take..
Inna na ganinta ba tulu tayi dariyar mugunta dan ta fad'i gassasa yau....
Game hanunta tayi tace dan Allah inna kada ki dokeni walahi su Murtala ne nan ta kwashe yanda sukayi ta fad'i mata..
Wani ashar tayi ta rarumo icce ta fara buga mata tace kicede yau asirinku ya tunu keda shii wurin gudu kika barar mun da tulun ga sheda nan harda cirewar riga ..dukan ta take baji ba gani ai kuwa dubu biyun da Malan ya bata ta fad'i kasa ..
Salati Murza ta shiga yi tace munafuka asirinki ya tunu ashe karuwancin naki me degree ne harda dubu biyu ...nan ta dauke kudin ..ta d'ago fuskarta za zazzabga mata mari ta kuma sa hannun a kwalmin idon ta dunga kyarkyarta saman idon har seda taga jini yana fita tace shegiya me kama da mayu wata ran sena fidda miki idon nan kowama ya huta ..sanan ta cigaba da duka har seda taga bata motsi tajata ta yar a tsayar rana..lokacin kiwo nayi ta sheka mata ruwa ta tashi tace maza tashi ki fice kiwo..
Tasan kotace zatayi sallah baza ta barta ba setace Inna abincin nafa?
Abinci fa ai kedashi se gobe kuma tunda yau kinyi kari ...
Haka ta fita gwani ban tausayi...
Haka rayuwa tayi ta tafiya wanda kullum se Murza ta caje Maysam inde harta fita ...ga kuma takurar da Murtala ke mata kullum inde sa had'u to seya nemi tab'a jikinta...shiyasama bayan anyi auren Ma'u ta sati ta gayawa Malan itama gwara asaka nata auren dan saboda tsaro..
Haka kuwa akayi nan aka saka ranar goma ga sabon wata kenan nanda kwana goma...
Iya tashin hankali Murza tashiga dan ga dukka alamu auren nan ba fashi gashi kuma da gani yarinyar zata huta idan ta auri d'an megari tunda ko kayen lefenta ya kere na kowace budurwa nanfa ta fara shige da fice ta ciru ta kullu dan ganin auren ya fasu ..
Nan ta wanke qafa taje gidan me gari har d'akin uwar Murtala ta shiga dayake sunsa sirukarsuce sesuka mata tarba ta kirki ......bayan gaishe2 tace dama wata magana ce take tafe dani...
Uwar Murtala ta gayra zama tace ina sauraronki..
Nan ina ta tsara karya da gaskiya ta fad'i mata wanda harda cewa ai yarinyar bin maza take yanda kasan kariya haka take bin maza ....
Inna Murtala tayi jim ...can tace shikenan barin zan sanar dashi Murtala kinsan yaran yanzu se abunda suka sa gaba sukeyi....
Nan ta kakab'e zane ta fito...dede kwanar gidan ta gamu da Murtala ..nan ya gaydata gatse2 bata wani damuba tace yauwa d'an albarka daman akwai maganar dana keson muyi ......
yace to ki fad'a kawai danni sauri nake..
Yauwa dama ba wani abu bane gayamaka ne zanyi kasan de yarinyar nan karuwace ko...?.
Ta 'aza zeyi mamaki seta ga ko aka sema cemata yayi toni ina ruwana...
A ranta tace kaji shegen yaro amma inkasan wata bakasan wataba..tace ai ba wanna ne matsala taba ai yarinyar tana d'auke da cutar nan me kashe garkuwar jiki ...
Wani uban ashar yayi yace ni za'a cuta a had'ani dame kanjamau...wly da sake..
Murza tayi wata dariyar cin nasara tace ai shi yasa nace gwara na fad'a maka tun wurin amma ka bari se ana jibi auren sekace ka fasa ..
To kawai yace ya fice se banbami yake..
Zuciyarta fari tas ta tafi gida...
Hakan kuwa akayi ana jibi d'aurin aure Murtala yace shifa ya fasa auren inkuwa har aka d'aura auren to a ranar ze saketa...nanfa yayi d'an jinjinb'in haukanshi har seda yaga an fasa zancen ...
Maysam tayi farin cikin wanan abu dudda batasan miyasa yace ya fasa auren ba..shima Malan da fari abun ya b'ata mishi rai aman gani Maysam bata damuba yasa shima jin saukin abun
Bayan sati da faruwar hakan ta dawo daga rafi taga su Murtala ...abin mamaki seta ga suna gudunta sab'anin da daze dunga famar fa'damata....daga d'an nesa da'ita suka tsaya Murtala yace karuwa Allah ya toni asirinki ashe kina dauke da cutar HIV kikaso na aureki danki gogan ko ..to ta Allah bata kiba...
Nuna kanta tayi tace ni kuma...
Kwarai ke Maysam har gida Innarki ta iskeni ta gayamun...
Batace komi tayi ficewarta..
Ranar kwana tayi tana kuka bata san mita tsarewa Murza a rayuwa da bataso taga farin cikinta...
haka rayuwa tayi ta tafiya inda yanzu har takai 13 years aman ba me zuwa wurinta da sunan saurayinta koda kuwa yazo to baya sake dawowa inkuwa kaga har ansa ranar aurenta to fa baqone shima kuma da zarar yaji labari zakaga ya d'auke kafarshi..anyi haka yafi sau biyar..dan haka ta daina sauraron duk wanda yazo mata da sunan saurayi
duniya tayi mata zafi ga wata rama data 'karayi ga jaraba da wahalar Murza kullum qara gaba ke..duk gari ya d'auka karuwace kowa gudunta yake wurin Qawarta Ma'u kawai take samun sauki se kuma Malan..
..shima Malan tausayin yarshi yake gashi babu damar ya tashiga cikin mutane ..dan zakaga mutane nata nunashi abunka da karamin gari...
Duk cikinsu Murza ce kawai wanen abun yayiwa dadi dan karenta takeci babbabaka..mugunta duka muzguna kuwa da ana sabo dasu da yanzu Maysam ta saba
Murza ayide a hankali duniya ce...
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:11 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/17, 1:13 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

*FASMA*
*Jinjina da ban girma ga yan kungiyar mu na STAR Writer's Ass* . **ina sonku sosai*
*Queen Baby*
*Momyn Mufeedah*
*Arfat Nurdeen*
*dama sauran yan* *kungiyar Star Writes Ass gaba* *daya ..Allah ya* *qara had'a* *kanmu..Ameen*
_Ban manta da ku ba_
_Maman Shuren_ ..
_Aisha__
___ Momyn Hajia_
_Momyn Waleed_
_Dizo_
_Zarbaby_
_Sambaby_
_Sarga_
_Dala_
Ya Yusuf.._
_kuna da yawa fa dan sena gama cika page_ _d'innan ban gama_ _zano kuba sede_ _ince Allah ya qara donkon zumuncin_ ...
_Alherin Allah ya kaimaka Yayana na kaina Mujaheed_ .. __da kuma ma petite__ _sœur de valeur Balkissa_
_Wannan page d'in na kune kuyi_ _yanda kukeso dashi_
.. _ina sonku irin totaly d'in nan__
Dedicated to All my Fans
_
09__10
```Manzon Allah (SAW) ya ce ''Mafificin ayyuka shine sallah a farkon lokacinta''
Tirmizi ya rawaito```
Duk duniyar ma ta fice a ranta Yau kam da wani irin matsenecin zazzab'i da headche ta tashi ga rashin qarfin jiki sakamakon damuwa tsangwama da sukayi mata yawa da rashin cin abinci ko fita daga d'aki ta kasayi ga kuma yau Malan Musa bayanan ..
Tun safe Murza ke bambami da zage2...
Har goma na safe ta kasa fitowa ..
Murza ta hasala ta shiga d'akin a shashame ta ganta kuma se karkarwa sanyi take ....
A memakon taji tausayinta a'a sema Wata tsawa ta daka mata...
har bata san lokacin da ta zabura ta zauna ba ....
Murza tace dan ubanki wa kike son ya miki shara da wanke2 ne da kika wani shigo d'aki kika kwanta wani sabon salon munafincine kika koyo ..to maza2 tashi ki fice kafin raina ya b'ace na miki dukan tsiya anan...
Haka ta fita da kyar tayi aikin zata zauna kenan
Murza ta fito da wani uban wanki tace kada ma ki zauna zo maza ki wankesu kuma su fita tas ehe
Ko rabin wankin bata yiba ta fara kakarin amai wanda babu komi ciki se yellown ruwa .saboda ba komi a cikin ...
Wani salati da tafa hannu Murza ta shigayi tace yau ni mizan gani a gidan nan CIKIn shege kika yo Maysam dama nasan za'a rina to walahi baze yiyuba Malan yazo da sake da. baza ki haifa mana d'an shege a gidan nan ba . .
Dafe kirji tayi tace na shiga ukku ni ..walahi Inna Murza bani da ciki..
Ba ukku kika shiga ba goma de Nan ta fad'ata da duka ..da kyar ta sarara mata ..
Ranar wuni tayi tana fad'i kuma taki bata abinci bare har ta tausaya mata kan aikin gida
Maysam kam duka karfinta ya qare banda kuka babu abunda takeyi...
Bayan isha'i sega Malan yayi sallama .
Murza bata bari ma sun gaisaba ta fara fad'i mishi qarya da gaskiya wai daman taga alamun batun yauba dan tana kyautata zaton ba wannan ne na farko ba...se yau da Allah ya toni asinrinta ne ...dama itama shegiyace gashi kuma zata haifi shege...
Wani wawan mari ya zabga mata yace kada ki qara shegan tar min da d'iya...Hankali a tashe Malan yake tambayar ina Maysam d'in.....
Bata bashi ansa ba se cewa tayi akan shegiya zaka mareni.. yo ba shegiyar bace..ai ba qarya nayi ba...
Dede lokacin Maysam ta futo daga tolet ..
Batasan lokacin da tasaki butar dake hannunta ba
Har ze tanka mata amman gani Maysam yasa yayi shiru ...da sauri ya isa wurinta ya riqeta ganin tana famar fad'uwa ....nan ya kamata ya kaita bisa taburma dake shinfid'e anan tsakar gidan ...
Yace tun yaushe ne baki da lafiya yar Abba..
Dakyar ta iya fad'in jiya ne kawai ..tace dama Abba ni banida Uba Shegiyace?
Rufe mata baki yayi yace a'a Yar Abba ke ba shegiya bace ki bari zan miki bayanin komi idan mun dawo..daga asibiti..
Allah de ya baki lafiya...
Nan ya d'ago ta ya saka mata hijab ya kamata suka fita zuwa chemist na nan cikin garin..
Nanfa Murza ta samu abun fa'din
Koda suka tafi gwajin farko akace tana fama da ''paludisme''(malaria)....nan aka mata allura tareda qarin ruwa aka rurubuta musu magani suka dawo gidan..koda ya fad'ima Murza Malaria ce ..bata yarda ba tace kunde je ancire mata zaku wani zo kuce wai Malaria ..
Girgiza kai kawai yayi ya shige d'aki...
Washe garin kafin dare kaf kauyen ya d'auka Maysam tayi cikin shege kuma taje an zubar mata ..yaran garin har zowa suke suna kallanta...
Bayan sati har bata iya fita saboda cecekuce mutanen garin da kuma jifan da yaran kauyen keyi mata....
Da dare bayan sun gama cin abinci tace Dan Allah Abba ka bani labarina ..shin da gaske ni shegiyace. ?
Malam Musa Yace Yar Abba ki saurareni da kyau kiji mi zance miki..
.
A ranar wata juma'a ce lokacin ban fara kasuwanci ba kiwo ne nakeyi ..a hanyata ta dawo daga kiyo da yamma nan ne Naganki kina yawo cikin jeji kina kuka banyi zaton mutun bace dan haka na fara karanto kowace aya data zo min baki..amma abin mamaki se qara tunkaroni kike lokacin baza ki fi shekaru ukku zuwa hud'u ba kusa dani kikazo kina fadin ruwa2 ..nan na baki kika sha na tambaye ki suna kikace MAYSAM sanna na tambayyi ina Parents d'inki amma shiru baki ansaba na sake tambayarki daga ina kike nanma ba ansa .na diba dama da hagu amma banga kowa ba gashi kuma babu wani gari ko kauye dake kusa da nan. .ganin haka yasa nayi ficewata na barki nan .ashe biyoni kikayi ban ganki ba seda na kusa shigowa gari ....
Ganin haka yasa na d'auke amman adu'a ce cike a bakina ..daga nan ma gidan mahaifiyata na kaiki dan lokacin banida aure matata ta fari ta rasu wajen haihuwa...
Hannu biyu 2 ta karb'eki nan ta raineki har Allah ya d'auki ranta lokacin kina da 8years..
To tun lokacin na d'auki aniyar barin garin dan daman ita kad'e ta rage min a dangina...
Dan haka na tattaro na dawo garin nan ..ganin rikon d'iya mace se mace yasa nayi aure na auro Murza .....kuma a lokacin na fasa yawon kiwo na fara kasuwanci..
To kinji yanda abun yake...nan ya d'auko wata riga me shegen kyau da wasu takalma da warwaro na alfarma yace wannan sune kayan dana sameki dasu..
Sekuma wani zobe me kyau kamar diamon a samanshi daga ciki kuwa ,wasu harrufane'' MM'' .yace wannan kuma a wuyanki kamar sarqa na ganshi sena cire na adana miki har lokacin dazaki wayoo sena bakishi..
ta ansa ta saka a hanunta sosai zoben ya birgeta ..
Nan tayi ta kukan Abba yana lallashi tace duda hakan Abba banida wanda suka fiku a fad'in duniyar nan
Murza tace to kinde ji da kunnenki ko ..
Itade bata ce komi ba a ranta tace lallai biri yayi kama da mutum ashe ba bazan kike azabtar dani dan ba kekika haifeni ba..
Ranar kwanan kuka tayi..
Two days later Malan yayi tafiyarshi....
Maysam ta fito kiyo amma yau kwata2 hankalin ta baya jikinta tana tafiya amma tashiga duniyar tunani....tambayyoyi ne cike da kanta tana son sanin wani daliline ya rabota da iyayenta?miyasa basu neme taba?a ina suke yanzu??shin ko dagaske ni shegiyar ce?
Wasu motoci sunfi goma na gani se gudu suke ...oda sukeyi mata amma ina batama jinsu tanacan tana tunanin ta irin gudun da suke yasa d'aya daga cikin motocin yayi qoqarin kauce mata amma inaa seda ya bugeta jikake kiiiiiiiiiiii...
Tofa !Ku biyoni danji yanda zata kaya...
Nice taku har kullum ...love you all
Fasma ce
Xan fara sabon littafi mai suna zuri’ar mu xamu nayin guda 2 lokaci daya kuma yawan posting yana hannun ku ko after 30 minutes ne naga 50 comments to xan kara wani posting din
Ahmed Gumel
[8/17, 1:13 PM] A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login