Showing 66001 words to 69000 words out of 99653 words

Chapter 23 - SANADIN ACCIDENT COMPLETE BY FASMA

FASMA   

05 Jul 2024

14097

haifa na Fari wato yayan Murad wanda ko sunanshi ba'ayi ba ya mutu ......kasa tsayawa tayi ta koma bangarenta cike da tausayin kanta da kuma tausayin Madina jin irin rayuwar data saka kanta saboda kishi kawai.....

Murad nan ya zube ya shiga rera kuka jin da sa hannunta ya rasa rabin zuciyarshi ...,,,Mahmud ya rumgumeshu yana bashi baki tare da yi mishi yar nasiha..da kyar ya tsagaita ya rakashi har bangaren shi....

Ganin abun kara gaba yake Sarki yasa akayi mata allurar bacci shima iya tashin hankali ya shiga jin ita ta kashe mishi dan shi na fari ...ba dan yana kumyar mahaifanta ba da shi kade yansan irin hukunci da zeyi mata ..to mahaifinta sarkin garin Diffa ne duk da yanzu ya tsufa ya barwa danshi na fari to amman akwai alkunya a tsakanin su ...akwai mutunci ...dan haka ya daga waya ya sanar mishi komi ....
Mahaifinta dantakon arziki kawai cewa yayi a mata hukunci dede da abunda ta aikata ... ..

Sarki Mustapha ya roki alfarma kawai da za'akowa ta nan de..

Da kyar mahaifinta ya aminci ..aka kuwa kara mata wata allurar bacci aka sakata a jirgi han se Diffa....
Ayya munai miki bankwanan se wata rana ๐Ÿค—wannan shine ake kira da kaykayi koma kan mashe kiya ..tana fatan haukata Murad gashi ta haukace ita din ...to hattara de Inna Murza abi duniyar nan a sannu .. saura ke..

'Muje de zuwa..


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน. ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
Wunin ranar babu wanda yayi shi cikin jin da dadi kowa yana jimamin abunda Madina ta aikata ..bama kamar wanda tayi wa abunba....danshi Murad ciwon shi ma yake son tashi..

Har dare Murad be kirayi Maysam ba......karfe takwas na dare ya tuna da ita har ya danna kiranta se kuma ya tuna yanzu biyu na darene acan ..har ze kashe ya ji ta daga.kiran..

Da kuka tayi mishi sallama ..seda ya sauke ajiyar zuciya yace mi kuma akayi ne kiyi shiru ki fada mun


..jin murya shi wani iri yasa tayi shiru tace yaya mi ya sameka ne bakada lfy naji muryarka wani iri..

Ya ce mata banida lfy ciwona yake son farmini ...

Wani waro ido tayi tace inna lillahi wa.....garin ya ? I mean mi ya tado maka da shi ne ..?.kamar zatayi kuka take mishi tambayar...

Da kamar baze fada mata ba se kuma ya gaya mata duk abunda ya faru yau....

Banda inna lillahi wa ... Babu abunda take fadi Duk jikinta se yayi sanyi tama rasa abunda zatace mishi ..se kawai ta fashe mishi da kuka..

Shima cikin sanyi yace haba dami kike so naji ne da ciwon dake damuna koda kukan ki ne..dan har cikin ranshi yake jin kukan nata..

Shiru tayi tana ajiyar zuciya tayi matukar tausaya mishi ..nan ta dedeta nutsuwar ta shiga yi mishi nasiha tare da kallamai masu sanyaya zuciya ......
A ranshi yace kenan de yarinyar nan ta iya kwantar da hankali dan A kashi dari yaji kashi 40 na damuwar ya rage mishi ...yace yanzu fa biyu na dare ne ki kwanta kiyi bacci kinga gobe akwai school kada ki makara...

Tace to naji amma pls kaci wani abu kafin ka kwanta dan nasan wunin ranar nan da kyar ne inka ci wani abun ..pls promise me zakaci sannan kasha maganin ka

Promise kawai yace mata....

Nan ya kashe wayar ...babu laifin ya dan ji karfin jikin shi kadan..

Tana saukawa da zumar shan koda tea ne dan itama kusan wunin yunwar tayi da kawai be kirata ba ..ga mamakinta ta tarar da Mufeedah suna hirar itada Mahmud.a waya.zama tayi tare da fadin pls kice mishi dare yayi anan gobe akwai school sannan kuma ya tafi ya kular min da mijina baya jin dadi yanzu ...

Duk abunda take fadi Mahmud na jinta sarai ..a hand free Mufeedah ta saka wayar yace to masu miji naji kada ki damu zan kula miki da shi ...

Babu ko kunya tace kai aman fa na gode nima kam zan kula maka data ajiyar ta nan.. . .
Se kuma ta jajanta mishi abunda ya faru ..daga baya sukayi sallama...

Tea tasha ta haye sama dakin Murad abunta.dan har yau taki ta koma dakin wanda take ganin na kishiyarta ne..
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน. ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
A bangaren Murza kam jin asirin ta be tonu ba yasa ta saki jikin ta kamar bata san komi ba ..sede kallo daya zakayi mata kasan tana cikin damuwa ..duk gani take itama haukacewar zatayi....fita ma kam yanzu ya gagareta kullum kunshe cikin daki ..abun har mamaki ya koma bawa M.Musa sede beyi mata magana ba.

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน. ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน


Satin shi biyu ya fara shirye2 komawarshi ..sarki da fulani suka sakashi gaba suna yi mishi nasiha dan tunda abun ya faru mutawar sweetbaby ta dawo mishi sabuwa abu kadan se ya fara zazzaga fada ...

Fulani tace kuma wly in kasan hantarar y'ata zakayi to tun wuri ka medasu hostel dinsu ..dan kada fadan nan naka ya hanata karatu..

To kawai yace aman a ranshi cewa yayi da kinsan abunda yake faruwa da bakiyi wannan maganar ba...
Shi fa komin bacin ran da yake ciki komin fadan dayake yi inde kiran wayarta kade ma ya shigo to se yaji zuciyarshi ta sauko ..in har suna waya kusan mantawa ma yake dayana da damuwa bare inyana tsokanar ta ita kuma tana sauke mishi kwandon shagwaba..se yaji ya tafi ...ko tafiyar nan surprise ce ze mata kuma gashi ta matsa mishi da yaushe ze dawo ne..

Haka suka mishi fada da nasiha shide da to yake amsawa tare da ban hakuri...karfe goma jirginshi ya daga se England. โœˆ
..safe a good journey

To nima bari na daga haka nan ....


Muje zuwa fans

Love you allโค๐Ÿ˜


Fasma ce๐Ÿ–Š(Yar mutan Zinder)
[9/11, 8:51 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ๐Ÿ“š๐Ÿ“š_*
[9/13, 9:49 AM] A A Dboy: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial ๐Ÿก&extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช



*Kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu*



Dedicated to all my fans๐Ÿ˜โค




๐Ÿ…ฟ91__92





```Manzon Allah(SAW) yace '' wanda baya roko a wajen Allah to Allah yana fushi dashi.
Bukhari ne ya rawaito shi.
```






[09/08/18 ร  23:26] karfe Biyu saura na rana jirginsu ya sauka a England ..lokacin su Maysam suna school basu sauko ba. Amman ko ina tsaf2 da shi duk da kuyangi ke gyara dukuna aman banda nata da na oga Murad..
Yana shiga dakin wani sanyi kamshi ya buge hancinshi besan lokacin da da lumshe ido ba tare da yin ajiya zuciya. ..wanka ya shiga yayi ya fice masallaci ..dayake bashida yunwa dan haka can yayi zamanshi har akayi la'asr anan suka gamu da Mark suka gaisa yayi mishi sannu da zuwa har yana jaddada mishi aiki na nan jibge a office din shi. .suna ta hirar du har suka iso. kowa yayi gidanshi duk da har yau Mark beyi aure ba aman yana da gidanshi anan kuma kusa dana Murad yake . ...

Yana zuwa kawai ya hau gado ga gajiya yana ji amma yasan baze iya yin bacci ba ..dan besa ba baccin bayan la'asr ba..

Gadon kawai ya hau ya shiga chat a whatsapp....

Katsam yayi karo da number Maysam kuma gata online..a ranshi yace karatun kenan?

Salut(hello) ya aika mata

Ai kuwa se gashi ta medo mishi da salut yayana comment vas tu?ita kam bata ma lura da wata numbershi ce suke chat din dan duk numbers shi MURADINA ta rubuta akai wasu da manya haruffa wasu kuma da kanana .shiyasa bata babanta su. ..

Be amsa mata ba se cewa ma yayi karatun kenan. ..kuma ma ashe da gaske ne kina chat dinko?

Wani yawu ta hade tama rasa irin amsar daza bashi .. ..dan ta kawar da zancen tace kai yaya wly nayi missing dinka dayawa kuma ma Momy tace tabaka sakona pls yaushe zaka dawo ne..brcause i need it dan wanda nazo da su sun k'are .

Ya ganeta sarai amman seya biye mata dan yana jiranta yau seta gaya mishi tun yaushe ta fara .....

Sun dan taba hira inda take sanar mishi ai har sun tashi ne driver suke jira bezo ba...amman yanzu zasu koma gida ...sallama sukayi tana ta murna abunta jin yace mata cikin satin nan zezo...

Su Mufeedah kam se tsokanarta suke tana ramawa..

Tun nan palon taji kamshin turaren sa amman seta basar..ai kuwa tana haurawa stair hancinta ya tambbatar mata da kamshi da karfi2 cikin hanzari ta tura kofar dakin ...

Tana hangoshi da gudunta ta isa batayi wata2 ta fada kanshi dan murna tana yayana sannu da zuwa yaushe kazo ne...

Rumgume juna sukayi ..sun dan jima a haka sannan ya saketa suna kallon juna tace ina Momy na ?.yanda ta wani langwabar da kai se yaga tayi mishi kyau .

Yace tana nan she is fine ..tace tayi missing din ki .itama.

Kwalla har ta ciko idonta tace nima nayi missing dinta a lot..

Goge mata hawayen yayi yana kallon dan karamin bakinta yace me rigima yau babu ko dan kiss din ma na welcom back..

Ya tsine fuska tayi tace ee..saboda na gaji da abun...

A ranshi yace kenan de taji zafin maganar dana yi mata ranar nan..

Basarwa yayi shima ..ya dan daure fuska yace ban wayar ki ...tunda de ke bakya jin magana ....dan na san a chat din nan kika koyi wani salo2 ..

Bashi wayar tayi ba tare da ta musa ba. Se kuma tayi haramar tashi ta bar mishi wurin ..

Dawo ki zauna yace da ita..

Ya shiga duba wayar ..whatspp kawai ne take shima numbers fulani data shi seta su Mufeedah ....jikinshi yayi sanyi ganin da alama ma yaune ta bude shi kuma Momy ce tasakata dan tayi mata baya nin sakon maganin data bada akawo ma ..se tana turo mata photon duk magani tare da yanda zatayi anfani da shi. Kamar su Misk, bagaruwa,ganyen magariya dade sauran su se kuma advise din ta zanki shan fruit a kai2... Se kuma turarikana wuta dana shafawa kamar su humra,kullacca etc..


Ita kam se turo baki gaba take tunda har be yarda da ita bane harda yake tamata bincike a waya..koma yana gane mata sirrinta na ita da Momy

Murmushi yayi ganin fa tayi fushi ...bakin ya dan buga kadan yana fadin ke bakinsan wata dununuwa kike komawa inkayi fushi ne...

Kamar wasa kawai yaga hawaye shar2 a idonta .....

Hankali tashe yake tambayar mi akayi mata daga dan bugan nan se kuka...

Maysam tace dama yaya baka yarda dani bane ...

Waro ido yayi yace in jiwa ?kinjiki da wani zance . .ke kam bakya rabuwa da rigima..

Maysam tace ba gashi nan ba har da wani min bincike a waya..

Murad ya sauke ajiyar zuciya tare da matsowa ya rumgumeta tsam yace ba haka bane yar renota ki fahimce ni ...

Yar reno kuma ta maimaita a zuciyarta ..

Yacigaba da fadin social media yanzu abun tsoro ne ..na fiso kimeda hankalinki ga karatun ki......''ce n'est pas ce que tu crois parce que je te fais confiance a 100%....

Se lokacin ta sauke ajiyar zuciya itama tace ''merci yayana...''se kuma tace naji kace yar renonka ,..mi kake nufi da haka ido cikin ido take maganar ....

Kauda fuskar shi yayi duk ya wani daburce .......dan ya kawar da zance yace idan zaki mun magana kada ki kara saka idonki cikin nawa...

Cike da mamaki tace 'pourquoi?still ta kafeshi da ido..

Juyowa yayi da niyyar bata amsa hallau sukayi ido hudu..

Fasa maganar yyi sema tashi da yayi ya shiga tolet jin ana kiran sallar magarib ...amma a ranshi fadi yake anya yarinyar nan ba wani abu take sakawa idonta ba...tun tana ya karamarta inde har mukayi ido biyu da ita to bana iya mata muso akan abunda take so.....se in wani dirirce gaba daya ...mtsss ya ja tsaki shi kade .a bayin ...

Yana fitowa fuuu ya fice ba tare da yakalli inda take ma..

Maysam alwalar ta shiga ta doro amma tunani ne fal ranta ..kawai mutum daga tambayya se ya hau fushi ..to Allah de ya kyauta .
Niko nace ameen

Sanin baya dawowa se bayan isha'i yasa tashiga kitchen ta hada mishi d'an specialitรฉ girki da jus..
Komi cikin sanyi jiki take yinshi ganin yayi fushi da ita .....bayan ta gama tayi sallah tazo dakin su Mufeedah ...exercice sukayi tayi har goma saura tukon sukayi sallama ..Mahmud ya kira Mufeedah suka fara zuba soyyayar su..

Itama Mariam babu laifi ta dan fara kula Mark dan ko kwawarshi ta isa a fara biye mishi. Ba laifi ta dan fara sonshi ..sede bataso ta zurfafa tunda tasan an riga da anyi mata miji a gida.....

Murad kam har lokacin be dawo gida ba..iya tashin hankali Maysam ta shiga..wanka tayi tayi shirin bacci ta bade jikinta da humra..tana jiranshi anan palo har baccin yayi awon gaba da ita.....

Se sha daya ya shigo .gidan.ganinta nan a takure bisa kujera se kuma ta bashi tausayi..dan yasan jiranshi ne take ...daukanta yayi da niyyar kaita cikin room kamshin humrar ya bigi hancin shi harda wani lumshe ido.... firgit ta farka ai kuwa tana sauke idonta akanshi ta saki mishi kuka ...

Shima se zuciyar shi ta tsinke ..zama yayi tare dayi mata masauki a cinyarshi yana goge mata hawayen yace ya isa haka to mima nayi miki da kin ganni kawai ki saki mun kuka....

Cikin kuka tace to ba kai bane kayi fushi dani banyi maka komi ba...harda wani tafiya kayi dare

Dan murmushin gefen baki yayi yace to ai ke ce se ki wani kafeni da ido ni kuma idon mu na sarkewa sena loosing control dina .ki dena bana so ''parfois j'ai l'impression que tes yeux me dominent mรชme''..don suna sani yin abun da banyi niyya ba
Se da yayi maganar ya farga ..amma seya mazge

Itakam kankameshi tayi tace ba zan sake ba pls kada ka kara yin fushi dani .tana yi tana wani shafa mishi fuska ..ta kuma ji dadin kalam manshi

Shima rumgumeta yayi nan ya shiga kissing dinta yau kam har da romance yayi mata sede bata hanashi ba kuma bata meda martani ba saboda tsaro๐Ÿ˜Ž...dan kada kuma yayi fushi da ita ma...da taga da gaske birkice mata zeyi ne sannan ta raba jikinta danashi lokacin idonshi har sunyi dan ja..

Tace nasan bakaci komi ba pls na kawo maka kaci ko,.?
Yanda tayi maganar seya birgeshi gyada mata kai yayi dan babu bakin magana ......

Sosai yaji dadin abinci seda ya gama cika cikinshi ta hada mishi ruwan wanka yayi ..sukabi lafiyar gado.....
Har bacci ya fara daukansu kamar wanda aka tsikara cuwat ta tashi ta zauna tace wai yaya har yanzu matarka bazata dawo ba ne...
Cikin magagin bacci yace mizaki mata in tazo din ..wai ma mi yakawo zancen nan cikin dare ...

Turo dan baki tayi tace kowa da abunda ya dameshi a rayuwa nikam itace damuwa na..kuma kawai ina son ganinta ne inga nida ita wayafi wani kyau.sanna da alama bawata katuwa bace tunda naga kayan dake wardrop kamar ma zamuzo kai daya...kaga kuwa wly tanayi mun in kareraya yarinya .....ehe

Yace kai yama za'ayi ahadata dake ai kin kere mata akyau bazama ta kama kafarki. Yanzu de barni nayi bacci a gajiye nake..

Ai kam kamar ya zugata tace ba wani nan kawai dan na kyalleka kayi bacci ne kace haka..bayan ranar nan kace ta nada zallar kyau Harda shure2 tana ita bata yarda ba...

Dayaga dagaske bazata barshiba tashi zaunan yayi yace to kiss me sena Gaya miki gaskiyan magana..

Yatsina fuska tayi tace a'a barshi kawai bana so ni na gaji da abunan ..

Murmushi yayi a ranshi yace na jawa kaina da yanzu ina more abuna ..rumgumeta yayi yace to ''dort bien '' yayi kissing forhead dinta..
Meda kanta tayi bisa kirjinshi tace'' passe une excellente nuit yaya..'''

Yace da ita shima '' pareil aussi et ne m'oublis pas dans tes rรชves''..

Murmushi kawai tayi ta kara makalkale shi . har bacci me dadi yayi awon gaba da su.. ..

Asuba ta gari



๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน. ๐ŸŒน๐ŸŒน

Wai fans ina labarin inna Murza ne?..yanzu kam tayi dan sanyi amma fa mumunan kudiri ta na nan makale a zuciyarta tana tunani sake taku ne tunda taga abun se kome musu yake. ..gashi kuma bata da kudin dazata na bawa bokayen ..

Madina kam abun ba sauki kullum haukanta kara gaba yake . . kai daga karshe ma a daki aka kulleta tare da daureta da sasari dan inta b'alle ..masu kamota ma se sunji jiki...
Mahaifinta ayanda ya fahimci abun kome mata ne yayi. Dan haka ya saka ana saukar qur'ani tare dayi muta Rukya.......

Mahaifiyar tama kullum cikin yi mata addu'a take dan hannuka baya rubewa ka cireshi ka yar ..kuma ma in tayi mata baki ko ta tsinemata itade zatayi walaha dan uwa bata iya supporting din taga danta yana surffing..shiyasa ta dage da rokon Allah tare da nema mata gafara da kuma shiriya... ..
Wannan kenan


Kuyi hakuri fans na rashin jina kwana biyu bana jin dadi ne ... I need your addu'a..

Wanda suka kirani ta waya da wanda suka mun text na gode muku Allah ya bar kauna da zumunci..merci bienโค๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜


Love yau allโค๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜



Fasma ce ๐Ÿ–Šyar mutan Zinder.
[9/13, 9:49 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ๐Ÿ“š๐Ÿ“š_*
[9/13, 9:54 AM] A A Dboy: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial ๐Ÿก&extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช


*Na gode da addu'ar ku gareni Allah ya bar kauna da zumunci ina alfahari daku fans ...love you all irin totaly din nan โคโคโค๐Ÿ˜..thanks all*


Dedicated to all my fans๐Ÿ˜โค




๐Ÿ…ฟ93__94




```Manzon Allah (SAW) yace''wanda duk ze rantse ,to ya rantse da Allah ko yayi shiru''
Bukhari ya rawaito shi```

[11/08/18 ร  22:30]A kwana a tashi ba wuya su Maysam har sunyi wata shida a England ..cikin watanin nan kuwa abubuwa da dama sun faru ciki harda saka ranar auren Mahmud da Mufeedah ,se kuma na Mariam da dan uwanta Ma'aruf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login